Showing 219001 words to 219669 words out of 219669 words

Chapter 74 - So Makamin Cuta Complete Hausa Novels Compelet By Surayyams.txt

14 Mar 2026

4120

su.

Abun abun tausayi amma sai suka maida shi abun tsokana ma junan su

Shi yake debe mata kewa
Itama hakan bata jin dadi in baizo sunyi yar tsokanan da shi ba

Haka shakuwa ya fara ninkuwa tsakanin ashraf da zahida tun kafin suna suka dawo real friends
Na ban mamaki.

Tare suka hada nasu hidiman ma babies din su jasmine wanda aka basu inkiyan sunan ammy wato shahida da shaheed.amma a zahiri lailah ne da kamal jnr

Wanda ash already yake kiran ta da ammy, shima baby boy ya dawo wasu sukan ce shaheed wasu suna cewa jnr.

Kamal da zahida suka dawo rlshp din su normal duk da ma tana dan jin kunyar sa
Amma ana wasa da dariya ita ta fara cewa Ba zata kira shaheed junior ba don kar ya dawo black kamar ita da kamal.


Haka suka cigaba da rayuwan su komai na tafiya dai dai
Har aka yi suna cike da gata da hidima nagani na fada

Mamy gaba daya sai taji duniyan ya mata dadi sosai
ganin yanzu kowa acikin su ita yake duba a matsayin mahifiya musamman ma zahida da ta dawo best friend dn Ashraf

yanzu shi yake koya mata addinin ta da abubuwan da da chan ta mance da su a matsayin ta na musulma.

Ganin ya mallake hankali sosai ya sa abba ya bashi damarl ya sake rike musu tatallin arzikin su kamar da chan.

Bayan shekara guda zahida ta dada wankuwa alaman ta amshi qaddarar Allah daya sauya mata halittan ta
Ta koma soma sa kayan mutunci ta dawo musulma tana sallah tana azumi da sauran su.

Sai ta kwantar da hankalin ta tana juya harkokin business din ta tare da yan uwan ta cike da so da kauna da amanan juna .


Da shike yanzu akwai ashraf sai ta mance ma da wani feelings ma Ashween har tana scolding kanta akan shirmen data yi da chan tana rudin zuciyan ta.

Ba da dadewa ba aka soma shirye shiryen auren su da ashraf
Lokacin salma tana laulayin sabon ciki

Ahaka zahida taga uban gata da soyayya wajen su duka
Musamman mamy data bata kula irin na surka da na uwa
Har aka ci taro aka watse aka kai ma ashraf new wife dinsa wato zahrod.



*After 5 years*



Lokacin Labarin mutuwar madam hidayat a prison har ya soma gushewa
A Lokacin Jasmine ta kammala karatun ta har ta kama aiki karkashin arzikin mahaifin ta.

Sai ya kasance kusan kowani wata biyu ko uku in yara sukayi hutu sai an taho abuja don a hadu baki daya as family and friends.

Jummai da salma already suna da yaran su bibbiyu ,bayan Ash junior akwai baby girl jawahir na jumai kuma fatima

Zahida kuma ta haifi baby boy kabeer da kyar don daga nan saida aka cire mahaifan ta kwata kwata
ga cikin ya zo da albarka shi yayi sanadiyar kara fito da sirrin kyau dake cikin sabon salon halittar ta
Shikuma aahraf yanzu an samu yana amfani da eye glasses suna rayuwar su mai dadi mai tsafta.


Frndship din iyayen ya koma kan yayan wato Kamal Jnr da yayan sa Ashween jnr wanda aka kaisu karatun su kasar waje under care na uncle dinsu jamal.

Anan dai jasmine ke fama da laulayin wani sabon ciki ga baby boy din da ta haifa mai suna oumran bayan twins a hannun mamy tana kula da shi.

Haka rayuwa ta cigaba musu cikin jin dadi, bunkasar arziki ,soyayya, fahimtar juna,amana da yarda da kyakkyawan zumunci.happy
One big happy family.











*Wassalamu alaikum masoya na Ayafe ni ayafe ni,in na bata rai wani sanadiyar wannan littafi ayi hakuri da ni*



```Na gode, nagode wanda suka biyoni har wannan lokaci Allah ya muku albarka ya kare ku daga sharri ya sada ku da alkhairi ya baku ladan karfafa min gwiwa har na kammala wannan littafi a saukake cikin jin dadi kaunar ku da kulawar ku.
Jazakhallahu khairan```








*SURAYYAHMS ke muku fatan alkhairi sai mun hade a littafi na na gaba mai suna:*
*🌺SAKAMAKO🌺 not anytime soon amma zan gaya muku kafin na soma rubuta shi NAGODE*








~Im gonna miss u fans~ 😭😭😭


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login