Showing 108001 words to 111000 words out of 219669 words
Chapter 37 - So Makamin Cuta Complete Hausa Novels Compelet By Surayyams.txt
jasmine ta haska don gaba daya ji take farin cikin yau na daban ne tunda ga salma.
Hatta cook nana saida ta fahimci haka don gaba daya suka ruda waje da suruutu wai tana ma salma girki.
Ba laifi sun kammala komai suka jera akan dinning,
Nan suka yi zaman su falo
Wanda yayi dai dai da shigowar su zahida su ukun su
Tana gaba ta bi ta ishi kamal da zance
Tuni jasmine ta dauke wuta jin muryan zahida sai aka bar salma da bin su da kallo,don wani irin kallon banza zahidan ma ta musu duka a takaice ta dauke kai kamar bata gan su ba
Ashween Ne last din shigowa a baya
Ya dubi salma ya sakar mata murmushi
Dan ledan hannun sa ya ajiye daf gefen ta
Wanda ke dauke da fresh pure grapes wanda shi kansa kamal baisan aena ya siyo su ba
Yace kina lpya ko?
Tace sannu da dawo yaya ash na gode...
Nan ne zahida ta kyale kamal ta dawo da hankalin ta kan su duka
Ba kunya ta ce baby waye wannan kuma,?
Cikin mamaki salma ta kalle ta
Kamal yace ' baby sai ka fada mata.
Ash yana kallon salma yace my wife,
Zahida Ta galla masa
Wanda ya sa kamal dariya sosai
Yace to maida wukar kar ki cakke min shi.
She s my wife ya tallafo salma ya janyo ta jikin sa yace itace mata na da nake fada miki
Nan ta mika hannu ma salma suka gaisa bayabo ba fallasa
Jasmine kuwa tuni ta harde karamin tsaki taja ta tashi ta haura sama abun ta.
🤐🤐.....🖊 mon amour my ppl kuna coments ana kari ❤..zahida na gaishe ku harda kari😊😸
*surriem*
[23/08, 05:42] +234 806 071 2446: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*littafin BABA MAI KOSAI*
Daga alkalamin marubuciyar bandariya da nishadi *AZUMIN ILU,ILU a BIRNI* da *HAKURI Da MASOYI*
wato *maman mamy* mai buhun nishadi,cikin salon ta na taskar bada dariya tazo ma na da *baba mai kosai* .ku biyo mu mu jibgi kosai ba wasa🤒😸
*Ena ta jira ena hange kar ku bari wannan lokacin yazo ya wuce ku ni naga draman don nayi harsashen soyayyan dake tahowa littafin HARSASHEN SO* daga alkalamim shaharariyar kamilar marubuciyar zamanin nan wato mrs *MEELAT MUSA*
ku zo muje mu leko 🤒🖊
Allah ya ba mu lpya dani da fans dina da dukkan yan uwa musulmi, mom khadie da ja'afar Allah ya dada baku sauki!
*Page▶51*
Kan gado ta koma ta na sauke numfashi duk haushin ta har yanxu bai ce mata komai ba amma kuma ai gashi ya dawo tare da zahida .
Wato wacce ya damu da ita kenan yaje ya nemo itakam ko oho.ta dan tabe baki tayi karamin tsuka
Nan cikin juyin nata taji an bude kofar,
Salma tace ke meye haka kin wani tafi kin barni nikadai
Tayi shiru ta sake yin juyi alaman tana fushi
Nan salma tace ikon Allah jasmine bana son iskanci fa kowa ready ya ke
Ke kawai ake jira aci abinci,
Tace too, sai yanzu kuka san dani awajen
Ai dama hade min kai kukayo,ke kuma
Har da wani gaisawa da ita ta karshe tana harar salman
Salma ta fashe da dariya
Tace daya daga cikin halin ki da nayi missing a wajen ki kenan
To ni dai bani da lokacin ki ehe, ki tashi muje muci abinci yaya ash ne fa yace ki sauko
Ta turo baki tace yaya ash? Toh bazan zo ba ya mutu mana in banzo na ci ba.
Bude baki salma tayi tace laaahhhh jasmine mijin kin ne zai mutu ?
Ta dada turo bakin tace eh mana, ai kina kallo bai ko kulani ba daya zo gidan kuma fa ahakan yafi sati fa awani wajen ni bansani ba.
Salma ta tabe baki tace to yi hakuri mana uwar gida ran gida....kemabai baki kula shi kuma kinga ai basu zauna ba
Pls tashi muje kar ki kashe min su da yunwa
Nan ta tashi tana turo baki tace toh muje
Amma wallhy darajar yaya kamal yaci, indai dan su biyun nan ne sai dai su mutu ba zan zo ba
Haka dai salma ta ke lallabata har ta sa ta sake shiri ta gyara make up ta sake feshe ta da turare mai dadi mai sanyi
Jasmine Duk Tana yi tana turo baki tana ta kukkuni har suka sauko.
Su kamal sun zauna ready amma Ba wanda ya taba abincin don komai fresh aka jera yadda ashween yake so,
Ita kanta zahida Allah Allah take ayi serving din su tsaban hidiman tadi ta manta da chan kafin yaje abuja itake serving dinsa abinci na munafurci a gidan
Cous cous ne da garnished miyan oguleaf wanda kayi shi kamar pepper soup amma ba abunda babu aciki.
Sai sukayo fresh carrot and ginger drink mai kamshi komai an jere su gwanin sha'awa
Suna tahowa Sai yauki jasmine take musamman da taga ya dan kalle ta farkon hada idon su
Nan salma ta dan ture ta alaman kar ta zauna sai tayi serving din su duka
Ba musu ta soma aikata hakan
Zahidan gaba daya sai satan kallon ta takeyi don bata so haka ba .
But kamal ya dauke mata kai da hira ba yadda ta iya dole tayi missing wannan chance din
Nan jasmine ta shiga serving dinsu gwanin sha'awa as matan gidan
Kowa ta sa masa tana zuwa kan zahida ta sa hannu ta karbe serving spoon din tace no thnks
Zan sa da kaina
Jasmine Ko ta amsa ta sake mata spoon ta juya abunta dama bakin cikin hakan take ji aranta
Tuni tayi tsiinin baki ta zo gefen salma zata zauna
Nan ma salma ta mata ido alaman kar ki sake ki karaso nan wajen zauna gefen mijin ki jor
Har ta soma sauya fuska zata bijire amma Lura da yadda taga zahidan ke satan kallon sa ya sa kawai tabi shawaran salman ta zauna
Tana zama Sai da ya dan juya ya kalle ta cikin mamaki don baitaba tunanin zata ma zauna kusa da shi ba
Wajen shiru Kowa santi yake, ana hira jifa jifa,
Ita dai zahida she is not so comptble saboda gani take bakin salma da jasmine daya tunda taga kamar friends ne
Hiran ma in bawai kamal bane ya kwakwulo ba mai cewa kowa komi a tsakanin su ukun awajen
Ashween kam, ba a magana don sosai ciwon kewar matar sa ya motsa musamman daya ji ta daf da shi,
Dama ya dade bai ganta tana cin abinci gaban sa ba ,sai yanayi kamar baya kallon ta amma in reality yafi kowa gani da yaba kwalliyar nata a zuciyan sa.
Ana kammalawa haka salma ta sa ta agaba suka soma clearin don tuni salma ta yada cewa ai jasmine ne tayi musu dinner,kamal ko sai yabawa yake har da cewa taci kyautar car.
Karamin tsuka zahida ta ja aranta don duk hankalin ta bai kawo yar wannnan yarinyar zata iya dafa food haka ba don taci sosai ba karya,
Zahida ta dubi ashween dake zaune shiru tace baby,i need to talk to you
Wannan abun ba karamin kona wa salma rai yake ba amma sai ta bisu da kallo
A ranta tace hmm i wonder how jasmine take zama a gidan nan da wannan fitsarriyar mata dube ta fa,msww
Nan kamal yace mata itama mrs, bafa inda zakuje hirar yau damu za'ayi
Tayi murmushi ta amsa don taso ace sun koma daki ta tambaya jasmine meke faruwa?
Su ukun suka zauna wajen ana hira, kamal sai tsokanan jasmine yake don ya fahimci ba a dai dai take ba,daurewa kawai takeyi ana hirar da ita
Kusan minti 20 sai ga Ashween ya fito daga site din zahrod,
Wani abun ya sake gullin ta Ta kalle shi, tayi saurin kau da kai nan ta mike tsaye tace salma tashi muje mu kwanta bacci nakeji
Kamal ne yayi saurin goyan bayanta yace tohm gudnite,
Salma tace Allah ya tashe mu
Ashween dake jin su Sai ya tsaya yana kallon su duka
A ranshi yace kaji min mutanen nan sai kace hirar munafurci ena wajen zuwa ana tarwatsa taro ko..hmmm
Salma kam kamar Allah Allah take su cige daga ciki,
Bayan sun kimtsa sun dawo sun zauna kan gado
Hakan salman ta sata a gaba tafada mata meke faruwa,kuma wacce xahida? Don ita tunda tasan jasmine tace yanada gf amma bata san wacece sabuwar ba inba tania ba
Nan jasmime ta zauna ta bata labarin komai duka abunda yake gudana
Duk dama kafin tagama salma ta rarrashe ta yafi sau 30.don idon ta har sunyi ja tsaban kuka.
Shiru salman tayi don Labarin sosai ya sa jikin ta yayi sanyi.
Ta sani sarai a yadda tasan jasmine da soyayyar yaya ash abune mai wuya ta zauna da kishiyar waje acikin gida musamman a wannan yanayi
Amma kuma a wani bangaren salman ta fahimci abubuwa masu dama a ranta sai tayi shiru tana nazari
Nan ta cigaba da bata baki ta rarrashe for the last time
tace mata suyi bacci ta kwantar da hankalin taa insha Allahu daga gobe matsalan ta akan su zahida ya kare..
*To Allah ya kaimu gobe muna jiran salma*🤒
*surriem*
[23/08, 05:42] +234 806 071 2446: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*littafin MUGUN MIJI na REAL ME DAMBU CE,..*
*Yana nam tafe da salon sa mai bam tausayi da tsatsar jarabawar zaman aure..Allah ya bamu da sauki*
*ku biyo mu dai real me dambu ce akan seat din*
*Wannan shafin naki ne my kakus UMMU FARHANA i missed u kadan kadan.😛*
*Page▶52*
Da safe jasmine ita kadai ce a dakin tana kokarin tsame jikin ta tafito daga wanka ,don tuni kamal ya kira matar sa suka samu kebewa so salma bata nan lokacin
Tana cikin hakan Bata hankara ba taji sallama har ta dan razana sai ta juyo
suna hada ido sai ta yi saurin control ta dauke kai ta dake sannan ta daure fuska ta cigaba da abunda take yi zuciyanta na bugu.
Fuska ba yabo ba fallasa yace ' jasmine pls
Ena son magana dake
Juyawa kawai tayi ta kalle sa sai taji wani irin mugun haushi ya turnuke ta, komai sai ya dawo mata fresh musamman ma tafiyar da yayi ya bar gidan bata sani ba.
Nan ta dauke kai cikin wani sqbon fushi Ko ta juya ta kalle sa
Har sai da ya sake maimaitawa sannan tace
Ai gani nan ,ena jin ka.
Yace ba anan nake so ba meet me in my room ya jiya zai tafi
Cikin fushi ta juya tace ni? Allah ya kiyaye na je dakin ka neva..kawai ka fice min in bazaka fada anan din ba ta karashe har muryanta na bari
Baice komai ba Ya danyi shiru sannan sai ya juya zai fita
anan suka ci karo da salma wacce tuni ta hango ranshi a bace ne don idanun sa sn riga nuna hakan
Sai tayi saurin wazkewa ta masa murmushi tace ena kwana yaya,
Shima murmushin ya kwawulo Yace lpya lau salma ya kuke..( don sosai taga alaman yafi abokinsa zumudin babyn dake cikin nata)
Bata amsa ba sai tayi dariya mai dauke da kunya ta shige ciki
Shima nan ya karasa dakin sa
Zaune ta same ta ta hade kai da gwiwa ta rasa me yasa ta masa hakan alhali cikin ranta ba hakan bane
Zaman shiru salma tayi tana kallon bata tanka ba sai chan ta dafo ta a hankali tace jasmine ki sassauta ma kanki mana.
Wai ke bazaki facing reality kibar feelings dinki a gefe ba ko?
Cikin wani kukan da bata san daga ena yafito ba tace salma na kasa cire abun araina ne ,i think
I cant ,
Wallhy haushin sa nakeji har yanzu.
Salma ta soma rarrashin ta tana dan tapping bayan ta ahankali,
Chan data samu ta nutsu
Tace " jasmine nasan ba lallai bane abunda zan fada ya miki amfani
Amma da zan baki shawara ki zauna kiyi dogon tunani akan lamarin nan.
Nan jasmine ta dago ta kalli salma tace nayi tunanin nan salma, duk da ma na fada miki Na lura akwai munafurci acikin lamarin
Amma har yanzu nakasa fahimtar yanayin dana gansa
i think abunda yake aikatawa ne agidan nan yake boye min ,nan kuka ya sake subuce mata ta ce"" don an raina ni sai akawo min wata mata har gida sannan a maida ita matan gida?..to ni wallhy bazan dauka ba im tired.
Salma tace to laifin waye ne,? Kinga laifin sa ne in ma yayi din.
Ta galla mata harara tace kamar ya fa..ohh laifi na ne ko salma?
Salma tayi ajiyan zuciya tace"
To Kiji abunda kike fada mana jasmine
Kince munafurci suke shirya wa tunda kika zo gidan nan,taya akayi kika sani?
Tace ai nafada miki, jin su nayi suna magana times witot number a haka na dinga bibiyan hirar su har na fahimci me take nema dani,
Salma tace good,
Toh meyesa kika zauna baki binciki halayen mijin ki kin sani ko daman asali hakan yake ba? Ko dama kin taba kama shi dumu dumu ne
Tayi shiru sannan tace a'ah ni ban taba ganin sa ba, sai ta kamo hannun salman tace but how?., ban gane Ya zanyi na gane halinsan
Salma tace , ai shi ya fi sauki jasmine,
To ta ya akayi kika gano munafurci zahida take miki ?ai kema sai ki lura sosai da shi,
Kinga anan zaki fi sanin ko yana aikata wa ko baya aikawa..amma yanzu kam ai zargin sa kike yi kike wahalar da kanki kuma kinsan ba kyau zargi ko?.
Ta dan turo baki tace,nasani uhmm to shikenan, indai hakane zan ko bincika komai da kowa da kyau a gidan nan
Salma tace, yaewa yar gari, yau ma zamu fara ba ita wawiyar tana bin su offfice ba kinga kenan takan ta zamu fara kafin tadawo ai bata isa ba mune da gidan,
Nan suka yi dariya tare harda tafa wa
Salman tace ko ke fa?
To Ki tashi to mu shirya kafin su fito.
Nan suka kimtsa tsaf
Anan ma salma itake sata abubuwa dayawa
Duk da ma ba son ranta ba.
Ko da su ashween suka sauko su jasmine sun riga sun kammala shirya break fast cook nana da karime na taya su
Tuni salma ta bude ma karime ido suka karbe keys din da zahida ta bata ajiya na stores fin gidan dama chan jasmine ba sake mata take yi ba sai taji gidan ya mata dumi tsoro tam ya cika mata ciki.
A shirye suke kan dinning harda zahidan tasha gyaran gashi bata sa ko dangwali ba,duk dama tayi kyau kam
Amma sai taji ranta ya cunkushe ganin yadda jasmine ta haska
Yau ma stil kusa da shi ta zauna sai dai kowa ya kasa gane masa don iya magana awajen ashween baice uffan ba ,
Bayan sun kammala Kamal ya ma salma sallama
Suka fice office su biyun da shike zahidan ta riga su tafiya abun ta,don tun jiya take jin gidan a atakure bata iya tsula tsiyar ta ma jasmine yadda take so.
A gefen su jasmine kuwa Suna zaune a daki salma tana kan scolding din ta akan rashin kammala amfani da wasu abubuwan da mamyn ta bata
Tayi tsuru tsuru sai kukkuni take ,tana cewa ita ta gaji ne,
Salman tace..uhm uhm kice dai kin zabe wanda kike so kikayi
To wallhy baki isa ba jasmine ena gidan nan sai kin yi amfani da kowanne
Ahaka suka kammala musun su
Ganin ko ena shiru ya sa suka setin hanyar mission din su ,
Tafe suke Har kofar dakin zahida suna hira jifa jifa suna dariyan su
Suna kaiwa setin wajen ta ji sautin tv na kanyi shikadai Nan mood din jasmine ya sauya tayi kamar jikim ta ya mutu
Salma tace meye hakan,? Ya ena magana kin wani saki jiki ko
Nan ne dakin na ta ,?
Ido kawai take fitarwa Sai kuma tayi shiru
chan da taga salman na kan kallon ta tace ehhh enaga nan ne
Salma taja tsaki tace kaji min iskanci wai ke da gidan ki baki ma san ko ena ba? Bata kula ba tayi shiru
Nan salma ta dan tura kofar amma sai taji gum a kulle
Jasmine dake tsaye kamar ruwa ya kwaso ta tace tunda a kulle yake salma
Kawai mu tafi ni bana son tsayawa anan wajen.
Salma tace bazamu tafi ba
Ai ba dan ita kadai mukazo ba
Nace ko ena sai kin duba agidan nan tunda gidan naki ne.
Ai Itama a Karkshin ki take
Jasmine tayi shiru ,bata ce komai ba
Nan salma ta hakura da masifar ta dawo tace wannan kofar fa?
Ko dakin oga ne na biyu?
Nan Jasmine ta dada daure fuska ta kauda kai
Salman dake lura da ita tace ,
To ai dole na tambaya naga dai kema akwai room dinsa a site dinki
Hala itama hakan ne ko?
A fusace jasmine taja tsaki tare da bangaje ta gefe ta ture kofar da karfi cikin fushi,
O.m.g Wow salma tace tana karasowa cikin dakin
Uhmm Gaskiya ne wannan shi ake kira haduwa versus wargajewa
Jasmine kinsan me gaskiya ban taba ganin tsararren gym kamar wannan ba? Kai gaskiya u missed tunda baki zuwa nan
Jasmine da tuni ta daskare bata ko jin ta shiru tayi don tuni brain din ta ya riga yayi hitting dinta ashe fa dakin data ji kukan zahida da ban dakin da yaya ash ya fito daban
Nan ta soma kawo tunanin da kyau tana
Warware yadda ta gansa ai tuni zuciyan ta ya karaya ta sulale kasa tayi tsuguno ta dafa kai
Da sauri salma ta dawo ta riko ta tace lpyar ki kuwa jasmine?
Me ya faru?
Ai kamar an kunna ta,nan ta shiga ruwan hawaye'cikin ranta tace menayi?
Nan Ta tashi ta ja wo hannun salma zuwa bakin Kofa don ta tabbatar da kyau
Tace salma nayi laifi ma yaya
Salma tace bangane ba jasmine? Me kike nufi kin masa laifi
Tayi nuni da dakin zahida dake kulle tace inhar nan ne dakin ta to tabbas ba tare da shi take wannan karan ba she just used me.
I saw him here,tayi nuni da kofar gym din
Tace , ko da yake min magana ranar hannun sa na jikin wannan kofar ne