Showing 180001 words to 183000 words out of 219669 words
Chapter 61 - So Makamin Cuta Complete Hausa Novels Compelet By Surayyams.txt
akan harkan business, murde murde,da warware dukkan wani matsala komin girman sa ..
Dan dole ashween ke kiran sa da sir fadhul don dama yasan ya kai ma ya haife biyun sa ,
sai kuma gashi yana bashi kulawa ,so, kauna da girmamawa cikin amana irin na asalin uba.
Ashween ya zo daf ana sa shi a wheel chair alaman an fito da shi daga life surpoting machine ba dadewa ba ,
Sai ya shiga jera masa sannu sannu,yana masa addu'ar sauki
Mr fadhul ya nuna farin cikin sa na zuwan ash sosai , don haka ya sake neman alfarman su akan ya biyo sa suje gidan sa.
mamakin ash ya ke binsu bayan dankarrun motan da suka zo daukan sa ,
Wani anguwa daban yaga anyi da su wato victoria island.
Anguwa ne wanda ko wa ya san ta kafa tarihi wajen ajiye masu kudin gaske har da na barazana a garin lagos.
Cikin wata mansion aka sauke su.
Ashween yayi gum baice komai ba don kansa a daure yake,sai yana bin tsarin gidan da ido ya dan tabe baki ,wato motoci tsadaddu tsaban sunyi yawa wasu a waje aka jera su.
Sai ma da yaga an soma bada mr fahdul girma da gaisuwa na ban gajiya ya dada shiga zulumi
Yace toh lallai in har wannan duk mallakin mutumin nan ne to ba aiki ya kawo sa company na ba,
Haka suka shiga ciki daga shi sai ashween
aka barsu a wani daki suna zaune
Nan ya dubi ash ya ce,kayi hakuri nasan na takura maka yau kuma na shiga hakkin ka,
Ash yace bakomai
Mr fadhul ya gyara Yace masa ba komai bane ya sa ya na kira ka nan illah yau nake so nayi cikan burina na karshe a duniya,
Sai ya soma hawaye,
ash yace ayi hakuri sir Allah ya dada baka lafiyan amin ,
Mr fadhul yace,nasan baka sanni ba sai a companyn ka amma ka sani lallai kai ka kasance da na ne na hakika,
Ash yayi shiru don abun ya soma daure masa kai kuma amma bai tanka ba
Mr fadhul ya kuma daurewa yace ashween da na, nasan bani da lokaci sosai a duniya yanzu.
Amma zanso ka biyo ni na nuna maka wani abu,
Ashween dake shiru ya tashi Ba tantama ya bisa ciki
Enda idon sa suka ci karo da katoton hotan jasmine a manne a bango.
Ash yayi sauri yaje gaban pics din yana nunawa yace mata ce fa?
Cikin kallin mamaki ash ya sake ceawa How comes,ena ka sami hotun matata haka ,mr fadhul baice komai ba
Ya dada buda ma ash ya ga hotunan kala kala manne a bango iya kallon ka,
Sai ya kyale sa har idon sa ya kai kan hoton asalin jasmine din sa wasu na tare da shi wanda sukayi a dubai, uk, har da wanda sukayi a ukraine tun lokacin da ta samu cikin farko,.
Sai aka barshi da tantancewa chan ya dawo ya dada duban na farkon yace kai amma wannan kamar ya baci da jasmine,ya kalli mr fadhul yace isshe ur wife? Sistr or ?
Toh mu kuma meye na mu da sa hotunan nan mu anan sir, ash yayi dan dariyan karfin hali,don ya san shikan sa a birkice yake ya kasa dago mr fadhul har yanzu..
Shi kuwa bai kula ba sai da yagama tattaro abubuwa ya baza a a kasa ya kama hannun Ash zaunar da shi nan ya zauna ya shiga zayyana masa labarin rayuwar sa kaf ba ragi.
Mr fadhul Yana kuka ashween na kuka,Ash tun yana jin haushin sa har ya dawo ya karaya ya soma tausaya masa sosai a ransa yana jin nadaman san har na taba kokon zuciyan sa ,
Duka suka kasa rarrashin juna,
Da kyar ashween ya dago yace yanzu me kake so nace ma jasmine,nace baban ta na raye yana tare damu, yana kula damu all this while amma yaki bayyana mata kansa?
Mr fahdul ya riko hannun ash gam gam cikin jimami yace, i dont know son,nidai bana so na sa jasmine a kuncin rayuwa ne ko da na seconds daya ne.
Kayi tunani en har zata kalle ni wata rana zata tuna da ni nayi sandiyar mahaifiyar ta akan wata ya mace,kuma na barta ta rayu cikin maraici.
Yadda kake son ta ka kuma rike min amanan ta haka nake maka addu'an Allah ya so ka ya kuma rike amanar ka kamar yadda yayi,nasan kanada ilimi,amana da tarbiya da gaskiya ka taimaka min ka sa yata ta yafe ni ko su shahida da yar uwan ta hamida zasu yafe min"
yace Ashween Kuyafe ni, lokaci na ne yazo yau, nima kuma zan baku aman junan ku kar ku rabu da juna ku har abada ku kasance masu hakuri da zaman duniya
Bai bari ash yace komai ba ya kira lawyers dinsa
Da shaidu ,sai ya ma ashween kyautar biron ban girma da ya mallaka a hannun queen elizabeth of england na jajircewan sa da basiran sa.
Yace d'a na,ena fatan duk abubuwan da nake daura ka akai ka na fahimtar su sosai ?
Ashween da kansa na kasa sai Ya gyada akai a sanyaye yace eh,
Sai ya dauko files yace masa yayi signing duka a gaban kowa yana gani.
Ba musu yayi hakan
Sannan mr fahdul ya soma masa bayani yace wannan arziki na ne wanda na bar ma yata jasmine halak dinta ne in kaje ka bata.
Sannan ya sa masa letter a ciki nan ma yace duk abata
Sai ya dauko dayan file din yace wannan shine na rayu akai na kai har enda kake tunani na kai yanzu a kwarewan aiki zan bar maka su a matsayin garkuwa da kariya.ba zaka taba fadi kasa ba har karshen rayuwan ka da izinin ubangiji,
Allah ya maka albarka ya baka farin ciki mai daurewa..
Ash ya amsa yana kokarin tare hawayen sa.
Sai ya bashi wani file kuma yace wannan na jikoki na ne ,nasan bazamu hadu ba amma kace musu su yafe mun ena son su, nan sai ya fara tari mai tsanani..
Ash ya rike sa a birkice duk aka dawo ana saisaita shi,
Sai yayi kokarin conrol da kyar yace ma lawyers ga ashween shine kadai dangin na anan ku tabbata an mallaka masa komai dana bar musu,
Kalman shahadar ma bata kai karshe ba sukaji shiruuu Allah ya karbi ransa...
😪😪😪😪
*surriem*
[23/08, 05:43] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*NI Dai a bar taheerr yaci uban sa, besty ba wani tausayi abunda ka shuka ....tam😪😪*
*Godiya marar adadi for all those surayyahms LOVERS da nake gani in many groups witout even thy knowledge ,those that choose me personally and think am a perfectly writing model ...may Allah love u the way u love me ameen.🌹*
*and Am gratefl to everyone that dosnt even know me but yet believe in me.ilsmuch🌹*
*Pageâ–¶78*
Bayan mutuwar mr fadhul a Nan lagos Ashween ya zauna yayi duk abunda ya kamata akan bison mr fahdul shi da aminin sa kamal,
Bai bar victoria island ba sai da akayi sadaqan uku,
Kafin nan an mallaka masa duk wasu takardu,IDs,da duk wani abunda ya shafi mr fahdul.
Nan ya kama hanyar abuja a zuciyan sa ba abunda yake kawowa kamar da ace a hannun sa jasmine take da sai yayi kokari ya kawo ta taga mahaifin ta ido da ido, ko da kuwa gawar san ne..
Gefen su zahida kuwa yanzu aka soma rayuwa, tuni ta soma jambade akan arzijin mahaifiyar ta ta tana shirin kafa kanta ,..
Sai dai sun rike amanan juna sosai da su jabir da jamal, duk da basu tare yanzu kowa yayi alkawarin ba zasu taba rabuwa ba ko don mahaifin su.
Cikin kwana ukun Zahida Ita kadai ce yanzu a mansion din rodriguez ,
gaba daya duniyar ta samu a tafin hannun ta, ita take mulki sai abunda ta ce ,a fuskan ta akwai annurin cikan buri da sanyin zuciya.
Amma sam cikin zuciya ba haka yake ba,
Tun da tayi juyi taga ita kadaice ga kuma dumbin arziki da mulki sai take jin rashin kwanciyar hankali,
she knew deep within her heart she is not happy, sai tana jin ta very lonely and left alone.
Hakan ya sa ta ke yawan zama shiru ta rasa meke mata ciwo.
A gidan mamy kuma ,Ganin jasmine din ta warke yasa Hajya hadizan kaita gidan wasu matan larabawan sudan masu gyara irin na amare,
tunanin ta tunda akan kishiya zata zauna tana so amata gyaran da karya wani namiji ya ce zai raina ta.
Jasmine bata san duk wannan shirin na miye bane ita dai ta kwantar da hankalin ta ne don abun yanzu yafi karfin ta.
Yau aka soma auna ta wajen gyaran sai mamy tace musu a gida za'a na mata saboda har yanzu da aure akanta ba zaiyu tana fita ba.
Nan aka gama biyan su a kayi komai akan in suka shirya zasu soma aikin su.
Abban ashraf ne ke jan motar sai hj hadiza da jasmine a baya...
Dai dai wannan lokaci ashween ya dosu kwanan anguwar su mamy.
Duk hankalin su baya wajen amma ita kam tuni ta sa ido tana leken sa kamar ta hadiye ranta don murnan ganin sa..
Ganin ta sakankan ce ta juya baki daya,ya sa mamy tace jasmine? Me haka ne, yau kuma wani sabon salon zama ne kika samu
A razane ta dan ja jikin ta sai ta kasa amsa wa tana mutsu mutsu,
Abban ashraf na shiru sabida shima ya gansa ta madubin motar sa,amma sai ya kau da kai.
Suna kaiwa bakin kofar gate a lokacin ash ya dan iso daf ,nan ne itama ta gan sa
Sai ta dafe kai tace tsaya nan abban ashraf kar ka shiga gida dan Allah,
Ba musu ya ja suka yi parking
Kowa ya fito ..
Ashween ya tsuguna a al ladabce ya gaishe da Abban ashraf
Wanda ya amsa masa cike da girmamawa da tausayi
Sai ya juya, kansa akasa yace ena wuni mamy, tausayin shi take ji yadda ya marairace fuska kamar maraya
Cikin dauriya tace bana bukata,
Fata na takardan yata ka kawo min.
Abban ashraf ya budi baki yana kallon mamy cikin damuwa a ransa yace wannan wani irin fitina ne hadiza ta sa a ranta game da yaron nan.
Ash yayi kamar baiji me tace ba, yace kiyi hakuri mamy na zo wajen jasmine ne,mamy kiyi hakuri ki barta na gaya mata abun da nake tafe
da shi pls na roke ki
Cewar sa hakan yasa jasmine ta soma satan kallon sa, duk sun dauka har yanzu akan maganan da yake so ya fada tun farko ne
Mamy tace ,tabbbb lallai ka cika marar kunya
Toh ba da ni ba ,ni dai nace jasmine bazata saurare ka ba ka kama hanya kabar mun kofar gida na.
Sai ran abban ashraf ya baci sosai yace haba hadiza, wai meye hakan ne?
Cikin fushi ta dakatar da shi ta soma hawaye tace
Kawai ya tafi ya bar min Yata bana son wani magana
Ashween ya mike tsaye a sanyaye bai kara kallon kowa ba ya
Nufi motar sa yayi gaba..
A ganin sa inya takura zai iya haifar da wani tarzoma tsakanin abban ashraf da mamy
Nan jasmine ta sa kuka mai dauke da fushi ta koma cikin gidan da gudu
Cikin bacin rai abban ashraf ya shige shima cikin gida ya bi bayan jasmine din
A kasa ta zauna ta takune waje daya abba ya shiga rarrashin ta yana cewa kiyi shiru abunki ya isa haka kinji,
Ta dan gyada kai, abba ya cigaba da bata baki har saida ta sassauta
Yace jasmine kar ki boye min komai nasan kina so ki saurari mijin ki haka ne?
Tayi shiru chan anjima sai ta gyada kai a sanyaye tace eh abba.
Yace toh Alhmdul, amma meyasa bazaki fada ma mamyn ku ba? Nasan duk tana haka ne don ke.. amma ku sani Allah ma akan masa laifi ya yafe ya kuma ba mu wani dama bare dan Adam ajizi..
Tace Abba ni tsoro nake ji, kar na matsa mamy na sake komawa wajen sa wani abu ya sake faruwa in na dawo nan mamy zata min fada nikuma bansan enda zanje dagabnan ba ammy na ta mutu...ta karashe tana tare hawayen ta.
Abban ashraf dake jin matukar haushin abun aransa yace, ba ga ni nan ba? Akwai wanda ya isa ya ki karban ki agidan nan ne.?
Jasmine ki saurare ni,ni bazan takura ki ba amma ena so kiyi tunani, kije ki same ta ki fada mata kina son mijin ki ,kuma kina so zaki saurare shi,
Duk abunda ta gaya miki ko ta miki kizo nan ki same ni ni san me zanyi..
Amma yanzu na baki dama kiyi tunani..
Ta amsa cikin kuka tayi masa godiya ya fice cike da tausayin ta.
Ko zama baiyi ba ya nufi site din mamy ya soma balbale ta da masifa
Har ya fada mata magana marasa dadi.
Kuka take yi amma sai tayi taurin kai, tace masa tana kan bakan ta,ba zata bada jasmine ba.
Har sai da suka shafi sama da awa biyu a a hakan sannan ta sauko akan zata gaya masa dalilin daya sa take yiwa ashween wannan tsatssauran hukunci akan jasmine.
Nan ya zauna yana jin ta .wanda yayi daf da zuwan jasmine bakin kofa da niyyar gaya ma mamyn abunda ta yanke game da shawaran abban ashraf
Sai ta kasa shiga ta rakube jin abunda mamyn ke fada
Mamy ta kwaso labarin mahaifin jasmine da mahaifiyar ta da duk abunda ya shafe ta ta sanar da abban ashraf
Cikin tsananin jimami tace, waya fada maka bana jin zafin abunda nake ma ashween,?
Na fiku ji amma ya zame min dole na tarbiyan tar da zuciyan sa da tsauri akan jasmine.
kai kana ganin Ena zan sa kaina in na bari jasmine ta salwanta, ta wulakanta akan kishiya?
Na san yana sonta amma ni halin maza nake gudu, .
Bana so in bashi a sauki ne na fiso in bashi yanajin a ransa ko sarauniya zai aura jasmine dole ta zamo ciwon ido musu.
Nasan hakan bazai hana komai ba amma nayi iya kan kokari na ne tsoratar da shi yasan ba da wasa muke so ya rike amanan jasmine ba,
Zan bashi matar sa ma na ,amma dan Allah ku saurara min na sama mata yancin ta Pls abban ashraf ka fahimce ni
Jikin sa yayi sanyi musamman akan labarin iyayen nata da yaji sai tausayin ta ya dada balbale shi,
Yace Allah sarki yarinyar arziki rayuwa bai mata adalci..amma Allah shi ya san dai dai.
Jasmine da ta riga ta sulale kasa bakin kofar tana silent tears mai dauke sa tsumayin tashin hankali sai ta tashi da kyar ta bar wajen ta wuce dakin ta
Abban ashraf yace toh Ni dai tunda suna son juna zan so a gaggauta wannan lamari komai ya zo karshe a maida ta dakin ta..
Mamy tace insha Allahu kwanan nan zan maida ta ku bani lokaci kadan,
Kaima sai ka taya ni atleast na samu na gyarata kadan don akwai damuwa a ranta.
Abban ashraf yace ba komai,Allah ya shige mana gaba
Hakan ya kasance a gidan kullum jasmine na kukan abun a boye amma sai ta ki nunawa kowa ta bari a ranta,
Har aka fara Ana zuwa ana gyara ta
mamy da abban ashraf gaba daya suka taru suna nuna mata kula da tausayi na musamman acikin kwanaki
Ko nawa ne kudi sukan kashe akan ta duk da ma har yau ashween na sa mata kudi a acct din ta after 2weekS ko fiye,
Bayan sati guda sai ta dawo very cold and silent
Cikin ranta tace dole tayi yunkurin gyara abubuwan dake mata ciwo ko zata samu sauki ta wani bangaren.
Ba bata lokaci ta shiga tura ma salma tex amma ta kasa kiran ta saboda kunya da nadaman da take ji akan yadda suka rabu..
Ta san itace da laifi gashi ta na ganin muddin tace wa mamy zata je gidan su salma za taga kamar hidiman ashween ne ,sai ta cigaba kullum tana mata sakon tex mesage
Salma na gani amma bata taba amsawa ba
Duk da ma tariga tasan zuciyar kawar nata ya sauko tana cikin bukatar ta,amma sai ta fiske itama ta sa aranta zata neme ta amma bayan zu
Ranar juma'ah da yamma lis ashween Ya shigo mansion din rodriguez
Ko ena ya duba ba zahida
Sai da ya fito mai aiki tayi masa nuni da ita achan bayan gidan wani bangare da aka yi kabarin mahaifin su
Zahida zuciyan ta yayi tsanani wajen rashin samun sukuni ta tsaya kamar statue gaban tomb din baban su tana silent tears tana kan maganan zuci..lallai duk wanda ya rasa familyn sa ya rasa wani fannin farin cikin rayuwa komin yaya bakin halin su yake.
Sanye da bakin kaya riga ne sharara mai shegen kyau iya sawon kafar ta breeze da rairayin iskan shuke shuken wajen na blowing suman kanta
Sai hawayen dake bin idon ta..
Har ya zo wajen bata sani ba
Sai da ya tsaya gefen daman ta shima hannun sa cikin aljihu,
Yace i gues ure happy now,
Sai da tayi wani hadiyan yawon kunci don tanbaya ne wanda ya kamata ace ta amsa da yes tunda ta same Ashween, ta samu dukiya ta kuma sa hidayat a wani hali,amma kuma sam sai ta kasa
Ya jawo hannun ta ya dan rungume ta ya rarrashe ta, nan sukayi zaman su wajen gaban kabarin
Ash yace mata kiyi hakuri zaki saba kwanan nan.
U just need a break yaci ace kije wani guri daban ki huta kafin ki dawo nan zaki ji sauki sosai
Tana gefen sa ta ce haka ne, ure right baby.
Sai ya tambaye ta kabarin waye wannan kuma a gefe, don dai shi an gaya masa zahida tana wajen tomb din baban ta amma da yazo kabari biyu ya gani.
Sai ta dan goge tears dinta ,tace she s lailah my sister
Su ne wayannan twins din da tun da suka shigo rayuwar mu ake samun matsala.
I hate them soo much sune cursed din da hidayat ta haifa mana .
Maganan yayi masa zafi sosai ,yayi mamakin irin bakin zuciya da tabewan imani irin na zahida.
Cikin dauriya yayi murmushi yace, hmmm zahida kenan,kiji tsoron Allah mana..kinsan mutum bai zama maka wani fitina sai dai in Allah yayi ikon sa don ya