Showing 162001 words to 165000 words out of 190762 words
Chapter 55 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
mararsa laifin su fada halaka HAKANE....., mu yi aiki da ilimin mu da addininmu, hukuncin baba a tsakanin uwa da d'an nan yayi tsaurin gaske...., an san cewa ita ta raba shi da nasa d'an, an san cewa nasa d'an itace silar barinsa duniya, ama kuma daga wannan sai wane?, ita nata d'an yana raye kuma Allah ya umarce shi da ya yi mata biyayya, shin idan wai aka rasu a haka me za'a cewa Allah?"
Khadeeja ta sada kanta, shikenan gaba daya zuciyarta ta idasa fita a nutsuwarta...., kuka take yi sosai domin du lamarin nan ya gama firgitata
A hankali aunty shareefat ta ce" ki yi hakuri Daughter am dan Allah ki yi hakuri kin ji?, na fada maki ne saboda ki taya mu, ta yiwu ke ki iya, walahi ba zan so mutun mai daraja irin tasa da tarin alkhairai ya afka tasku sanadiyar fushin kakansa ba, lokaci kuwa ba shi yake jira ba, ba kakansa yake jira ba"
A sanyaye khadeeja ta ce" Mama, ta yaya zan iya taimakawar? Mama kuma da kuke tare da shi tun yana yaro baku iya cenza wani abin ba Ni da na shigo rayuwarsa kwana uku kawai anya zan iya yin wani abu?"
Aunty shareefat zata yi magana aka bude kofar baban falon ya dano kai a nutse da waya a kunnensa yana amsa kira , sannan ya dakata ganninsu a falo ya juya ya amshi sakon da aka riko masa da hannunsa ya yi alamun a juya sannan ya karaso lokacin da suka mike daga auntyn har ita a nutse ta furta" Barka da shigowa, "
Sai kuma ta kalli aunty ta ce" A huta gajiya Mama, sai na shigo"
Daga haka ta juya a nutse ta shiga haurawa
Rakata yayi da ido a hankali ya kalli aunty shareefat wace ke kallonsa kasa kasa ya ce" inaga ko tsawa ce na yi mata dazun nan? Fushi dai ne Hajiya karama ke yi da ni maman AL'WALED "
Aunty shareefat ta yi murmushi ta ce" Amaryar ake yiwa tsawa yaron shareefat? Ka yi gaggawar neman kanka big son"
Murmushi ya yi yana shafa kansa ya ce" Dama yanzu na ajiye kakan kurma, ya Salam kakan kurma gidan rigima, da kyar suka hakura shi da baban nasa kamar an musu laifi, kuma muna zuwa gidan muka tarar da wani saurayi ya zo , sai da ya bani tausayi ya duka yana kuka yana bashi hakuri wai yana son yarinyar wajensa, kakan kurma cewa yayi ina shi ina ba mai jan ido y'a? Hum nadai yiwa yaron alkawarin idan na yi bincike na ga nagartarsa zan bashi ita"
Aunty shareefat ta saka dariya tana tafa hannu ta ce" wai baka san waye kakan kurma ba ke nan? Ai bana gajiya da shi, idan na zo zuwa nake yi in share kafa in sha dariya kala kala, saima idan ya kawo karar gimbiya nan zaka sha dariya , shi da baba kuwa kamar sa daku haka suke wuni ama da zarar daya bai ga daya ba zaka ga ya bi bayansa"
Yayi murmushi kawai
Aunty shareefat ta ce" bari in je in yi isha, take Care big son "
A hankali ya furta" Good night mam"
Bayan ta tafi ya dan jima yana kallon kulolin abincin dake jere
A hankali ya karasa yana kallo da tunanin shin yayi kiran masu aikin su hauda masa kayan abincin ne ko kuwa ya zuba?
Gannin yana ta tsaye sai kawai yayi kiran maman baby ya sanar mata a kai dakin madame sannan ya haye saman ya nufi dakinsa
Wanka ya yi, dan rabonsa da shi tun na safen nan, cikin nutsuwa ya cenza tufafi da turare ya dauki sakon nan da wayarsa daya sannan ya rufe ko'ina ya nufi dakinta a nutse ya tura bai nemi izinin ba ya shige a hankali ya rufe ya ajiye ledojin a hankali ya karasa inda take tsaye kanta duke tana ta faman daidaita gashin ta da ta gama busarwa ta shafa mai, caje shi ne zata yi ta daure
A hankali ya saka hannayensa ta wajen cikinta ya rungumeta tsammmmm cikin nutsuwa ya kai kansa wajen dokin wuyanta a hankali yana hannata furgitan da ta yi ta hanyar furta" Ninehhhhhhhhhhh HAJIA karamahhhhhhhh"
Khadeeja ta lumshe idannuwanta tsigar jikinta na mikewa, a hankali ta sauke ajiyar zuciya turaransa na sake shigewa hancinta
Juyo da ita yayi a hankali yana duban idannuwanta kamar yadda ta saka nata cikin nasa..........
A nutse ta hade lips dinsu sannan ya lumshe ido ya shiga bata kular da ta dace, har sai da tsayuwar ta nemi gagararta sannan ya aureneta ya nufi wajen kujerar nan ya zauna da ita a jikinsa a hankali ya janyo ledar nan ya ciro kwalin wayar dake ciki , ya bude ya fitar da wayar wace tuni an saka layi da komai a ciki ya kunna wayar a hankali ya saka a tafin hannayen ta kasa kasa ya ce" ga wayar ki, kin ga numbobinki nan"
Ya fada yana nuna mata a karamar wayar da ya dauko din daga dakinsa
Murmushi ne ya subuce mata, wayar baba da ita, duda ba sanin harkar waya ta yi ba ama tana gannin a wajen kawayenta kuma sunna cewa iPhone 16 ta fito ama ta yi mugun tsada, rike ta sai manya, sai ta ga a jikin kwalin wayar haka aka rubuta
A hankali ta furta" Allah ya saka da alkhairi, Allah ya karra budi ya......."
Janyota da yayi jikinsa ya saka ta ɗan katse maganar, a tausashe idannuwansa a lumshe ya furta" Amen, but ni ba godiya nake so ba, i'm sorry , ki daina fushin haka"
Khadeeja ta dago ta zubawa fuskarsa ido, a'a Masha Allah ashe ya kula da fushin nata har ya yi magana a kai? Hakan na nufin fushin nata yayi dan tasiri kennan?, bari ta gwada wani abin ko a dace
A hankali ta ɗan turo bakinta gaba kasa kasa ta furta" AA, ba zan iya daina wannan ba har sai mun yi kiran wayar Mama, ina so in gaisheta"
Murmushi yayi yana dagota ya janyo wayar Tata ya ce" abu mai sauki, saka mana numbar idan ma bidiyo call zamu yi sai mu yi"
Khadeeja ta ɗan noke kafada kasa kasa ta ce" Ba fa ta Aban larabawa ba, Mama dai Mama wace ta yi kira da safe, ina son jin yaya jikin nata"
A hankali yake kallon ta har ya ajiye hannunsa daga miko mata wayar, sai kuma ya dan dauke dubansa
Sun jima a haka har ta ga bafa zai ce komai ba, sai kawai ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta furta" i'm sorry"
Sannan ta mike daga saman cinyar tasa ta juya da nufin tafiya
Kasa hakura yayi, yana yadda yake din nan kasa kasa ya ce" ama ai dazu nace maki kar mu kuma yin maganar ko?"
Khadeeja ta dakata, a sanyaye ta juyo tana dubansa, a hankali ta furta" Kana nufin kar mu kuma yin maganar mahaifiyarka?, to wace magana zamu yi mai daɗin Tata?, ai inaga babu wata magana da ta kai Tata dadi ba......., idan har za'a yi kiran maman gidan Abanmu a ji sanyi a zuciya to kuwa za'a yi kiran Mama ta gidan nan a ji sanyin nan.........."
Ta ajiye a hankali maganar, sannan ta ɗora da fadin" in ba baban princesse ba, kwallon mangoro ai shi ke bada itaciyarta......., Anya kuwa zuciya zata dadada idan aka wayi gari litle na raye sai dai babu wani abinda ke hadata da mahaifinta? "
"An gaya maki babu abinda ke hada mu ne?, HAJIA karama bana son fitina da jan magana, duk wani abu da kika sani na duniya yana hada mu da ita, ko rashin lafiyar ai an je an Kaita asibiti , babu abinda na rage ta da shi a duniya, " Ya katse khadeeja yana dan fada da dan karfi
Da ace ba rainon gidan aba bace yannayinsa zai saka ta yi shiru ba zata kuma tayar da maganar ba, sai dai a yanzu sai kawai ta sada kai, kuka a duniya khadeeja ta yi na banzama bale mai dalili, tana dagawa hawaye ya gama wanke fuskarta a raunane ta furta " Ka yi hakuri.........." Sai kawai ta fashe da kuka ta ajiye wayar nan a hankali gudun fashewa ta juya da dan gudu gudu ta bude dakin bata rufe kan ba, bale ta ɗan yafa mayafi ta fice a dakin ta..........
😠😠😠😠. Daf nake da zane yar nan, koma saka hijab😕😕😕😕😄......., happy juma'at
46
07/12/2024, 17:30 - samiraharounayacouba: Ajiyar zuciya kawai Mama ta sauke ta mayar da hankali ta yi abinda yace din suka shigo tare da Abubakar ya kwashi kayan ya tafi kaiwa mota
A nutse take biye da shi har suka karaso wajen mota ya bude ya shiga
A tausashe bayan ta saka kanta kadan ta ce" Aban Sadik, dan Allah idan ka je ka GAISHE da baban, sannan dan Allah ka yi hakuri ka yi tunanin da kace zaka yi a kan lamarin yaron nan mai neman auren Karima"
Kai ya gyada bayan ya tabe baki ya ce" to gimbiya zan yi tunani a kan aurawa y'arki mai jan ido tunda kin dage kin kuma hanna yayanki zuwa dauko min fansa, wato an sakani a tsakiya sai dai in yi yakin Ni kadai....ba laifi ai"
Mama dai bata ce komai ba dan ta san ita ke so ya dubi maganar ta, domin ko a jiya da dare sai da ta zaunar da karimar ta yi mata tambayoyi a kan lamarin, kuma ta yarda cewa itama tana son saurayinta sai dai idan an hanna tarayarsu ne kawai, wanda hakan na iya haifar da wata ilar
Bayan sun tafi ta juya ta nufi baban falonsu a nutse
Tana shigowa ta tarar da Karima tsaye tana kallon amarya dake zaune itama tana kallon ta, sai dai yannayinsu kamar magana Amaryar ke yi dan a irin tsayuwar da karimar ta yi kamar wani abu Amaryar ta fada da ya sakata a wani yannayi na mamaki haka
Bata wani tsaya ba tana tafe ta ce" Karima babanku yace kunna iya biyawa ku ga jikin maman naku sai ku wuce gidan na anmy, dan haka idan kin gama ki dauki manyan kula ki zuba mata abinci na dubiya"
Karima jiki a sanyaye ta ce" to mama" sai kuma ta dubi amarya wace ta tabe baki tana yi mata kallon sama da kasa ta ce" Ba kin gani ba?, ana anfani da ke ana cutarwa mahaifiyarki da ke din da kanki, Karima kina gani fa, ke aka zabawa mijin nan Ama matar nan ta cira ta kullu ya juye kan y'arta, in har maganar gaskiya ake bi kafin y'arta ba lubna ce a tsakani ba? In abinda take miki nufin gaskiya ne cewar dan kin kiya aka bashi daya daga cikin y'an uwanki a kan me aka tsallake aka rasa wace za'a bashi sai khadeeja?, sai ki je ki zubawa maman naki abincin ki kai mata, salon gobe a yi mata gorin yunwa ace abinci sai an kai mata daga gidan tsohon miji, ke baki Sani bane a ciki ake barbada masifar dake hadasu fada har ya ringa zane maki uwa, kin wani zo kin zabi uwar wani a kan taki, ai sai ki karra hima "
Tana gama fada ta mike ta nufi cikin dakin cin abincin su tana dana wayarta zuciyarta cike da farin ciki da tunanin ko yayane zata saka kiyaya tsakanin gimbiya da yaran nan, idan ta ga irin yadda suke mata mama mama wani takaici ke kule mata zuciya, yan rainin hankali ita kuma sai dai su kirayeta da amarya, sai kace ba matar ubansu ba! Dan kuwa su samarin sarai ta kula wani gani gani suke yi mata, Bama kamar idan sunna yar rigima da gimbiya irin kallon da suke yi mata har tsoro ke ratsa ranta kar aje wata rana su maketa kamar ta taɓa mahaifiyarsu, ita da kanta gimbiyar in sunna waje ko me za'a yi bata biyewa dan da bakinta ta taɓa nuna musu cewar su guji idannuwan yara, yara fa sun girma, ba zata so a basu muguwar tarbiyya ba ko a basu wata kafa da zasu raina daya a cikinsu ba,
Karima ta dan jima a tsaye kirjinta na dokawa kafin ta juya jiki a mace ta nufi corridor din dakunan su
Lubna ta gani a tsaye rike da abaya a hannunta
Irin kallon da lubna ke yi mata ya sa ta ji gabanta ya dan fadi
Sai dai ta ga lubnar ta yi dan murmushi ta ce" Ke fa nake nema, ashe kina falo? Dan in ce maki ne mu saka wannan abayar ta wajen aba wace aka kawo mana a cikin kayan saudiyar da aka bugo masa, zamu fi yin kyau"
Karima ta yi murmushi ta nufi dakinta tana fadin" To"
Daga haka bata karra komai ba, ita kuwa lubna ta rakata da ido kafin ta juya ta shiga dakinta ta rufe ta zauna bakin gado
Ta jima tana dan tunani kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Allah ya sa wannan karon ki yiwa kanki adalci, Allah ya sa a cikin halayyar masu harin zuciyarki ki iya jajircewa ki dubi zahiri ki yiwa wace ke rungume da ke adalci Karima"
Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye rigar ta mike ta shiga shirin shiga wanka
Lokaci daya kuma ta sauke ajiyar zuciya hadi da murmushi mai tsada a lokacin da ta tuna firarta da mama a jiya da dare, tambayar da ta yi mata kan idan tana da wanda take so? Da ta tabbatar mata cewa babu, sai ta tambayeta shin zata iya zaman aure da ƴaƴansu na bangaren mahaifiyarta? Wato dan mijin mamanta ne baba, lauya ne mai zaman kansa , sannan dan kasuwa , kuma bai taba yin aure ba har yanzu dai yana jira ne tun lokacin da ya cewa babansa yana sonta akace yayi hakuri har ta girma sai yayi hakurin, kuma cikin ikon Allah aba ne da kansa da maman tace masa to lubna fa? Sai yace lubna ai da mijinta , shin ta manta wanda ya yiwa alkawari? Shi yasa ai ya zabawa AL'WALED khadeeja dake bi mata saboda ita da mijinta ai, .....abinda ya tsayar da lamarin aurensu suma na Karima da ummi ne kawai........., Ummi yace zai bata dama ta hadu da wanda ya zaba mata idan sun daidaita shikenan, Karima ce har yanzu ya ki ya ba saurayinta fuska, yaron kuwa kamar wanda ya fada jarabawa a kan karimar, hatta mahaifinsa jira yake yi yace an basu damar su nema masa aurenta dan kuwa sun gane da gaske yake ba da wasa ba.
A nutse ta shiryawarta, sannan ta bude dakin da ake ta buga mata ummi na fadan WALAHI zasu yi tafiyarsu ne idan bata fito na, dan kuwa har sha daya ta yi basu fita ba
Sai da mama ta yi musu nasiha sosai sannan ta ce" Ta yiwu ku samu su Fatima a cen, dan sun tafi su tuni da kayan nata, Allah ya dawo da ku lafiya"
Lubna ce karshen mikewa ta amsa da" amen mama, ai kuwa bari mu yi gaggawa saboda mu tayata ayyukan gyara kayan nan"
Daga nan suka karasa mota suka shige, Abubakar ya ja su
Mama ta sauke ajiyar zuciya ta yi murmushi, wato Karima bata zubawa mahaifiyarta abincin ba, bata wani rike a ranta ba saima zuwa da ta yi ta duba asibitin da zata yi aiki yau ta hau shiri saboda tana son fara fita aiki a yau.
Kofar gidan su Karima suka tsaya, suka fita gaba dayansu suka shiga gidan ba tare da sun sanar mata da zuwan su ba, domin Karima dai a yanzu ba waya a hannunta shi yasa ko uwar sai da ta bi ta wata hanya kafin sako ya samu gimbiya cewar bata da lafiya saboda ta sani ta hanyar nan kawai ce zata iya gannin y'ar Tata har su yi maganar da take so su yi, ba wani rashin lafiya kalau take, ta bi duk wata hanya ne dan ta samu gannin Karima abin ya gagara shine ta biyo ta nan ko a dace
A filin gida suka same su sunna shan innuwar dalbejiyar dake cikin gidan, kakar Karima na yamutsa tafasa da kulli, mamanta kuwa tana shan koko a kwano da ludayin roba
Gaisheta suka yi su duka , sannan suka tambayi jikinta
Kakar Karima dake mamakin gannin ya'yan elhaji ya'u su duka ta kalli y'arta a dan tsorace da tunanin yauwa ga dalilin da ya kawo ya'yan elhaji gidan nan gaba dayansu
Lubna a tausashe bayan sun zauna maman Karima na yi musu tayin kokon ta ce" alhamdulilah mama, ai sai da muka karya sannan muka fito ma"
Maman Karima ta tabe baki ta ce" Dama na san ai ba iya sha zaku yi ba lubna bismillar dai na muku saboda ido , ina zaku je haka?"
Lubna jikinta yayi sanyi dan ita ba haka take nufi ba, a hankali ta ce" Gidan anmy ne zamu je"
Maman Karima ta Dube ta a yatsine ta ce" kina nufin gidan khadeeja?"
Lubna ta dago ta Dube ta, ta dubi Karima, sannan ta dubi ummi da Sadik
Maman Karima ta girgiza kai ta yi murmushi ta ce" uhum, koda yake ai dama HAKANE idan mai kudi aka aura har uwar yarinya sai ta je bale yayunta, Ama kuwa elhaji ya bani mamaki da har zai tura ku gidan da kanwarku ke aure, koda yake ba komai shi din a gaban mai gidan kanwar taku shima ba kowa bane face mai neman arziki da neman sunna"
Abubakar ya dubeta da mamakin halaya irin na matar nan, sai kawai ya mike yana fadin" Ga dukkan alamu lafiyar ta samu, Allah ya sa a wuni lafiya, idan kun tashi ina mota"
Sai kawai ya wucewarsa dan ba zai iya zaunawa matar nan na zagin iyayensa a banza a wofi ba, shi yasa sam baya son harkarta, ta cika fitina da neman balaki, yaya za'a yi wai ka zagi uba a gaban d'ansa? Yana daf da ajiye fadan mama gefe ya fara tijara a kan darajar su WALAHI!
Yana fita lubna ta yi murmushi bayan sun raka shi da kallo ta ce" Allah ya karra lafiya maman gidan iya, zamu wuce"
Daga haka ta mike tana riko hannun ummi suka kama hanyar fita basu tsaya sun jira abinda zata ce Bama bale har