Showing 30001 words to 33000 words out of 190762 words

Chapter 11 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

4014

ido ya ce" Wai wani d'an, nawa? na cikina? tarda saurayi? kan uba, to ai idan takamar ya'yan yanzu su ya'yan yau ne, nima d'an yau ne, kai ina, bude hanyar iskanci kennan, gimbiya me yasa du tunaninki na yan iska ne?"

Tagumin da ta rafka ta janye tana kallonsa ta ce" Ni ce y'ar iskar?"

Kai ya girgiza yana mata nuni da hannunsa ya ce" Ban ce da ke haka ba, tunaninki nace, kar ki hade min maganata saboda rashin tsoron Allah, ke yanzu idan nace yaran nan su fara zance kya yarda? haba jama'a wai menene yasa ne ba za'a bi fadar ma'aiki ba? me yasa karfi da yaji sai an koyi nasara? meye a zama zance banda a lalubewa mutun y'a? Au so kike yi in yi kisa kuma in shiga uku ko? wato so kike ki sakani a uku ko? "

Mama ta sauke kaffafuwanta daga saman gadon ta dauki hijabinta bata ce komai ba da nufin tafiya

da sauri ya sauko ya riko hijabin rai bace ya ce" Ga shashasha kin samu shine da na fara magana sai ki tafi ki barni in ci kaina ko?"

A tausashe mama ta dube shi ta ce" Sai da nace idan shawarar bata yi maka ba kace a'a baka amince ba shikenan an bar maganar , ama sai ka kama jaye jayen da bashi da anfani, ba tafiya nake yi dan in Barka ka yi ta magana ba, wace Ni din banza, tafiya nake yi saboda yannayin lafiyata elhaji, wannan abin ba zai haifar min d'a da ido ba, ka ga ba lafiya ta isheni ba, dan Allah ka yi hakuri ya isa haka ka yi hakuri"

Baba ya tabe baki ya matsa ya ce" To na ji, koma ki kwonta kuma ki bar maganar nan, kar ki kuma kawota dan Ni ba shashasha bane, yaran nan su yarda su yi mana, kin fa gani yadda na saka tsaro a kansu, du wani motsinsu a kan idannuwana yake, basu isa su aikata wannan sabon ban sani ba, du kuwa wanda ya yarda ya aikata Allah kadai ya san abinda zan masa, jeki kawai ki kwonta wannan maganar ma ai ta rashin ilimi ce sak ta masu ta'amali da koyarwar yahudu "

Tana jinsa ta yi shiru bayan ta kwonta ta bashi baya ta lumshe idannuwanta

A hankali ta sauke ajiyar zuciya a ranta ta ayana'" Allah, ya Allah yaya zan yi kennan? idan na fito na fada masa dalilina na tabbata a yau ba jikinta ba, nima nawa jikin sai ya gaya min, kuma na riga na gane dukan babu abinda zai gyara a rayuwar ya'yan nan, an kai wajen da duka baya ce masu komai........, da ace zai yarda da ya bani dama na basu damar kawo wanda ke son su da aure, idan har aka ga mutun da gaske yake shikenan sai a yi masa aurensa ya je yayi karatunsa a dakinsa, shikenan Allah ya raba mu lafiya da su, amma tsabar fitina irin ta wannan bawa naka ya Allah har cin alwashi yake yi a kan d'an yau? lalle na tabbata bai san su waye ya'yan zamanin nan ba da bai tarki cin alwashi a kansu ba, wai har fadi yake motsinsu a kan idannuwansa, ko wani motsin yake nufi, takamarsa in ya dawo da yama zai yi tambaye tambaye a anguwa da masalaci dan ya gane me ya'yan suka yi me basu yi ba, bai san cewa sun gama ganewa ba sunna boye Laifukan su daga idannuwan da zasu gansu su yadda su? hum lalle Elhaji '

Tana ta sake saken nan har barci ya dauketa, sai kiraye kirayen asalatu suka farkar da ita kamar wace idon kawai ta rintse ta bude......

haka ta sauko daga gadon tana motsawa da kyar, kwana a wajen Elhaji kennan maimakun ka samu hutu a'a, sai dai ka samo guzurin ciwo na damuwa.

A wannan ranar ma da shiga mai kyan gaske ya tafi, kuma bai shigo gida da wuri ba sai bayan sallar isha'i , ya dawo a gajiye tilis, sannan ya ki maganar daga inda yake, ama fuskarsa fesss da farin ciki ya kwonta, sai da aka yi sallar asubahi bayan yaran sun yi fatiha ya dube su da kula bayan sun gaishe shi ya ce" Karima, daga yau ina mai umartarki fita da nikaf, sannan ki karra kame kanki, daga yanzu zuwa kowani lokaci mai neman aurenki zai zo, ina fatan zaki nuna tarbiyyar da na baki ta yadda yana tafiya za'a yi komai a gama, ku tashi ku tafi Allah ya muku albarka"

Mikewa suka yi jiki du a sanyaye suka fice, Bama kamar Karima da Khadija

Ita Karima tsoro ne ya darsun mata, kar dai aje wani katon ustaz ne? kai da ta shiga uku domin du kudinsa ba zai taba iyawa da ita ba, ta ina zata iya rayuwa da ustaz? haba dai mafarkinta namijin da zai riritata tamkar a Film din Indiya, tana da burin fafadan namiji mai cikar zati, tana da burin kashe soyaya iya soyaya da mijinta, walahi tana so mijin da zata aura ya zamo uban romeo a duniyarta , ina lalle zata fara shirin gannin waye wannan? ga dukkan alamu ya gama mamaye zuciyar babansu, sai dai kashhhh zuciyar babansu ba zuciyar Karima bace!


Bayan yaran sun watse ya rage daga Hajia, sai amarya da baba a saman kujeru , shiru ya dan ratsa, mama na son tafiya sai dai tana da magana a bakinta, amarya kuwa dama yau ranar girkinta ce , bata da inda zata matsa ta bar wata ƙatuwar da mijinta!


Ajiyar zuciya mama ta sauke da kula ta ce" Ni babansu wanene wannan miji da aka yiwa Karima?"

Baba ya dubeta yana murmushi ya ce" Idan lokaci yayi kya gani mamansu, ki sakawa ranki dai kawai y'arki ta gama dace a duniya sai fatan Allah ya sa ta dace a kiyama"

Mama ta yi murmushi ta mike tana fadin" Amen, ama ka ji da kyau ba zai sakawa y'ar nan tsare tsare tun kafin ta je gidansa ba, saka nikaf ba laifi ama daga nan a tsaya iya nan"

Har ya daga murya zai yi sababi ya maido hannunsa ya talabe habarsa ya ce" Na shiga uku, na auro daidai da Ni, wannan mata kamar bata son albarkar tawa ma"

Amarya ta ce" Inafa, ina fa, ai albarka ta kowa ma bata so, sam ba zata yi albarka ba ai matar cen"

Ya dago da sauri yana kallon ta, haka kawai sai ya ji ai shi ta zaga, haka kawai har kasan ransa ya ji kamar bata kaunar sa, yana dubanta ya ce" Hajiar ce ba zata yi albarka ba?"

Amarya ta dube shi itama a dan zabure ta ce" abinda ka fada ne na talaba"

"Lalle kina daf da gane shayi ruwa ne, kika talaba? Hajiar? to idan bata yi albarka ba ai na kade, kar ki saki ki zagar min matar rufin asiri wace na tabbata yau ko bani da ko sisi zata zauna da Ni da tsufana da dukkan halayana, ke kuwa fa? ai kin san na san auren kudi kika yi, da da wani saurayin da ya fito ya kai Ni kudi neman aurenki ai ba zaki auri tsoho ba, bana son haka, in na zagi abina ki aka ido ki yi kallo bayan Ni babu wanda yake da wannan damar kin ji na fada maki!"

Gaba daya amarya sai ta rasa bakin magana, shi fa ya fadi maganar nan, ita kawai ta taya shi ne, ama shine zai nemi juye mata, kai innalilahi wannan mutun da baudaden hali yake.


Gidan Elhaji Hamza



Tafiya suke yi a baban filin gidan ta wajen shukoki, bayansu kake iya hange daga nesa zaka gane wanda ke rike da hannun dayan ya fi shi tsayi sosai uwa uba ya fi shi yannayin budewa nesa ba kusa ba, idannuwanka zasu tabatar maka bambancin shekaru ko na ciwo daga bayansu kafinma ka ga fuskokinsu

A hankali na gane Elhaji Hamza ne aka dan talaba , tamkar wanda ke ciwo? a'a ba ciwo yake yi ba, tafiyar ce haka, in dai a gefen ELHAJI AL WALID zai taka kafafuwansa

A hankali Elhaji Hamza ya ce" Baka gaji ba? ka sakeni mana malan in taka da kaina"

Murmushi kawai yayi ya sake riƙe hannayensa ya sake juya akalar tafiyar tasu

Elhaji Hamza ya ce" Kai na fa gaji, excercise idan ya wuce haka sai ku sabon jinni"

Sai a wannan lokacin ya bude baki a hankali ya ce" Shi yasa ciwo ke saurin kai malan bahaushe kasa, a Chaina tsofaffin sun fi masu sabon jinin kokari, ka kuwa san irin anfanin tafiya a jikin dan Adam?"

Aba ya girgiza kai ya ce" Du anfaninta tunda ba zata hanna mutuwa ba ai ta yi zamanta D'an nan, kai dai kawai gurzani na yafe maka"

Murmushi ya sake yi suka karra zuwa suka juyo suka nufi ciki, bangaren Hajia inna , har zuwa lokacin shiru kake ji tun daga filin gidan har falukan, ba kuma dan basu farka bane, a'a , sun farka kawai bakon gidan ne baya son bayaniyar da zata hada shi da ciwon kai shi yasa kowa ke zaunawa har ya bar gidan kafin su fito dan baya zama shi din mutun ne mai fita nema du irin yadda ya tarra kuwa

Kujerar da zai zauna ya ajiye masa sannan ya zauna daf da kaffafuwan Hajia da suke kumbure abin rashin tafiyar da take fama da shi

A hankali ya saka hannayensa yana dan dadanawa hankalinsa gaba daya a kan kafar

Shiru ya ratsa dakin, cen ya dago a hankali ya furta" Allah ya baki lafiya"

Hajia inna ta saki murmushi tana kallonsa, dama yannayinsa suke kallo daga ita har Elhajin,

ELHAJI ya dauke kansa , Hajia kuwa a hankali ta furta" Amen Al' WALID"

Elhaji Hamza ya sake juyowa ya mata alamun ta fara yin maganar da suka yi mana, ama sai Hajia ta yi shiru ta ki yi

Murmushi yayi ya ce" Ni wai in tambayeka, baka da damuwa da lamarin aure ne?"

Al Walid ya dube shi, a nutse ya ce" Inada mana"

Aba ya dan sake dubansa ya ce" Haba, Ni in ce, kaima zaka so a ringa yi maka girki, ana yi maka sannu da zuwa idan ka sauko"

Al Walid ya mike yana duban agogon hannunsa ya ce" Bani da wannan damuwar, sai dai wata"

Daga haka ya nufi dakin kurma, Aba kuwa ya zarro ido ya raka bayansa da kallo har ya shige ya rufo sannan ya maido dubansa kan Hajia wace take yar dariya tana kallonsa a tausashe ta ce" To in ba abinka ba, girki ko sannu da zuwa ai ba ta nan zaka hau ba, kawai ka fadi abinda aka yanke ka kuma yi umarnin a maka biyaya shikenan fa"

Elhaji Hamza yayi murmushi shima ya sake gyara zama ɗan ya sani mutuniyar zai yi jira ta shirya su fito ta yiwu su kama yawo dan hakane idan yayi tafiya ya dawo ba dai ya huta a washe garin ba sai ko zuwa kwana biyu haka kafin yake samun hutu

Al'walid na shiga dakin ya samu Kurma zaune tana mulka mai a fatar jikinta, tuni ta yi wanka har ta saka doguwar rigr abaya ta daidai shekarunta

bata ji karar bude kofar ba sai hasken da dakin ya karra ne ya tabbatar mata an shigo

Da sauri ta juya, dama du saurin nan da take yi dan ta je inda yake ne, domin da ya zo jiya ta yi barci kuma ba safiyar zuwar masa bangare ake yi ba saboda mutun ne mai bukatar space,, ko ba komai aikin motsa jikin da yake yi da kananun kaya zai sa a bashi fili har yayi ya gama dan ba zaka so kai da kanka ka same shi a haka ba,

Mikewa ta yi tana murmushi hadi da dariya da hannayenta ta ringa nunin farin cikinta da gagawa kuma ta karasa ta je ta rungume shi tana sake nuna tsabar farin cikin da take ciki

Murmushi yake ta saki tun daga kahon zuciyarsa har suka zauna a bakin gadon nan yana sake kallon fuskarta a hankali ya yi mata nuni da yarenta cewa yayi missing dinta sosai, kuma ta yi kiba bulbul da ita

Dariya ta bangalar ta ringa nuna masa irin abubuwan da take ci da hannunta da yannayin motsin jikinta masu dadi sannan ta nuna masa agogo tare da nuna masa waje, wanda hakan ya tabbatar masa nufinta su je wajen kosan nata na gado ta ci

Murmushi yayi ya gyada kansa ta dauko hijabinta ta saka ta karra zuwa ta kamo hannunsa tamkar wanda baya gani , dan in dai yana kusa da ita ko me zata yi sai ta riko hannunsa,
suka fice suka nufi dakin Hajia ina, itace a gaba ta shiga sai Yaren bebaye take yi ta cika dakin da ihun murna tana nuna musu babanta, wanda ya ja ya jingina da kofa ya harde hannayensa yana murmushi yana kallon yadda take ta kokowa da hannun Elhaji Hamza tana kwatanta masa babanta fa ya zo, shi kuwa da gangan yana zarro ido yana fadin a ina shi bai ganshi ba, sai da ya wahalar da ita sannan ya mata alamun shi tun jiya ya ganshi suka yi dariya tare, ta sake tunkaro mahaifinta zata kamo hannunsa ta kai shi gaban Hajia inna idannuwanta suka sauka a kan Mufeeda dake tahowa

Dakatawa ta yi dan nesa da shi kadan, shi kuwa yana jin Muryar mufeedan tana gaisar da mutanen gidan kamar haka take yi kulun , ya ki juyawa sai idannuwansa da ya dan sauke a kan Elhaji Hamza kafin ya dauke dubansa ya bata hanya ta shigo

Fuskarta tamkar gonar auduga, kwaliyar da ta dauka dole zata shiga ido, haka kuma tunda ta shigo sai ta rasa ina zata saka kanta dan farin ciki, sai sannu da zuwa take yi masa tana karrawa bayan ta gaisar da su Elhaji Hamza ta zauna nan saman cafet din sai sada kai take yi

Hajia inna da kula ta ce" Yarinyana kece da safe haka? koda yake karfe goma ta yi yanzun ai ko?"

Mufeeda ta sake sada kai a tausashe ta ce" Eh Hajia har ta gota, girki na yiwa bakon shine nake sauri kar aje ya karya bai ci nawa ba"

Hajia inna ta gyada kai ta ce" Allah ya yi albarka, ai kuwa bai karya ba kuwa"

Da sauri Mufeeda ta mike tana fadin" Bari in kawo nan sai ya ci a nan inna"

Hajia inna bata kai ga bashi amsa ba ya kama hannun Kurma wace ta zama kamar wace ke tsoron motsi a hankali ya furta" Ina zuwa"

A nutse ya shiga tafiya da kurma, Mufeeda na biye da su har sai da suka fito falon baba , a raunane ta ce" Mine......"

Kasantuwar shi kadai yake jinta ya sa ya dakata

Kurma ta ja hannunsa, sai dai jinsa a tsaye ya sa ta juyo ta dube shi ta hanyar daga kanta
Gannin wace ke biye da su ya sa ta yi gaba kadan sannan ta basu baya tana dan kallon kasa

A tausashe ta ɗan karra matsowa kusa da shi ta ce" Mine, bamu gaisa ba fa"

Ajiyar zuciya ya sauke kadan ya kalleta sannan ya juya ya yi gaba, dan kuwa ba zai tsaya Mufeeda ta bata masa mood da sanyin safiyar nan ba, ita ta san yaya suka yi da shi, tun shekaran jiya ya gama kwatanta mata ta daina irin haka, shi yasa ya nuna mata Bama sai ta zo ba, ashe tuni ta zo garin? ta yiwu ta sanar masa bai daga wayar da suke waya bane, but why ita ba zata yiwa abinda ya yanke biyaya ba? ta sani sarai baya son musu, ama take yi ko? fine!


Mufeeda kuwa jingina ta yi da dogon coridor din ta raka bayansa da kallo

Bak'ar jalaniya ce ya saka doguwa ama bata kai har idon sawunsa ba, ta dan dangale din nan kuma da wani wando dogo Dan ya dan leko kadan daga kasan jalabiyarma

Shigar jalabiya dai shiga ce da maza ke yi kusan koda yaushe, bai ci ace ta wani birge idannuwa ba, sai dai wannan shigar tasa ta matukar karbi jikinsa kamar yadda kowace shiga ke yi masa kyau, ko dan ya zamanto abincin ruhinta ne idannuwanta ke yabon dukkan motsinsa? a gaskiya Al Walid duniya ne, kuma na zaka taba bashi shekarunsa ba, in fa ba gannin wannan kurmar tasa ka yi ba sai ya fada maka cewar yana da y'a ka musa,
Jik insa mai kyau ne, ga ni'imar lafiya masha ALLAH, uwa uba hutu ga sport da yake ba mahinmanci .........Tabas zata ci gaba da jira, jiranta ba zai zamo na banza ba, kuma ita ta san yana son ta, haka kuma son da take yi masa ba na wasa bane......

Murmushi ta yi ta juya ta koma ciki kusa da Hajia inna, dan ta san duk tsiya zata ci albarkacin ta, ba zai taba yi mata wani wulakanci a gabanta ba, domin maganar kar ta zo shima wasa yake, ya san ba zai taba yiwuwa ba, ita zata yi wasa ta zauna ya mata wasa da rayuwa.............ko ketare da yake zuwa ba da ita ba ita kadai ta san halin da take tsintar kanta a ciki........ama lokaci, idan auren su aka daura yau an gama wannan wasan .




A nutse suka taka har wajen mai kosai

Tun kafin su iso ake miko masa gaisuwa da girmamawa da darajantawa, haka shima yana tsayawa su gaisa da mutane kafin yayi gaba har suka karaso inda tsohuwa mai kosai ta mike tana ta lalle lalle da Sarkin anguwa, uban talakawa da masu kudi lalle da baban masoyiya

Murmushi kawai ya mata, dan ta saba ba zata daina wannan kirarin nata ba, almajirai kuwa tuni suka layu dan sun san watan morewarsu kuma ya kama, zasu ci kosai su koshi kuma zasu samu kudin kashewa du safiya ta Allah har ya bar garin, shi yasa idan ya bar garin kamar sunne iyalansa sunna shiga damuwa sosai

Zama yayi a bencin da yaron shago ya dauko da sauri ya gyara masa da kyau , ya mika hannu suka gaisa a tausashe ya ce" Ya kasuwa sharhabil? ya Elhajin ya fito?"

Sharhabil ya karra rage tsayinsa sosai ya ce" Alhamdulilah Elhaji, eh ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login