Showing 192001 words to 195000 words out of 219669 words
Chapter 65 - So Makamin Cuta Complete Hausa Novels Compelet By Surayyams.txt
witch,
Wai wayace miki ena bukatar taimakon ki?cioin zare da ido da masifa ta cigaba da cewa
Ohhh i see' haukan ne yau ya taso ta kaina ?mrs hidayat tayi shiru tan bin zahida da kallo,
anan ma
Sai ta dan jawo ta da karfi in a disrespecting and disgraceful way tace hidayat maza ki bar min nan gurin kar ki zubar min da mutunci na don ke bashi kike da shi ba wicked monster, ta karashe tare da tura ta gefe,
Mrs hidayat ta tsaya shiru gashi angama chinchirindo a kansu ana kallon ta,, ranta a bace yake amma cikin zuciyan ta ta kudiri niyyar duk ritsi sai ta fada ma zahida maganan nan amma ya za'ayi tafada wannan Babban magana agaban mutane? Take tayi kasa ta zube kan gwiwar ta ta kamo kafar zahida don tasan zahidan tan akwai rauniin zuciya
tuni saita sauya murya kalar tausayi tace haba zahida ,ni fa uwa ce
duk da nasan na cancanci duk wani wulakanci awajen ki.
Amma ena so ki daure ki saurare ni na gaya miki abunda ke tafe dani dan Allah..
bazan iya fada Anan bane don ena kaunar ki sosai har yanzu yata ki tuna fa nina raine ki na kula da ke pls beauty ki saurari mum din ki mana..
Zahida da tuni abun ya ratsa ta amma sai fiske ta dada daure fuska, tana so ta saurara amma Sai ta kasa yanke hukunci don sam sam bata jin ko digon yarda tsakanin ta da mrs hidayat yanzu..
Kawai sai ta juya zata koma ciki abun ta mrs rod tasake dukar da kai kasa tace zahida pls dont go and leave me here ki saurare ni kiji
Zahidan ta ja tsaki amma abun na dada damunta ta sai dai takasa furtawa,
Ko da ta juyo
Bata ce ma mrs komai ba
kawai sai ta sauke bala'in akan mutanen da ma'aikatan da suka taru suna kallon Draman
Cikin seconds kowa ya watse itama ta shiga ciki sai da ta shiga office ta zauna sannan tace aje ace mrs rod din ta shigo
Tayi murna sosai don har ta fara tafiya ganin zahidan taki aminta da ita..
Nan tabi bayan security aka kawo ta gaban zahida.
Tace nagode yata daman nasan kinada imani gurbata ki ake so ayi..
Tuni zAhida ta mata wani banzan kallo tare da mata hannu tace dakata malama
Na baki minti 5 ki fadi abunda zaki fadi kiyi waje bana bukatar bata lokaci na dake..
Gum tayi da bakin ta tana wani hadiyan bakin yawu nan bada bata lokaci ba ta soma bata labarin komai har da yadda tayi da saminu har da ce ma zahida ai tinda ya munafice ni kema zai miki shyasa dole ya muti ko ya ta?
zahida na shiru har ta soma bada labarin na ashween
da yadda tayi ta gano ashween ne lateef sannan ta soma kokarin kawo mata wasu alamomi tana dada zuga ta,tana cewa ki duba dai da kyau ki gani zahida Ashween shine lateeef fansa kawai ya zo dauka akan ki..
Still Zahida na shiruuuuu tana kallon mrs rod, da ta gama sakankan cewa tana dada koro bayanai don sosai ta shirya maganganun ta dama
Chan sai Zahida ta jingine baya tare da lumshe ido nan ta sake Wani mahaukacin dariya mai sautin ban mamaki
Tayi sosai har hawaye na droping tana nuna mrs hidayat da hannu kamar kashi take kallo ajikin ta amma dariyar kawai take bata ce komai ba
Mrs hidayt tuni ta ja baki tayi shiru don harga Allah ta kasa gane kan dariyar zahidan izit for her?ko againts her.?
Ta dai daure tace zahida pls believee da gaske na
Ke fada miki wannan magana, kar ki ji komai ena tare dake bazan barki ba,zan taimake ki plz zahida
Nan zahida ta yanke dariyan chak ta taso in full ta karaso gaban mrs rod daf da daf
Tace sake maimaita min naji?
Kikace wai lateef shine Ashween? Ba tantama
Mrs rod tace eh shine, sai fas zahida ta dada wanka mata mari akan bakin ta
Abun yayo mata zafi sosai ta kame bakin sai ta dago jajayen idanun ta nan taci karo da na zahidan shima wanda babu alaman wasa aciki
Tace tufff da bakin yawo munafuka makiran mata, ashe bazaki saduda ki bar min rayuwata ba?
Why did u hate me so much mena miki a duniya ta fada a raunane idon ta suna shirin cikowa"
A daburce Mrs hidayat ta budi baki zata yi magan a
Zahidan ta daka mata wani mummunan tsawa tace" amma kin ma cuci ashween da kika hada shi da mummunan danki nakasashhe,? Tirrrrrr Allah ya kiyaye
Dube ki? Oh din ana miki kirarin kin haifi kyawawa is dat why ure now claiming my man?
To ai ba sai kin masa sharri ba wai to Meya sa zaki rabani da shi bayan kin rabani da iyaye na?
Look,U must be a fool da zaki sake tunanin ni zahida zan yarda da ke da kuma wayannan ridicoulous tales dinki na karya da munafurcin da kika shiryo, am tired of ur lies hidayat just get out of my life..tayi mata nuni da hanya a fusace
Mrs rod dake cikin wani yanayi na kunci da rudani ta kasa motsawa sai hawaye sai ta dukar da kai kasa gwanin tausayi tace kiyarda dani zahida ashween dan uwan ki ne he's just fooling you..
Abun ya ishi zahidan don gani take duk dan kudin ta mrs rod ta hada wannan plan Din .
Sai ta ja cheque book ta rubuta kudi mai yawa ta wurga mata
Tace ki dauka ki fita nasan damuwan ki kena if not dont blame me in nayi miki wulakancin da dani dake ba za muji dadi ba and listen ke ..baki da mahaifar da zaki haifi ashween,domin yayi miki nisa har ki mutu bazaki haifi kyakkwan yaro kamar sa ba.
Ga hanya
...ta dan tura mrs rod da tayi zugum tana kallon kasa kalar tausayi
Sai itama ta dan fizge cikin bacin rai tace zahida nagode da kika ki yarda dani afterr all i did to u.ba kunya ta tsuguna ta dau cheque din ta ce toh na barki da Ashween zahida ya kashe ki in yaga dama, but ki saurare ni da kyau wata rana ke da kanki zaki zo ki nemi ni kuma kice na gaya miki...kaiwa nan ta juya zata tafi
Zahida tayi wani wawan yinkuri ta shagaban ta tsaya..
Ta bi ta da munanan harara kafin tace,..wannan duk ba damuwa na bane,so listen and listen carefullly ki sani duk maganan da mukayi da ke gasu nan anan ta mata nuni da recoder da secret cameras tace to walhy wallhy hidyaat ciwon kai ya taba Ashween zan miki wanin irin kisa wanda za'a kafa tarihi da shi a duk duniya
..na rantse miki in har kin ga nida hannu na ban tarwatsa ki ba to tare muka tarwatse..
Get out and neva come back forever ta gaya mata cikin idon ta..
Tsaki kawai mrs rod tayi ta kama hanya ta fice abun ta..
Zahida ta zauna kan chair tare da sauke ajiyan numfashi don bawai maganan bai shige ta bane amma sam ta kasa ganin alakar Ashween da lateef sai ta yanke kawai hauka da son zuciyan ne ke damun hidayaat ba wani abun ba..
A gefen jasmine yau ma tun safe ta bar gida ba wanda ya sani
Da shike site din ta akwai enda zaka sauko ta balcony kayi kasa ta bayan gidan
Sai ya zamo in ta yi niyyar ganin mijin ta sai kawai ta saci jiki ta fita tayo iya yadda take so sannan ta sake satar jiki ta shigo baki shiru..
Ashraf a dakin sa yana kwance ba abunda ya damu dashi sosai kamar change of behaviours din nata gashi tunda mijin ta ya dawo rayuwar ta duk wani rama da fuskan damuwa sai ya kauce ya bar ta a asalin jasmine din ta.
Shi burin sa yanzo ya shawo kanta ya sami biyan bukatar sa amma ya rasa ta ena ma zai fara.
Tunanin me yayi oho sai ya tashi ya fito ya kama hanyar dakin ta ya tarar a bude kam amma ta bai ganta
Cikin dabara sai ya zo ya tambayi mamy sai ta ce mai ai jasmine na daki tun tuni.
Nan ya fahimci cewa hala ta fice ne ba da sanin kowa ba amma where could she be?
Gashi ana neman 9.44pm na dare
Waje ya fita shima ya zauna cikin motar sa a asalin bakin gate inda ba wanda zai gansa
Ko minti 10 baiyi ba ya yaga dosuwar mota amma bai san nawaye bane'
don tuni ash ya sauya fita da wani motar da ba wanda yasan shi da ita don idan jasmine ta saci hanya ba daman daukar motan gidan mamy a napep take zuwa wajen shi.
a hankali suke tafiyar su don haka sai ashraf ya dada sa ido da kyau ga duhu ya soma yi baya ganin waye aciki da kyau
Dan daura da gidan ya tsaya charaf sai ya hango ta gaban motar alaman tana magana ne da wani sai langwamewa takeyi a jikin sa yana kissing dinta har suka rabu ta fito..
Tafiya take yi kamar bazata yi ba tana juyawa tana kallon sa don dama in ya ajiye ta har sai ta shiga sannan shima ya bace
Hakan kuwa akayi a idon ashraf sai ya daura hannun sa akai baki bude yace innalihh, tabbbbbbbbbb lallai jaraba ya kai jaraba ..yana dada leke yace ashe haka yarinyar nan take da bin maza shine ni take raina min wayo ?
Karuwan ci ashe take zuwa da Auren nata sai ya karashe da dariya mai ban mamaki...
Chan ya tabe baki kawai ya shiga gida ya kwanta a dakin sa yana nazarin yadda zai ga waye ne wannan da jasmine take fita dashi a sace ba a sani ba.
*Thnks for ur time*
*suriem*
[23/08, 05:43] +234 806 071 2446: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶83*
Tun ranar ashraf ya qudiri niyyar sa na sa mata ido don ya fahimci kan abun da kyau.
A ganin sa in har ya kama ta dumu dumu da wani namiji toh tabbas zai yi amfani da wannan dama yama razanar da ita cewa zai gaya ma mamy har ya samu biyan bukatun sa.
Ashween yana komawa gida cikin daren zahida ta kira sa don tun zuwan ta sai yau suka sake waya da shi.
Ganin ta damu tana son ganin sa ya sa kawai ya amsa mata da cewa zAi biyo jirgi kawai ya zo.
Ya katse wayar Yayi baccin sa Da kyar ma ya iya tashi washe gari da safen ya shiga harkokin gaban sa sai wajen 4.55pm ya je mansion din rodeiquez enda zahidan take..
Zahida Taji dadi sosai a ganin ta musamman ya baro lagos don ya saurare ta bata san shikam yana nan garin abuja ba
Bayan sun dan taba hira ne sai Tace baby kana chan lagos kana hutawan ka ana nan ana maka sharri
Ya dan yi mirmushi yace sharri?
Kamar ya fa..
Nan ta kar kace ta zubo masa labarin da mrs rod ta bata tsaf ba ragi
Cikin ransa yace innalihhi wa enna ilahi rajiun !! ba karya sai da zuciyan sa ya dan girgiza
Amma sai yayi saurin sa murmushi akan fuskan sa ya cigabaa da binta da ido har ta gama bayanan ta tana cewa:
Duk na fahimce ta baby, so take na dawo dai dai da ita zaman bakin ciki da kunci ya kashe ni
Ba uwa ba uba kai ma da kake so na tana so ta raba ni da kai
da karyan ta"she just hate me..
Ash ya dan sauke ajiyan zuciya kamar abun sound nothing to him sai ya saukar da murya yace
Kai, amma na tausaya mata fa,..
Kinga Baby just relax kar ki biye mata da zafi haka kiyi tunanin in kece kika saba da jin dadin duniya rana daya kika rabu da ita kika koma wani irin rayuwan rashi ya zakiyi.
and to add to that kinga ta rasa yayan ta gaba daya,a ganina abubuwa ne suka mata yawa kuma akwai matsalan brain anya kuwa bazaki taimaka ki kaita asibiti ba? As in ko therapist haka su duba ta
Shes just imagining all this things gaskiya har tausayin ta ya kama ni sosai, yanzu hala ma bata san ena ta samo labarin nan ba.
Zahida kam tuni ta takune fuska tana kallon sa cikin mamaki tace hmmm baby kenan, tabb ashe baka san qaccw hidayat ba "ena nuna maka hanya kai kana chan wai tausayi to ta haukace din mana.
O ni dai nagaya mata ta taba min kai zata sami duk abunda take nema na bala'i a duniya
Yace hey calm down zahida..ke ma sai ki nisantar da kanki daga ita kawai bana sin hayaniya
Kuma kinsan Nidai bana bukatar nace ki yarda dani akan wani abu
Saboda kinfi kowa sanin yadda muka hadu dake ena da yan uwa na and you saw my mum right?
Tace of cous itace dama take shirmen ta,nikam har na soma yarda da maganan ka kamar hidayat ba lpya ne,if not ai kaikam ma ba kasar nan ka girma ba kuma nagaya mata,
ga yar uwan ka jasmine ma ai tagan ta, in fa aka barta halaa ma da zata iya cewa jasmine lailah ce yar ta ce tunda itama kyakkawa ce
Ash Yayi dariya yace hmmm Allah dai ya kyauta, just take off this nonsense kiyi abunda ya dame ki kawai kar ki damu da wani.
Tace toh baby kwanan nan ma zata ko sha kunya in taga weding iv na zaga duniya
Nan ma yayi murmushi kawai baice komqi b
Sai tace uhmm,baby zaka jira na gama aiki na zuwa jibi kafin ka koma lagos ko?
Yace anything for you..
kinga nima sai na dan duba mum dina.
Tace ok ,tayi murmushi(dom dama bata san da mutuwar ammy ba ita)
Hakan dai sukan yi waya sama sama da zahida a kwana biyun sai da ya tabbata ya cire mata abun kwata kwata a ranta
Ash ya riga ya sanar da kamal halin da ake ciki dan kansa ya dan kulle kadan
Shawarwari kamal ya bashi sosai akan yadda zai shawo kan matsalan cikin dabara sannan ya dada sanar da shi date din haihuwar salma next month 26th don ko zaiji dama dama ya cire komai aran sa.
Take kuwa mood dinsa ya sauya ya dawo farin ciki don dama yafi kowa zumudin abun gani yake kamae mashi za'a haifo
Sai ya sanar da kamal cewa insha Allah suna dawowa daga ukraine da jasmine za su zo su duba su tare.
Washe gari Ranar da zahida zata tafi da safe hakan ma jasmine ta sake neman izini wajen mamy cewa zata je tayi updating bank cards dinta da sauran su don ta tsaya wajen sa.
Mamy ba tayi musu ba as usual sabida dama ita kam bata san ma jasmine na zagawa tana fita bada izinin kowa ba.
Ashraf ya kalle ta ya dada binta da kallo a ransa yace lallai kam kwana biyu baizo ba xa aje neman sa kenan? Amma wani tsinanane ne wannan
Nifa Naga alama yarinyar nan sai ta karar da zuman jikin ta kaf a wajen maza sannan ni zan samu
Ita ko tayi shirin ta tsaf ta sanya hijabi ta kama hanya dama sun yi dashi akan zata same sa wani wajen ne na daban ba gida ba sai su kara so tare
Don haka bata da fargaba sai ta fita kai tsaye ta hau a dai daita ya sauke ta a bakin titi,
Ashraf na biye da ita a boye yana kallo the same car ya zo ya sake daukar ta suka bar wajen
Sai ya shiga bibiyan su a a hankali yana so lallai yaga waye jasmine ke fita da shi din nan.
Hankalin sa ne ya dada tashi sosai don wani mummunan kishin hakan ke damun sa
Ya daure yan biye dai kansa sai ya dada kullewa ganin hanyar da ake bi da su har yaga suna shiga gidan ammmy
Cikin mamaki Yace kan facalin bala'i?
Dama nasan za'ari na
Wato baza ta ma hakura a sassaita su ba sai ta biyo shi da sanwar jikin ta ?wannan wacce irin mayyar yarinya ne tabi ta nanike ma namiji daya kamar ance mata shi kadai ya iya yi da mace?
Gashi Ya sani sarai security suna Nan don haka yayi zaman diris awajen yana monitoring yana hada plan din da wani lokaci ne zai samu ya shiga gidan free ya gansu da idon sa ya dada tabbatarwa shi din ne?
Cikin wannan nazarin saiga Motar zahida wacce ta kira iya kira ashween bai daga ba.
Ga kofar gate din a kulle kamar ba kowa hakan ya sata sauka tana dan bubbugawa A hankali
Tsaban kallon da Ashraf ke bin ta da shi sai da yafito don ganin tsaban kyau irin nata a fili
Sai ya shagala sosa
Cikin haka har mai gadi ya fito
A ladabce ya gaishe ta ashraf na jin ta tace baby na fa?
Mai gadi yace ai ya dan fita kai maman sa airpot yace anjima zai dawo
Tayo ajiyan zuciya tace ohk ,ba komai in yazo kace nazo,kaiwa nan ta juya
Ashraf ya girgiza kai cikin wani sabon salon yanayi yace 'tabb amma Ashween cikakken dan iska ne ,wata tana ciki wata na waje.
Hhhh wato An share ma mai gadi karya ya zo ya fada ana shagali bara a iya fitowa ba
Im sure wannan itace budurwan nasa da yake cewa zai aura kuma nima sai na bita na latsa banza na koshi yadda yake latsa mim jasmine..
Nan bai jira ba ya kama hanyar bin zahida a baya a baya don yaga enda zata je
Haka ya bata lokacin sa ranar kaf bakin mansion yana tsaye da motar sa har ta fito masu aiki ana biye da ita tana waya
cikin motar sa ya sake shiga ya bi bayan ta har ta iske airpot
Ba laifi yake sanda yana mata shisshigi batare da ya bari tagan sa ba
A Waiting area ta zauna lokacin anci kusan wani 30 minut da isowar su chan sai yaga Ashween ya shigo
Ya dada labewa ya dauki jarida yanq zaune shima daf bayan su kamar shima jira yake anan yake jin
Tana cewa