Showing 30001 words to 33000 words out of 219669 words

Chapter 11 - So Makamin Cuta Complete Hausa Novels Compelet By Surayyams.txt

14 Mar 2026

4121

..

Jabir ya san da plan din nan kenan ?
Yes zahida ,ya sani..shi na fara haduwa da shi ya bani labarin komai
Nd I felt sorry fr yhu,.in kika duba meye ma duniyan nan ne?

Kifi kifi take da ido tasa fuskan tausayi tace
"kayi hakuri
Dan Allah ka yafe min . I so much love you ash fatan im still d same a zuciyan ka?.

Murmuswa kawai yayi kafin yace karki damu.
Just don make it look like ena tare da ku kinji?

A hankali tace Trust me...

Murmushi mrs rod tayi itama tana kallon su tace baka da matsala
Zaka samu duk wani hadin kai daga wajen mu
Na maka alkwari

Baice komai ba ya mike tsaye yace toh
Na barki lpya ...ya ma zahida ligh peg a kuncin ta ya fice abunsa
Sosai abun ya basu mamaki
Gani suke kamar a mafarki
Banda jamal da ya san nashi tagama karewa yanzu kam
Sai jimamin yadda gobe zata kasance masa yake

Bayan kwana uku
Komai ya soma sauki
Wa su zahida ashween sai dada shiga jikin su yake yi musamman mrs rod da gaba daya taji yana burge ta
Ena ma ace ita ta haife sa ?
Lawyr ne mai ji da ilimi da kwarewa Ashween ya hada su da shi don haka
Jamal ya kasa samun sukuni a zuciyar sa
Kishin abun na matukar damun sa
Ga maganganun banza da ya ke artabu da su wajen yan jarida da abokan gaban sa

Ganin hankalin mummyn nasu da zahida ya komA Kan sabon lawyr ya sa shi jan jikin sa kwata Kwata

A daki yake wuni yasha wannan ya sha wannan
In dare yayi ya sa akawo masa mata ya kwana dasu abun sa

A haka a haka kafin ranar shiga kotu ,,ashween ya zama zuma wajen mrs rod
Bata jin maganan kowa sai nashi
Musamman Da ya nuna mata zallan gaskiyar sa akan al'amarin

Duk da yadda zahida ta so ace tana tare da shi
Hakan baiyuwa
Gashi yanzu bata iya bacci tsaban radadin son shi da take kwana da shi ta wuni da shi

Ranar da aka shiga Kotu
Komai kaMr yadda ya tsara musu suka bi
Alkali ya wanke zahida tas akan cewa tania ta mutu ne sanadiyar samun wani choke a breathing tubes din Ta , sannan ya kori karar

Murna wajen su ranar kamar yaune suka soma shaRia suna lashewa

Musamman ma zahida data ga tashin hankali da bata taba ganin irin sa

Da daddare bayan waje ya lafa Kwance mrs rod ta same ta tana chat da alaman ashween ne kan layi " murmushi ta sakar mata ta dana shafar suman kanta
" komai ya wuce zahida na

Mirmshi itama ta mayar mata tace yes mummy
Komai ya wuce
Ya kamata na gwada ma yaron nan godiya ta koya kakice?

Of cous, nima nayi tunanin haka
Kinsan ma wani abu kuwa zahida ?
Yanzu nake ganin abubuwan da kika dade kina gwada min akan sa
Hes so matured" wani abun in yanayi sai naga kamr jini na ne ke bin jikin sa zahida

Dan dariya zahida tayi kafin tace
Mummy kenan
Kawai kice electric shock din ya kama ki kema
Ashween ya iya sace zuciya mummy
And im not letting him go
Murmushi muumyn itama tayi tace
Sosai ma ,zanso na malleke sa a nan familyn nan
Don kuwa we definatly need him..

Yes ,mummy
Uhm. Kin kuwa duba
jamal? Naga kamr baijin dadi ko court baizo ba fa

Hmmm kyale shi
Nasan matsalar sa
Ai yanzu baida wani amfani awaje na sosai
So i dont have his time
Yanzu so nake ki dage ayi ayi bikin nan
Na tabbata ashween is part of rodriquez kinji beauty na?

Dan shiru tayi tana jimamin maganan jamal din
Amma saita basar ta sake murmushin Yake tace toh mummy

Nan sukayi sallama ta fuce abun ta

Ta shi tayi ta sulale ta nufi site din jamal din
Jin karar music na tashi ya sata turo kofar a hankali
Da sauri ta kau da kanta amma ena abunda ta ci karo da shi ya tsaya mata a ido

Ko ajikin sa sai riding din ta yake
Ga dayar budurwan a gefe tsirara tana kan lashe sa
Ganin ba kula ta zAiyi ba ya sa ta fice ta bashi guri ya cigaba da abunda yake yi

Dan tabe baki tayi ,
Tace hmm
Jamal ya saya makan sa wahala
En nine shi kawai zAn cigaba da aiki na ba sai nayi suna ba

Mummy kam dama In kana da shi kaine nata amma inbaka da shi ure useless".



🤓



*surriem*
[23/08, 03:02] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*



💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_


_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥



*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.


*Masoya A duk enda kuke surayyahms tana kaunar ku* 💋❤💯




*Page▶11*






Zaune suke a karkashin wani open air cool down,suna shan drinks sai kyalkyelwa sukeyi da dariya kamar kananan yara
Amintaka irin na kamal da ashween tamkar jini daya ne ya hada su
Duk da ma a secdry achl suka hadu ba wanda zai iya cewa hakan
Domin savuwr tasu yayi kama da wanda suka tasu tun suna kanana..

'lallai yaron nan ,
Ka tabbatar min da zaka iya jefar tsuntsu goma ma da dutse daya

Dan murmushi kaqai ashween yayai yace
Nothing is impossible bro
Sun dauka abun wasa ne ,
dama mutanen da suke kallon rayuwa a irin wannan madubin ba wahala zasu fada cikin kowani irin tarko,
Wht yhu need is ka nuna musu abunda suke so, to shikenan ka gama da su

Kaml ya nitsu yana jinshi " Hmm amma Allah ya dai sawwake ,to ena ilimi da power ? Ba basirah mswww
Yanzu shi jamal ka gama da shi tashi ta kare tunda yan jarida ma naga sai dada hura qutan abun suke' yanzu sai kuma waye next?

Uhmm bari fa ai jamal hakki mutane ke binsa sai dayan wawan ,,shikam ai one blow ne zan masa muje zUwa
Don Yanzu bani da wani matsala sosai tunda na samu shiga wajen uwar tasu
Sannu a hankali zan durmuryarta da ita da yarta ,amma nafiso komai ya tafi steady
clean bana son nayi garaje ka fahimta

Of cous, kar ka manta ena tare dakai,kasan
Ciwon dayafi zafi shine wanda ba ganin sa sai da aji sa,

Dariya sukayi tare ,sannan ashwewn yace kaga ni zan koma gida kwana biyu ban kula da tsohuwa ta ba duk aikin wayyanan banzayen sun sha min kai,
Ya mike tsaye ,,
Tohh shikenan ash send my regards ,nikam jiya naje ai
Later,suka yi musabaha sannan ya kallesa ya dan kashe masa ido yace
And my princess too
Da sauri ya kwace hannun sa yana harar sa cikin sigar wasa
Kwara ma ka cire my din nan
Princess din dan ma kaine ?

Shikam kamal dariya kawai yake don yasan dole ya amsa shi haka suka rabu kowa yayi nashi hanya


*Bayan wata daya,*

Haka rayuwa ta cigaba wa ashween da familyn rodriquez
Sosai yake samum karbuwa yanzu ya kaiga madam hidayat ta sake masa wasu harkokin ta yana juya mata su

Yarda da so sosai ta soma qallafawa akansa dun dama tun tuni takejin sa kamar dan cikin ta,

Zahida ko hankalin ta kwance sai baza mulkin ta takeyi iya son ranta,
Cikin kawayen ta kuwa har takanyi birgan cewa ta kashe tania ta gaje ashween ma kanta,

Ranar laaraba da aafe misalin karfe10 Zaune tayi gefen sa ta hanasa sakat, shiko sai aikin sa yake baya ma kallon me takeyi
Yana sane da Duk ma aikatan sa ba su samun sakewa musamman inta na offishin
Saboda zahida asalin ta bata san darajar dan adam ba' wani abun ma don tana tsoron ashween ya sa take ragewa

Baby"? Ta kure sa da ido tana kashe muryan ta
Ya akayi,yace a takaice bai dago ba

Sai Yau naga kamar ranka a bace
I mean, lpya kuwa? Yhu look sick ko kwalliyar ma da aka saba min yau ba ayi ba" ta karashe a marai raice

Dan takaitaccen kallo ya bita da shi yace
Kar ki daga ma kanki hankali beauty
Im ok,just need some time alonee
Shyasa ma naga zai fi dacewa kije gida zamu hadu anjima kinji? Ya kau da kai

Ranta baiso ba amma sai ta yi saurin kawo murmushi kan fiskan ta tace
Anything for yhu,
Kar ka manta duk aBunda kake bukata ena nan,
Gyada kai kawai yayi baice komai ba harta fice
'yana jin karar rufuwar kofar ya kife kansa da tebur tuni wasu zafafan hawaye suka soma sauko masa"
Yakai minti 20 a hakan kansa har na hargowa tsaban ciwon dayake ji
Karshe rufe file din yayi ya wuce gida abunsa

Haka ya wuni a daki sai juye juye yake' yaki sanar da kowa yana gidan don kar hankalin ammyn sa ya tashi
Ita kadai ce ta san yadda ya tsani ranar zagowar haihuwar sa
Don tun safe take kafa kafa da shi amma yaki nuna mata komai

Kamal ma ranar shiru bai neme sa ba don ya tsani ganin yanayin ashween a ko wani ranar bufdayn nasa
Gashi duk lokacim da ya so ya shiga al'amarin yakan so ya zame musu sabani,
sai ya yanke hukun cin masa addua da sadaqa duk ranar zagowar haihuwan sa ba tare da ya sani ba ma

Gefen ashween kuwa yayi nafila ranar ba adadi, amma sam jikin sa yaki sake sa,a hankali ya jingina kansa da pillow idonsa a lumshe yace "ya Allah ,kullum dai haka ne...pls ka saukaka min
Sai bai kara cewa komai ba

Tattara kaya ammy keyi bayan ta kammla rubuce rubucen ta ,
Bata hankara ba jitayi mutum agefen ta but

Ke,kaji min yarinyar nan ai sai ke tsorata ni tafada cikin sigar fada ,
Ita kam shiru tayi saida ta kammla karanta dan papern da ta sa mu a kasa sannan ta ce Ammy"
Daga zuwa duba ki sai kimin masifa? , share ta ammyn tayi batace komai ba

Ta rike kogun ta ,sai kiriniya take
Cahn tagaji dan kanta tace
Ammy naje?

Ohhhh jasmine wai ena zaki je ne?

Zaro ido waje tayi tace " tuntuni nake tace wa zanje kasuwa ammy ashe bakki ma jina ?

Ohh sorry ,
Ke da wa?
Nida driver ne kawai

Ammy tace Ok
Ena fatan bazaki dade ba ko don wallhy ba ruwa na tohm
Da sauri ta gyada kai tace " yanzu zan dawo ammy
Toh shikenan ..nan ta fice a gurguje

Wanka ta sha mai shegen kywu cikin atamfa dark green
Ta nufi kasuwa don yo shoping
" zuciyan ta fall take tafiya cikin mall din
Tunanin ta gaba daya me zata siya wanda zai burge yaya ash"
Kiran salma ne ya sake shigowa wayar
Ba jira ta dauka
Tace yawwa dazu muna magana"
Kinsan ban san yau yake bufday ba sai da naje dakin ammy
Naga ta rubuta masa wish a wani paper,ai itama bata san na gani ba na yar mata abun ta
Ta karashe da dan dariya

Hmm jasmine kenan,
Toh me da me kika saya
Ko har kin gama?
Ehmm toh gani nan dai

Huhh,ta yarfa hannu a gajiye tace
Na ma rasa me zan dauka masa salmah
Im so confused
Uhum uhm dont be ,kinga take your time kiy masa abunda ya dcw da shi
Nikam bari na je my prince charming is coming today

Hmmm kaji masu love,to ki gaishe sa,
No wonder bangan shi a gidan mu ba ashe wajenki ya nufa,

Dan dariya salma tayi
Barshi kawai,shifa har yanzu baisan kinsan shine saurayi na ba,

Uhmm ai ni kanwa ce,na masa uziri. Allah dai ya tabbtr mana da alkhairi

Ameen jasmine,ke ma insha Allahu daga yau komai zai daidaita tskanin ki da yaya ash insha Allahu

Karamin murmushi tayi tace" Uhmm toh Allah ya sa ,ta karashe a sanyaye
Nan sukayi sallama ta cigaba da dube duben ta
Wasu haddadun bunches na red roseflower tagani masu shegen kyuw anyi rubutu " "only for my soul" Murmushi ne ya kufce mata lokaci guda takai hannu zata dauka wani

hannun ne mai taushi mai laushi ya sauka akan nata
a tsorace ta juya tare da ja baya,
Murmushi ne kan fuskan sa
Yace im sorry"
Ni ma yamin kyu ne,ashe kuma kin rigani ni"
Batace uffan ba ,sai cahn ta dan kalle sa tace ena wuni yaya ashraf

Lpya jasmine ,ke da waye anan din
Nika dai ce ,tace tana dukar da kanta kasa ' gaba daya mood dinta ya canza
Don ta tsani ganin sa ma amma sam shi baya lura da hakan,

Sa hannu yayi ya zaro mata abun na ta daga sama
Ba kunya ya tambaye ta'
For someone special i ques?
Da kyar ta dago tace
No,
Its mine..

Hmmm toh ko zaki bani ne? I like it yafada yana lura da ita
Shiru tayi batace uffan ba ,
Ta juya zata var wajen

Jasmine, tsaya,. yace amma sai ta juya masa baya
Uhmm Nace ba? Yaushe zan zo na amshi amsa ta ,
Ko har yanzu baki kammala tunanin naki bane
Wani dumm taji a zuciyar ta
Ita kam ma harta manta da wani yataba cewa yana son ta,
Kinji kuwa? Ya sake maimai tawa
Nan ta budi baki tace naji
Ban gama bane yaya,
Tayi sauri ta wuce abun ta,
Lumshe ido ashraf yayi ,don a duniya ba abunda yake kauna kamar jasmine ..komai nata irin na matan daya ke so ne barin ma
Dirin ta dayake dada rikata shi inya ganta
Shiyasa ma bai boye ba ya gaya ma mahaifiyar sa wato hajiya hadiza wacce take aminiya kuma yar uwa ga ammyn su

Itace dai ta dakatar da magana don shi ya so ace ta nema masa izini wajen ammy ya fara neman jasmine tun tuni

Cikin sauri sauri ta kammala packaging iya
Abunda ta samu ta dauka duk da ma taso ace wannan bunces din rose din na ciki
Ana kammalawa ta bar wajen


Gefen ashween kuwa Kamar yadda yake haka nan ba wani canji,white tshirt ya sa da jean yana kunshe a dakin sa ba abunda ya ci ma cikin sa tun safe'sai ruwa da dabino kwalli uku

Wajajen karfe 8 saura bayan ya kammala sallar ishai ya nufo cikin gidan
Nan ya hango ta sanye da hijabi tana tafiya bata ko lura da shi ba

Daga kai da zaiyi don ya hango enda zataje nan ne ya lura da motar dake parke cikin compund din nasu
Haka kawai yaji ransa ta cunkushe lokaci guda
Amma sai ya dake yana kallon karshen zancen

Daga gefe ta tsaya
Da alamun wanda yake cikin motar yayi iya kokarin sa ta shigo ciki taki
Shine sai ya sauko da kansa ya zago enda take
Shidai baiji mai suke cewa ba
Gani kawai yake ashraf na famar murmushi ita ko jasmine kanta na kasa ko kallan sa batayi
Daga karshe gani yayi ya bude motar sa ,ya fito da gifts bags har biyu a cike dam da kayan shoping,
Sannan ya mika mata wannan bunches din roses din
Bai jira yaga ta karba bata karba ba kawai ya juya a fusace ya koma cikin dakin sa da sauri ya fada kan gado
Numfashi sosai yake saukewa kamar wanda ranshi zai cire,
Take yake jin wani irin haushi da fushi sun lullebasa,
' shiruu yayi yana rarrashin kansa ,
Da kyar ya samu ya nitsu,"
Juye juye yake abun na dada dawo masa a ido"
Nan ya tashi ya zAuna," cikin ransa yana cewa wato ashraf ne yarinyar nan take kulawa ?
Shikuma Marar kunyar yaro ai tuntuni na fahimce shi sonta yake yi' which is imposible jasmine ba ta shi bace har abada,
Ya furta a zuciye,

,kusan karfe 9 saura yana famar sake sake a ransa haushin ganin ashraf din da kuma abinda ke damunsa sun gama sauya masa yanayi
Komai ma haushi yake bashi,
Magani ya hada ya sha enda gajiyayaen Bacci yayi nasarar daukar sa

Ko minti goma baiyi ba da baccin
Ya rike kansa idonsa gam, amma jikin sa sai karkwa yake yi, juyi yakeyi yana karkada kansa da sauri
' muryan sa ne ta soma canzawa yana kiran" lailah,...lai...l..ah.
Kar ki tafi ki barni,ki bude idonki nace ...zan .rrra..m..aa miki,
Lailahhhhh ya kwalla ihun sunan firgit ya farka a tsorace
Zufa na keto masa ko ena'
Sai xare ido yake ,yana haki.

Wanda yayi dai dai da shigowar jasmine ganin shi hakan ya sa ta
Cikin sauri ta tsiyayo ruwan sanyi ta mika masa tare da cewa sannu
Wani kallon fushi ya bita da shi
Bai karba ya dago kai ya ce lpya?
Meya kawoki nan din...

Wani iri taji aranta gashi ta yi kyu don kuwa special dressing tayi domin sa, haka ta daure tace
Dama na zo ne ....

Taji ya daka mata tsawa
Kinzo me? Ya fada rai a bace
Tsoro ne ya soma kama ta,amma sai ta tino da maganar salma
Akan cewa kar ta na nuna masa tana tsoran sa
Batare da bata lokaci ba
Ta dauko gifts din ta ajiye masa a gabnsa
Batace uffan ba
Sai da ta juya zata tafi tace happy bufday"

Daga ido yayi ya kalle ta ya kalli abin data ajiye masa chraf idon sa yayi artabo da wannan bunches na rose flower daya gano a hannun ashraf da zu
Baisan lokacin dayayi wani irin shot da kayan ba
Sai da ta ja baya da gudu dan tsoro
'are you crazy? Ya fada a tsawace yana yiwu kanta
Hmm

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login