Showing 66001 words to 69000 words out of 190762 words
Chapter 23 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
sha Allah gimbiya, yana Dubai ama matarsa ta tabatar min yana Niamey jirgin gobe na safe zai shigo ya karaso, mu kuwa in sha Allahu goben karfe goma a nan zata mana mu yi jiransa"
Tsabar takaici mama bata ce masa ci kanka ba, hanya kawai take kallo har suka karaso gida ta fita ta bude baya ta kama Karima ta fito da ita, zata riketa su shiga ciki Aba ya ce" saketa dan ubanta saketa kar ta lalata maki lafiyar jiki da ta kwakwaluwa shegiya mai son masu jan ido, ke mike ko in karya ki"
Ai da sauri Karima ta mike daga duku dukun da take yi ta yi cikin gida da gudu tana sakin wani kukan
Mama ta zuba masa ido kafin ta tabe baki ta ce" Elhaji daidai nake da kai, daidai nake da kai ka san da wannan, kuma maganar da zan fada maka babu mai kai Ni neman aure bayan ni ke da y'ar, ubansa zai zo a bashi a mutunce ba mu zamu je ba, ka shafawa yarinyana lafiya hakanan laifi ne ta yi an yafe mata , karma ka shigo da maganar nan sauran su ji dan ka sansu da tsokanar junna, kuma su da kansu a kiyayewa kunnayensu jin hakan saboda tarbiyarsu"
Tun a nan Aba ya rike kugu ya ce" Eh to yayi uwata, nace sannu uwarmu, ke yayanki kikam haifa banda Ni, an fada mai son masu jan ido, ya yi hajia madan, kin manta mai daraja ake tarawa kasa ko? kika san ko ta jima tana zuwa neman auren nasa ita? Ni ai d'an yau ya watsan kasa a ido, kaf sai kin duba min su yaran nan kar in dauka in ba mutanen kirki a zageni"
"Babu wanda zan duba, ka ci gaba da daga murya yan anguwa su ji a watsammu a social media a ฦi auren ya'yan naka su taru su kasheka a gidan, kuma in fada maka gaskiya ashe auren jari zaka yiwa Anmy, sai ka fada mai kudi kake son ba y'ayanka in sani mana, ana wani danewa bayan komai a bayane yake. mai kudi aka lalubo ake wani kwana!" Ta karashe tana buga kofar motar tasa da karfi ta yi cikin gidan da sauri dan ta kula ciwon balakinsa ba mai warkewa bane
Turus yayi yana kallon kofar gidan, sai kuma ya juyo ya karewa wajen kallo, ya ga babu mai kallonsa sannan yayi ciki yana ihun kiran sunnanta.............
(Wannan kennan.)
Tun karfe takwas na dare bayan an yi sallah Mufeeda ke zaune a falon gidansu na Damagaran tana duban agogo tana kuma duba wayoyinta dake ajiye, ama shiru, ba kukan waya, ba karar bude gettttt ba salamar mai gadi da sanar mata hasken idanuyarta ya karaso
Wayarta ta dauki kuka, ta rarumo da sauri tana dagawa, dan ta yi tunanin shine, sai dai gannin sunnan kawarta ya sa ranta ya sosu ta daga tana duban akaifunta da suka sha gyara a kasalance ta ce" Kawatah "
Itama kawar Tata da isa ta ce" Mufee, ina ta nemanki a whatsup bakya online ina fata lafiya?"
Mufeeda ta sake duban agogo a hankali ta ce" Ina nospa ne kawata, kin san yau mine zai kawo min ziyara, bani da time din waya"
Kawarta ta saka murmushi tana fadin" Dole ne, hajiata ba zaki yi lokacin waya ba, honorable ya zo gari ashe? wauh, wauh bari in barki, ama kawata wai ina labarin y'ar nan tasa? wai haka zaku yi aure ku tare gida daya da ฦatuwar budurwar yarinya ta hanna ki yawo da karamin skettt?"
Ta tabe baki wani haushin kurma na tukota, sai kuma ta yi warrrr da idannuwanta ta ce" No plz,.kema kin san in dai an saka rana sai mun yi zaman makokin yarinyar nan, dan ba zai yiwu ba, haba dai a kurumcinta sai na karra mata shiru, yarinyar musakiya ce fa, bata magana , sai shegen sonta da yake yi ko meye na so a musaki?"
Kawar ta dan zarro ido ta wayar ta ce" Wai ban gane ba, sakawa zaki yi a yi kidnaping dinta ko me?, kawata baki da mutunci fa, idan aka yi mata wani abu ai ba zaki mori amarcin da kyau ba duba da hankalinsa tashe ko?, kuma kike maganar so kahon kyale ne fa, ko yaya yarsa take shi ai yana sonta, bale an ce ya so Mamanta sosai fa?"
Takaici ya sa Mufeeda datse kiran, dan ta tsani tuna mata da ake yi cewar hasken idannuwanta ya so uwar kurmar nan, hum, wai kidnaping kidnaping ai ana kyautata zaton a samu mutun da rai, .....ina zata yi wanann saken?......idan lokacin yayi zata san abin yi, ama ta san cewa matsalar sai ta girmami kidnaping, sosai take jin haushin yarinyar nan, dan ta san sai ta zama a tsakaninsu da mijinta idan aka yi aurensu, abinda ba zata lamunta ba kennan, babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu
Sake duban agogo ta yi, gannin tara ke neman yi sai kawai ta mike da dogon takalminta ta nufi waje tana kiran sunnan kanwarta tace da ita ta tafi gidan su AL'WALID
Ita dai kanwar by kawai tace mata dan ta san ko me zata ce mata ba zata saurareta ba a kan AL'WALID!
Mota ta shige da kanta ta ja ta dauki hanya, tana tafe tana ayana' idan baka zo ba Ni zan zo, tunda furta yau zamu ga junna sai mun ga junnan, tunda ka zo baka bani minti goma nawa na kaina ba, kulun kai cikin uzuri, ka ga damar yau dinma ka ki nemana, ba zan iya barci ban ganka ba'
Tana karasowa aka bude mata da aka ga ko Wacece
Tunda ta dano hancin motarta ta haske su Kalisat a jikin wata mota a tsaye sunna zance
Abinda ya bata haushi dariyar da khalisat ke yi , shi kuwa wanda ke tsaye kusa da ita yana zance wanda kana gani zaka gane maganar tasa ce ke sakata nishadi
Sai da ta zo gaf da su ta taka birki wanda su duka sai da suka tsorata kuma suka kasa guduwa dan abin ya zo musu wani iri
Bude motar ta yi ta fito ta bar wayoyinta a ciki sannan ta rufe ta dakata da ky din motar tana kare musu kallon raini
Khalisat ta dauke kanta tana duban saurayinta ta ce" Bab kana magana, ci gaba"
Saurayin nata ya sauke ajiyar zuciya ya dubeta zai yi magana Mufeeda ta ja tsaki ta tofar da yawu sannan ta juya ta nufi bangaren AL'WALID kanta tsaye
Wani irin bacin rai ya rike kirjin khalisat ta juya ta nufi cikin gida bangaren iyayensu tana saka kukan da ya fitar da mahaifiyarta daga daki, wato aminiyar maman karima
Khalisat na kuka ta ce " Mama, walahi walahi wannan abin ya isheni, Mama idan ba zaki iya yin magana a bar wannan wulakancin ba gwara mu bar gidan nan, domin idan har aka yi auren Elhaji karami da wannan mufeedar ruwa sai ya gagaremu sha a gidan nan, irin yadda take wulakanta mu, ki duba ki ga da ta shigo kamar zata take mu da mota , kuma ta fito ta watsa mana yawu ta yi gaba, walahi mama a kashe sai in kasheta dan ba fin karfina ta yi ba, muna kallonta ne dan ga wanda ya kawota gidan, ama ita har ta iya masifa ne?"
Ran uwar ya ษaci, dan kuwa kulun kokensu kennan, yarinyar nan ta fitine su tun kafin ta shigo, sai kawai ta juya bata ce komai ba ta nufi waje a ranta tana ayana' Yau bari in samu mai kankat din in fada masa damuwarmu, idan bai dauki mataki ba mu sai mu dauka in yaso a Korea mu daga gidan, tunda Elhaji yana ji yana gani ake wulakanta mu!'.
...............
07/12/2024, 14:53 - samiraharounayacouba: ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*FARKON GANIN IDONA*
๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*๐ณ๐ช
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you ๐*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ฦAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAฦIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na sha tara (19)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ
๐0912 262 1080
LABARI
Hajia zainabu na gaba, khalisat na Binta a baya basu zame ko'ina ba sai bangaren AL'WALID, domin Bama zata yarda baba ya ji ba, dan a kulun idan ya ji katsewa yake yi, baya bari wanda take yin abin dominsa ya ji ma bale ya yiwa tufkar hanci, walahi yau sai dai ran Elhaji Hamza ya ษaci sai ta samu AL'WALID da maganar nan, iya shegen mufeedan nan ya isheta
Sunna zuwa baban filin Kofar dakinsa suka yi turus sakamakon bakin da suka samu a saman manyan kujerun wajen na alfarma sunna zaune su hudu, sai biyu dake tsaye sunna kai kawo
sun so juyawa, sai dai da ta tuna waye AL'WALID, mutun ne da baya rabo da baki, kuma ta yiwu idan ta koma din a yau da asubahi su ji ya bar garin, shi yasa kawai ta dakata ta nemi iso zuwa ciki, a wajen masu kai kawon nan dan ta san masu tsaron part din nasa ne
Shiga yayi, minti kadan ya dawo ya basu damar shiga
Du irin tsare tsaren sauran part din gidan nan idan suka zo wannan part din kauyanci suke zubawa, abin baya zame musu sabo ma, ko dan ana yawan cenza kayan wajen ne? a kulun idan suka samu shigowa wajen nan sai ya birge su
Khalisat ta saki murmushi tana karra kallon falon farko , har sai da mahaifiyarta ta yi mata nunin su je baban falon sannan suka karasa sunna magana a hankali , domin Kalisat din ce ta ce" Mama, me zaki ce masa? kin san baya son an yi an yi ko? shi yasa take cuta mana ai"
Itama kasa kasa ta ce" Duda baya son an yi an yi ai yana girmama mu, zan je masa a matsayin kakarsa in kai masa abinda yake damuna, in bai yi maganin wannan tsagerar ba walahi sai mu yi maganinta ba tsoro ya sa muke daga mata kafa ba, muna dagawa ne dan mun san wanda ya kawota yana da daraja a gidan nan mai girman gaske!, in ba dan wannan ba da ko ta tsiya sai ta bamu lafiya kangarariyar yarinya kawai"
Sunna bude babar kofar suka samu kukunsa tsaye yana jiransu
Gaishe su yayi kafin ya yi gaba yana basu damar su bi shi
Ta hanyar da suka bi sun hangi AL'WALID din a cikin falon baki tare da wasu baki mutun biyu sunna fira, da yake madubi ne aka saka mai haske wanda ana iya hango baban falon idan har ba wutar jikin madubin aka kashe ba, a yanzu kuwa a kunne take, su na ciki sunna iya gannin na baban falon, hakama na baban falon sunna iya gannin na cikin.
Sunna karasawa ya nuna musu wajen zama ya karasa frij ya dauko musu abin sha ya ajiye da girmamawa ya ce" Aunty , bosss yace ku zauna minti kadan yana zuwa"
Hajia zainabu ta amsa shi sannan ta dauke kanta , saboda tunda suka shigo khalisat dake zaune tana chating a wayarta kuma tana dan taba soyayan dankalin turawan da ta sa kuku ya yi mata ta dago ta zuba musu ido tana tunanin me suka zo yi?
Kuku na tafiya kasa kasa ta ce" Ya dace gidan nan ku iya bambance lokacin da zaku zo maularku da lokacin da zaku barshi ya ji da bakinsa da kuma Ni matarsa!"
Khalisat ta kalleta da sauri da mamakin ta, hakama Hajia zainabu
Ta ci gaba da fadin" Dan kawai ya zama shi kadai ne mai maski ba shine zai sa a nemi kashe shi ba, a takurawa aljihunsa a takurawa lokacin hutunsa ba, .....koda yake, lokaci nake jira, idan ya zo babu wata ฦatuwar da zata zo ta hanna min hutu da mijina ko Wacece"
Khalisat da tarin takaici ya isheta tana kallonta ta ce" Dadin abin koda maula mula je ba wajen Maiga muka je ba, kuma a cikin yan maular d'ana AL'WALID Ni na ga Maiga da IDONA!, ba zaki taba Sannin daga maki kafa muke yi, ba zaki taba Sannin su waye ahalin gidan nan ba sai kin shigo, da takamar gidan mijin naki ne sai ya gagareki zama, daidai muke da ke, muna fatan zuwan naki muma!"
Mahaifiyarta ta dubeta a nutse ta ce" Me kike ci na baka na zuba khalisat?, ki yi shiru kawai..............ki yi shiru dan mu mun san waye shi, zata gane shayi ruwa ne tsohuwar mace"
Mufeeda ta yi murmushi tana sake dora kafa daya kan daya zata yi magana ya bude kofar madubin nan ya shigo
A nutse ya karaso wajen kafet din falon idannuwansa a kan Hajia zainab ya ce" Barka da warhaka kaka z"
kusan a tare suke gaisar da junna, Kalisat kuwa na gaishe shi
Ya dubi khalisat da murmushi ya ce" Maman AL'WALID me zan samu? da gani an kawon wani abin dadi ko?"
Khalisat ta yi dariya tana sake gyara zamanta, dama akoy yannayin barkonci a tsakaninsu, yakan tsokane su lokaci zuwa lokaci, yakan shiga cikinsu idan ya zo ya same su a baban falon Hajia inna, yana jiran iyayensu kowace da sunnan kaka A, wato kaka Amina, kaka z, wato kaka zainabu, sai kaka B wato kaka Binta, ฦดaฦดansu kuwa kowace yakan kirayeta da maman AL'WALID hade da sunnanta , yana daraja su, yana basu girman da ya dace, sai dai hakan baya hanna shi yin hukunci ko jan kunne da babar murya, idan wata ta yi laifi ba ruwansa da shi jika ne a cikin gidan yakan zauna da ita su fahimci junna, ko dan shine namiji baba? ko kuwa namu na Hausa ne wato mai shi a hannu shine mai girman daraja? shi dai yanada darajar nan a gidan su mai girman gaske, kuma idan ya tsawatar ana yi masa biyaya, a yanzu haka budurwa hudu ce bata da aure a gidan, sauran kowace na dakinta, sai masu aiki da jikoki dake gidan, a haka ake tafe da rayuwa ana yinta yadda hali ya bada, a cikin jikokin ne Allah ya albarkacesu da maza, sunne ke kama masa wasu abubuwan na gidan idan baya nan, domin baba dai yana nan ne, ama ya ajiye komai a yanzu bautar ubangijinsa kawai ke gabansa, sai yanke manyan hukunci ko tsawatarwa idan AL'WALID ya yanke wani hukuncin mai tsauri ya kuma kin yin hakuri.
Bayan ya zauna, Mufeeda da ta je kicin ta dawo dauke da jug ta ajiye ta zuba masa tana murmushi ta miko masa tana fadin" Bab, ka jima, ko abinci baka ci ba fa?, ya dace yanzu ka ci abinci kafin ka ci gaba da gannin wasu"
Jus din da ta miko masa kasa amsa ya yi, ba dan komai ba sai dan irin yadda ta matse masa waje, uwa uba irin suturar dake jikin yarinyar.....bai san me yasa Mufeeda ke son wulakantar da kanta har haka ba, bai kuma san me yasa take yi masa kallon shashasha ba, domin shi ba mutun ne mai saurin shiga rayuwar mutun ba, ama kuma yana da tsantseni da kiyaye hakokin addininsa sosai da sosai
Yayi tunanin idan ya bi Mufeeda da ido zata cenza wasu abubuwan, sai dai ga dukkan alamu dole sai ya yi mata maganar, dan ba zai yiwu ba, matar aurensa ba irin shigar nan ta dace da ita ba, ko kadan, haka kuma wannan yawon ba na matar aurensa bane!
Da yan yatsunsa kawai ya mata alamar ta ajiye, dan haka ta zauna rike da abin shan, Bata ajiye ba, tana jiran su gama rokon su tafi sai ya sha, dan ita bata ga wani cenji a tare da shi ba, bata ga laifi a zama daf da shi ba, bata ga matsala a kawo masa jus da ta yi bata ga matsala a shigarta ba, uwa uba a tunaninta wata bukata ce ta kawo su Hajia zainabu wajensa, dan haka tana jira su gama su tafi, kuma walahi sai ta tarda Hajia zainabu da khalisat har daki yau ta musu rashin mutunci, ita khalisat zata zaga? zaginma da ubanta? ba laifi zata je itama ta zagi Tata uwar ta ji idan da dadi, zata tuna mata in ba son abin duniya ba uban me ya haษa Hajia zainabu aure da Elhaji Hamza? tsoho da shi ama ta zo ta zauna, har ta haifi khalisat da shi ana cewa khalisat din auta? kai har ubanta fa ita sai ta zaga, zasu san da daidai da su zasu zauna, babu wanda bata gane munafurcinsa ba,, kaf dinsu, kuma daidai take da su.
kan Hajia zainabu a kasa bayan ta sauke ajiyar zuciya, cike da kisa irin Tata ta himar da take samun duk wani abinda take so a wajensa , wato ta hanyar sada kai da yi masa biyayar da shine ya dace ace yana haka a gabansu ta ce" ranka ya dade, damuwa ce mai girman