Showing 27001 words to 30000 words out of 190762 words

Chapter 10 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

4011

sosai, da abin ciwo shi yasa take kwonce a gadon nan shekara da shekaru ibada kawai ke tashinta

Da murmushi, murya a cen ciki Hajia ta ce" Mufeeda, yaya iyayenki? ina fata kunna lafiya gaba daya"

Mufeeda ta yi murmushi ta furta" Fine Hajia, dazu na sauka, shine nace sai na ganki kafin in je gida, dan a gidan baba zamu sauka harda su huwaila "

Hajia ta gyada kai ta furta" Masha Allah, Allah ya muku albarka, Allah ya tsare"

Mufeeda ta amsa da amen sannan ta mike tana yiwa Hajiar salama da murmushi ta dan shafa kan kurma, wace ta ki dagowa har sai da ta tafi sannan ta dago ta bi kofar da kallo sannan ta kalli Hajia wace ke kallonta da mamakin lamarin kurma

Wato ba lamarin kurma kadai ba, harda na Elhaji Hamza lamarin na bata mamaki ainun, ta rasa gane dalilinsa na daukan wannan matakin da ta tabata sai hankali ya tashi a kansa, shin me yake faruwa ne da ita kwakwaluwarta ta kasa haska mata? yarinyar nan Mufeeda idan tsatson ne ta fido daga na kirki, in maganar dukiyar ce itama ta gadota, ama fir ya ki maganar aurenta da Al Walid , karshe ma ya nuna in dai auren za'a yi ba damuwa ama yanada wace zai bashi kafin ita? yanzu al Walid ne zai yiwa auren hadi? yaron da auren soyayar ma yaya ya kare da shi bale na hadi? marigayiya Allah ya karra mata haske a kabarinta kowa ya san ya so ta, ama ita dinma yaya suka rayu wai bale auren hadi? rigima dai yake son janyowa kansa da shekarunsa bai gaji da yin shara'a ba, bayan wannan fitinar da Mufeeda zata iya yi a kan maganar nan ai sai mai tsayin rai zai iya gani, ita dai tana tsoro, tana matukar tsoron lamarin nan, ama kuma shi Elhajin da ake magana a kansa din ne mai taurin kai, du wani hali na Al Walid nasa ne, mutun ya tsufa ama ba'a shawara da shi? sai shawarar mutun daya yake saukowa wato Elhaji kowa banza, to Elhaji kowa banza ai ya gama tada gari, Allah dai ya kyauta Allah ya sanyaya

Bata san me yasa Bebe bata son lamarin Mufeeda ba, Mufeeda kuwa na sonta, koda yake halayan d'an yau sai Allah, su in dai ba iyayensu ba sam basa yiwa kowa karra Allah ya kyauta


Mufeeda da ta fito sai ta tsaya ta bi acn falon da kallo, gannin ac hudu gaba daya a kune ta nufi wajen commande ta dauka ta kashe biyu hankali kwonce sannan ta juya da abin kunnawar tana dan yatsina baki ta kama hanyar fita

Hajia A'isha da ta summa a zaune da mamakin iskancin yarinyar nan ta kalli y'arta Salima ta ce " Ke salima tashi ki amso min abin kunnawar nan tun kafin raina ya ɓaci"

Salima ta mike tana fadin " aunty Mufeeda, mama tace ki kawo abin kunnawar nan"

Mufeeda ta ja ta tsaya ta juyo tana kallonta har ta karaso, Sannin cewa yarinyar ma ba baya ba wajen iya fitsara sai kawai ta dan juyar da kanta ta ce" Ki ce nace ya dace a rage shan wuta dan a tausayawa Mine."

Daga nan ta fice ta nufi inda motocinsu ke parker ta shiga ta zauna tana wurgar da abin kunnawar ta gyada kai ta ce" Zaku ci ubanku daya bayan daya, yan wulakancin banza da wofi, ba'a saba da abu ba an samu rana tsaka ana son a nuna fin karfi, aikin banza da wofi!"

Komawa salima ta yi ta sanarwa mamanta abinda Mufeeda ta ce

Hajia ta gyada kai tana kallonta ta ce" Shine kika ki dauketa da mari?"

Salima ta zarro ido kasa kasa ta ce" Kin sani sarai gobe zai zo kasar nan fa, kin kuma sani sarai koda bai aureta ba ta riga ta shiga rigarsa dole zata ci alfarmarsa, ki barta kawai zata hadu da daidai ita a gidan nan ama bana so Aba yayi fushi da mu saboda wannan"

Hajia A'isha ta gyada kai tana dauke kanta ranta bace ta ce" Shi yasa du kyan gidan nan yake fita daga raina, idan na tuna a rabe muke sai in ji komai ya fita daga raina, ama ba komai lokaci nake jira kowa zai amshi abinda ya shuka a hannayensa!"

Daga wannan ta tashi ta yi tafiyarta bangarenta, dama zaman nan ba wai kulun ake yinsa ba, sun fi yinsa ne idan Al Walid na gari ko zai zo gari, Abin takaici Elhaji baba yace idan ya zo wannan karron zai jima a gari ba tare da yayi tafiya ba, dama ba wai a cen inda yake zuwan rayuwarsa ta fi yawa ba, a'a , ya fi zama a gida fiye da tafiye tafiye, sai dai kuma yana da tashi cirat, dan kana iya wuni da shi washe gari ace maka yayi tafiya, hakan na nufin Dole zasu ringa zuwa idannuwansu na gannin abin bacin rai, abin bacin ran daga wajen matar da ko aurenta bai yi ba, ko me zasu kirayi wannan soyayar? ita dai ba zaman dadiro suke yi ba, ba kuma na auren ba, ama kuma takan zo ta sha kwanakin ta idan yana gari, ko abinda take so take karewa ko mecece wannan hikima Tata ? aikin banza kawai.




A gidan baba

Sai da sawaye suka dauke Mama ta nufi dakin Karima bayan ta gama yin salama da yan uwanta ta bude ta shige ta rufe sannan ta kunna fitila

Tunda ta kunna fitila Karima da barci ya gaza daukanta ta ringa barin jiki, ama ta kasa tashi saboda tsabar firgita, jira kawai take yi ta ji duka ta ko'ina ko ta ji Muryar babansu sama sama

kujerar dake gaban dan madaidaicin table na karatu ta janyo ta zauna tana fuskantarta da kyau a tausashe ta ce" Tashi ki zauna mu yi magana"

"shikenan innalilahi Shikenan asirina ya tonu, innalilahi wa inna ilaihi raj'une" Karima ta shiga fadi tana mirginowa daga saman gadon ta sauko kasa gaban Mama lokaci daya kuka na bale mata, murya na yi mata rawa ta ce" Mama ,babu abinda ya hadani da shi, mama taimaka min yayi ya rage min hany..........''""



"Au, raina min wayo zaki yi? nace wayo zaki raina min?" Mama ta fada tana katseta a tausashe, hakan ya sa Karima langwabar da kanta hawaye wani na korar wani ta sada kai

Mama ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" Idan kika yi fashin makaranta shi kike tardawa? ki kula du abinda zaki fada ki tabatar da gaskiyar ki kennan, domin du binciken da ya dace ace na yi na gama yi"

KARIMA na gyada kai da sauri ta shiga magana kamar haka" A'a, a'a walahi ban taba tarda shi ba, a nan bayan makarantar mu muke zama mu yi zance, daga nan sai in biyo su gida mu dawo, kuma sau hudu ne duduudu aka yi daga nan ba'a kuma ba kuma ba za'a kuma ba mama dan Allah dan annabi ki rufa min asiri mama kar ki fadawa baba ya kashe Ni" Ta idasa tana sake barkewa da kuka

Mama ta bata dama har ta ci kukanta ta gama a tausashe ta ce" Mahaifiyar ki ta san da maganarsa ne?"

A zabure ta dago tana kallon Maman, sai dai ta riga ta san ba damar yin wata karyar, ta fadi gaskiya shi zai kwaceta

A hankali ta gyada kanta tana sake sune kan nata

Mama ta sauke. ajiyar zuciya a tausashe ta ce" to me yasa idan ta zo kuke tsayuwa a kofar gida ne bayan rumfa ke da ita da shi? me yasa ba zata shigo ta ganki ba? me yasa kike son nuna masa dabi'ar haduwa da ke a bakin titi ne?"

KARIMA ta dago a hankali ta ce" Mama dan Allah ki yi hakuri, walahi ba zan kuma ba"

Mama ta fuskance ta da kyau ta ce" Karima, nutsu mana, ban fa zo dakinki dan mu kasa fahimtar junna ba, ba kuma zan so raina ya dugunzuma ta yadda za'a ji sirrin mu ba"

A hankali Karima ta daina kukan tana gyada kai

Mama ta ce" Kin ga Ni mamanki ce, amanarki a hannuna take, shin idan kina da manemin da kike so in kin fada min ba sai in bi hanyar da ta dace ba dan koda Allah yayi shine mijinki ya ganki da daraja ya kuma rike ki da daraja? KARIMA saurayinki ne? sonsa kike yi ne?"

Gaba daya Karima sai ta rasa amsar badawa , gannin haka mama ta ci gaba da fadin" Kin san du abinda yake kilace, to kuwa ya fi daraja tabassssss, Karima idan kika koya masa ku hadu a titi ku yi zance bashi da wani shamaki ko tsoron ya wulakanta ki, ke in Allah ya tsiratar da ke daga wannan tashin hankalin ya sa ya aureki walahi a cikin gidanki na aure zaki ga wulakanci kala kala, dan kuwa ba zai taba baki yarda ba ko kankani, shin haka kike so ki rayu a gidanki?"

KARIMA ta girgiza kai da sauri,

Mama ta ce" Zan sake tambayarki, saurayinki ne? kina sonsa? idan har haka ne zan kai maganar gaban Babanku dan a neme shi ya fito in har ya shirya in ba haka ba kuma a raba tsakanin dan ban ga daraja a tare da shi ba tunda har zai ringa tsare ki a bakin titi"

Da sauri Karima ta girgiza kai, bayan dogon tunani da tuna maganar mahaifiyarta a kan zancen da ta ji tsakiyar dare, ko tace fadan da mamansu da babansu suka yi a kanta, cewar ta jira ta ga ko waye, dan ta tabbata idan fa ta ba mama dama to kuwa tabas za'a nemi Mudansir in kuwa wannan din ya fi Mudansir ai ta yiwa kanta asara

Murya a raunane ta ce" Mama, dama fa kawai dai yana zuwa wajena be, Ni banma sonsa"

Mama da mamaki ta ce" Bakya son nasa kike tsayuwa da shi? bakya son nasa har kike fita ko tsaya da shi a boye? bakya son nasa mahaifiyarki ta yarda da shi har ta bari kika ganshi a boye? kin san bakya son nasa kike wasa da karatu domin sa?"

Hankalin Karima ya tashi ainun, ta rasa yaya zata yi sai hakuri da take ba Mama

Mama ta mike bayan ta sake Binta da kallo, a tausashe ta ce" Ki kula, ki dauki wannan a matsayin kin yiwa mamanki laifi na yafe, idan har kika kuma makamancinsa sunnan abin garaje kuma zan maki garaje tabassss!, ki kama mutuncin kanki shi kadai na roke ki, in har masoyinki ne zai nemi manyan ki ya kashe kudinsa da lokacinsa da komai nasa dan ya same ki, ta haka zai mutunta ki, idan kuwa dan wasa da lokacin yan mata ne wannan yawon shi zai koya maki, wanda ba zan lamunta ba, idan har na kuma tsintar irin haka a waje Karima da Ni kike magana kuma sai na yi maganinki daga ke har du wani wanda ke daure maki kin fahimta?"

Da sauri Karima ke gyada kai, sai godiya take yi har mama ta bar dakin

Wani irin zama ta yi tana sauke tagwayen ajiyar zuciya a bayyane ta ce" Allah na gode maka, yanzu da wani zancen ake yi da bosss ya ji, kai innalilahi "

Sai kuma ta sake gyara zama a ranta tana ayana' Ni har yanzu shiru baba ya ki min zancen mutumen nan, ga dama ta samu da zan gabatar da wanda muke tare kuma na kasa saboda kar aje in yiwa kaina sakiyar da ba ruwa......Hum koda yake, zan ɗan karra jira in gani ko a dace'

Wannan ya rufe babin firgicin Karima, sai dai kuma ya bude mata wani tunani mai zafi na yanzu kennan ina zasu ringa haduwa da Mudansir?......
(wannan kennan)

Lokaci ya ja sosai, ama haka ta nufi bangaren baba tana cike da tunanin hanyar da zata bi dan ta samu wata yar mafita a kan abinda take gannin ya kutso mata da ya'yanta

ya zama wajibi ta gabatar masa da muradinta,, hakan ya sa ta je da salama da zaman lafiya kuma ta dukar da kanta bata yarda neman fitinarsa ya hasalata ba, koda yake shi dinma yau du kamar ba shi ba, wani abu na saka shi farin ciki a bayyane dan ya gaza boyewa,


Cen cikin dare bayan sun gama ibada Mama ta dan sake dubansa, gannin kamar har yanzu hankalinsa a kwonce a tausashe ta ce" uhum baban amarya baban amarya, Ni kam yanzu kennan biyu zamu aurar , yau da gobe sai Allah"

Wani murmushi ya saki ya dubeta ya wani karra sakin murmushi ya ce" Ni na san y'ar aljanna ce ke gimbiya, eh biyu ne cif "

Mama ta yi murmushi ta ce" Allah ya sanya alkhairi, Allah ya basu zaman lafiya"

Baba ya ce" Amen amen amen amen gimbiya amen"

Mama ta dan dauke kanta tana ta addu'a a ranta, a hankali ta ce" yaran nan fa Anmy kanta ta isa auren nan babansu, itama fa yanzu ta shiga shekara ta sha tara"

Baba ya dan kame gemunsa kafin ya ce" Walahi kuwa, Ni abin ba wuya , du na zata Anmy bata wuce sha biyar ba""

Mama ta dan zarro ido ta zauna da kyau ta ce" Kai, Anmy din? girmanta ya girmi shekarunta, baka kula ba?"

Baba ya girgiza kai yana dariya ya ce" Ni har yanzu tausaya mata nake yi, y'ar nan ko wa zan ba sai na saka ido sosai dan walahi ba zai kai min yarinya ya halaka min ba, gaba daya kalar hutu ce kalar turawa y'ar nan"

Mama ta tabe baki a boye a ranta ta ayana' haka fa, son kai, shi ya dagargaza ya'yan wasu ama nasa kulun yana da tsari a kansu

A fili mama ta ce" Allah dai ya basu mazaje na gari, Ni wai babansu in dan kawo shawara mana, in har bata yi ba sai ace bata yi ba shikenan?"

Baba ya dubeta, ya sake dubanta sannan ya ce" Uhum ina jin ki"

Mama ta sake dubansa da kyau ta ce" Dama cewa na yi, me zai hanna y'an matan nan naka ka basu dama du wata mai saurayi ta bashi dama ya zo ya ganka, idan har yayi maka sai ka basu dama su fuskanci junna, in kuwa bai yi maka ba sai ka dakatar da su, ka ga wannan hanya ce mai kyau da za'a iya barin d'an yau ya ringa abu ba tare da boye boye ba, kar a hanna musu yin saurayi su ringa tarda samarin ko?"

Baba ya kalleta a zabure, ido cikin ido ya ce"



🫠🫠🫠🫠🫠🫠🫠🫠🫠🫠🫠🫠🫠🫠
07/12/2024, 14:52 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*🇳🇪

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi tara (9)*


*TALLAH, TALLAH, TALLAH*

*META FORCE*

*menene meta force*

business ne ingantacce business ne mekyau business ne daizaibaki kudi 💯
tunda ake duniyar network marketing ba’atabayin business din dayake bada kudi sosai kamar meta force ba kuma dollars ne sukebadawa sannan inkinason canja dalarki cikin mintuna qalilan zaki canja dollars dinki zuwa naira hankali kwance kinadaga gida dollars suna sauqamiki hankali kwance yawanci yan nigeria ko ince yan arewa bakuda lbrn wannan business din business ne daya karade duniya akwai qasashe da dama wanda sukafimuma cigaba sunacikin wannan business na meta force

*shidai meta force crypto currency* ne

kuma munsan cewa yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency

akwai program dayawa acikin meta force wanda akayi lunching da wadanda ba’ayiba amma za’ayi nan bada jimawaba

yanzu bari mudau programs guda 1muyi dan taqaitaccen bayani akai

*TACTILE*

1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zakshiga meta force saikafarayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din
tactile yanada levels guda 12 1 to 12 kowani level da kudinshi level 1 5 dollars
level 2 10 dollars
level 3 20 dollars
level 4 40 dollars
level 5 80 dolllars

hakadai
kudin kowani level yake ninka na bayanshi saikzabi wanda zaka iya saikayi shi tactile ananne akasamun abunda muke qira

*Spillover*da*over flow*

wato kanazaune baka kawo kowaba zakaduba wallet kaga ansama mutum har dollars sun sauqama anbiyka kuma bakayi aikin komaiba a wadannan levels din dakasayadin ko wani levels dakasaya idan spillover yatashi fadoma to adadin kudin wannan levels dinne misali level 1 5 dollars to ynada dakuna 6 duk lokacin da kayiwa mutum register kokuma spillover yafadoma zakasamu 5 dollars ne akowani daki 1 amma banda dakuna 2 na farko da daki 1 na qarshe amma daki na 345 dukka sunafadowa biyanka za’ayi kaga 15 dollars kenan dakuna 3 sannan idan dakunan suncika za’aske sharemaka kasake zuba wasu mutane inma kaikanemosu inma spillover kasamu

to haka zakayita samun wannan dollars din a kowani levels dakasaya duk zagaye daya zakasamu adadin kudin daksayi levels dinnan sau 3 kagdai kudin dakasyi levels din sundawo harda riba kuma hak za’ayita sharema dakunan anasa wasu mutane koda mutanen sunkai millions 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Atakaice kenan sauran bayanin kubiyoni awannan number domin jinkarinbayani
👉0912 262 1080
*Sannan zaku iya zuwa kuyi browsing google youtube*

*zakusamu kowane irin bayani kukeso game da meta force
Aunty Hajja








LABARI



Baba ya kalleta a zabure ido cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login