Showing 153001 words to 156000 words out of 190762 words

Chapter 52 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3973

ki, Nine zaki rasa Inna........ za'a maki abinda kike so, ama ki ga docter, zai zo yanzu idan ya bada magani ki sha shi"

HAJIA Inna ta turo baki tana dauke kai, ya bita da kallo cike da mamakin fushinta na yau, tabbas HAJIA Inna na cikin mutane masu sassaucin da ya sani a duniya wa'inda suka yi ƙaranci a rayuwarmu ta yanzu.

A hankali ya dubi Khadeeja da kanta ke kasa, fuskarta ya talabo wanda hakan ya sa ta dago idannuwanta da sauri ta saka duban ta a cikin nasa

Idannuwansa ya lumshe kasa kasa ya furta" A sassauta min, dan Allah a sassauta min hukuncina"

Hawayen da ya cika idannuwanta ya sake balewa, a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya hade hannunta da na Hajiya kasa kasa ya furta" ina zuwa"
domin Muryar Alhaji ya'u ce sama sama yana fadin" kai, innalilahi kai meye wai, bude idon bana son lumshe lumshen nan haka kaji ke yi su cuci mutun sai dai ka shafa ka ga sun bar duniyar, ka ga bude min idannuwanka, wai meye? Lafiya lafiya muka rabu da kai fa, waye ya taba min uba?"
Ya fada da karaji saboda irin yadda Alhaji Hamza ke shasheka kamar mai cutar athma

Alhaji Hamza Muryarsa na rawa ya rike hannun elhaji ya'u ya ce" wai ba zata sha magani ba saboda matar da ta kashe mata d'anta, wai ba zata sha magani ba bayan ciwonta ya tashi, mu tafi, mu yi tafiyarmu, kaini wajen Usainar larabawa in yi zamana a cen"

Talabarsa aba yayi hankalinsa na neman tashi ya ce" Kai ina, lumshe lumshen nan ne bana so, wace ba zata sha maganin ba, sai ta sha ko wacece Ni za'a dagawa hankali a sa ubana ya ringa lumshewa?, ka ga ringesa a nan in Shiga in ba wace ta ki shan maganin maganin ta sha in fito mu yi tafiyarmu, nima ba zan Barka ba kar a kashe min kai a min asara ina dalili!"


Yana aniyar ringesar da baba Hamza AL'WALED ya karaso ya tsaya yana kallonsu kafin ya gyada kai yana tabe baki ya karaso ya rike hannun aba dake zarro ido ya ce"
07/12/2024, 17:27 - samiraharounayacouba: Ta fice a dakin ta nemi sauka kasa, domin ta sakawa ranta in dai bai dakatar da ita ba zata tafi ta yi kwonciyarta wajen HAJIA Inna hankali kwonce ne, idan har zai iya yaki da zuciyarsa har ya bude baki yace wai ya tsayawa mahaifiyarsa dukkan bukatunta a tunaninsa bukatun nan na yau da gobe ne kaɗai uwa keda bukata a wajen d'a? To kuwa zata nuna masa itama aiki irin na yarinya da danyen kai irin na y'ar ya'u!

Shi da kansa bai gane cewa bin bayan yarinyar nan yayi ba sai da ya riko hannunta ya dauko ta daga kokarin saukar da take yi daga dwstr ya koma daki da ita ya zaunar da ita ba sai da ya saka idannuwansa a cikin idannuwanta da ta yiwa kalar tana daf da fashewa da kuka ya fahimta

Ido ya dan zarro mata bayan ya yi mata nuni da hannunsa ya ce" kar ki soma, kar ki saki hawayen nan su zubo"

Kai ta gyada sai kuma ta fashe masa da kuka ta shige kirjinsa tana matso kwalar dole a shagwabe tana furta" ba zan bari su zubo ba hawayen, ba zan bari ba, AM sorry elhaji karamihhhhhhhhhhhhhh"

Gaba daya neman fita a hayacinsa yayi, rikicewa ya nemi yi, du irin girman shekarunsa da tunanin cewa a yanzu a duniya babu, karya ne, ba'a yi ba ba za'a yi ba irin abin nan, gayanan yana samunsa ba tare da shi kansa ya fahimta ba

A birkice ya dago fuskarta ya share fuskar ya mika hannunsa ya janyo wayar tasa a hankali ya rubuta numbar mahaifiyarsa bai ko dubi lokaci ba ya aika kira sannan ya saka handsfree ya ajiye wayar a tafin hannunta

RINGIN daya jal wayar ta yi aka daga, sai dai yau ba'a fara yin magana ba sai saurarawa da aka yi ana jira a ji maganar mutun

Da ido khadeeja bayan ta langwabar da kanta ta masa alamun yayi Magana mana??

A hankali ya sauke jajayen idannuwansa a kan wayar, sai kuma ya sake duban ta, yadda ka san itace ke rike da wani abu da zai saka shi yin magana , tana sake langwabar da kanta ya budi baki a hankali ya furta " Asalamu alaikum"

Zumbur ta mike daga kwoncen da take a gadon alfarmar dake dakinta, a hankali ta furta" Wa alaika salam, gudaliya......, kai ne? Ya Allah, ya Allah......."

Sai kuma ta yi dif, da sauri ta furta " kaine ka yi kirana? Kai da kanka? Kana ina? Baka da lafiya ne? Wani abu ya sameka ne? Ina kake ne? Ina baba ne? Ina Hajiya Inna? Ina matarka? Kowa lafiya dai ko? Ina mamanka karama? Gudali kana ji na?"

A hankali ya lumshe idannuwansa, sai kuma ya mike da sauri ya fice a dakin gaba daya

Da ido ta raka shi rike da wayar a hannunta, ga maman sai hello hello take yi

A hankali ta furta" Alhamdulilah Mama, lafiyarsa kalau, yaya jikin ki?"

Shiru ne ya wanzu a wajen na dan lokaci jin Muryar mace

A hankali Mama ta ce" Alhamdulilah, na zata shine ya min magana, to ama ai babu mai kirana sai yaronsa kawai, shi kuwa bai jima da barin gidan nan ba tare da iyalinsa, Ni na yi zaton kamar muryarsama na ji....."
Maganganu dai a rarrabe, a sanyaye ainun, ga ajiyar zuciya wata na korar wata

A hankali khadeeja ta ce" Mama shine ya kira, mun yi kiran ki ne dan mu ji sauƙin jikin ki"

Ido mamansa ta bude sosai sai kuma ta saki murmushi hadi da hawaye a hankali ta ce" Gudaliya ne ya kira? Kai, ashe zai yi kirana? Alhamdulilah"

Khadeeja ta yi murmushi zuciyarta na sake karyewa da tausayin matar nan, a hankali ta ce" zai yi kira Mama, zai zo ma da kansa Mama in sha Allah zai zo da kansa ne Mama"

A hankali mahaifiyarsa ta kankame hannayenta Muryarta na rawa ta ce" Yaya sunnanki yarinyana? Ke ce matarsa ko?"

Khadeeja ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Eh, sunnanmu daya da ke Mama"

Mama ta sake bude ido da mamaki tana maimaita maganar khadeeja ta ce" kina nufin sunnanki Nana khadeeja?"

Khadeeja ta gyada kai a nutse ta furta " Eh"

Mama khadeeja ta langwabar da kanta a hankali ta ce " Ta yiwu baba ya yafe min, tunda a da cewa yayi ko mai sunana ba zai kuma bari a yi a gidansa ba, sai gashi ya aura wa jikan da ya fi so mai sunan nawa? Ikon Allah tabbas zuciyarsa ta ɗan sassauta min, ta yiwu tun da raina zan ga ya yafe min ne ko yarinyana?"

Khadeeja ta gaza sake bude baki saboda kukan da take ji na neman sake kamata

Mama ta ce" ina son gudaliya sosai yarinyana, kema ki so shi ɗan Allah saboda kiran nan nawa da kika sa yayi na tabbata ba ƙaramin tasiri kike da shi a zuciyarsa ba, dan Allah ki so shi, ama ki ji tsoron Allah kar ki yi masa mummunan so wanda bashi da anfani irin wanda na yiwa mahaifinsa "

A hankali khadeeja ta ce" Mama"

Mama khadeeja ta yi gaggawar amsawa

A hankali ta sake fadin" Mama, kowani bawa da yannayin kadararsa, ki yi hakuri Mama, ki yafewa baban litle, in sha Allah zamu zo"

"Ban taba kwonciya barci ba tare da na fadawa Allah cewar idan na mutu a cikin daren nan na yafewa gudaliya gaba da baya ba yarinyana, haka bana fara wuni ban fadi haka ba, Ni ce nake da bukatar yafiyarsa, nice nake da bukatar yarona a tare da Ni, Allah ya baki ikon saka shi dubana yarinya ta, Allah ya yiwa rayuwar aurenku albarka, kwarai kin sakani farin cikin da na jima ban yi ba, Allah ya nuna min ranar da zan ganshi a gabana"

A hankali khadeeja ta furta" Amen ya Allah "

Haka dai suka ɗan sake yin magana kafin su yi salama

Khadeeja ta jima a zaune tana duban wayar kafin ta mike ta nufi wajen kayan turarukanta

A nutse ta yiwa jikinta wanka da turare, sannan ta juya ta dauki hijabinta ta saka ta kashe komai ta bar wayoyin a nan ta rufe dakin nata ta nufi nasa zuciyarta na bugawa da tsoro, sai dai ta riga ta sakawa ranta cewa abinda bai kashe wasu ba, ba zai kashe ta ba,

A nutse ta tura ta shiga a hankali tana yin salama hadi da nemansa a dakin da tunanin ko baya nan?

A nutse ya kunna fitilar gefen gadonsa yana sake zuba mata jajayen idannuwansa

A hankali ta mayar da kofar ta rufe sannan ta nufi inda yake gabanta na faduwa a duk takun da zata yi dan kusanta kanta da shi

A hankali ya lumshe idannuwansa a lokacin da ta hayo gadon sakamakon hannayenta da ta saka a wajen fuskarsa tana kallonsa

Kasa kasa ta furta" Ka yi hakuri, Aban litle Please, ba zan kuma ba"

Hannunsa ya sa ya janyota da karfi har sai da goshinta ya daki kirjinsa ya sakata a cikin jikinsa sannan ya yi shiru

Irin yadda kirjinsa ke dokawa ya saka ta rintse idannuwanta a hankali tana shafa bayansa

Sun dauki lokaci a haka, har ta yi tunanin ko barci ne ya dauke shi? Sai dai rikon da ya mata a kirjinsa bai sassauta ba hakan ya sa ta gane idonsa biyu


Cen cikin kuryar murya ya furta" Ita ta sha maganin nata? Ko wannan ciwon ma kin shan zata yi? Yaya jikinta ne ?"

Khadeeja ta dago fuskarta tana dubansa, a tausashe ta furta" ai ta samu maganin ta , mama na jin Muryar ka sai da ta yi dariya na kashe kiran"

Idannuwansa ya lumshe yana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya sake matsota jikinsa yana jin wani irin nutsuwa na ratsa zuciyarsa, cen kasa ya furta" Ni menene a tsakanin hannayena da fatar ki hajia karamahhhhhhhh?"

Khadeeja ta yi sauri sake kallonsa, wannan karon ta taki rashin Sa'a shima ya bude idannuwansa a kanta

Da sauri ta lumshe idannuwanta a hankali ta furta " a'a fa, kai da baka da lafiya?"

"Na fada maki?, kalau nake ai, kuma so nake yi mu yi mu daga tumbin nan, idan ba'a yi aiki da kyau ba, ba zai dagu da wuri ba"

Ido ta zarro a hankali ta nemi juyawa, sai dai bai bata dama ba a nutse ya rabata fa hijabin nan kas akasa ya ce" aa, babu wani abin karuwa a bayan nan, nan din dai ya fi ....., kin san me?"

Khadeeja ta bude idannuwanta tana kallonsa

A tausashe ya furta" i love You......."

Khadeeja ta wara manyan idannuwanta a kansa.......
A hankali ya furta" haka kawai......, na tsufa, a wani taso min tsumi......, mu yiwa musulunci hidima hajia karama bani dama mu kashe arnan nan"

Murmushi ya kubce mata, da sauri ta boye fuskarta tana jin yadda yake yawo da hannayensa a sasan jikinta .........ya zamo tun tana jurewa har ta idasa shigewa jikin nasa ba tare da ta tuna azabar da ta sha a jiya ba,.....kai a matsayinta Na likitama ta ɗan cewa tana iya dake jure wata azabar kawai....mema ya fi ran baban litle ne? Sai dai jikin yayi tsamin......da wannan suka baje zance har sabo ya karra jadada tare da shedar albarka da tunatarwar kauna uwa uba gurnanin maza mai tsayawa a zuci (😭😭😭😭🥺😫😫😫😠😉🙁😁😁😁)


__________________________________




Washe gari kusan karfe bakwai da rabi

Mama ce ke kicin tana faman juya kunnun gyadar da za'a kaiwa baba Hamza , tana yi tana ankara da girkin da ta ɗora wanda za'a diba a kai masa da kuma wanda za'a ci a gidan dan kari

Shigowar aba ta hudu ce kenan yana kai kawo da wata tsangalaliyar jalabiyarsa fara da katon carbinsa yana lekowa yana komawa, wannan shigowar da yayi ya ja ya tsaya yana kallon mama dake ta aikinta ya ce" Rainani ma ake son yi, so ne ake yi a wulakantani kawai a kuma wulakanta min uba, sai da nace maki bashi da lafiya yau ki yi safiya ki masa kunnun nan ko zai sha, ama tsabar wulakanci irin naki gimbiya ga rana ta hudo tsuntsaye sun koma lambu ubana bai karya ba"

Mama ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" ka yi hakuri baban Sadik, girkin nan ne ke daukan lokaci wajen gyaransa, ama na gama ai dan Allah ka dan kara hakuri kadan"

Tsaki aba ya ja ya shigo da kyau yana fito da kulolin masu Kyan gaske da abin zubawar, ya juyo yana murmushi ya ce" gimbiya gimbiya, wadannan kwanonin yaushe kika siye su? A ciki zan kai masa saboda kallonsu kadai zai sa tsohon cen cin abinda ke ciki"

Mama ta ɗan dakata ta Dube shi ta ce" zaka kai? Wani irin zaka kai? Ama ka san yanzu anmy ke aure a gidan nan ko? Kuma mijinta na gari, ya zaka ringa shiga lokacin da ka so ne? Jiya fa nan ka ce min a gabansa ka ringa abin nan, haba baban anmy kar ka janyo mata magana mana, kuma ka manta ne jiya na fada maka yau za'a kai mata kayanta tare da sisters dinta harma na sanar maka maman kareema fa ba lafiya ya dace ta je ta ganta kace ai sai dai su je tare da yan uwanta kai baka yarda da ita ba?, yaya za'a yi daga kai yarinya sai mu yi ta shige da fice a gidan nan fisabililahi?"

Aba ya yi shekeke yana kallon ta kafin ya dage kansa ya ce" Ai sai ki yi, ku yan gargajiyar nan sai balakin saka ido, gimbiya ina daf da kai karar ki inda za'a min maganinki WALAHI, wajen uwata!, au yaushema Aka haifi hajiyar? Kafin ta zo duniya ma ina tare da ubana, zuwan ta babu abinda zai hanna, abinda bangarensa daban nasu daban? Ni tunda nake shiga Allah ne shaidata ban ganta Bama, Ama yau zan je in ga dakinta da kaina in sake fada mata idan bata yiwa elhaji karami biyayya ba ubanta zan ci, bari dai in saka dogon wando a kasa in tafi juye min duka kafff, kara mulda masa madarar nan dan so nake yi ya mike sak, babu mai kashe min uba!"







😉😉😉😉 Hello jama'a, kun san me? Da muka dawo ne comment ba karfi.....shine lamarin sai a slow...., Ama ga bonusssss



46
07/12/2024, 17:27 - samiraharounayacouba: Ajiyar zuciya kawai Mama ta sauke ta mayar da hankali ta yi abinda yace din suka shigo tare da Abubakar ya kwashi kayan ya tafi kaiwa mota

A nutse take biye da shi har suka karaso wajen mota ya bude ya shiga

A tausashe bayan ta saka kanta kadan ta ce" Aban Sadik, dan Allah idan ka je ka GAISHE da baban, sannan dan Allah ka yi hakuri ka yi tunanin da kace zaka yi a kan lamarin yaron nan mai neman auren Karima"

Kai ya gyada bayan ya tabe baki ya ce" to gimbiya zan yi tunani a kan aurawa y'arki mai jan ido tunda kin dage kin kuma hanna yayanki zuwa dauko min fansa, wato an sakani a tsakiya sai dai in yi yakin Ni kadai....ba laifi ai"

Mama dai bata ce komai ba dan ta san ita ke so ya dubi maganar ta, domin ko a jiya da dare sai da ta zaunar da karimar ta yi mata tambayoyi a kan lamarin, kuma ta yarda cewa itama tana son saurayinta sai dai idan an hanna tarayarsu ne kawai, wanda hakan na iya haifar da wata ilar

Bayan sun tafi ta juya ta nufi baban falonsu a nutse

Tana shigowa ta tarar da Karima tsaye tana kallon amarya dake zaune itama tana kallon ta, sai dai yannayinsu kamar magana Amaryar ke yi dan a irin tsayuwar da karimar ta yi kamar wani abu Amaryar ta fada da ya sakata a wani yannayi na mamaki haka

Bata wani tsaya ba tana tafe ta ce" Karima babanku yace kunna iya biyawa ku ga jikin maman naku sai ku wuce gidan na anmy, dan haka idan kin gama ki dauki manyan kula ki zuba mata abinci na dubiya"

Karima jiki a sanyaye ta ce" to mama" sai kuma ta dubi amarya wace ta tabe baki tana yi mata kallon sama da kasa ta ce" Ba kin gani ba?, ana anfani da ke ana cutarwa mahaifiyarki da ke din da kanki, Karima kina gani fa, ke aka zabawa mijin nan Ama matar nan ta cira ta kullu ya juye kan y'arta, in har maganar gaskiya ake bi kafin y'arta ba lubna ce a tsakani ba? In abinda take miki nufin gaskiya ne cewar dan kin kiya aka bashi daya daga cikin y'an uwanki a kan me aka tsallake aka rasa wace za'a bashi sai khadeeja?, sai ki je ki zubawa maman naki abincin ki kai mata, salon gobe a yi mata gorin yunwa ace abinci sai an kai mata daga gidan tsohon miji, ke baki Sani bane a ciki ake barbada masifar dake hadasu fada har ya ringa zane maki uwa, kin wani zo kin zabi uwar wani a kan taki, ai sai ki karra hima "

Tana gama fada ta mike ta nufi cikin dakin cin abincin su tana dana wayarta zuciyarta cike da farin ciki da tunanin ko yayane zata saka kiyaya tsakanin gimbiya da yaran nan, idan ta ga irin yadda suke mata mama mama wani takaici ke kule mata zuciya, yan rainin hankali ita kuma sai dai su kirayeta da amarya, sai kace ba matar ubansu ba! Dan kuwa su samarin sarai ta kula wani gani gani suke yi mata, Bama kamar idan sunna yar rigima da gimbiya irin kallon da suke yi mata har tsoro ke ratsa ranta kar aje wata rana su maketa kamar ta taɓa mahaifiyarsu, ita da kanta gimbiyar in sunna waje ko me za'a yi bata biyewa dan da bakinta ta taɓa nuna musu cewar su guji idannuwan yara, yara fa sun girma, ba zata so a basu muguwar tarbiyya ba ko a basu wata kafa da zasu raina daya a cikinsu ba,

Karima ta dan jima a tsaye kirjinta na dokawa kafin ta juya jiki a mace ta nufi corridor din dakunan su

Lubna ta gani a tsaye rike da abaya a hannunta

Irin kallon da lubna ke yi mata ya sa ta ji gabanta ya dan fadi

Sai dai ta ga lubnar ta yi dan murmushi ta ce"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login