Showing 72001 words to 75000 words out of 190762 words

Chapter 25 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

4012

irin yadda ahalinsa suke daukan tsufa ya riga ya kai shi bangon nan ya sa wasu lokutan a gabansa suke yin aikin aikata goshin, sai daga baya a nemi ganewa ko yana fahimtar abinda ake yi? shima sai ya nuna baya gane komai, bale idan akace kasa ta birni idannuwansame zai faru? , in Hajia ina ta samu kula a asibiti ita fa kurma? ya hayu ya kayum, dole a gaggauta daura auren nan ko zai samu nutsuwa a zuciyarsa.....idan yaso in yana so bayan wata daya a daura nashi da Mufeeda wannan su ta gano.

Da kyar ya iya samun barci ya dan fige shi kiraye kirayen sallah suka tashe shi

A masallaci suka hadu da AL'WALID din, suka yi sahu tare aka gama sallar asubahi suka zauna a masallacin har haske ya fara fitowa

A lokacin da ya mika masa hannu dan ya tashe shi dan su dan zagaya a kafa kamar yadda yake yi masa , baba Hamza ya sake duban idannuwansa da kyau ya ga shima da alamun bukatar hutu a tare da shi , sannan ya amshi hannun nasa ya mike suka fito suka shiga takawa


A hankali AL'WALID ya sake dubansa, a tausashe ya ce" Me ya hanna ka barci ne Elhaji?"

Elhaji Hamza ya yi shiru na dan lokaci, sai kuma ya ce" Tunanin mutuwa ne ya hanna Ni Elhaji karami"

AL'WALID ya dakata ya zuba masa ido kamar yadda shima shi din yake kallo, sai kuma ya dauke kansa a hankali ya ce" In sha Allah sai ka yi dari biyu zaka tafi"

ido Elhaji Hamza ya zarro kafin ya ce" A ina? haba dai, yanzu haka ai na kai mizanin da tafe ake da Ni dan na zama dole ne, ina ga na kai dari biyu? a'a barni in tafi tun ana marmarina"

AL'WALID ya masa shiru, suka ci gaba da takawar nan

Cen Elhaji Hamza ya fitar da dan huci a tausashe ya ce" Maganar aurenka"

AL'WALID ya dube shi, a ransa yana ayana' au bai dai bar maganar ba, Ni yarinyar ma da ta fito ban gama gane kamaninta ba ta juya tana harare harare , gidan nan dai na kakan kurma ya'yan nasa kamar du basa jin magana

A hankali ya ce" Uhum, auren dai zaka min?"

"Eh, kuma nan da kwana biyu za'a daura in sha Allah " Baba Hamza ya fada ya sake daure fuska tam ya riko damtsen hannun AL'WALID yana dubansa cikin ido a hankali ya ce" AL'WALID, koda na mutu a yau, daga yanzu zuwa an jima, ka tabbatar da ka amshi auren yarinyar nan a wajen mahaifinta, cikin girmamawa da darajantawa, ka tabbatar da ka bata kulawar da ya dace, ka sani matar aure na baka kuma auren nake so ka yi da ita, so nake yi ka kula da ita,, ka kiyaye hakokinta, in sha Allah zata yi maka biyayya......, AL'WALID ka ji bukatana? ka cika min burina a kanka, ina mai yi alkawarin in sha Allah kaima y'ayanka zasu yi maka biyayya, na san baka so, kuma na san abin mamaki yake baka ace baban mutun kamarka an yi irin haka a rayuwarka, ba zan hannaka auren Mufeeda ba, ama ka tsaya ka yi dogon nazari bayan ka auri yarinyar nan, in ya kama ka auro Mufeeda ba damuwa.....ama ka sani du takamar namiji mace ne shi, du nagartar namiji idan ya hadu da macen da ba ta kirki ba AL'WALID ya lalace, du kyawawan halayarsa sai sun zama tarihi, kai harta ibadarsa sai ta samu rauni........ka kiyaye" Daga haka baba yayi shiru yana kallonsa kamar yadda yake kallon baban shima

Idannuwansa ya lumshe ya saka dayan hannunsa ya talabe baban kamar ya samu kanninsa

A nutse ya nufi bangarensa da baban, ba bangaren baban ba

Sunna shiga ya wuce dakinsa na barci da shi , da takalmansa a ฦ™afarsa dan bai cire masa ba, shine ma ya cire nasa

A nutse ya karasa da shi wajen gadonsa ya zaunar da shi, sannan ya duka gabansa ya rike hannayensa da du abin yaba ya tafi da karfi da naman jiki

A sanyaye sosai ya ce" Kwana biyu ....gobe jibi? ko kwana biyu ta hausawa?"

Baba ya ce" Jibi in sha Allah "

AL'WALID ya gyada kansa yana dubansa a hankali ya ce" Allah ya nuna mana, dan Allah kwonta ka huta, jikinka babu karfi kuma yanayin ka ya nuna kana da bukatar hutu"

Ajiyar zuciya baba ya ringa saukewa , haka kuma fuskarsa ta washe da fara'a, a hankali ya ce" To ka bani waya in sanar da kakan kurmar sai in kwonta"

Dan jim AL'WALID yayi, sannan ya mike ya karasa ya dauko wayarsa wace ke ajiye cen saman sif, domin a kashe ma take bai cika aiki da ita ba

kunnata ya yi ya zauna daf da baban ya shiga lalubar numbar Elhaji ya'u wanda yayi sevng da kakan kurma, saboda wasu lokutan idan yayi tafiya in ya nemi baba Hamza bai samu ba yana kiran kakan kurma yake bashi shi

Aika kiran yayi, lokacin da Aba ke kwonce saman kujera Mama na yi masa aune aunen hawan jinni da sauransu, saboda tunda asubahi juwa ke yawo da shi, ko yara da suka zo karatu sai a bangarensu suka yi, du yadda take fushi sai ta gaza zama ta kwaso kayan aikinta ta je bangaren nasa ta shiga bashi kula a matsayinta na likita

Ringin din wayar ta saka shi mirginawa da karfi yana fadin" Innalilahi, an yi mutuwa, in dai kika ga kira da duku dukun nan wani ya mutu, innalilahi"

Da sauri ta tare shi saboda kusan dimowa da ya yi daga kasa a hankali ta ce" Ka kula mana Elhaji zaka ji rauni fa"

Aba ya ce" Gimbiya bani wayata, na tabbata wani ya rasu, wayo Allahna oioooooo mutuwa sai ta dauke mu daya bayan daya, gimbiya bani"

Mama ta juya ta dauko masa wayar a dakinsa na barci ta kawo masa tana fadin" Baban kurma aka rubuta......"

Kamar ta kyala masa mari, gaba daya sai jikinsa ya dauki rawa, murya na rawa ya ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une wani abu ya samu tsoho, walahi wani abu ya samu tsoho....., na shiga uku gimbiya a duniya shi kadai yake tausayina bayan ke, in wani abin ya same shi ina zan sa kaina, ba zan iya dauka ba , gimbiya kirawo direba ya kai Ni gidan"

Mama ta yi sororo tana kallonsa, in ka ga Elhaji a cikin irin wannan yannayin abinda ke damunsa ba karami bane walahi, kuma tabas lamarin Elhaji Hamza na taba cen cikin zuciyarsa......ko dan zumuncinsu mai karfi ne? sai ta ji tausayinsa na sake rufe zuciyarta,

Bata ce masa komai ba ta amshi wayar ta daga a tausashe ta furta" Asalamu alaikum wa rahamatulah "

Daga dayan bangaren AL'WALID ya amsa salamar a kamilance , sannan ya furta" Barka da asuba, fatan kun tashi lafiya"

Mama, itama jin Muryar ba ta Elhaji bace sai ta kasa mikawa Aba wanda ya tsareta da ido kamar zai summa, a tausashe ta ce" Alhamdulilah, ya su baba? ina fata lafiya yake"

AL'WALID ya furta" Yana lafiya alhamdulilah, dama shine yace a yi masa kiran Elhajin zai yi masa wata magana "

Mama ta dubi Aba tana furta" Ok gayanan"

kasa kasa kuma ta ce" Dan Allah Elhaji ka kwontar da hankalinka yana lafiya shine yace a yi kiran ka "

Baba kuwa sama sama ya ce" Wace lafiyar? in har yana lafiya ganninsa zaki yi ya tardoni ko me yake son gaya min ya fada sannan ya tsaya in fadi ta cikina in ta masa a daidaita in bata masa ba ya min sumul yayi tafiyarsa tunda ba tsorona yake ji ba, gimbiya tashi ki kaini gidan tsoro nake yi aje bashi da lafiya ne"

Kasantuwar a handsfree AL'WALID ya saka wayar ya zamo dukkan magangannun sunna ji shi da baba Hamza, Baban ya yi yar dariyar da ya saka AL'WALID sakin murmushi yana kallon yannayinsa yana karra girmama kusancinsa da Bawan Allahn nan da shakuwarsu......

Baba Hamza ya ce" Kai meye wai, da mutuwar na yi ai kawai ce maka za'a yi babanka ya tafi, Ni magana ce zamu yi ka wani saka min y'a a gaba da fitina"

Ajiyar zuciya Aba ya sauke yana amsar wayar ya wani maze ya ce" Kai tsoho wai kai ba zai daina min takurar sasafe ba? ka san dai ai ina barcin safe mai kudi ne Ni Ko?"

Baba Hamza yayi dariya bayananiya ya ce" Kudinkan banza Kudinkan wofi, Ni ina ruwana da barcin safenka Allah na tuba, meye muryarka ke kurya jikin ne? an salameka daga asibitin ne?"

Da sauri ya kalli Mama dake gefe tana hada magani kasa kasa ya ce " A'a ai gimbiya tace ta raina aikinsu sai kawai muka kwana a gida , ganima da sauki sosai ai zan fito shago in an jima"

Baba Hamza ya gyara zama yana fadin" Baka da gaskiya daga jin muryarka , kuma kar ka saki in ganka a shagon nan yau ka zauna ka sha magani kakan kurma!"

"BA kurma bace bebe ce, kuma sai an fito" Aba ya fada yana zarro ido

Baba ya tabe baki sannan ya sako yannayin serius a firarsa ya ce" Dangane da maganar auren nan ne"

Aba ya zauna da kyau yana kwada tagumi saboda Allah yana ganni maganar auren nan ta shiga cen cikin zuciyarsa ta zauna, ya ki jinnin a dauko maganar ma dan kar a fasa, bai san dalili ba yana so a yi auren har cikin zuciyarsa

Baba Hamza ya ce"
07/12/2024, 14:56 - samiraharounayacouba: ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ
*FARKON GANIN IDONA*
๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you ๐Ÿ˜*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ฦŠAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAฦ˜IN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na ashirin da ษ—aya (21)*


*TALLAH, TALLAH, TALLAH*


https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ
๐Ÿ‘‰0912 262 1080





LABARI



Baba Hamza ya ci gaba da fadin" Yaya za'a yi yarinyata ta gane cewar na matsu a daura auren nan?, idan da hali nan da kwana biyu?"

Baba ya mike tsaye, hakan ya sa Mama juyowa ta kalle shi domin yanzu ta gama yi masa maganar irin mugun motsin nan a yannayin da yake ciki, bashi da lafiya, hawan jinninsa bai sauka ba, du yadda yake yin karfin hali kuwa ita bai isa ya boye mata asalin abinda yake ciki ba

A hankali baba Hamza ya ce" Kana jina kuwa?"

Aba ya ce" Ina jinka Elhaji, wai kana nufin gobe jibi? ko nan da wasu watanni?"

Elhaji Hamza ya ce" Gobe jibi nake nufi"

Aba ya dafe gaban goshi ya sake kallon Mama ya ga magungunan take haษ—awa, sai kawai yayi ciki ya shige dakinsa ya rufo ya ce" An gama, in dai kun shirya shikenan, meye na wani y'arka ta yarda? ai ta yarda bata yarda ba sai na yi, y'ayana ne fa kuma na isa da abina!"

Baba Hamza ya ce" Ka ga bana son fitina, ko menene ka bi shi a hankali, bana son abinda za'a zo a tada fitina ka ji dai na fada maka"

Aba ya yi murmushi yana fadin" Ka fa san namiji nake na isa da gidana, kawai an gama ina zuwa , da yama mu hadu mu gama magana in sha Allah"

Daga nan bai wani tsaya jin ta bakin baba ba ya kashe kiran yana washe baki da murmushi

Shima baban murmushin yayi ya mikawa AL'WALID wayarsa yana fadin" Yaron nan akoy mutunci, Allah dai ya masa albarka"

AL'WALID kuwa amsa kawai ya yi, zuciyarsa cike da tunanin irin yadda babanta ke gaggawa kamar yadda baba Hamza yake yi, gaba daya bai gane lamarin nan ba, ita fa kanta yarinyar ba zai iya cewa ga kamaninta ba, kanwar nan Tata kawai ya gane.......wai a haka za'a daura masa auren da ita? gashi auren nan ga dukkan alamu sai an saka masa abubuwan tsauri masu yawa a kansa, tun yanzu ana fadin aure aka daura masa auren ake so yayi? da waye zai yi auren? girma ai girma ne , ba kuma zai fadi a gaban kowa ba

Wuta ya kashewa baba ya sake jaddada masa hutawa yake so ya yi sannan ya fita ya tafi dakin motsa jikinsa



A gidan Aba


Bayan ya kashe kiran da suka gama da Elhaji Hamza sai ya fada bayi ya yi wanka sannan ya fito ya saka jalabiyarsa bayan ya shirya ya fito da ky din motarsa

Gannin mama a falon a zaune har yanzu ya saka shi sake daure fuska sosai sannan ya zo ya zauna inda ta haษ—a magungunan da ruwa ya dauka ba tare ya yi mata gardamar sha ba ya sha abinsa ya bude madarar da ta ajiye masa ya shanye itama sannan ya dubeta kamar yadda take kallonsa ya ce" Zan je nan in dawo"

Mama ta sake dubansa da kyau, a tausashe ta ce" Ama ka ga ai na auna lafiyarka baka da lafiya, kana da bukatar hutawa koda na yau kadai ne, in ba zaka yarda da maganata ba ka wuce mu je asibiti gado zasu baka Elhaji "

Aba ya sake dubanta, kamar ta sauko fa, saboda jiya zuwa yau yadda take yi masa magana daban da yanzu, kamar ta sauko kamar ta koma gimbiyarsa ta da, sai dai ba zai yi sake ba aje so take yi ta ga ya saku ta sake juye masa

Kai ya girgiza ya ce" likitocin nan naku me suka iya banda son kudi? rike mutun din da suke yi ai ba dan ciwon ya kai a rike shin bane, sunna son yan kudadensu ne kawai suke yin munafurcin nan, ama ai kin ga yanzu da sauki kuma fitar nan mai mahinmanci ce sosai da sosai in ban yita ba akoy matsala"

Mama ta sake fuskantarsa a tausashe ta ce" Elhaji, dan Allah ina so mu yi magana"

Gabansa sai da ya fadi , ya dubeta ya ce" Ina jin ki"

Mama ta sake sada kai, sosai da sosai da yanayin girmamawa ta ce" Elhaji, dangane da maganar Karima ne, dan Allah ka yi hakuri, ka yi hakuri Elhaji, ama dan Allah kar ka aura mata yaron da ya koya mata bijirewa iyayenta, idan ka aura mata shi ba zai riketa da mutunci ba, kana ganninsa ka ga irin kangararun yaran nan da basu dauki kan kowa da gashi ba, yanzu irin wannan ne abin a hada zuri'a da shi? dan Allah ka yi hakuri ka bata dan lokaci ta fitar da wani mijin, ko kai ka sake samo mata wani mijin mai mutunci da zai riketa da amana, ama dan Allah in na bata maka ka yafe min "

Har ga Allah sai da ya ji har cikin zuciyarsa ya karaya da lamarin gimbiya, ya Salam, zai iya rantsewa ko yanzu mutuwa ta dauke shi ya bar baya a hannu mai kyau, bale Allah ya taimake shi kaf iyayen ya'yansa uwar KARIMA ce kawai ke kawo masa rashin mutunci da kutse a cikin gidansa, bayanta kaf dinsu sunna girmama gimbiya sunna kuma Binta da fatan alkhairi na irin rikon da take yiwa ฦดaฦดansu da zuciya daya, shi shaida ne, domin malan Lubna har kyauta take yiwa gimbiya na mayafai ne da sauransu domin a naija ta yi aure tana kasuwancinta , du in zata zo direct take zuwa gidan a zauna a sha fira da sha tara ta arziki, kuma idan zata siyawa Lubna pant sai ta siyawa sauran, ama uwar KARIMA? uwar KARIMA? ya fada hannun y'ar daba da ya aureta

A hankali shima ya ce" Gimbiya, yanzu yarinyar da ta wulakantaki, ta bude kofa ta yi guduwarta cikin dare, ta je ta hadu da uwarta har suke son binki da shari ce zaki ce wai a kyaleta? da ki barta gimbiya in aura mata shi din, tunda shi ta zaba kina gani fa, shi tace tana so"

Mama ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Yaya zan yi? abinda ta yi khadija na iya aikata min in ta samu muguwar kawa ko mugun mai bata shawara, shi yasa nake yi mata uzuri, kuma yaron nan walahi Elhaji sam bai kwonta min a rai ba, tsoro nake ji ace an aura mata shi ya wulakantata"

Aba ya gyada kai ya ce" Zan daga mata kafa na duka, ama ba yana nufin zan barta nan da nan ta kuma fita ba, kuma yaron nan ki yi hakuri gimbiya shi ta nuna tana so, idan ba'a bata shi ba ko waye aka bata ba zata zauna ba, kin ga yarinyar nan? wannan salihancin da ya sameta ba komai bane wuya ta sha, da zarar ta samu sauki zata ci gaba da abinda take yi, kuma mahaifiyarta ta riga ta hure mata kunne, ki yi hakuri daga ita har mahaifiyarta in ba dandanawa suka yi suka ji wuya ba , ba zasu dawo hayacinsu ba, bana yi mata mugun fata , ama in har ba shi ya koya mata hankali ba ,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login