Showing 39001 words to 42000 words out of 219669 words
Chapter 14 - So Makamin Cuta Complete Hausa Novels Compelet By Surayyams.txt
kuma yaya ashraf me namaka na munafur ci?
Ohh..tab...baki ma sani ba ko, ai dama bazaki sani ba tunda kin mayar dani shasha sha..wawa uhm
Ranta ne ya soma baci amma sai ta dago calmly tace
Ban fahimce ka ba fa har yanzu?
Tswa ya daka mata " Meyasa a gabana kike gwada min kokarin ki akan maganar auren mu alhalin ke kike cewa su ammy baki son auren? Answer me ya karashe a tsawace
Shiru tayi tana kallon sa , don tuni taga alaman bacin rai sosai tattare da shi ,ko tsayuwa mai kyw bayayi
Gashi Tarasa me zatace don batayi tsammanin maganan zaije kunnen sa da wuri ba
Kayi hakuri yay ashraf, ni ba wai cewa nayi bana so ba,
U just misunderstood me
Cikin kunan rai yace"da Allah malama kimin shiru ..ko tausayi na bakiyi jasmine ko dan kinga sonki tayi min illah ne ? Aure fa nace ba wasa ba...
Nan idon sa ya ciko da kwalla ya soma binta da wani irin kallo ....nasan baki dauki komai da muhimmanci game dani ba shiyasa kike min haka
Amma ba komai ,
Zan baki dama kije kiyi tunani na miki alkwari duk abunda kika yanke a zuciyar ki ,zan karba ..kaiwa nan ya juya ya tafi ya barta anan tsaye
Durus ta tsaya kallon sa har ya lume ,mamaki da tausayin sa ya kamata lokaci guda,
Dan tabe baki tayi cikin ajiyan numfashi tace" ohh ni jasmine wallhy
Ba laifi na bane, zuciyata ce ta ksa aminta da soyyayr ka yaya ashraf..don ban taba tunanin da gaske har haka kakeyi ba .gani na jiki na kawai yake so"
Juyawa tayi tana tafiya cikin nazari tace "But I think i will give him a real chance..tsakani da Allah ko dan naga in dagasken yake.
Inshi ne miji na Allah ya bayyana alkahirin dake ciki
Ta karasa magananta tare da shiga cikin main hause
Bayan kwana biyu bata kira shi ba haka shima bai neme ta ,
Don ita kam tsaf take shirin inta juya kan yaya ashraf ba abunda zai karkata ta kuma sai aure kawai,.. ..sai dai kullum inta soma wannan tunanin sai ta kasa kaiwa stoping point..shiru shiru mafita taki fitowa
Gefen ammy kuwa kwana biyu da shike ashween bai cika zama ba, sosai shakuwa mai karfi ta sake ninkuwa tsakanin ta da jasmine
A Kullum acikin mata nasiha take,wani lokacin tayi kuka wani bin suyita dariya don kuwa ammy cikin fasaha da hikima irin na manya take koyamata har da tattalin zaman aure da rayuwar zama da mutane
Duk da haka sam taki bari jasmine ta fahimci ciwon dake damun ta duk da ma ta sha kama ta tana shan magani a boye.
Yau ma kamar kullum
Tana kwance ta rasa abunda ke mata dadi
Zafi jikin ta yayi sosai gashi yaki sauka duk da maganin data sha da daddare
Hannu ta daura akanta tana ambaton ubangijin ta a hankali
Tana maimaita addu'o i kala kala,
Tanayi Amma Kamar ana bulbula ciwon kai haka takeji
Jim kadan jini ya soma fita daga ramin hancin ta
Hawaye ne mai zafi ya sauko mata zuciyan ta na neman ya zama weak
Sabida yanayin data shiga ciki tunanin rayuwar da zata bar ma ashween da jasmine a lokacin
Muryan ta na karkarwa ta daga kai ta kalli sama tace"
Ya mujeeb,
Yah zul jalal wal- ekram
Ubangiji na mafi tausayi da rahma kan bayin sa
Kai ka rike ni ka rike yaya na ,kai kaba ni ikon tafiyar da su bisa amanar iyayen su
Nayi imani da rayuwa da mutuwa, nayi Emani zaka rike min su kan amanarka tabbatacciya bayan rai na,
Yah kareem
Ena rokon ka ka basu rayuwa bisa kan tsarin ka,ka kyautata imanin su,ka basu juriya da hakuri ko da bana nan tare da su,
Sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya
Bakin ta na bari ta najin wani zafi a zuciyar ta,
Shigowar hajiya hadiza ya sa ta jin komai yatsaya mata chak tunanin ta ko jasmine ne ta shigo gaishe ta,
Don lokacin da ashween ya zo sam taki juyawa don kar ya fahimci wani abun, sai tayi luf kamar tana bacci har ya gaji yayi tafiyar sa
Sauke ajiyan zuciya tayi jin muryan hajiy hadiza,
Hajiya shahidah? Subhannalhi
Me nake gani ?
Abun naki ya yi tsanani hakan ne tace a rude tana neman zama daf da ita
Hmm bari kawai ,yanzu Ba wannan ba hjy hadiza
Ai har na tsorata da naji shigowar ki
Ah ' karki damu nice, Ai ena ganin shigowar sakon ki na ce ko lpya?
Ammy tace "Uhm lpyar kenan,kinsan doc tayi tafiya,ciwo kuma ba kai kake da shi ba shi yake dakai
Daga ni na kimtsa kafin yaran nan su zago
Ba musu mamy ta taimaka mata
Sai yanzu ta ke ganin yadda ta rame fuskan ta yayi fau kamr ba jini,
Nan ta shige bathrum da kyar ta samu ta kimtsa kanta sannan ta fito
Nan ta samu Tsaf hajiya hdiza ta gyara wajen
Sannan ta taimaka mata ta gyara kanta ssma sama jikin ta ya dan samu karfi
' ko minti biyar ba suyi da zama ba saiga jasmine ta shigo
Ena kwana mammy,
Ta gaida hajya hadiza a ladabce
" da murmushin ta ta amsa
Jasmine sai girma takeyi ,kwanan nan zamu yi shagali ashe
Kunya ne ya rufe ta cikin sauri ta mike tafada jikiin ammyn nata tana murmushi
Ke kinga irin abun ko?
Ai sai ki fada jikin wacce tayi maganan ba ni ba
' dan dariya kawai tayi chan kuma kamr an tsakureta tace
Ammy ya naji jikin ki zafi
Fever ce?
Uhm uhm,cewar ammy tana forcing smile a fuskan ta
Ahhhh ni dai kifada min ko na miki allura tafada a shagwabe
Ammy tace To wa ke jin tsoron allura in ba ke ba
Ni tashi min toh . ammyn ta daga ta da kyr
Murmushi hjy hdza tayj tace yawwa autar ammy
Jeki ki shirya mana,ogu sausage na kifi da white rice yanzu ki kawo auta na,,
Da murnan ta ta amsa
Cewa toh
Dan tana mugun son tagan ta a kitchen tana girki kamar amarya,abun na burge ta tunda ammy ta soma mata training irin haka
Duk murmushi suka bita da shi har ta fice
Nan hjy hadiza ta maida kallo wajen ammy
' nikam yaushe zaki fahimtar da yaran nan naki halin da kike ciki ne?
Dan shiru ammyn tayi
Daga baya tace
Baza su sani ba hadiza
Ba yanzu ba,nan annurin fuskan ta ya dauke
Ah ' a hajiya shahida toh sai yaushe ?
ni dai anawa ganin
Wannan babban kuskure ne
Qaddara yau ace wani abu ya sameki a gidan nan ya zakiyi inba ni ba doc?
Ai ko adduan su ma babban makami ne awajen ki,sai Allah ya ji tausayin su fiye da mu ma ya sawwaka miki lalurar ki
Tace Haka ne ,amma hadiza
Me riba ta in na fada musu ciwon da nasan mutuwa ce kawai saukin ta?
" ena tausayin su fiye da yadda nake tausayin kai na hadiza
Hawaye ne mai zafi ya soma saukowa mata
" shiru ne ya ratsa wajen sannan ta ce
Nasan kinsan jasmine jini na ce
Yar twin sister na ce da mijin ta yayi sanadiyar mutuwar ta a plane crash don kawai son ransa da na karuwar sa"
Dama itace dangi na kwalli daya a duniya
Ta tafi ta bar min yarta ,
Yau Jasmine bata san ma wacece mahaifiyar ta ba bare mahaifin ta
ni kawai ta sani iya rayuwar ta ,
Kina ganin en nazo mata da wanann labari taya zance mata mahaifin ta ne ya hallaka mahaifiyar ta akan wata ya mace?sannan ko sau daya bai taba neman ta ba ai yasan tana raye,
Toh Da na mata karya gwara ban fada mata komai ba hadiza
Ita ma hjya hadiza shiru tayi jikin ta ya dan yi sanyi
Tana famar nazarin maganan
Chan kuma sai tace shi kuma ashween fa
Kinki gaya ma kowa alakar ki da shi
Tun kafin yaya abbas ya rasu ya sha fushi dake akan yaron nan amma sam kinkii bude baki kice komai
Shikam ai ba jinin ki bane ko?
Wani dogon numfashi ammy ta sauke
Ta sa hannu ta share hawayen ta
Sannan ta dubi hajiya hadiza
Labari ne abun al'ajabi kuma mai tsawo
Amma zanso kimin alfarma daya hadiza
'fade ta ko wani iri ne
Uhm, ena so Ki min alkwari wannan maganan da zan fada miki anan zaki binne ta
Ena nufin bazaki fada ma kowa ba,
Kin amince?
Dan shiruuu tayi sannan tace duk da ban san dalilin ki ba amma na amince shahida"
Waye ashween? Menene asalin sa?ena iyayen sa?
Ba bata lokaci ammy tace 'kin tuna wani hoton yaro da kika gani a drawer ta ranar tun muna turkiya har kika tambaye ni waye ne ?
dan shiruu tayi cahn tace Ehhh na tuna
Yawwa ,toh da farko dai zan ce ke kadai kika taba sanin asalin kamannin ashween amma na boye miki nace miki ba shi bane!
Ba don komai ba saboda na tsare sa daga mugun hannun daya fito shiyasa nake boye sa ma kowa,har ma ku yan uwana
Ta cigaaba, Ba anan ya tsaya ba
Bayan dan binciken danayi akansa da zaman fahimta da na ma yaron anan na gane asalin waye shi
Shine kawai na qudiri masa jinya a boye,
Hadiza Da hankali na Na yi saurin amincewa da jinyar plastic surgrey da doc yace zai masa don itace hanya daya na tseratar da shi daga jami'an tsaro dake neman sa zasu kamasa
Dafe kirji hajiy hadiza tayi tana salati, kanta har ya kasa zama waje daya tace
Ban fahimce ki ba hjya shahida
Kina nufin wannan nakasasshen yaron dana gani shine ashween?
Gyada kai ammy tayi tace tabbas shine
Wani salatin ta sake bugawa cikin mamaki
tace to waye iyayen sa? Meya hada sa da jamia'n tsaro a dan wannan shekarun nasa
Murmushin takaici ammy tayi
Ta sake goge kwallar dake gefen idon ta tace
' a hanya ta ta dawowa daga asibiti lokacin jasmine na karama bata karban ruwan nono sai madara
Sam Ban lura da haddarin dake gari ba nasa musa driver Allah ya jikan sa"
Ya dawo da mu gida
A hanya wannan ruwan ta same mu,gashi ba wajen fakewa driver mu ba yadda ya iya haka muka kusa kai cikin ruwa muna tafiya sannu a hankali
"sanadiyar tafiyar mu a hankalin ne na hango wani abu a kasa a shimfide gefen wani mutaccen itace na ni dauka irin kayan nan ne na datti na mahaukata a dunkule..amma damu ka iso kusa
Sai kuma naga ashe fa mutum ne
Munzo daf da shi charaf muka hada ido
Ashe yaro ne a nakashe ya dunkule sai kyarma yake ruwan nan na dukan sa amma bai motsa ba
Lokaci guda zuciyata ta kamo da tsananin tausayi sai na kawo ace dan da na haifa ne cikin wannan yanayin ' ba yadda musa baiyi ba kan cewa mutafi kawai mubarsa
Dalilin sa kuwa cewa mutanen duniya abun tsoro ne ba kowa zakaga ni a titi ka tausaya masa ba
Amma haka naki fir,
Sai da na dawo na dauko shi,
Share hawayen ta tayi ta cigaba da cewa
En takaice miki sai da yakai kwana uku yana zazzabi sannan na ma gane kansa
Kullum yana mugayen mafarki' mai ban tsoro
Ciki yana kukan mutuwar wata wacce yake kira lailah"
Dana ga abun ya yi tsanani ga shi yaro ne
Sai Na kaisa asibiti na mika sa ma therapist,
Anan suka tabbatar min da emotional trauma ce ke damun sa, ban bata lokaci na soma jan sa ajiki har na samu nayi nasara muka fahimci juna sosai
Da bakin sa ya bani labarin yadda uwar sa da yan' uwan sa suka juya masa baya sannan suka laka masa mutuwar twin sis din sa wacce yake kira da lailah a mafarkin sa.
Ashe ma daga prison detention na yara ya gudo
Kwanan sa uku yana tafiya shine ya rakube wajen nan da na tsince sa,
Kuka hajiya hadiza ta fashe da shi tana salati tana sallamewa
Chan da zuciyan ta yayi sanyi tace
Toh me kikayi akan hakan,nasan dai ba ZAllan wannan ba ne tarihin ashween
Kinko san suwaye iyayen san?
Kuma a wani gari suke?
Ammy tace Tabbas na sani mana,
Nadai yi kokari na sauya sa ta hanyar jinya
Saboda na samu daman bashi kariya
Kafin na bincika al' amarin sa da kyuw
Ganin yadda mood din hjya hadizan ya sauya ya sa tace
Yanzu dai muci abiinci anjima zaki ji komai"
nasan duk yadda akayi jasmine ta kammala kar ta shigo ta fahimci wani abu
Ha ka ne cewar hjiya hadiza da tuni jikin ta yayi lukwi yayi sanyi ...
Falour suka fita suka ci abincin cikin raha da dariya kamar ba abunda ke damun su
Kiran ashween din ne ma ya dan katse su
Nan ya sanar mata bazaii samu dawowa da wuri yau ba ,
A Haka sukayi sallama da kyar don yana mugun jin ammyn san nan aransa
Jasmine da ke murnan dawowar salma tuni ta nufi gidan su hankali kwance "
Nan suka tattara suka suka ka daki don cigaban lAbarin ashween.
🙌🏾👀
*surriem*
[23/08, 03:02] +234 806 071 2446: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
I just published "part1page16" of my story "SO MAKAMIN CUTA". https://my.w.tt/oQgZpZyw6N
*Page▶15*
Zaman su ke da Wuya
Hajiya hadiza tace ena sauraron ki ,
Wani dogon numfashi ta ja sannan tace
A Shekaru 18 da suka wuce, anyi wani hamshakiyar mata da mijin ta ....nan labari ya soma...
"Daga nesa ake hango bishiyoyi a jere tsaf cikin layi gwanin sha'awa Waje yayi luf luf,ga sanyi mai niima na ratsa ko ena,
Akasarin mutane 40 ke faman aikin su bisa tsari a wani makeken gonan yayan tufah na zamani wato hydbrid plantation
Duk da komin wajen dai dai yake amma hakan bai hana ma'aikatan nan cigaba da kimtse kimtse da gyare gyare ba
Wayyo Allah na"asabe daya daga cikin ma'aikatan tafada tana rike kugun ta dayan hannun ta durkushe akan gwiwar ta
Gashi Sai diga take da zufa..
Subhanallhi" as..a..be
Meya faru kuma ?
Dan Allah ki mike kinji asabe saura kiris madam rod ta karaso..cewar wani dattijo daya zo kanta mai suna mlm habu
Malm habu cikin yanayin damuwa yatallafo ta yana cewa
Sannu asabe .ki daure
Haka ma Yawancin sauran maikatan ke fada
Asabe Nishi take fitarwa kadan kadam
Sannan ta tsaya ta cize bakin ta don radadi azabar data keji a cikin ta amma sai ta cigaba da aikin
Faruwar haka da mintuna 5 motocin alfarma kirar prado formated na suka soma tururuwar shigowa wajen
Kuuuuuuu cikin kowa ya soma wasu a bayyane wasu a asirce
"" Gata nan...Sun iso fa ku gyara
Babbban cikin su yake rada musu a hankali yayinda kowa yayi tsuru tsuru bisa layi na kallon yadda ake jera parking ana saukowa
Turawa ne guda uku tare da hajiya hidayat rodriquez mai dauke da juna biyu kimanin wata takwas
Sai karamr yar mijin ta ZAHIDAH wato yar marigayiya first wife na alhji abdul fatah rodriquez
Gefe kuma Sai jamal da jabir da wata baturiya wacce uniform din jikin ta ya bayyana matsayin ta na nanny mai kula da su ..
Masha Allah"tubarkallah
Daga hajiya hidayat har yayan cikin ta wato jamal da jabir kyawawa ne farare tas kamar an zana su da hannu
kyawun su irin na bugawa a jarida
sai dai duk da hakan zahida ta so da tsere musu 'karama ce kimanin shekara 10 amma sosai body structurn ta yake dauke hankali
yar das das ce kamar model ga suma kamar balarabiya,
tana makale a hannun alhj abdl fatah cikin customised gown dinta sai rigima take tana yauki
Don a duniya bata jin ita ba sarauniyar kyawu bane
Sosai take mugun ji da halittar ta bugu da kari da matsayin ta wajen mahaifin ta na yar sa ta fari.
Atakaice yaran rodeiquez Dukan su abun kallo ne gwanin sha'awa suna tahowa cikin shigar su na Qasaita da kwarjini
Jamal? Hjy hidayat Tace cikin muryan ta daya yi kama da na turawa
'Kuje wajen dad dinku let me show dem around' bata jira ya amsa ba ta juya tabi bayan turawan nan
Nan ta soma bin lungu da sako na gonar tana musu bayani cikin harshen turanci
Sai dai zuwan su wajen ko amsa gaisuwar ma'iakatan ta batayi ba bare ta musu kallon arziki
Daga chn gefe su zahida da kannen ta suke hira " oh my' ta yamutsa fuska sosai tana cewa
Jamal,dubi waccan mummunar matar wai ahaka suke aiki anan din? Cewar zahida
'hhhh c'mon sis meya hada muni da aikin gona kuma yace yana bin asabe da kallo da bata ma san sunayi ba
Cikin yatsine ta dubi jamal din tace
Kalan ta sa fruits din ma suki fitowa da kywu suyi muni ka duba dai kagani shes so ugly ..tafada a wulaknce tana tuf da yawu
Kasan me?
In nice eta bazan taba nuna wannan fuskatan awaje ba ..kai munin yayi yawa.
Dariya jabir yayi sannan ya dago don ya kalli wacece su zahida da jamal suke kare mata tanadi sannan shima yace
Wow' gaskiyar ki ne fa big sis.akwai muni kam
But U know what 'ya murmusa idon sa cikin sigar yabo yana kallon ta'" i think ba wacce zata iya hada kanta da kywun ki a fadin garin nan "
Wani rangwadi tayi tana juya kai cikin jin dadin kalmar nasa
Ta dan dafa sa tace " of cous brother" shiyasa kake burgeni ka iya fadan gaskiya'tana yi tana kallon kanta tana rausaya sannan tace"
I