Showing 111001 words to 114000 words out of 190762 words
Chapter 38 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
bale har ta barbada masa wata jarabar!
(Wannan kennan)
Jerin manyan motoci ne suka dira a kofar gidan Aba, tunda aka salamce sallar magariba , sun sha kwaliya irin ta motocin dauko amarya mai daraja
A cikin gida kuwa ana fitowa daga sallar magariba Mama FATEEMA ta gama shirya Khadeeja dake cikin zazzaɓi, domin har allura Mama ta yi mata da yama saboda zafin jiki da take fama da shi ga amai dake dawainiya da ita na tarin damuwar abinda take ciki, uwa uba idan ta tuna yau fa ana nufin za'a rabata da Mama sai kawai hankalinta ya idasa tashi
Mama na wajen su Karima tana rarashinsu ta ki fitowa domin ita ta fi kowa jin wani irin kewa da radadi a cen kasan zuciyarta, har sai da Muryar Aba ta karade falon yana gyaran murya yana kiran sunnan Maman kafin ta mike jiki a mace ta fito ta amsa shi, tana kallon sabuwar shigar da ya maka yanzunma,
Dubanta yayi ya saki murmushi ya ce" Ina y'ar albarkar? an fa zo daukanta"
Mama ta nuna masa dakinta murya a sanyaye ta ce" Tana ciki"
Aba ya dubi Mama ya ga da gaske hawaye take tarewa, ga mutane nan na gida su sunna nan, harta dangin amarya du sunna nan sai an kai amarya ne zasu watse, ga yan matan mama du sun fito, ya yi y'ar dariya kadan ya ce" Gimbiya kuka zaki yi? kar ki yi, yi hakuri, abinda a gari guda ne? kin ga dai ba ke kadai bace kar ki yarda wani abin ya samu abinda ke....."
Da karfi mama ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une"
Da sauri ya juya, dan wa bilahilazi ya zata wani abin ya shigo gidan, sai ya ga wayam, ya juyo yana kallonta ya ga da sauri ta yi gaba ta nufi dakin nata ta shige ta mako kofar
Ido ya zarro ya sake kallon mutanen dake kallonsa ciki harda amarya da ta zarro idannuwanta kasa kasa ya ce" Anya matar nan kalau take kuwa? ita uwar Anmy din?"
Amarya ta juya da sauri idannuwanta har sunna rufewa ta nufi dakinta, matan kuwa dake wajen sai suka shiga rangada guda sunna dariya, shima ya dage kafadu ya nufi dakin nata yana fadin" Daga yiwa y'a aure sai ki rikice? Anmy kam dakinta zata kwana yau gaskiya in sha Allah"
Mama dake zaune tunda ta shigo Anmy na kwonce a jikin cinyoyinta a hankali ta sake shafa kanta kasa kasa ta ce" Na hada maki box din magungunnanki da alurai, ki cire damuwar dake ranki Anmy, abinda kika san dole ne zaki daga min hankali har haka? haba Anmy aure ne fa, kuma a gari daya muke, ki yi hakuri mana"
Mama FATEEMA ta mike sakamakon shigowar Aba zata fita, Aba ya dubeta ya ce" Yi zamanki maman Hajia karama, ai ba za'a jima ba zaki kai y'arki dakinta"
Ya karasa ya zauna ya zamo sun saka Khadeeja a tsakiya, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Khadeeja, bai san me yasa ba yake ji a cen cikin zuciyarsa sai ya yiwa yarinyar nan da gaske, bai san dalili ba yake ji a ransa yanzu ne ya dace ya karra yin sallar dare dan nema mata tsari a wajen Ubangijin samai da kasai....., yana ji a ransa kamar da wahala sabuwar rayuwar Tata bayan ya san a hannu mai kyau ya sakata
A tausashe sosai ya ce" Anmy, taso ki ji"
Khadeeja da ta dauke kukanta tunda ya shigo ta dago a hankali, rufar da aka yi mata na yayewa, ya zamo gashinta da ya sha wanki ya bayyana domin ko kunshi ba'a yi mata ba, mama FATEEMA tace gobe in sha Allah zata kai mai kitso da kunshi
A tausashe ya ce" Ki yi hakuri kin ji? ki daina kukan haka , in sha Allah yadda na yi gaban kaina da ke kika yi min biyaya sai kin ji dadin auren nan, kuma sai y'ayanki sun maki biyaya kema da izinin Allah...."
Mama fateema a tausashe ta ce" Allah ya amince"
Aba ya dora da fadin" Anmy, za'a kai ki gida mai dauke da jama'a, baban gida ne da ya tara mutanen da suka ninka na nan, kin ga kuwa zaki hadu da kowani irin hali a ciki, abinda nake horonki da yi shine ki rike tarbiyyar da mahaifiyarki ta ɗora ki a kai, Anmy ki yiwa mijinki biyaya, ki girmama danginsa, ki bi su sau da kafa, ki yi hakuri ki rike adininki in sha Allah Allah ba zai jarabceni a kanki ba, in sha Allah Allah zai hada hankalinki da na mijinki, in sha Allah zaki ji dadin zama tare da danginsa kin ji?"
Khadeeja ta gyada kai, idannuwanta sun kumbura dan kuka, a hankali ta bude ta kalli mahaifinta, sai kawai ta fashe da kuka ta ɗora kanta a saman ƙafarsa
Elhaji yayi tsuru tsuru ido na cika da hawaye, ya juyar da kai ya yarfe yana sake hade fuska dan kar a yi abin kunya, a hankali ya ce" Ki rike azkhar, duk rintsi ki tabbatar da kin rike Allah daya , ko menene ki roka wajen Allah, sannan idan abu na neman fin karfinki ki sameni kawai in sha Allah zamu yiwa tufkar hanci"
Ya idasa maganar a tausashe sai kuma ya dubi Mama da kanta ke kasa a hankali ya ce" Nace ki bar kukan nan Gimbiya ko dan abinda yake....."
"Kai kai kai, innalilahi wai dan Allah ba zaka rufa min asiri da maganar nan ba, ...." Sai kawai ta mike ta yi waje ta nufi dakin su KARIMA suka hadu suke kukansu na rabuwa da Khadeeja domin yace yan matan ba zasu je kai amarya ba, sai zasu je gidan daga baya dan kar a daga mata hankali da yawa domin kukan da take yi idan aka ce za'a tafi a barta tabas wani abin ne kuma, iya iyayenta ya yarda su bita, sai yayunta da ya wakilta biyu da zasu riketa dan yace a tabatar da mama fateema ke janye da mayafinta, Muhammad da Sidik kuwa su sakata a tsakiya, haka ya tsara abinsa
Aba ya sake kallon hanyar da mama ta bi zuwa yanzu ya gane salatinta na dazu, sai kawai yayi dariya yana kallon Mama FATEEMA ya ce" Au, ikon Allah, ki ga fa sai kace wace ta kunso shege, kama y'arki FATEEMA ku je , Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci, ke daina kukan nan kin fa fara isata, aikin banza abinda gobema ina shago kuma gidan naki kusa da ni ne?"
Mama fateema ta saki yar dariya tana fadin" Au, tototo ikon Allah, to ai shikenan Allah ya bada lafiya"
Khadeeja kuwa ita ba ta wannan take ba ta yi shiru tana ji tana gani aka lulubeta Mama FATEEMA na rike da ita, yayunta da suka sha dakakiyar shada suka sakata a tsakiya suka fito aka sakata a motar da aka kawo ta amarya suka dauki hanya kanta a saman kafadar Sidik ta rike hannunsa gam hawayenta wani na korar wani tana jin karar tafiyar motoci da odarsu na daukan amarya, auren da nan da kwana biyu bata san ya tabbata a kanta ba, gashi dai ya tabata, karin tashin hankalinta shine harta kanshin cikin motar ban tana ji ta gama gane ba karamar mota bace, ire irin motocin da babansu ke kira mai numfashi ne, innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ita kam ina zata je???
A kofar gida su Aba tsaye suke da yan daidaikun mutanen da suka rage da sauran samarin ya'yansa, Mudansir ya karaso yana dan rabewa tunda ya sauka daga mota ya duka daga nesa yana gaisar da Aba hadi da fadin" Dala zuwa yayi dan yayi Barka da watse taro Allah ya bada zaman lafiya"
Aba ya sake zuba masa ido, kasa kasa ya ce" Kai dan baba wannan kamar dan daudun nan?"
Nasiru ya kalli Mudansir a hankali ya ce" Baba ba dan daudu bane ba fa, Mudansir ne wannan dai na gidan Elhaji"
Aba ya gyada kai ya sake kallonsa ya ce" Oh to mai jan ido, sannu, daga ina ake ?"
Mudansir ya sake sada kai a hankali ya ce" Baba dan Allah ka yi hakuri, dan Allah ka yafe min, ka ga har aski na yi na sauke gashin nawa kuma na daina saka wandon azdawn, dan Allah ka yi hakuri"
Aba ya ce" To to, masha Allah, to tashi mana"
Mudansir ya mike zai sake yin magana kennan jerin motocin su Mufeeda suka karaso kofar gidan Aba
Tunda Baba Hamza ya yiwa Aba maganar hadin auren yarinyar wajensa da Elhaji AL'WALID Aba ya sakawa motocin su Mufeeda ido, wato ko numbar motarsa bai hardace ba kamar yadda ya hardace tasu, dan idan suka zo shiga har fitowa yake yi yayi tsaye yana kallo har su shige ya koma ya zauna yana tabe taben baki da ayana abubuwa kamar su an yi asara da ake tardo namiji, da su ko dai marainiya ce yarinyar nan bata da uwa bata da uba bata da dangi bata da abokan kwarai da zasu yi mata fada? da su aikin banza su za'a nunawa mota? dai da sauransu, hakan ya sa motocin na tsayawa ya gane su harma ya tuna da maganar dazu
Ido ya zarro ya kalli Nasiru a lokacin da aka bude mota mahaifin Mufeeda ya fito cikin shiga ta kece raini, kasa kasa aba yace" Kai Nasiru shadata dai bata yamutse ba ko?"
Nasiru ya dube shi da tunanin shadar sabuwa dal da aka saka yanzu yanzu me zata yi to? zai sake yin magana Aba ya gyara zaman hularsa a kansa kasa kasa ya ce" Shiga ciki ka yi sauri bayan motar wajen gimbiya akoy kotar nan da na saka mata wace nake koya mata fada da ita, dauko min ita, Nasiru idan ka yarda baka fito yanzu yanzu ba yau ko uwarka gimbiya ba zata iya amsarka a hanuna ba!"
Ido ya zarro da gudu ya juya, sai dai yayi ciki da mugun gudu yana ihun fadin" Mama, mamanmu Aba yace a bashi kotar motarki walahi gayacen kar yayi kisa ya saka ki a uku, Mama"
Mama ta zabura tsaye ita da su Karima suka yi waje, hakama su amarya suka fito da gudu, haka kuma Nasiru ya je da gudu ya dauki kotar yayi waje ya kai dan gaskiya ba zai yarda ya ki kai kotar nan ba, ko yayane Mama na tafiya ta barsu da aba watarana, idan har yace zai kama ka kuwa kyaleka yake sai babarka bata nan ya nadi banza amarya nata ido ne
A lokacin da suka fito suka samu ELHAJI Maiga da masu tsaronsa biyu a gaban Aba, Elhaji Maiga bayan ya gama bin kofar gidan Aba da kallo bayan salamar da ya masa da isa yace" Dan Allah gidan Elhaji Ya'u nake tambaya"
Aba ya ce" Nine ai Ya'un eh Nine, Wadinnan kuwa y'ayana ne, wancen kuwa saurayin yarinyata ne, eh mai jan ido shine"
Elhaji Maiga ya dube shi da kyau domin yannayin da yake yin maganar kamar da raini raini ko mema zai kirayi abin?"
Mama kasa kasa take kiran elhai? ama yayi mirsisi dan shi Baima gansu ba a bayansa suke a labe sunna dan lekowa sunna komawa ne, ita da amarya ne suke gaba gaba
Elhaji Maiga ya ce" Ok, ina son magana da kai mai mahinmanci ko zamu shige ciki?"
Aba ya girgiza kai ya ce" A yi a nan, idan an shiga ciki ana iya katse min hanzari ne ai"
Duk yannayin Elhaji Ya'u bai ankarar da Elhaji Maiga waye a gabansa ba, sai da ya dan tabe baki ya ce" Dama dangane da y'arka ce da ka aurawa Elhaji al''''''''"
Du girma irin na Elhaji Maiga, Aba bai gani ba ya sauke masa yan yatsu biyar ido waje ya kwashe babar rigar da ihu ihu yace" Y'ata? y'ata ka ambata, la ila ha ilalahu, Nasiru zaka ban kotar ko sai na ci ubanka "
Abin ya zo musu a mugun bazatar da ya sa suka nemi gigicewa, Nasiru kuwa ya danka masa kotar, a lokacin da masu bashi tsaron suka so shiga suka ga kota rike da ihu suka ringa tura Elhaji Maiga da tumbin ya hanna shi gudu, shi kuwa Aba ya aniya sakar masa rankwashi a molon kai har sai da suka saka shi mota Elhaji Maiga na maida numfashi Aba ya dan turo kai ya ce" Ka ga, idan bakinka ya kuma ambaton Anmy sai na........."
Kwal shima ya sakar masa rankwashi da ihu ihu yana fadin "innalilahi ashe mahaukaci ne? mu je mu je ku tashi motar mu tafi!"
Aba ya dafe kai bayan ya auna musu kotar nan ya daga murya yana fadin" Ka cira bata nuna ba, ka zo ka kawo gayata, ka jirayi nawa zuwan dan sai na amsa gaya!"
Ya juyo ya ga har za'a yi masa taronsa na kansa domin har an fara tsayawa kallon ikon Allah su da abu baya zama sabo a wajensu!
Idannuwansa suka sauka a kan amarya, domin bata san cewa Mama ta juya ba da ya'yanta tunda ta ga ya kwashe babar rigar, ita kuwa ta tsaya gannin abinda ya turawa buzu nadi
Aba ya murza ido yana kallonta ya ce" Innalilahi, ke ji sababi ke kuwa uban me kike a cikin karti?, a gabanki aka min rankwashin? innalilahi wa inna ilaihi raj'une, Gimbiya, gimbiya an wulakantani an min rankwashi a gaban yarinyar nan, kai ku kuwa uban kowa ya watse!"
Ya fada da hargagi a lokacin tuni amarya ta fada gida da gudu tana haki ta yi dakinta shi kuwa ya nufo gidan sama sama yana fadin "
😒Bama zai bari yan kai amarya su dawo mu ji yaya suka baro Anmy baiwar Allah ba, Bama zai bari mu ga yaya aka amshi Anmy ba, ba zai bari mu ga yaya za'a hadu ba, Bama zai barmu mu ga shaukin ba🙄🙄🙄🙄 kai! kai dai Elhaji Ya'u Allah shiryeka😒
07/12/2024, 15:14 - samiraharounayacouba: *FARKON GANIN IDONA*
PAGE 32
TALLAH TALLAH TALLAH TALLAH
*Zumar 3in1 zumace ingantacciya mekyau megyara jiki sosai zatasaka kayi bulbul breast sugyaru hips yafito kiyi yar duma duma hajiya bazakigane abundanake fadaba dai kinshata zakigane*
*08030861857*
*Zumar breast Zumar hips duk munadasu masu inganci sosai da sosai*
*Akwai pills na 3in1 shima aikinsu Daya da zumar 3in1 gawayanda basashan zumane mukayi daminsu*
*08030861857*
*Infection flusher Ingantacce maganine mai magance dukwata matsalar mara Kai harda rashin haihuwa yanayi banahaufi akai don angwada angani mace indai rashin niima ne na cutar sanyi yararaketa kuraje kaikayi dattin mara zonabaki infection flusher kisha mamaki yar uwa Insha Allah zakigodemin*
*Kayanmu guarantee ne sai angwada akansan nakwarai location gombe munaturawa koinah Insha Allah* *08030861857* Kira KO WhatsApp Insha Allah
Mama dake zaune a falo ta buga tagumi ta dago tana kallonsa, daga shi sai rigar ciki hannunsa rike da babar rigar, dama bai jima da korar babar yarsa ba yace ba zata kwana ba ta je dakinta in kuwa hauka ake ta kwana, haka mijinta ya zo ya dauketa suka tafi yana yi mata dariyar kayan da ta kwaso wai ita ana biki a gidansu
zama yayi daf da Mama ya ce" Gimbiya ana wulakantani a kasar nan, tashi zaki yi tunda an gama auren Anmyn mu je ki samo mana jujun da zai ci min uban mutanen nan biyu, kin ga da uban mai jan ido, da kuma uban wannan mararsa mafadan? sai na yi shara'a da su, Ni zasu wulakanta? gimbiya kin ga har gida ya kawo min farmaki ya sakar min kwonda a kai sannan ya dakar min tumbi innalilahi wa inna ilaihi raj'une "
Mama ta sake saka dayan hannun ta talabe habarta , sai kawai ta fashe da kuka wiwi har tana ɗora hannun a saman kai
A rikice Aba ya mike yana fadin " Kalu innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ke kuwa meye haka? wannan ai shashanci kennan dan kawai kin aurar da yarinyar maimakun ace warhaka muna nan muna cin tsire sai ki dora mana kukan sababi? gaskiya wannan bai dace ba aure fa kika yiwa y'ar nan Gimbiya!"
Mama ta mike bata bashi amsa ba ta yi ciki tana rusa kukanta, har ga Allah idan ba kukan zata yi ba me zata yi? wannan mutumen so yake yi ya kasheta, shi kulun baya rasa abin yin dambe? ace yanzu yanzu aka tafi kai y'arsa dakinta yan rakiya basu dawo ba ya kwabe babar riga ya daku? wala haula wala kuwata ila bilah, ina zata saka mutumen nan? kai Dole ma su rabu, rabuwar dai zasu yi, aikin banza aikin wofi
Aba kuwa da ya rakata da ido sai ya tabe baki ya juya ya yi tafiyarsa saboda ai abin arziki suke ciki yau, ba zai tsaya a mayar da shi shashasha ba ana masa kukan godiyar Allah ba, aikin banza dariya ake yi ba kuka ba idan aka ji dadin duniya, bari ya koma yayi jiran su Fateema su dawo ya ji yaya suka baro y'ar albarka? Allah dai ya yiwa haihuwa da irin arziki albarka.
A gidan Baba Hamza
Baban get a bude yake, hakan ya sa sunna zuwa suka ringa shigewa da gudu har suka layu a wajen da suka tsara zasu layun
Masu guda na yi, masu daukan vidio na yi a lokacin da yaya Sidiku ya bude ya fito da Khadeeja yana talabe da ita a hankali ya furta " Anmy, kar ki fadi fa, ki daina kukan nan kuma alkur'an zan kifa maki mari"
Muhammad ya dan harareshi kasa kasa ya ce" Easy mana Habu, ka barta ta zuba bacinta yau ai ranar ta ce"
Mama FATEEMA da ta gama gyara jakar Anmy ta hannu da ta riko a tausashe ta ce" To bismillah, kar ku manta ta yi addu'a a duk wajen da za'a shiga, kuma ku tayata, mu je"
Ya zamo yanzu Mama FATEEMA na take sawayensu ne dan zata fi gani da kyau, su kuwa samarin gidan Aba sunna talabe da kanwarsu suka nufi matan gidan Elhaji Hamza dake zazaune domin Imane ce ta sanar da su nan za'a fara zuwa, sai su yi musu jagora zuwa dakin Hajia inna, daga nan sai a kaita dakinta
A hankali suke tafe da ita har suka karaso gaban kakanni da iyayen AL'WALID
A nutse suka duka da ita a gaban iyayen bayan makeriyar