Showing 132001 words to 135000 words out of 190762 words

Chapter 45 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3969

bismillah mana karaso plz"

Malan Abdullahi ya fito yana rabe rabe har sai da Muhammad ya riko hannunsa ya shiga tsakaninsu da d'an uwan nasa

AL'WALID ya fuskance su a nutse ya ce" Alhamdulilah, zuwa yanzu babu abinda ba'a nuna min ba, kuma na fahimta sosai, Malan dan Allah a yi hakuri a daina shiga duk wani abu da zai janyo zubar da mutunci, kuma a yafewa Muhammad yama yi kokari gaskiya, domin iyaye daban ne, darajarsu kuma a idannuwan ฦดaฦดansu mai girman gaske ce, ba kowa ne zai jure wasu abubuwan da suka wuce misali ba"

ya sake duban su Elhaji Maiga ya ce" Elhaji, idan har ana bukatar magana da Ni a nemi layina in sha Allah, saboda nan din bana so ko da wasa irin haka ya sake faruwa.. , bismillah mu je "

Ya musu nuni da hanyar tafiya fuskarsa a hade SOSAI

Gaba dayansu babu wanda jikinsa bai yi sanyi sosai ba, saboda du abinda ake yi bai taba yi musu irin haka ba, ita kuwa Mufeeda gaba daya jikinta rawa yake yi, a yanzu ta wuyanta take yi fiye da komai , dan haka ko da mahaifinta ya ja hannunta binsa ta yi muryarta ko fita bata iya yi da kyau suka karasa motarsa

A nutse AL'WALID da yayi waya ya ce" Muhammad, ku dakata a kai malan "

Muhammad sai da ya sauke ajiyar zuciya saboda dama tsoransa kar aje kafin su ajiye shi su yi masa abinda zuciyarsa zata idasa bugawa,

Elhaji Maiga ya fada mota ko magana bai yiwa direbansa ba ya ja suka tafi Mufeeda na sake fashewa da wani kukan

A tausashe AL'WALID bayan motar ta zo ya dubi Muhammad ya ce" Ga katina Muhammad, ka same Ni ranar monday da takardunka, ka zo da sassafe mu fita"

Daga Muhammad har malan sai da suka ji sun wartsake, malan ya ringa godiya yana hawaye

AL'WALID yayi murmushi ya ce" Malan Allah ya karra lafiya, zan shigo gidan da baba in sha Allah, idan an je an fara shirin kaura...., dan Allah a kula da lafiya a kuma kauracewa duk wani abinda zai taba lafiya da nutsuwa...., malan babu mai yi sai Allah a duniya, kuma musulunci bashi da tozarci, baya yarda da tozarci"

Daga haka kawai ya wuce wajen direban dake tsaye suka yi magana ya sanar masa idan ya ajiye su ya ba Muhammadu ky din motar ya hayo taxi ya dawo, ya sake ja baya ya harde hannayensa ya musu salama hadi da dakatar da kukan da malan ya fashe da shi, Muhammad kuwa kamar bakinsa zai yage dan dariya da farin ciki, sai maimaitawa yake yi Allahu akbar, shi dai yana tsayen nan yana kallonsu har suka tafi

Da farko ya so fita, sai kawai ya ji ina zai je? cen kasan zuciyarsa ke raya mana ina zai ne kuma? sai kawai ya samu kansa da juyawa ya nufi bangaren nasa a nutse ya shige har baban falon da salama

Saminsu yayi kamar wa'inda ke wata sabga, fira suke yi da dariya su khalisat kuwa kamar zasu tashi sama dan farin cikin abinda shi ya gaza ganewa

Zama yayi cikinsu aka bashi abinci a nutse ya dan taba sai kuma ya mike yana kallon aunty shareefat ya ce" Maman AL'WALID me likitar tace ne?"

Aunty shareefat ta ce" Zazabi ne d'an shareefat ai da sauki yanzu haka sunna sama fa ita da y'ar sun dage tun yanzu litle zata kauro, mun so ta bari har a kwana biyu dai ta gama cin amarcinta lafiya sai kawai ta gudu sama"

Shima maganar sai da ya ji kunya sai kawai ya basar, ya yi saman ba tare da yace komai ba, kaka Z kuwa har kamar ta tashi ta bi shi dan ta ga abinda zai yi a saman, sai dai ba hali dan ita kadai ce ta zauna cikin yaran , sauran du sun koma wajen Hajia Inna dan su kwontar mata da hankali, itama ta kasa ta tsare be saboda kawarta dake ta damunta kan dan Allah kar ta yarda ta bari wani abu mai sunna shakuwa ko makamancinsa ya shiga tsakaninsu, da dazu zata zo gidan da ta sanar mata Elhaji Ya'u fa ya zo, yanzu haka yana shago sai tace sai da yama idan ya rufe zata zo dan kuwa tana tsoronsa kamar me.


A nutse ya shiga dakin bayan ya dan kwonkwasa

Samunsu yayi zaune tsakiyar cafet sunna buga game a ipad din Kurma

Tunda ya shigo kurma ta mike tana ta watsa haฦ™ora ta shiga yi masa yarenta, wanda shi idan ka ga ta masa rubutu to a rikice take ta yadda ba zai gane yarenta ba, saboda yana gane dukkan abinda take nufi da alamun da take yi da yan hannayenta

Murmushi kawai yayi saboda fada masa take yi Mamanta ce, kuma bata dukanta dai da sauransu

Da hannayensa ya yi mata tambayar akoy wanda ke dukanta ne dama?

Sai kawai ta dan juyar da kanta ta ki cewa komai

Ajiyar zuciya ya dan sauke da hannunsa ya yi mata alamun ta je kasa gayanan zuwa

Juyawarta ta yi da dan gudu gudu ta fita ta rufo dakin

A nutse ya dan murda ky a kofar , hakan ya sa KHADEEJA dake kallon kasa dagowa da sauri ta zuba masa ido

"Ki je zan neme ki" Ya sake amsawa a kunnenta, hakan ya sa ta mike tsaye da sauri ta juyar da bayanta idannuwanta na cika da kwallah, ta share tana tuna kashedin da Lubna ta taba yi mata da ta yi mata kukan iya shege dan ta ga Abdul karim da budurwa, cewar idan akoy abinda zata yi ya ga damarta ya rainata shine ya gane tana sonsa sosai da sosai, lokaci daya kuma ta samu kanta da yima kanta tambayar "SO? WANI IRIN SO?"

Tunda ta mike ya bi rigar dake jikinta da kallo har zuwa inda rigar ta tsaya ya samu kansa da shakun karasawa inda take, domin ya jima rabonsa da gane cewar lafiya kalau yake sai yau da duk wani ntc ya kunce masa daga kallon nan da yayi har ya ji kirjinsa na amsawa da karfin da ba zai iya dakatar da shi ba......, ama....., ama.......sau nawa yana gannin mace da riga irin haka wace ta lafe a jikinta sosai, bai ji haka ba sai yau??????

A hankali ya ce" Yaya zaki shake y'ar mutane a gaban babanta kuma ki yi kuka Hajia karama?"

Khadeeja ta ji wani takaici ya shake mata wuya, ta juyo da dan hanzari dan bata san cewa daf da ita yake sosai ba tana fadin" A gaban babanta ko a gaban masoyint......"

Diffff ta tsayar da maganar saboda kusancin yayi yawa sosai

A nutse yake kallon gashin idannuwanta dake kallon kasa kirjinsa na sake dokawa

hannunsa na dama ya makala a bayanta a hankali ya sarkafo shi, sannan ya dan duka ya saka dayan ya dauketa cimak

Da sauri ta rike gaban rigarsa hakan ya sa ta yamutsa rigar dan a tsorace ta cimuimuye rigar tana rintse ido domin kawai ta zata zubar da banza zai yi ya huta da fitsara saboda ai kamar rashin kunya ne zata yi masa shi kuwa shine baba a gidan nasu ai, kuma dai babanta ai ya zamo mai kai duka ne in ana haya haya gaskiya shi yasa ta yi jiran jin nata itama yau, sai ta ga daukanta ne aka yi, kuma aka yi tafiya da ita har wajen gadonta

A nutse ya shinfidar da ita, sannan ya dan rankwafa kusan fuskarta yana gannin yadda ta rintse ido da karfin tsiya ya furta" Ba'a hararan miji fa, babu kyau, kuma Ni ban iya fada ba hajia karama"

Idannuwanta ta bude wa'inda suka cika da wata kwalar da bata san ko ta mecece ba, a hankali tana dubansa ta ce" Me yasa ba zaka ce min Khadeeja ba?, "

Bakinta da ya furta sunnan yake kallo, a hankali ya lumshe idannuwansa kasa kasa yace" Hajia ฦ™aramar ya fi dai"

Khadeeja ta dan zubawa karan hancinsa ido tana dane hannunta dake so sai ya taba , haka kuma tana hanna tsoron kusancinsu bayana ta dan turo baki a hankali ta ce" A'a, sunnana yana da dadi sosai, sunnana yana da daraja sosai, sunnana ya...."


"SHUIIIIIIIIIIIITTTTTTT" Ya fada a hankali yana dora yar yatsarsa a saman lebenta hadi da kafe leben nata da ido

Gabanta ya yanke ya fadi, lokaci daya kalaman da Aba ke fada yana fada suka fado maka a lokacin da yake fadin KARIMA mai jan ido? wato mashayi ko hariji? , a lokacin da Mama ta damki hannunsa suka fita daga cikinsu suka je suka sasanta
Idannuwansa sun tsoratata, yannayinsa ya tsoratata, a lokacin ta ga wata jijiya a gaban goshinsa wace bata sanshi da ita ba, bugun zuciyarsa kuma ya kara kaimi fiye da dazu....lokaci daya tsoro ya gama mamayeta na yannayinsa

A hankali ya furta" Baki da lafiya, ki huta plzzzzzzzzzzz, idan zaki fito zuwa bangaren su Baba, ku saka hijab Hajia karamahhhhhhhhh, kin ga gidan cike yake da mutane kuma du ba yara ba....................."

Buga kofar da aka yi a karro na biyu ya katse maganarsa a dole ya lumshe idannuwansa yana dan juyawa dan daidaita kansa sannan ya ja baya sosai ya bata space, wanda da yayi sai da ajiyar zuciya ta kwace mata, tsoron da take ciki ya karu, zazabinta ya karru ta ji kamar zata summe

A nutse ya juya ya dan kalli yannayin jikinsa ,
Wata irin kunya ta kama shi a nutse ya dan juyo ya kalleta, sai kuma ya yi murmushi ya nufi hanyar fita daga dakin gaba daya yana jin kansa na neman daukan ciwo, wato abinda ya jima bai ji bane ke son bayano masa lokaci guda

Da ya bude dakin yana gannin kurma sai ya kasa fita saboda ya jima rabonsa da fita da shiri mai sunnan shiri koda ta kwana, hakan ya sa a yanzu du ya tsargu da kansa

Kurma ta masa nuni sannan ta yi masa yaran kurumcinta wanda ya gane cewar kaka Z ce tace ya zo

Ya dan dubi kurma da tunanin kaka Z kuma? lafiya? kai ko dai kurma bata gane ba?, shi dai yayi mata nunin ta je gayanan , bayan ya ji ta fara sauka ya fito ya rufe dakin ya nufi nasa dan sai ya cenza tufafi , lokaci daya yana duba wayoyinsa dan tunanin ko sun yi ta kiransa , ko babu lafiya? dan bai ba dalilin da zai sa a irin wannan lokacin kaka Z ta yi kiransa ba in dai ba wani abu mai mahimmanci bane.............................









๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜
07/12/2024, 15:21 - samiraharounayacouba: ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ
*FARKON GANIN IDONA*
๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you ๐Ÿ˜*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ฦŠAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAฦ˜IN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na arba'in (40)*

*IDAN KINA DA BUKATAR TALLAH KI TUNTUBENI TA LAYINA KAMAR HAKA 93811618*





LABARI





Dakinsa ya wuce yayi wanka a gagauce saboda lokacin sallar azahar ne sannan ya fito ya saka jalabiya bak'a sidik doguwa sannan ya dauki karamar wayarsa kawai, wace ke dauke da layinsa na sirri ya fice a dakin ya sauka kasa

Ya tarar da aunty shareefat da kaka Z kadai, aunty shareefat na danna wayarta ta ki tashi ta tafi ne dan haka kawai irin yadda kaka Z ta nace a kirawo shi ya dan so daga mata hankali, ko dan ya zamo sunna da shakuwa sosai da AL'WALID ne, ko menene? haka kawai dai ta ga rashin dacewar haka din bale da yana hawa suka hada ido da sauran yan uwan suka saka dariya da ido suka yiwa alamun su tafi, sai gani suka yi mamansu Hajia z ta kasa mikewa karshema sai ta saka kurma ta kirawo AL'WALID din, ko da ta nuna a barshi mana zai tarda su idan da wata maganar sai kaka Z ta nuna a'a a je a kirawo AL'WALID din tana jiransa, shine fa har sun fita kawai ta dawo tana call ta ki tafiya

A nutse ya karaso yana duban agogo Gannin yanzu za'a kira sallah ya ce " Kaka Z, zan je masallaci in dawo, idan na zo sai mu yi maganar"

Hajia z dake bin sabuwar suturar da ya cenzo da kallo ta yi gagawar fadin" Aa big son dama lokacin sallar ne ya gabato nace bari dai a kirayeka kar aje ka rasa jam'i"

Aunty shareefat ta kalleta da dan mamakin furucinta, sai kuma ta kawar da kai bata ce komai ba

Shi kuwa murmushi kawai yayi ya fice dan kar ya rasa sallah

Hajia z ta mike tana dan tabe baki tana jin kamar ta je saman ta gano abinda ke faruwa, sai dai ta san idan suka hau sama abu ne mai girman gaske zai kai su, dan tunda aka kawo amaryarma ita bata je saman ba, tun dai gyaran da aka yi rabonta da saman nan

Aunty shareefat na kallonta har ta fice kafin ta mike ta danna abin kiran mai aiki tana ta tunanin me yake faruwa ne haka kuma da kaka Z?

Mai aikin na zuwa ta dubeta da kula ta ce" Maman baby a tabbatar da an gyara wajen nan sosai, sannan a kula kar kowa ya wuce falon nan, idan baki ne a ajiye su a falon baki kawai, in an jima zan zo kafin mu je kai kaya, a barta ta huta bata da lafiya, ko baki suka zo kar a tashe ta plz,.idan tana da bukatar wani abu na gwada mata komai zata yi muku magana, kar a bari kanshi ya katse a ringa sakawa ana kula da wutar kin ji maman baby?"

Maman baby ta dan duka tana fadin" In sha Allah Hajia, a fito lafiya"

Aunty shareefat ta fice, ita kuma Maman baby ta yi kiran mutun biyu cikin ma'aikatan suka shiga sabon gyara da kwashe kaya , su fa tunda suka gane cewar ba wannan mai zuba musu wulakanci bace uban gidansu zai aura hankalinsu ya kwonta, dan kuwa cikinsu babu wace bata yiwa alkawarin kora ba idan an yi aurensu ita da Elhaji, su kuwa aikin nan shine rufin asirinsu nan gidan duniya


A bangaren Hajia inna suka ringa jera akwatunnan da zasu je su kai gidan Aba, domin da farko sun so a ajiye mata abinta kawai a nan sai baba Hamza ya nuna a'a sai an je an kai idan yaso yadda iyayenta suka tsara mata za'a yi, wannan dalilin ya sa suka jere saitunnan akwatunnan da kamfanin dake hada musu harkar lefe suka hada babar motarsu ta kawo, kuma yanzu haka motar na nan sai an kai kayan gidan Aba sannan zata tafi , saboda idan motocin gidan za'a saka za'a laya motoci ne dauke da kayan , motocin iya mutanen familly zata dauka kawai


Hankalin kaka Z sai da ya tashi sosai da ta ga irin uban kayan da aka dankarawa KHADEEJA,
Na fa halayarta bane kyashi da bakin ciki, hasalima tsoro ne ya fi jagorantar zuciyarta da tunanin ana daf da raba su da yaron su mai kaunar su, ta dauki vidio sosai da sosai ta tura a wayar maman karima tun kafin ta gani da idannuwanta sannan ta sanar mata cewa ta hau online ta ga kayan KHADEEJA.


Maman karima na cikin dama fura zata sha ta ajiye ta kunna data hannunta har yana rawa ta shige whatsup din sannan ta shiga daukan vidion dake cikin wayar

Tun a vidion farko zufa ta keto mata, ta zuba ido tana kallo har ta gama kallo kawai ta ajiye ta hade kanta da gwuiwarta ta fashe da kuka mai tsananin gaske

Mahaifiyarta da ta shigo da kora dan jiran ta gama dama furrar ta zuba mata ne ta karaso tana fadin" Ke kuwa ta yabuwa me yayi zafi da ba wuta ba wannan zafin zuciya haka? kukan me kike yi ke kadai a nan a zaune ? "

Maman karima ta dubi mahaifiyarta ta ce" Yanzu inna kiyayar Elhaji har ta kai nan? ya dauki miji irin wannan ya ba KHADEEJA bayan ga karime a gabanta itace baba?, "

Inna ta zauna da kyar tana bismillah ta ce" To, to , to, wato ba zaki rabu da lamarin gidan Elhaji Ya'u ba ko? ba zaki taba dadara da shiga lamarin gidansa ba ko? salon ki janyo min mafisa ya zo har gidan nan ya hade mu ya zane mu? kin ga ta yabuwa idan har kin gaji da zama da Ni ki maida Ni kauye in lalaba rayuwa har in koma ga ubangijina, inma ba mantuwa ba irin taki kin manta karime din ya fara zaba yace ya bata mijin ama a nan a filin gidan nan ta bugo maki tace da ke miji ba kowa bane , kika yi tsalan albarka kika nuna ta bijire? ai ba wannan maganar a yanzu kice ba haka ba?"

"Inna" Ta fada da karfin da ya saka uwar zabura tana kallonta

A kausashe ta ce" Inna, walahi, walahi ba zan yarda ba, ko naman jikina zai yanka gutsi gutsi ba zan yarda ba, sai Karima ta shiga gidan nan"

Da tsoro uwar ta ce" Ta shiga wani gida? ke kina cikin hayacinki kuwa?, Karima fa yar uwar Khadeeja ce uba guda, idan ba mutuwa ta yi ba mijinta ba zai taba halastawa Karima ba!"

Mikewa ta yi ta dauki wayarta ta shiga aikawa Hajia z kira ta ce" Du wanda ya kama shi za'a yi, abinda na sani shine ya zama wajibi Karima ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login