Showing 135001 words to 138000 words out of 190762 words

Chapter 46 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3981

shiga gidan nan, ko ana kare jini biri jini ne!"

Hajia zainab na daga wayar maman karima ta ce" Kawata, idan an jima kar ki bi su kai kayan nan dan Allah, ganinan zuwa gidan dan ki min jagora Wajen Khadeeja"

Hajia z ta ce" A'a me zaki yi a wajenta ke kuwa? ki bi komai a hankali, Ni ina gannin gwara ki zama ta hannun damanta kin ga ko menene kya kwashi rabonki"

Maman karima ta girgiza kai tana dafe kugu ta ce" Ga dukkan alamu baki yarda da abinda na fada maki ba, baki yarda cewa yarinyar nan da kika gani ba walahi sai ta yi sanadiyar da ko hanyar inda kuke zai daina kallo, kin ga magana tsakaninku da shi sai ta gagara, jinnin Usaina ce fa, jinnin asiri jinnin munafurci, sai ta sa ya manta kowa da komai sai ita sai uwarta da danginta da ta zaba,, fada maki ne nake yi , ke kin ga yaya nake da mijina kafin ta zo gidanmu, da ta zo masifa kala kala ta Kunno Kai, a yanzu ko sunnana Elhaji ya ji sai ransa ya bace, an fada maki banza ta barni? tun daga lokacin da na bar gidan nake zubawa malamai kudadena dan a karya asirin da ta min ama har zuwa yanzu abu ya gagara, bari ki ji cikin kawayenmu a kulun kece abin mangari, ko taro in dai naki ne babu wanda ke jiran katin gayata kai kanmu muke yi, idan har wannan rayuwar ta farin ciki kike son zubarwa ki je ki kama wace bata daga tabas irin rawa, rayuwar kunci da bakin ciki, rayuuwar a jika kwaki a kora da ruwa kuda na wawar nasa sauro na cizon rabonsa ba damuwa sai in tayaki addu'ar komawa zaman lungu da ƙatuwar budurwa a gabanki, dan kin sani ne babu mai rike maki y'arki a cikin gidan nan"

Jikin Hajia Z ya karra yin mugun sanyi, ita da yanzu ta gama fadin kalar kayan da zasu saka su uku matan Elhaji Hamza idan zasu je kai kayan nan, dan Hajia inna ce da kanta tace da su tana rokon alfarmar su tafi su kai kayan jikansu su da kansu, yanzu yaya zata yi kennan?

Jiki ba karfi ta ce" Ki kasance cikin shiri da sun fara tafiya sai ki taho"

Maman karima ta saki murmushi a nutse ta ce" Ko ke fa"

Hajia z ta ce" To ama, wai yaya zaki yi hakan ya kasance Ni fa bana cikin abinda ya shafi allhakin rai fa? kuma yaya zaki yi ki shigo ba tare da wani ya ganki a cikin yaran shago ko shi da kansa mai shagon? tunda kurma tana cen fa hakan na nufin bai tashi ba har yanzu bai koma gida ba"

Maman karima ta tabe baki ta ce" Kin ga, Ni nikaf dina kawai zan dauka in saka baban hijab ba zasu gane Ni ba, kuma maganar yadda zan yi ta halastan kuwa wannan Ni na sani, sai dai ba boka babu malan zan bi da kirsa ne idan ta gagara in gwada karfina a kanta Ganinan zuwa jira zan yi a nesa kadan da an bude baban get din zan shigo!"

Bata tsaya ta ji daga gareta ba ta katse kiran ta shige daki daya jal ta dauko hijabinta zumbulele da nikaf dinta

Mahaifiyarta da jikinta ke rawa ta ce" Ta yabuwa, ki guji muguwar kadara ko in kirayi hakan da janyowa kai jafa'i, ta yabuwa ke dai in ba Yaren kudi ba bakya gane komai? rayuwar da kike ciki ce kike zagi haka ta yabuwa? ai kuwa babu baban arzikin da ya wuce rai da lafiyar da kike da shi, ki kiyaye kar su kubce maki cikin garari ta yabuwa, meye a arzikin banda fitina da tashin hankali"

Bakin gyauton dake jikin uwar kawai ta kalla ta gyada kai ta ce" Ba laifi, idan arzikin ya samu dama ke babu inda zaki je dan baki iya ci ba, gayanan ai da na je rabo ki daga kwonciyar tabarmar kaba a kauye da gudu kika biyoni kika zo koke cin dadi, da na rabu da gidan Elhaji kin fi Ni kuka dan jar miya ta kare, yanzu kuma da bakinki kike maganar wai kudi ba farin ciki bane? ama kuwa in ba dan uwata ce ke ba yau da ban san me zan gaya maki ba, hummm!" ta yi gaba da sauri ta barta nan tsaye tana kiran sunnanta ( Allah ka rufa mana asiri duniya da kiyama, Allah kar ka jarabcemu da ya'yan da ba zasu ji kunyar harshensu a kanmu ba, Allah ka shirya mana zuri'a ka rufa mana asiri duniya da kiyama)

Hajia Z na gannin wayar ta mutu kawai ta yi kai kawonta sau biyu ta rasa madafa sai kawai ta cire dan kwalin kanta ta yi flashing din khalisat ta ajiye wayar a nan ta yi bayi da sauri ta rufo

ƙatuwar buta ta cika ta bude WC ta saurara, tana ji an shigo ta aniyar zubawa a cikin WC din tana kakari da karfinta dan ta jiyota

Khalisat ta karaso da sauri kusan bayin tana dan fadin" Subahanallah, Mama? lafiya?"

Hajia Z ta yi shiru ta karra abinda take yi har sai da ta ga sosai Khalisat ta rikice sannan ta wanke fuskarta hadi da dan jika gaban rigarta ta fito tana numfashi sama sama ta rike hannayen khalisat da ta miko ta rikota da kyau suka nufi bakin bed dinta ta zaunar da ita tana fadin" Mama lafiya? subahanallah yanzu fa na neme ki akace kin nufi daki"

Hajia Z ta make murya sosai ta ce" Bari khalisat cikina ne ya dan juya min fa sai na shigo na shiga bayi, tun dazu amai ne nake yi da gudawa"

Hankalin khalisat ya tashi sosai domin nan da nan ta fita ta kirawo mama B suka dawo tare

Hajia Binta cike da tausayawa ta ce" Subahanallah Hajia wani abin kika ci ? bari a yi kiran docter subahanallah "

Hajia Z na nishi ta ce" Nima ban sani ba, Ni dai kawai abin ya kece min, baki ji murdawar da cikina ke yi ba"

Mama B ta ce" Subahanallah bari in je in yi kiran docter in dawo"

Da sauri ta ce" A'a Hajia, haba Hajia daga ciwo sai a taso Docter? "

Kaka B ta ce" A'a fa Hajia amai da gudawa ai abin tsoro ne yanzu da yana iya fitar da ke a hayacinki?, ai shi matsalarsa akoy saurin karar da ruwan jiki"

Hajia Z ta ce" Duda haka a dan bari zuwa an jima idan bai tsaya ba sai a kirawota, Ni yanzu damuwatama bai wuce tafiya kai kayan nan ba, kin ga kayana har na fitar fa, gashi har lokaci yayi ke har kin shirya, ban san yaya zan yi ba"

Hajia B ta ce" A'a haba dai, ciwo ai yana gaba da komai Hajia, ki huta bari in je mu tafi mu dawo, khalisat ta zauna a wajenki sai in ringa kiranta ina ji daga gareta jikin naki, kin ga Hajia inna ma masu aiki ne ke wajenta du tafiya zamu yi"

Kai ta gyada ba tare da ta so an Bara mata khalisat ba, dan ba zata taba son kowa ya san shirin su da kawarta ba, ama kuma ta san tunda aka riga aka ce haka din idan ta kawo wata gardamar za'a iya fassarata ne

Haka Hajia Binta ta wuce ta sanar da sauran abinda yake faruwa, du suka lekota kafin su wuce, Hajia inna ce kawai basu sanarwa ba, ita kuwa dama in ba abu ya zama baba ba basu cika fada mata ba dan kar a daga mata hankali, domin abu karami ke daga mata hankali


motocinsu na tafiya tun ba'a rufe get ba ta shige bayan an yi mata tambayar wace ita ta sanar cewa daga gidan su amarya aka aikota ta kawo sako, ta nuna musu leda dauke da abu, dan haka suka bata dama ta shige

Tunda ta shigo ta sanar da Hajia Z, wace ta mike da sauri tana neman dan kwalinta da hijabinta

Da sauri khalisat ta mike tana kokarin kamata ta ce" Sannu mama, mu je in raka ki ya murda ko?"

Hajia Z ta dan dakata ta dubeta ta ce" Au, a'a da sauki ai , kin ga yi zamanki ki yi game dinki ina zuwa, na yi bakuwa"

Yannayin da take da kuzari da magana da kuzari ya saka khalisat dubanta da dan mamaki ta ce" To ama mama ko Wacece ai sai a sanar da ita baki da lafiya sai ta dawo ko?"

Da dan hasala ta ce" Ke Khalisat!, Ni Lafiyana kalau, nace kuma ki zauna ta yabuwa ce ta zo, ina zuwa!"

Daga nan ta saka hijab dinta ta fice a dakin ta bar khalisat tsaye da mamakin abinda ya faru, ta yabuwa? mahaifiyar Karima kennan sister din amaryar AL'WALID, wace suka zo kwanaki wajen baba cewar babanta ya mata miji bata so?

Mikewa ta yi ta fito dan du sai take gannin kamar maman nata ba lafiyar gareta ba dan dai kawarta ta zo ne ta fito, domin khalisat akoy sarkafar uwa

"Rike min kwanon nan da na dauko, maganin nan ne na sako a ciki saboda kar su hannani shiga su ja min tsayuwa a kofa, na ga Elhaji Ya'u tsaye da Elhaji Hamza da kurma sunna ta dagawa masu tafiya da kayan hannu kamar sunna tsaye bakin hanyar da shugaban kasa zai wuce"

Maman karima ta fada

da sauri Hajia Z ta amsa ta tura shi nan lungu ta ce" Magani kuma? na me? kin san sai da na yi karyar rashin lafiya sannan suka tafi suka barni? mu je bangaren nata Ni dai ko menene kar ki yi abinda zai ja min matsala a gidana da mai gidan nan, saboda walahi kin ga yana kyale komai ya wuce banda abinda ya shafi yaron nan, sam baya yafe abinda ya shafe shi, kennan kin ga ko menene ya zamo wanda hankali zai dauka, kin dai ji na fada maki"

Ta yabuwa ta tabe baki ta ce" Ba dai kin tabata babu abinda ya shiga tsakaninsu ba? domin a nan ne matsalar take, idan kuwa wani abu ya shiga tsakaninsu karma mu je mu batawa kanmu lokaci in je in shirya mata shirinta na kanta wanda zai halastawa y'ata shigowa gidan nan, dama gidan nan na Karima ne, kwacewa suka yi ita da uwarta!"

kaka Z ta dubeta da kyau, idan tana fadin haka sai ta ji kamar ta janye daga lamarin nan dan ita fa babu wanda zai sakata a hakin rai, ba ruwanta da wannan gaskiya, koda yake bari dai ta bitan yanzu ta ga nufinta, hanya kawai ta nuna mata suka fita sunna dari dari kamar munafukai abinka da marar gaskiya

Khalisat da kirjinta ke bugawa har shasheka take yi ta tashin hankali ta juya da sauri ta koma dakinta tana zarro ido hadi da fashewa da kuka ta ce" mama? me yake faruwa? mama me yake damunki? me ya saka ki a cikin wannan abin na tashin hankalin Mama? mama big son bai cencenci haka daga gareki ba, mama me yake faruwa ne Ni? innalilahi wa inna ilaihi raj'une me yake faruwa ne??????"



Basu samu wahalar shiga ba saboda Hajia Zainab dake jan ragamar tafiyar

Sunna shiga suka so karasawa baban falo , sai mai aiki ta tare su take sanar da su sakon Shareefat

Hajia Z da haushi ta ce" Ke dilla kauce min kuma ki ce mata ta yi baki bana son shashanci, Wacece shareefat a gabana? "

Gefe mai aikin ta ja kanta a kasa ta ce" Ki yi hakuri Hajia, dama mai gidanma da ya zo sai da ya Bara mana salahun kar wanda ya hau saman bale mu yi kiranta"

A tare suka ruko ido har sunna hada baki wajen fadin" Yana gidan dama????"









Rabi inee lima anzalta ilaya min khairin fakir 🤲🏻😍🥰
07/12/2024, 15:21 - samiraharounayacouba: Mai aikin ta dube su da yannayin tsamtsamta da lamarinsu, domin ita ba yarinya karama bace, da wahala a yi wani abu ya shige mata duhu ko yayane

A hankali ta ce" A'a, ya fita dazu"

Hajia Z da wani haushi ta zabga mata harara ta shige tana fadin" Irin ku baku iya cin ribar zance ba, yaya zaki ringa magana a dunkule ne? , je ki aikinki ai ga waya nan bari in yi kiran dakin nata da shi" ta karasa wajen wayar dake ajiye tana nunawa maman karima wajen zama wace ke kallon falon kamar kanta zai cire

Da kyar ta iya daidaita kanta ta je ta zauna tana share hawayen bakin ciki tana jin Hajia zainab na waya da Khadeeja, Khadeeja dai Khadeeja ce ake yiwa yar murya, Khadeeja dai ta gidan Elhaji Ya'u da aka haifa a gabanta ce yau take aure a gidan nan? ina ba zai yiwu ba!


Kashewa Hajia zainab ta yi ta karaso ta zauna daf da maman karima tana fadin" Ki sha mana jus din, kuma ki saki fuskarki in dai so kike yi ta saki jiki da ke, Ni walahi bana so kowa ya same mu a nan dan bana son wata fitina da ya'yan gidan nan domin ba yarda suke yi a taba shi ba ko kadan"

Maman KARIMA ta tabe baki a ranta tana ayana' haka fa, kwa ji da shi, nice nan zan dawo zama gidan, walahi ganninsa sai ya gagareku, kuma zan barku a kusa ne ina ciyar da ku da abinda na ga dama, ko anguwa zamu je sai jin zama mai rike min jaka, zan ga karyar arziki ne!"

A nutse take saukowa daga benen tana sauke dubanta a kan bakin da akace sun zo, bale da akace Mamanta ce sai ta yi tunanin ko mama Fateema ce ta zo, dan ba zata yi tunanin Mama bace domin bata hasasota nan kusa, ko YAYARSU da aka aurar da kyar ta yarda ta je, sai tace wai dan Allah a ganta a gidan y'arta ace mata me itama tace me?

A nutse ta sauke dubanta a kan Maman karima dake washe baki tana fadin" Masha Allah yarinyana sannu da hutawa"

Mamakinta ya kama Khadeeja, sai dai bata nuna ba, ta sauko da kyau tana lure da gabansu ta ga an ajiye musu kayan tarba dan haka sai ta zauna a nutse tana dubansu ta ce" Barka da yama kaka Z, Barka da warhaka maman gidan inna"

Wannan sunna na maman gidan inna na bata haushi sosai a ranta, wai dan wulakancin ya'yan Elhaji Ya'u kulun sai sun jaddada mata Wacece ita
Danewa ta yi tana murmushi ta ce" Na'am y'ar albarkana, masha ALLAH hutawa ake yi ashe har kusan magariba?"

KHADEEJA ta yi murmushi kawai ta ce" Ya su Inna, fatan sunna lafiya"

Maman KARIMA karra kallon shigar jikinta take yi, wannan suturar Karima ma nada irinta, sai dai a yanzu da take jikin Khadeeja kamar na Khadeejan ya fi na Karimar kyau, ko dan da abin kyalin amarci ne ko menene?

Ta basar tana fadin" Alhamdulilah tana gaishe ki, ai yanzu haka zuwa na yi in kawo maki sako in wuce saboda kar magariba ta shigo min a wannan anguwa taku mai karnuka"

Khadeeja ta gyara zama da kyau ta tsura mata ido da kyau da duban da ya saka maman karima dan kawar da kanta daga fuskar Khadeejan saboda sai da ta ji wata fargaba da tsoron kallon yarinyar, shi yasa yarinyar nan take matukar bata haushi, komai nata irin na mahaifiyarta ne

Hajia Z ta mike tana dan yin gaba ta ce" Jika bari in yi jiran maman naki a waje ta yiwu sirri zaku yi, kin san aminiyata ce, Ni din banda lafiya ne shi yasa suka je kai kayan naki banda Ni, Ta yabi idan kin taso ina jiranki sai mu je in sa direba ya kai ki gida"

Maman KARIMA ta gyada kai, Khadeeja kuwa a tausashe ta ce" A huta gajiya "

Sai da ta fita maman karima ta matso sosai kusa da Khadeeja, wanda hakan ya sa Khadeeja dan muzgutawa tana dubanta

Maman karima kasa kasa ta ce" Haba gwara da ta bamu waje yarinyata, domin maganar mu sirri ce, Anmy kin san abinda ke tafe da Ni kuwa?"

Khadeeja ta girgiza kai tana dubanta

Kasa kasa sosai ta ce" Zuwana mai mahimmanci ne matuƙa, kin san ku yara baku san duniya ba, ku abinda kuka fi maida hankali a kai kawai ku yi kwaliya ku birge miji, bayan shi namiji sai ana da baban sirrin da za'a iya rike shi da shi, sirri mai darajar gaske irin na malaka da magungunnan mata, kin ga wannan a wajen wata mata cen cikin jeji na samo shi, ki rike shi da kyau ki tabbatar da kin yi aiki da shi a matsayin abinda zaki zuba masa a sobo , ki yi zubawa uku ina mai tabbatar maki an gama, kin san yadda na dauke ki haka na dauki KARIMA, abinda zan yiwa Karima na taimako haka zan yi maki a rayuwa shi yasa na je na hado maki wannan gagarumin maganin"

Kallonta kawai Khadeeja take yi
A shekarunta na yarinyar bayan bayanta sai ta auna ta ga ai kamar maman karima bata yi tunani Ba, ko kuwa wani abu na damunta da bata sani ba

Misali, tunda suke in haduwa goma zasu yi da ita zagi goma ne, zagi kuma babu kalar wanda bata yi mata, ta yi mata ta yiwa mahaifiyarta, inama dadin da ya haɗa su har da haka zai faru?

Na biyu abinda take magana a kai ai ita bata sanshi ba,bata taɓa saninsa ba a wajen mahaifiyarta, a yanzu da mahaifiyarta ta yi mata aure ba zata yarda ta sanshi daga wajen wani Bama bale wai maman KARIMA

Na uku abinda ya fi tsaye mata a rai shine menene dalilin maman karima na aikata haka? me take nufi? me take boyewa?, to ta san tana da mallakar ne bata malake babansu ba ko ta samu wani ta malake hakananma? a me ta dauki iliminta a me ta dauki hankalinta, to in har zata fada cikin irin wannan ramin sai Hajia iya ta yi kukan barinta zama cikin mata masu aji mata masu daraja manyan matan anguwar su da suka rike biyaya, iya zama , kisa, sada kai, iya ey yane dan zama lafiya da miji ba wai wannan hanyar ba, to ai ita da ace ma haka ta ga Mamanta na yi sai ta amshe itama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login