Showing 126001 words to 129000 words out of 219669 words

Chapter 43 - So Makamin Cuta Complete Hausa Novels Compelet By Surayyams.txt

14 Mar 2026

4088

nata tana binsa da kasallaen kallo , shiko bai fasa ba cikin sanyi murya yace na kawo? Jasmine Ya kamata kisha tea fa ko bashi kike so bane? Pls say sumting

Ta girgiza kai ta dada matse hannun sa tace ni bana son komai kawai kazauna anan yaya bana son katafi,

Dan murmushin yayi ya gyra zama Kallon ta yake har ya karaso daf da fuskan ta yace ,but i want u to take sumting kinga baki da lpya fa ,and im guilty i know is all my fault..

Tace uhm uhm...pls do wat i want ta langwame masa wuya tana kashe murya, sai yace toh shikenan angama madam nan ma yayi kissing hannun ta yace gani nan anan yadda kike so
Tayi murmushi batace komai ba,
Dan Shiru ne ya dan ratsa wajen da shi kowa na kallon kowa sai yaji bazai iya barin maganganun da zuciyan sa ke fada ba
A hankali ya shafo gefen fuskan ta, yace jasmine im so proud of u, u make me happy,nagode.

Dauke da murmushi fuskn ta Tayi kissing hannun sa itama a zuciyanta tace u desrv it my ruhi,im urs har abada
Jin bata amsa shi ba
Yasa ya dada shafo kanta yana maganan sa ,nan taga ya dan ja bedside drawer sa ta jikin bango wani waje tagani na daban
amma sai wajen yadan banbanta da asalin kalar wajen

Duka hannun sa biyar ya manna sai wani wuta blue ya kawo nan wata karamar kofar glass ta budu da kanta .

Ido ta sa Tana kallon ikon Allah
Nan mA Taga ya zaro wani karamin box dan karami a ciki sannan bai kuma taba abun ba sai ya danna wasu abun daga wayar sa tuni gurin ya koma ya dawo bango da kansa kamar ba'ayi ba ,sai ya tura drwersa da kyau ya juyo

Abun ya burgeta sosai har Ta so tayi xclaiming amma sai ta dan ja aji, ta bishi da ido bata tanka ba

Fuska ba yabo ba fallasa Hannun ta ya riko ya tallafa ta zauna suna fuskan tan juna
Sai Ya manna mata kiss sannan ya bude box din ya ciro wata ring.

Waje manyan manyan idonta suka fito in xtreeme suprise a yayin da taga ya na sa ma dan yatsan ta wata shakikiyar diamond ring wanda daga gani kasan special ne akayi sa.

Tuni taji wani shaukin dadi ya lullube ta har ta budi baki zatayi murna ya rufe mata shi da hot kissses saida suka kusan dauke numfashin junan su

Nan Yabi ya mayar da ita kan pillow ya bita da smiles mai kayatarwa
Ita dai idon ta nakan ring din Murya kasa kasa tace i like it. Na gode sosai

Sai ya da yi kunya kadan, ya kasa cewa komai.

Daga nan Ko magana basu samu damar yi ba aka turo kofar dakin
A nitse ashween ya juyo..
Zahida ko ganin su hakan ya sosa mata rai sosai Har ta fizgo zata soma tada bayanai
Amma saita tuno yanzun nan madam hidayat ta surfa ta awaya akan karta manta tabi jasmine sannu a hankali

Nan Sai ta wayen ce, ta karaso wajen su tana cewa baby lpya kuwa naga jasmine haka a kan gadon ka?meya faru wht,and hapend to her room

Fuska ba yabo ba fallasa yace uhmm, bata da lpya ne ,and im due ya fada yana kallon jasmine din da ko taji da mutum ya shigo wajen

Leko ta Zahidan tayi Badon ranta ya so ba tace
Ohhh, im sorry
Toh Ai sai aje asibiti ko. come i will take her tayi yunkuri tare da saurin miko hannu kan jasmine nan ya dan ture hannun tan gefe yace ah 'a yanzun muka dawo daga nan.

Ranta nan ma ya sosu sosai ,burin ta dai a daga jasmine a gaban sa don har cikin kokon ranta take jin kishim yanayin su
sai tayi saurin cewa to bari na tayaka mukaita room dinta ai zaifi mata nan din ko ?

ba tare da ya kalle ta ba yace ,no thanks. Nace yau a gaba na zata zauna ai ni nakawo ta nan din ,
If u want to help pls go and her make break fast naga ko zata iya ci.

Tayi kak cikin ranta tace iyeeee. Maganan shin har shake ta yake yi tsaban takaicin abun a ranta
don aganin ta bata ga dalilin ma da wata mace zata kwanta nasha nasha haka agaban sa ba da sunan ita causin ba,

Abun na cinta sai ta kasa daurewa ta ce baby ciwon yayi tsanani haka ne whts d problem pls?

Ya daga mata hannu yace zahida pls, enough of this questions in baza kiyi abunda nace miki ba just ba lemme be ,bana son hayaniya fa,i just ssid someone is sick here ya karashe tare da maida kallon sa kan jasmine da tuni ta narke ta shagwabe fuska kamar baby mai shirin yin fitina.


Nan Zahida Tayi saurin dauke kai tace o.o..k..shikenan
I wil get d break fast nan ta fice a fusace zuciyanta na kururuwan haushi,
amma kash !! burikanta dana mumyn ta akan sa sun hanata tada boma bomai da yau da ba makawa sai ta daga su.


Ficewar ta keda wuya ya riko hannun matar sa Murmushi suka sakar ma juna kamar munafukai sai ya kara kissing fore head dinta suka cigaba da kallon love din su.





😍kikiki love is blind my people
😍zahida taci sunan drama "a fool for u"🤣😂👯🏻‍♀i lov her tho😛



*Mrngs💋 so whts ur review akan wannan ena jiran amsa*🤒




*surriem teamSMC🤝🏼*
[23/08, 05:43] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*



💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_


_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥



*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.



*Page▶55*





Kusan mintina 20 suna zaune sai soyayar su suke faman sha tana kan zuba masa rigima gashi dama sunyi mugun missing juna a dan kwanaki da suka wuce suna fada.

Su biyu ne a dakin amma kamar ba su nan don ciki ciki suke maganan su kamar wani zaiji su
Ashween gaba daya ya wani bada hankalin sa kamar yana deban lectures tana rike da hannun sa shikuma ya dan tallafo kansa daf fuskn su na kallon juna


Yayi nisa bai jin komai ji yayi ta dan tsame hannun ta cikin nashi da dan sauri ta juyo tana kallon bakin kofa

Ido hudu tayi da karime dake bin zahida da tray din abinci,

dama a gidan kowa da yadda yayi speacilising a fannin girki,
Ita karime ba irin counry food da bata iya ba har dana gargajiya ita oe dafa musu in bukata ta taso
don har catering clases ashween ya sata lokacin farkon zuwan ta gidan duk dama bai cika zama ba

ita kuma cook nana ta san kan continental dishes da kayan kwamulashe amma sai dai bata da hayaniya sosai kasan cewar ta tadan manyan ta kadan kuma bazaura ce.


Ashween Bai juya ba yana zaune daf da jsamine ,har zahidan ta iso tayi tsaye a kansa .
Baby ga break fast din,

Yace ok, nan karime ta ajiye gaban sa akasa tayi saurin ficewa ta basu guri

Bai jira ba ya shiga budewa yana gani ba laifi pepper chicken ne wanda yaji komai da komai gwanin sha' awa sai akayi dan french mosaic na breadi wanda yaji koyi sai tea wanda aka hado masa kayan qamshi, mint da kayan yaji,

Wai a hakan duk sun kure a daka ne wajen girkin don muddin jasmine taci zata samu qwari ta warke.

karime ce tabi ta ruda zahidan tun a kitchen tace mata ai sanyi ne ke damun jasmine shine take barbaran namiji ,
sabida haka Ta san maganin ta yanzu zata warware in aka hado mata breakfast mai kayan yaji yaji..


Jasmine Kallon abinci tayi sai ma taji ya fice mata akai, don tasan bata bukatar wani abu daga wajen su biyu har cikin ranta.

Ya kalle ta tare da kashe muryan da baisan ma yayi ba yace 'oya tashi haka food is ready,ya dan zare mata ido yace
Kar kice min kuma ba zaki ci..

Tayi shiru ta shashantar da fuska
Tana son tayi magana amma sai ta kasa yi

Tuni zahida ke aiko mata bomabaman harara
Ita dai Tayi musu tsayuwan babakere ne tana jiran taga me zai faru

Ganin ya nace sai taci ya sata dan dole ta amince zata tashi da kanta taci
Ai kamar da wasa jasmine tana danyin yunkuri zata mike ta sake wani uban kara sai da dukan su suka farga suka kalle ta

Zahida tace lpyar ki kuwa jasmine?

Ta shagwabe ko ta kula ta ta dube sa da fuskan kuka tace yaya ni zafi nake ji bazan iya tashi ba Allah..

Sai da yaji wani dum a ransa yace o.m.g yau jasmine zata kunna min wutar fitinan anan wajen kenan

Sai yayi saurin waskewa cikin kulawa ya ce sannu,sorry.. sannu kinji,

Zahida ta danyi tsuka ta kau da kai sai can tace baby wai nikam faduwa tayi ne? Naji tana cewa zafi take ji meye ke mata zafin?

Dama Zuciyan sa sam ba a kwance yake da presncw din zahidan ba ba don yasan inba sakalci irin natan ba ma yadda jasmine ke narke masa tana shagwaba yaci ace ta dago wani abun.
amma sai Ya mata shiru bai amsa tambayar nata ba can kasan makoshi yace eh

Ya cigaba da hidiman sa da jasmine" C'mon ya kamata kici abincin nan if not zan kai ki asake miki allura fa

Ta make kafadar ta ta wani narke tana karairaya murya "yaya ai bazan iya tashi bane..akwai zafiiiii tanayi tana shagwabe fuska tana satan kallon zahida
da tuni take cikin rudanin amsar nashi
Yace mata eh kawai...,amma bata san na wani tambayar tan guda daya ba ne ya amsa"shin faduwa jasmine tayi ne ko wani ciwo ne ke mata zafi wanda ita bata ma ganshi ba.
ganin bata lokaci ne wannan muhawarar a zuciyan ta sai ta hakura ta Kada kai Ta dan tabe baki ta sake kura musu ido tana jin sa

Yace ok relax ni zan iya ai, as long as zaki ci abin ci, nan ya shiga serving abinci tayi kifi kifi tana wurga ma zahidan kallo
Wacce tuni hankalin ta ya koma kan ashween dake faman aikin hada abincin a kasa kamar ba shi ba

Zahida Ta rasa meke mata dadi aranta duk sai taji ta daburce ta kasa kamo setin tashan draman da akeyi agabn ta ,
a ranta tace wai ni meyey ma'anan wannan rayuwar yarinya tabi ta zame min kashin kifi a wuya? Yar uwa mai kamr kishiya, amma baby bai gaya min sun shaku haka ba ai, ji duk ta gama kalmashe zuciyan sa da sakarcin banza
Munafuka kawai, ai ena nan bana motsawa daga nan ,
Yar iska jarababbiya ai tunda bai taba jiki na ba ba jikin wata shegiyar mace da zai taba eheh..
Ta kuma karashe maganan tare da dago kai tana bin jasmine din da wani mugun ido,

Jasmine da ita ma ta gama dura mata buhun zagi a ranta tace aiyau ba daga kafa wallahy sai dai ki haukace babu enda zaije haka nima ena nanike da shi anan,wawiya karuwa kawai.im first, yarinya na miki nisa kuma sai kin gane kuran ki a gidan nan muzuba

Dai dai nan ya dago kai lokacin duk sun kammala maganan zucin su yace ma jasmine shall we?

Zahida dake magana kasa kasa tace kut man uba , shall we what?me za ayi kenan.?chab di

Jasmine kuwa ta gyada kai kamar wata salihar kyanwa tace ehm, sai tayi saurin mika masa hannu ta bishi da wani killer smiles alaman ya dago ta

Shikan sa baisan lokacin dayayi complying ba fuskan sa cike da kaunar ta
Ya tallafo ta kadan Tuni ta dan fada jikin sa da dabara tana sauke wani susutaccen nishin shagwaba tana dan kakkame shi
shikuma bainkula ba ma aka barsa da ce mata sorry yana lallashin ta a dabaran ce,ya dauka ko zafin ne har yanzu

Lokacin Bakin zahida a bude yake tsaban mamaki tana binsu da ido, gashi ba halin tayi magana don ta sani sarai inyaga dama zai ce zai haura mata and she knows deep can cikin ranta ba dadi, she is already chocked up abu kadan zai iya sa tayi bursting yanzu

Ganin bazata iya tsayawa tana ganin sun ba , ta karaso Cikin wani shakurraren Murya tace baby,, c'mon ure doing so much, kabari mana na taya ka kula da ita, i think zata fi jin dadi in mace yar uwan ta tana kusa ko? Wai Me amfani na anan wajen.

Baice komai ba tukun Ya dada gyara ma jasmin zaman pillow ta jingina bayanta sannan yace ma zahidan ok fine, amma
Zaki iya bata a baki? Kinga zafi take ji har yanzu bata warware ba, she cant stress ya dan kashe ma jasmine ido da wayo ,tayi murmushi

Zahida ko Fadan hakan dayayi yasa Ta watsa masa hara bazata tace ,uhm naji,ai sai ka tashi kuma ni anan zan zauna ai

Ba don ya so ba ya ja gefe tayi saurin maye wajen sa daf jasmine ta zauna

Jasmine bata ce uffan ba ,don ta riga ta gama hada abunda zata mata cikin ranta
Nan zahida ta zauna ta soma yunkurin dauko abincin sama
shikuma ya ja gefe yana kallon abunsa yana binta da murmushin kauna tana cafkewa.


Zahida Kamar bazata deba abincin ba don idonta ya gama cicikowa da tsaban haushi da kunan rai

Nan dai ta dangwalo abincin dan kadan zata bata a bakin jasmine tayi sauri ta kau da kai gefe tana yatsine kamar taga kashi...
Nan yayi saurin cewa meya faru kuma jasmine? tace bana son wannan fingers din nata ne yaya zai cakke min ido..ta karashe cikin muryan kuka

A fusace zahida ta dangwala spoon din ta sunkuyar da kanta cikin takaici ta na kallon well polished nails dinta daya ji cotex yayi kyau
sai tayi shiru tana calming kanta ranta na kuna tana maganan zuci, wallhy mum kin cuce ni da kika ce kar na ci uban yarinyar nan, bura uba..hmm"
Ta tabe baki a hankali

Nan Maganan Ash ya dawo da ita yana cewa jasmine yi hakuri ba zai cakke ki ba, ba ga spoon ba c'mon eat kinji?

Ta turo baki cikin shagwaba ta juyo tana fuskantar zahidan alaman ta hakura,

'Jiki ba kwari zahida ta sake debowa wannan karon da dan yawa acikin spoon din
sai ta kai zata bata a baki ba laifi jasmine ta bude bakin zata amsa

Ai kuwa Zahida na kaiwa kan harshen ta tayi saurin tofarwa ta bi ta watso mata shi a fuska tuf tuf,tufff,,sannan ta hau yin tarin karya

A hujajan zahida ta sake spoon a kasa ta channa ihu ta riko idanuwan ta dam tace ouchh my eyeesssss.. '
Tuni ta danyi gefe cikin radadi tana jimamin barkwano a idon tan

Shiko ena ma ya san ena take ,tarin da jasmine take yi ne kawai ya ruda shi don haka ruwa ya rarumo a bottle ya yo kanta yana mata sannu jasmine 'cikin kula yace da barkono ko,? Im sorry yanzu za acanza miki wani

Ta langwame ta dan damko sa ta nayinbtarin kadan kadan tace yaya bni ba barkwano bane da zafi ne, ya kone ni ne sai tabishi da sassanyar kallo innocently.

Ba shiri Ya zauna a gefe Ya tallafo ta da niyar ganin bakin nata daya kone bai sani ba har ya ture zahida dake fama da idon ta agefen su cikin azaban radadi

Tana ji Ya shiga lallashin jasmine din kamr zasu gogi juna.

A lokacin Wani irin jiri ne ya ke neman rufe zahida ga zafin barkwano a ido ga jasmine ta bi ta narke gaba daya ta susutar da shi sai hakuri yake bata

Chan abun daya ishe ta sai ta sake ta tsala ihun sunan sa,cikin bacin rai tace baby ido na faaaaa

Nan ne ya juya kadan yace toh kitashi mana ki wanke idon zahida
Nan Tayi saurin hadiye hawayen ta tace pls baby help me bana gani

Yayi ma kamar baiji ba yana rike da hannun jasmine din da tayi shiru tana dariyan abun aranta, har zahida ta sake cewa babyyyy magana fa nake ..yace oooooooh zahida pls ki tashi mana ke karamar yarinyace kam i hate dis fa? Ya bi ya dan daure fuska sounding very annoyed.

Nan Bakin ciki ya gulle ta Duk abun duniya ya cunkushe mata arai sai tayi yunkuri a daddafe ta tashi tsaye hannu a ido tana tangale Ta galla masa harara a fusace ta shige bath room din sa kamar mayya

nan ta soma wanke fuska tana goge wa a hankali sai uban Azaba datake ji

Ta kai mint 10 cikin batrum din ta rasa me zatayi musu guda daya sai kawai ta fashe da silent kuka cikin ranta na kan tafasa,
Tace wannan wani irin abun kunya da cin zarafi ake min, ta kalli jajjaywn eyes dinta a mirror tace wallhy yau da badon badan ba,ko son da nakeyi wa ash bai isa ya hana ni tarwatsa rayuwan yarinyar nan ba.
I hate her, i hate her sooo much ...ta fada tana dunkule hannu tana dada kallon kumburaren idon ta dayaji yaji yay ja


sukam Kafin ta fito har sun koma dai dai shiru kakeji aahweeen har ya dawo ya zauna a position dinsa yana famar bata abincin a baki Tana karba a nitse

Bude kofar bathrum din zahida tayi a hankali ta tsaya tana binsu da kallo musamma shi ashween dom alokacin ji take kamar ta je ta shake shi ta huce,

Da gefen ido jasmine take duban ta amma sai tayi kamar bata san da shigowar tan ba, dai dai ya kai mata a baki ta karba sai ta dan riko hannun sa ta karbw spoon din tana murmushi ta debo dayawa shima ta bashi abaki cikin kula har tana taya shi rike habansa kadan alaman sauran kar ya zubo waje

Ta dube sa tayi murmushi shima ya mayar mata don shikam harga Allah bai san zahida ta riga ta fito ba

Boyayyen hawayen nata ne suka sauko tayi saurin goge su Nan ta zame a hankali za ta bar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login