Showing 57001 words to 60000 words out of 219669 words

Chapter 20 - So Makamin Cuta Complete Hausa Novels Compelet By Surayyams.txt

14 Mar 2026

4108

ki bar ashraf din naki ba,
Ammmy ce, ko kin manta ke kika amsa mata kin amince? Ko zaki karya alkwarin nata ne?

Cikin jin kunyar abun da tayo ta sunkuyar dakai ba tace uffan ba,
Zuciyan tane ke cike tam da haushin kasa danne tunanin ta a kowani lokaci inta na gaban sa..

Chan ta budi baki Murya dishi dishi tace im sorry,

yaya naga wai kaima kanada wacce kake so ne ai kuma fa aure zamuyi

Nan ya tari numfashin ta shima yace
Haka ne,enada wacce nake so
Amma ke bazaki so ki cika ma ammy burin ta bane?

Duk da amsar ya kona mata rai
Haka ta daure ta gyada kai ta koma ta kwanta jikin sa

Shiru ne ya ratsa wajen,kowa da abunda ke masa zafi
Ganin zai iya jefa kansa matsala ya sa ya kauda tunanin tan

Nan ya takura ta suka ci noodles din
Har yayi nasara hankalin ta ya dan kwanta kafin ya fice a dakin



🙂😌




*suriem*
[23/08, 05:42] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*



💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_


_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥



*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.



*Page▶22*






Hakan rayuwar su ya kasance a gidan
Yau ana saura kwana biyu kacal da cika sati da rasuwar ammy

Hjy hadiza da har yanzu bawai jimamin mutuwar ammyn ya sake ta bane amma hakan ta daure ta soma shirye shiryen auren jasmine da ashween kamr yadda ammy ta bukata

Bangaren Ashraf kuwa ba yadda baiyi ba don yaji shirin meye mamyn shi keyi amma sam taki gaya masa komai
gashi ya jira jin amsar jasmine har ya gaji ya zuba mata ido, don shi mutuwar ba wai ya damesa chan chan bane.

Toh amma ba yadda ya iya a dole Mutuwar ammyn ya sa shi dakatawa da maganar don yasan yanzu jasmine bata hankalin ta sosai ,
tunanin sa tunda yanzu ba wanda zai tsawatar masa mutuwar ammyn ai tamkar an share masa hanyar saukin samun nasarar auren ta ne

Duk lokacin da ya tuno ashween kuma gani yake kamar bai isa ya hana shi jasmine ba
don karara yake nuna gabar sa a fili da shi.


Gefen Ashween kuwa yana iyakan bakin kokarin sa wajen kula da jasmine duk da cewa kullum sai tayi kokarin ballo maganan bata son auren nasu, a duk lokacin data fada hakan kuwa shima sai ya nanata mata itama cewa akwai wacce yake so kuma ba ita ba ce.

Duk da Abun na matukar damun sa don iya sanin sa jasmine dinsa shi kadai take so to meya faru?
Yana cikin wannan halin wayar sa ta buga kara ganin kamal ne ya sa
Bai bata lokaci ba ya dauka
bayan sun Gama gaisuwar su
Ya tambayesa salma,don yanaji jasmine din ke complain rashin samun layin ta kwata kwata

Na kamal yace ' wallhy akasi aka samu amma zansa ta neme ta kafin nazo,

Mekake nufi kafin kazo ita bazata zo bikin kawar tan bane?

Uhumm mubar wannan maganan tukun,, zahida fa zata kashe min aure jiyan nan da kyar na kalmaso salma"duk ta bi ta isheni da kira wai layukan ka basu shiga in kaji ta tamkar zata tashi sama.

Dan Karamin tsuka yaja sannan yace
Ai nafada mata bana bukatar disturbance bata ji ne kawai,
Kuma kaga bana son tasan ammy ta rasu before she starts thinking odawise..don wallhy yanzu yadda nakejin kaina zan iya mata illah.

Ohh my god ash, Hakane nasan baka bukatar ganin ta ,toh amma
Tace min dai nan da kwana uku zata dawo nigeria kuma zata shigo yola
ranar jummu'ah nan agidan ka zata sauka kamar yadda ta saba

Cikin halin ko enkula yace ""Kyaleta tazo mana ,ai ena dai dai da ita

Nan suka dan taba hirar su kafin ya tashi ya nufi dakin sa,
Ko minti biyar baiyi ba yaji turowar kofa dakin sa a hankali tare da sallama,jasmine ne a tsaye
A ladabce ta gaishe sa,sai kallonta yake don kuwa hijabin data sa bakaramin kyu ya mata ba,
Light make up ta danyi wanda ya sa ta dada fresh,tayi so cute and innocent

Dan lokaci ya dau yana starring akanta Chan ya ce, ena fata lpya dai ko?ko kina bukatar wani abu ne.

Tace, Dama mamy ne ta aiko da driver ni zan wuce

Wani garas yaji maganan a kunnen sa don har wani ciwon kai ne ya soma masa a take,
Uhum, toh Allah ya kiyaye inkinje ki gaishe ta..taKe care
Ya fada ba yabo ba fallasa
Dan karamin murmushi ta mayar masa tace toh yaya,sannan ta juya ta fice ,

Saukar ta kawai ya keji daga steps amma sai yaji kamr ya rugo da gudu ya bi bayanta su tafi tare
tunanin sa kawai kar ashraf yace zai kula masa ita a bayan idon sa,
Tuni ya zaga jikin windown ya cigaba da kallon ta
daga sama yana gani har ta lume cikin motar suka bar gidan

Itama Guntun hawayen ta ta share don tuni take jin wani mugun missing dinsa a zuciyar ta,

duk da ma tana kokunton samun soyyayr sa a rayuwar ta
wannan karon duk lokacin da sukayi sharing tare cikin sati dayan nan yasa ta sake jin wani zazZAfan kaunar sa a ranta

Cikin tunanin sa Bata hankara ba har suka iso gidan mamy,
A hankali ta sauko ta najin kanta daban sai sum sum takeyi

Gani na farko da hajiy hadiza ta mata yasa ta jin hawaye cikin ranta tace" hmm duniya kenan kowa akan hanyar sa yake 'Allah ya jikan ki hjya shahida,
Ji yadda yar nan ta jeme lokaci guda kamr bata da lpya, ohhhhhh
Allah ka bamu da sauki,

Tana kan jimamin haka jasmine ta rusuna ta gaishe ta, murmushi tayi ta kamo hannun ta tana mata jagora cikin gidan


Nan ma Basu ko kammala gaisuwar ba kiran ashween ya shigo
Enda ta tabbatar masa isowar jasmine din lpya
"
Daki mai kyau ta ajiye ta da kayan ta, domin tayi kokarin
Komi anyishi yadda ranta zai so duk da ma bazama zata yin ba..

Itako jasmine zugum take zauna gefen gado tayi tagumi
edan bata tuno ashween ba to salma take tunani"

Washe garii da safe bayan kammala shirin ta don ko fita ba tayi anan dakin tayi komai har breakfast da da kyr ta iya ci ita kadai

Ba laifi mamy ta sa baqin ta na larabawan sudan suka soma dan gyarata emergency dai dai gwargwado
komai ya tafi dai dai da shike a daki take wuni bata leka ko ena ba
kafin ace rana na biyun
Take fatan jikin ta ya dada yin sumul da tsantsi
sai dai har yanzu damuwan dake tattare da ita yana nunawa

Cikin kwana biyun sosai mamy ke mata nasiha irin intazo mata bayan isha"i don debe mata kewa,
musamman takan fahintar da ita avubuwan da suka shafi zaman auratayya sannan da tuni akan alkwarin su wa ammy

Ana washe gari daurin auren da yamma tayi nan tayi nan duk ta rasa me ke mata dadi a ranta

Nan bangaren yana tunanin ammyn nata bazata ga auren ta ba,wani na tunanin salma.amma babban fargaban ta yadda zaman su ZAi kasance da yaya ash

dan tagama bari akan auren alkawari kawai zaiyi da ita ba don ya so ba

Cikin wannan tunanin ta mike tsaye da niyyar fita sam chan balcony don ta samu fresh air ko zata ji saukun wani abun

Ita wannan auren ko shirin sa batayi va don haka zuciyar ta baya ko kawo tunanin ya goben zai kasance ""aranta tace da ma salma tana nan da bani da matsala""i really missed u friend

Tana tsaye cikin ta dafa karfunan balconyn cikin wannan tunanin taji sanyin hannun sa a kafadar ta wanda ba shiri ya sata juyowa .

Dan karamin murmushi ya sakr mata tare da cewa 'yan mata,
Dama kece yau a gidan namu ai na dauka wata ce mai mugun kamamin da ke

Kallon sa kawai batace komai ba... Jin tayi shiru bata amsa ba yace "toh
Ya hakuri,c'mon zo mu zauna

Ba musu ta bi shi suka zauna nan gefen wani dan veranda dayabi corridorn wajen zuwa matakalan kasa

Nan ta dago kai ta dube shi ta ce ena wuni yay ashraf....
Galala ya sake vaki yana duban ta kallon kurel don sai yanzun yaga sheki da dan hasken da fatar ta ya dadayi ga virgin lips dinta da suka yo pink sosai gwanin sha'awa

Gashi fuskan ta ba alaman make up sai tayi fresh and natural,
Wani shu'umin murmushi yayi ba tare da daga idon sa ba yace
Wow, baby kin ganki kuwa?
Me kika ci ne a kwanakin nan kindada yin kyaw kamr na zama angon yau haka nakeji

"" Wani dum taji a kunnen ta ...sai yanzu ta tuna ashe fa baisan da maganar auren ba

Shiko sai smiling yake yana dada dubar ta "uhm Jasmine ki ce wani abu mana,kinsan ni wallhy ke kawai nake jira dama,

Ko kina so na vaki lokaci tunanin ammyn mu ya dan kauce miki ne? Like kwana nawa kike bukata? Ai dama nayi shiru ne don naga kamar ma baki fita sai gashi Allah ya kawo min ke har gida
So,ena jin ki

Shiru tayi tana wasa da yatsun hannun ta
Wanda suka sha jan lalle fresh
Wanda aka mata a
daren jiyan,,bata iya dagowa ta kalle sa ba tunanin ta kar ta sake hurting dinsa irin na ranar
Nan ta rasa bakin magana, wani zuciyar ce ke zugata kawai ta tashi ta bar wajen inyaso goben yaji daga bakin mamy

Tana mikewa cikin sauri son aikata hakan
Shima ya bita ya sha gaban ta...

Da shike daga ita sai riga da skirt na atampa bata riga ta yafa wani mayafi ba nan ashraf ya shagala
Ba abunda yake kallo sai wuyan ta da zanen shatin boobs din ta da suka cicciko

Lura da haka ya sata soma jin tsoro
burin ta kawai ta kufce masa ta bar wajen

Baki na bari tace yay ashraf ni zanje daki, zanyi sallah ne Lokaci na kurewa
Ganin gaba daya tsoro ne fal idon ta yasa shi dada azama yana tunkaro ta yana lashe baki da wani annoying smile a face dinsa

A haka Yana matsowa tana ja da baya har takai karshen jikin karfen balconyn

' ya isa haka yay ashraf ka kyale ni mana sallah fa nace zanyi
ta fada a dan fusace

Ko ya kula ta ya kai hannu zai shafa kan lips dinta
cikin sauri ta kaucar da kanta gefe
Inda ta samu tayi wuf zata gudu ba zata ya sake cafko hannun ta
juyi daya ya dawo da ita gabansa tana fuskan tar sa
duk yunkuri da ficcika tayi amma ena ya kurman ce
Sai ma dada yunkuri da kokarin matse lips din ta yakeyi zai daura nasa akan nata

Charaf sai a idon ashween...




😹🙆🏽‍♀




*surriem*
[23/08, 05:42] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*



💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_


_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥



*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.


*Ohhhh Allah,😔🤭 im so sorry ma wanda suke gani na da chan a groups dinsu yanzu kuma basu gani na,hakan tafaru ne bisa dalili..amma en na samu sarari zan dawo..thnks*
😧😦👏🏻🤝🏼



*Page▶23*




Jasmine dake 'bari san tsoro Bata daga ido kan ashween din ba saboda yanayin yadda take karantar bala'i da fitina aciki
Nan take tayi yunkuri cikin azama, ta Ture ashraf gefe da Wani karfin da bata san tana da shi ba
Da sauri ta sunkuyar dakai tana gyara zaman rigar ta da ya cukuikuya mata shi,

Wani irin kallo kawai ashween ke binsu da shi kamar zaki mai jin yunwa, shiko ashraf yanzu ne ma ya gansa
sai ya dauke kai kamr ba ruwan sa ko kallo na biyu bai sake masa ba
Kowa yayi shiru ba wanda ya tanka
Ashween bai kara wani minti 3 ba ya juya a fusace ya bar wajen

Tana ganin haka Da gudu tabi bayan sa, hawaye ne da babu kuka tuni suka wanke fuskan ta bata ma sani ba,itadai tana Allah Allah ta iske shi amma ena kamar walkiya haka ya Bace mata..

Zuciyan ta ne ke gaf gaf kamar zai fice
Musamman data ga ficewar mota a bakin gate duk ta dauka shine yayi fushi ya tafi,

Tsaye tayi a tsakar gidan tana dan bubbuga kafar ta alaman ta shiga uku....nan kuma takawo aranta"" amma meyasa nake ganin kamar na masa laifi?

Ba ta tsaya nemar amsar tamvayar tan ba ta juyo cikin gida
dakin ta ta nufa strght jiki ba kwari ta zauna ,

Nan ma Sallah kawai tayi ta sauya zuwa dogon riga iya gwiwa ta rasa meye ke mata dadi
' tagumi tayi gefen gado tana danasanin fitar ta wajen ma yau gaba daya.

Ji tayi an bude kofar a hankali ta dago kai sai taga ashe mamy ne

Ajiyan zuciya tayi ta mike tsaye ,nan taji mamyn na cewa gata nan, shigo
Sannan ta juya ta fice abun ta,

Fuska ba yabo ba fallasa ya shigo
Tuni taji wani gaf gaf a zuciyan tan yana dada tasowa
Burin ta kawai ta bashi hakuri amma bata san akan me zata bashi ba

Ledojin shoping dake hannun sa ya ajiye mata , baice uffan ba ya juya zai fita
Ba shiri ta dago kai ta ce "uhm yaya sannu da zuwa"uhmm... umm..
Sai kuma tayi shiru

Dama shi kam tunda ya sa kai bai juyo ba don ji yake kamar ya makure ta ya huce haushin dake hargowa cikin ransa ,duk tunanin sa ya bari akan tunda tazo abunda sukeyi kenan da ashraf din
kuma dama chan fargaban sa kenan

Jin tayi shiru yasa shi sake kai hannu zai murda kofar ta sake cewa .....yaya""
Nan ya juyo ya kure ta da rinannanun idanun sa stilk bai tanka ba,

Jikin ta ne ya shiga kadawa tuni tace "ah "a ,kayi hakuri,.. bakomai,
Ko sake seconds baiyi ba ya fice abun sa

Tsintar kanta tayi da sulalewa kasa ta fashe da kuka sosai kamar xata cire ranta
Sai da tayi mai isar ta sannan ta mike ta dauro alwala tayi sallahn isha'i
Tana kwance tana azhkar har ta soma jin sanyi a zuciyan ta

Nan ne ma ta sami gwarin gwiwar daukan ledojin daya shigo mata da su
Guda uku ne, nan ta bude na farko .....
Kayan sawa ne kala biyu tsaddadu masu kyun gaske daya lace ne royal purple an masa daon silver stones masu tsada kwarai, daya kuma material ce pitch dukan su a dinke suke gwanin sha'awa da mayafin su sharara manya

Dayan ledan kuma jeweries ne komai seti hatta agogon ciki na gold ne
Sai kuma shoes da purses dinsu komai ras

Gefe ta tura su dan tasan duk don gobe ne yasa aka kawo wayannan,
Sannan ta jawo dayan ledan karshe wanda tuni ya gauraye wajen da qamshi mi dadi na abinci
Kayan ciye ciye ne exactly yadda sukan siyo da salman ta in suka fita shoping haka yayo mata shima

Ba bata lokaci ta bubbude su a hankali ta gyara takai bakin ta nan take ta soma tunowa da shi

wani bin kuma sai ta tuno da salma sai ta danyi murmushn karfin hali
Iya yadda zata iya taci sannan ta da saura wa mai aikin gidan.

Nan ma bacci ya gagara tayi juyi nan tayi cahn

Karshe Har ta yanke shawara jawo wayarta ta dago ta soma rubuta masa sako
Sai da tayi sau shida tana gogewa karshen ta
" nagode yaya, shi tayi nasaran turuwa

Shima aahween anashi bangaren ita kawai yake tunawa amma ransa a cunkushe yake dan idon sa yaki dena Maimaita masa hannun ashraf a jikin nata

Ganin sakon nata ya sa shi jin dama dama don yazan duk yadda akayi ta tuno sa ne, da hakan ya soma samun nitsuwa a ransa
Nan har bacci yayi awon gaba dashi



Yaune ranar faraqar hidimar auren nasu,tun Wajen karfe 6 na safe ta tashi don zazzAbi ke sandan ta amma haka ta daure ta cigaba da abubuwan da mamyn ta sata tayi, nan tayo
Wanka tayi sallah sannan ta cigaba da hailala da kai kukan ta gun ubangiji akan al'amarin auren nata da ashween

Bata jima ba saiga wasu mata su biyu da fara'ar su ,suka shigo dakin nata
Da shike dukansu sun manyan ta sosai ba su dauki dogon lokaci wajen debe mata kewa ba

A cikin wasa da dariya mai kama da wasan da da jika suke gaya mata ,anjima kadan wata tazama dauko riga, dauko wando, dayar tace
Saura kije kina sanya akwai masu pure water a titi zasu na kashe masa murya murya"ssssssss ogah a sai pure waterrrrrr...

Dariya sosai tayi ganin yadda matar ta ke maganan cikin barkwanci da annashuwa

Dayan tace..ah' a hakan bazai faru ba, don nasan wannan jikar tawar jaruma ce ,daga yau bashi baci ko sha awaje bare ya ji muryan wata mai pure watar ta cigaba..
Ki duba mana ki gani ko da muka shigo dakin nan ya kika ji ?...ai gamshin nasa dakin sai yafi haka ta sannan ta dubi gadon tace """ehen nashi ma sai yafi haka gyaruwa
Har na shirya ganin jikoki na ,
Nan duka suka danyi dariya da guda lokaci daya...
itako ta sunkuyar da kai kawai tayi don kunya. Haka suka ci gaba..
ita dai batasan su ba amma a cikin wasan nasu take tsintar shawarwari sosai gwanin birgewa

Gefe guda Kuma Ashraf ne tsugune sai kukkuni yake hannun sa rike da kuncin sa alaman ya karbi mari mai zafi daga wajen mamy datayi tsayin daka akan sa tana azalzalan sa
" to sai ka hana abunda Allah ya riga ya qaddara mu gani ,ta Balla masa harara
Da Allah fice min karka bata min rai

Ba musu ya tashi rai a dagule

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login