Showing 174001 words to 177000 words out of 219669 words
Chapter 59 - So Makamin Cuta Complete Hausa Novels Compelet By Surayyams.txt
karka damu komai zai tafi mata dai dai.
Cikin mamaki kamal ya dago yace kana nufin zahida zatayi nasara kenan?
Ash yadada yin murmushi yace of cous
Zatayi nasara sosai ma.
Kamal yace hmmm shikenan dai suka cigaba da tafiyar su har suka kai asibiti enda aka daura ash ana observing yanayin kansa a computer
shikuma kamal yana waje don zahidan ta sake kira lallai tana bukatar magana da ash
Wani bangaren cikin asibitin kuma mamy ne da ashraf dA yamman suna tsaye hankalin ta duk ya tashi ganin halin da jasmine ke ciki.
Tun ashraf yana calming dinta har ya yi shiru ya kyale ta.ta gama kawowa aranta cewa stressed ne da depression din rabuwa da miji ya sa jasmine take bijera wa abinci har ya mata illah haka.
yau mamy ji tayi kamar ranta ake cirewa ganin yadda jasmine din tayi ta suma ba adadi a gida.
Daga kan gadon asibiti ta bude ido dishi dishi ta hango likita a kanta,
Docton bature ne, sai sosai ya nuna tausayawan sa akanta Cikin sanyin murya yace mata ya ki keji yanxu?
Ta soma hawaye a sanyaye tace meke damuna doc?ka fada ma mama na?
Yace a'a dama basu sani bane ?
Amma ai ke ya kamata ace kin sani
Sai tayi shiruuu ba tace komai ba
Sai yace toh ki huta ni bari nayi magana da su, a hujajan ta daddafe ta damko sa ta fashe da kuka,
Yace lpya dai ko?
Tace doc dan Allah kar ka fada komai na roke ka
Kar kace na zubda ciki am going trou alot ka taimaka min pls
Abun ya basa mamaki sai ya dakata yana kallon ta tana kuka gwanin tausayi""
Yace ohh, dama da sannin ki kenan kike so ki kashe kanki?kin sha maganin zubda da ciki ya kuma zube
Kinsan muddin jini daga mahaifa na zuba mace na bukatar kulawa na musamman shine kika bar kanki ba ci ba sha? Ko su da suka baki maganin basu fada miki ana bukatar kulawa bane?so kike ki kashe ka kanki ko?
Ta dukar da kai kasa gwanin tausayi tana kan rokon sa ita dai ya rufa mata asiri kar ya fada ma kowa
shi dai baisan meya faru ba
Amma daga gani Ya san tana cikin matsala sosai"
Ya mata fada yace banji dadi ba da ya kasance kinsani sarai kika kwabar da cikin ki
duk da ma bansan dalilin ki ba, amma fa kisani
Abortion Ba abu bane mai kyau sai ya zama dole, u have no idea irin dumbin matan da suke yawo suke neman haihuwa da iya karfin su da imanin su amma Allah bai basu ba..kar ki sake yin haka, shi Allah daya baki shi zai raya miki sannan ya fitar dake da ga duk wani halin da kike ciki
Ta ce hakane doc nayi kuskure amma dan Allah kar kace mata na zubda ciki
Yace gaskiya bazan iya ba ,is againts my oath as a doc nayi miki wannan aikin karyan ,
ko ma ba don komai ba ai bazan so na sake jefa rayuwar ki cikin hatsari ba dole asan kin zubda ciki saboda a baki kulawar da ya ce
Ta daura hannu akai tace na shiga uku,nan ta shiga rusa kuka tana roko har yace calm down to ki saurare ni,zan miki alfarma daya in kin mun alkawari zaki bada hadin kai wajen Tattalin lpyar ki
Da sauri ta gyada kai tace nayi alkwari doc
Yace to shikenan ,zan gaya musu kinada ciki ne kuma ya zube baki sani ba.ke kuma sai ki tabbata kin basu hadin kai sun kula dake.
Tace zan bayar na gode doc,
Yayi mata murmushi sai ya fita,
Nan ya tarar da mamy wanda already bpn ta yana kokarin hawa duk bata jin dadi sosai
Sai ya sanar da ita yadda suka shirya da jasmine
Sosai abun ya mata ba dadi a ranta, sam bataji dadin rasa cikin jasmine ba sai tausayi ya gama balbale mata zuciya .
Amma a fuska sai ta nuna madallah da cikin Ya zube kawai ita a sakar mata yarta.
Ashraf kam har ranshi yake jin dadin abun don dama jira yake kiris ta fashe musu
Mamy tabi bayan doc akan itama a duba ta sanan ta umarce shi da ya fara yin gaba da jasmine kafin ta taho
Ba musu ya amsa mata ya shiga dakin
Tana kwance ta kau da kai tana kuka, yanzun ne take mugun jin nadaman abunda ta aikata ma kanta.
Ya tsaya yana kallon ta ,chan yace
Hmmm, ai dama wanda baiji bari ba ,
Ta juyo a hanakali tare da dakatar da shi
Ta ce ya isa haka yaya ashraf,bana son surutu
Yayi murmushi mai kama da dariya yace toh muje na kaiki gida ,nidin da aka ki dole za'a dawo min
Ta masa shiru ta daddafe
Zata sauko ya soma yunkurin kawo hannun sa
Ta kauce ba bata lokaci ta fice ta barsa a wajen
Bai damu ba yana biyota a baya yana gaya mata magana son ranshi
Gefen su ash kuwa an kammala komai an tabbatar musu he's normal sai dai a kiyaye na gaba
Amma sai yaki sam a cire mai bandage din sedative' din da aka jona masa akai don yana soothing jijiyan brain din nasa .
Kamal yace malam ance fa yanzu ka warke ka cire mana muga sarari
Ash yayi yar dariya yace ka bar min abu na ni ena so a haka.
In fact bari ma na dada gyarawa ya juya jikin wani washroom jikin madubi yana dada gyarawa.
Sauri takeyi tana so ta kauce ma ashraf dake binta da maganan banza
Ga kwarnafin amai yana so ya dago mata gaba daya taji cikin ta na yatsunewa sanadiyar ba komai aciki sai magani da dari darin ruwan allurai..
Ta kasa daurewa tayi saurin shiga washroom ta shiga kwaza amai bata lura da shi a gefen ta ba
Sai Ya dawo daf ya kunna mata ruwa bisa ga dukkan alamu amai mai daci ke fita don da kyar take fitarwa
Hawaye ke sauko mata ganin shi din ne
Sai ta soma tunanin ko dai imagining dinshi kawai take, har suka kammala tare.
ba tace komai ba
Ta mike Zata bar wajen
ya kamo hannun ta ya jawo ta jikin sa sam ya runguen ta ya kwantar da kansa a kafadar ta
Cikin sanyi murya yace,ya jikin ?.
Sai ta lumshe ido tana kan zubda hawayen takaicin komai da ya faru
Ya kara cewa forgive me for not being there for you,ba son raina na barki cikin wannan wahala ba.
Maganan san nabkashe mata karfin gwiwa Ta soma juyowa a hankali da niyyar masa tambayar'ya gaya mata me zaice mata ranar yanzu tana so taji,"
Sai dai suna hada ido
Kasa bude bakin tayi tana kallon sa ko da ba' ace ba tasan ya sha wahala sosai shima.
cikin haka ashraf ya banko kofar wanda ya sa ta dan janye wa ajikin sa tayi gefe
Ya watsa musu harara yace ohh dama abunda kikeyi anan kenan ko mamy tace ki fito maza
In kuma zama zakiyi ki yanzu naje na gaya mata tazo da kanta.
Ba musu ta fice ta barsu a wajen don harga Allah tagaji da ganin wannan fitinan
Tsaki ashraf yayi ya juya yana dariya kasa kasa yace an daiyi asara
Dai dai lokacin kamal ya shigo
riko Ash Yayi don ya hana shi tankawa har ashraf ya bace
Kamal yace relax dan Allah kar ka tada ma kanka hankali mana
Yace kamal magana zata min i see it in her eyes
Kasan ko wani abun ke damun ta ? Ni gaskiya zanje na duba lpyar ta ai matata ce, ya bangaje sa ya fice a gagauce
Kamal ba yadda ya iya haka ya kyale shi ya fita
Gani yayi gata chan gaban motar ashraf yana jan su sunkai kusan bakin gate
Ba jira ya shiga mota shima ba yadda kamal baiyi ya bashi tuki ba amma yaki roughly yake yi har Suka sha kwanan anguwar su mamy
Tunda ashraf ya lura da biyosu yake yi, yake faman tsokanan ta da mugayen maganganu
Yace 'madallah, dama karshen rashin ji kenan
Aure da dan iska kuma ai kadan kika gani,
Hakki na ke bin ki da mani kika bada jikin ki da bazan ci amanan ki ba
Ya sake juyi ya kalle su daf ya dan yi dariya mai ban haushi yace " sunan wata wai anci biredi an yada leda..
Jasmine ta kifa kai ko jinsa batayi ...bare ya dameta wani strange guilty concience ke cinta arai game da ashween amma ta rasa meyasa
Daf da bakin gate din ash ya wani wawan u turn ya sha gaban su
Ashraf ya kwashe da dariya sosai sai ya kashe motar sa shina ya fito a xafafe ya tamke fuska yana masifa
Yace wannan wani irin hauka ne kai mahaukacin ina ne?
Kamal bai iya taro sa ba don ko rufe door din motar baiyi ba ya dosu inda jasmine take abunsa
Dai dai setin kofar ta ya sa hannu zai bude kofar ashraf ya damke hannun
Yace kar ka sake ka taba min mota na wawa matsayaci,kai wai wani irin jarabbabe ne bakayi ya ishe ka ba, ai cikin ma ya zube sai kabarmu mu dana muma,
bai hankara ba yaji naushi a bakin sa
Ash tunda ya juya ya chakumo sai da ya masa jina jina kamal da kyar yayi ceto ya damke shi sosai
Sai ya fizge a hannun kamal din ya zo daf da ita don tsoron tashin hankalin nasu ya sa ta fito da niyyar barin wajen
Ash ya karaso daf ya juyo da ita y rike kafadun ta tana fuskantar sa.
Yace ,im here jasmine dan Allah ki zo mutafi kinji?
I dont want to leave u here bana son ana bata miki rai kina kuka ,i love you...
Ya kamo hannun ta ta dan janye kadan cikin bori
Kan yace zai sake bude baki ya hango mamy dake kusa daf cikin mota tana mika musu mugayen
Kallo
Nan ya dada zafafa maganan
Yana kallon ta yace jasmine dan Allah ki zo muje kar ki barni ni kadai
U know i wont hurt u i want to xplain myself to you kuma nasan kina so ki saurare ni.
Sai ya mika mata hannu ya marairice fuska alaman ta zo su tafi..
Mamy na kokarin parking
Ashraf sai yayi wuf ya iso wajen shima yace ki zonan ki wuce gida
Itako har ta gama karaya, tayi sanyi zata mika ma ashweenn hannu su tafi,
Ashraf ya chakuma hannun ta na hagu daga gefe sai Ash shima yayo saurin rike hannun da take shirin mika masa
Suka sata a tsakiya suna cece kuce sai da suka rikita ta,nan har mamy ta karaso cikin masifa
Tace kun sake ta ne ko sai na ci muku mutun ci?
Dagan gan ashraf yaki sakewa shima dan yasan ashween da taurin kai ne bazai sake ba,
Sai ta sa hannu ta zare na Ash da kyar, ita kuma jasmine ba abunda take kallo alokacin sai hannun sa dake zamewa cikin nata nan ta sake fashewa da kuka.
Ashraf yayi murmushin keta ai tun kafin mamy ta bashi odarbya kaita ciki ya soma janta suka koma cikin gida
Ko da ganan hankalin ash ya soma kwanciya
Don ya kasa dauke kai akanta musamman da take yi tana jiyowa tana masa kallon tana so ta bishin furtawa ne kawai bazata iya ba
Mamy ta watsa masa harara kamal na gefen sa ya dan riko hannun sa..
Tace malam sannu da aiki,nace ena takardan yata?
Kamal yace mamy dan Allah kiyi hakuri
Ta dakatar da shi,tace kayi shiru ena ganin girman ka kamal.
Kar ka kuma sa baki anan na fada maka
Kai kuma in na sake ganin ka zo kusa da jasmine hukuma ne zai raba ni dakai,
ka ga tunda ka raina ni daganan ai dole mutum ya bada takarda
Nonsense,
ta ja tsaki ta wuce ta barsa a wajen
Baiko dago kai ba bare abun ya kai masa zuciya kamal ya ce Ash kayi hakuri mutafi,
Bana son wani fiti na
Hankalin sa kwance yace wallhy bazan rabu da jasmine ba kamal sai dai tayi duk abunda zatayi
Lets go ,nan suka juya suka bar kofar gidan
Tun wannan lokaci mamy ke sa ta agaba tana matsa mata akan wasu abubuwan
Dan ta lura jasmine mijin ta kawai ke ranta.
Amma mamyn sai tayi kamar bata masan tana yi ba, cikin ranta tace bana bashi ke har sai nagama duk abunda zanyi ba zaki koma masa a hakan ba
Ta dawo Kullum cikin rarrashi, wani bin sai anyi masifa kafin ta ke yin abunda ya dace.
Komawar su gida kamal ya kyale sa ya huta ya tafi, shikam key ya dauka ya fice abunsa
Bai tsaya ko ena ba sai babban gidan alkalin mrs rod ,dama tun a mota ya kammala shirye shiryen me zaice don yasani sarai kaf mutanen ta yan son cin hanci ne.
Ana haba haba da shi wajen don yaje ne da asalin identityn sa
Anan ya fara dada bayyana masa kansa a matsayin ashween,
sannan ya fada masa shi ne twin din mrs rod data rasa achan baya amma bata sani ba.
Alkali ya sha mamaki sosai ,duk da ya kasa amincewa da hakan a ransa
Cikin hikima da basira ash yayi wasa da hankalin sa sosai wanda hakan ya samu yin tasiri ne saboda shikan sa judge din yaga ci sosai a harkan.
A tunanin sa to meyasa bazai bada ash hadin kai ba ga fitar da gaskiya ga ladan aiki mai tsoka...
Ash ya masa bayani yace shi baruwan shi da su shyasa yake life dinsa daban
Amma baya so mahifiyar sa ta cinye gadon sa hasali ma yana so a mika ma jamal da jabir ne,
Nan ma ya toni asirin will din zahidan yace in har ya amince zaiyi ma zahida adalci akan dukiyar ta shikuwa zai ninka masa albashin sa na this month 5times .
Alkali ya birkice da murna ya ce ban taba ganin mai adalci irin ka ba.
Amma shine kake so kar dusan kana raye' but why? Ai kana da kudin da ba mai iya maka komai yanzu, zaka iya sayan rod riquez baki dayan ta ka kuma zauna lpya
Ash yace tabbas haka ne, shyasa bana bukatar wani abu na su,
Kaima kuma kar ka sake naji maganan nan a bakin wani don ena da evidence din da zan sa wannan case din ya zama sanadiyar karewar career ka har abada.
Ni adalci kawai na biya ka kayi ma family na ..
Alkali ya jinjina a
kai yace angama.
Yanxu zaka bani nan da sati guda ena son na nemi kwararren lawyer da zai zo a matsayin mai bincike da tantance abun
Har mu kwato hakkin marainiya zahida da sauran..
Ash yayi takaitaccen murmushi yace, good
Zamuyi magana, ena dai fatan zaka sake karawa ya dawo sati biyu, don nafiso ayo komai a idon su jamal da jabir
Alkali yace ba komai, wannan ba matsala bane
Sai sukayi sallama nan ash ya dawo gida abun sa.
Ya gama juyi iya juyi yana ganin abubuwan yadda zasu kasance....
Yace mrs hidayat kwana 14 ya rage ma sauran rayuwar ki...yanzu lokacin ki ne.
*gudnite meet tmao peeps*😴😴😴😴😴
*surriem*
[23/08, 05:43] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*🌹🌹AMARYA PRINCESS na cikin group din SURAYYAHMS fans page,Allah ya bada Zaman lpya ya kuma sanya Dubun Alkhairi cikin sabon Auren ki,Allah ya kawo juria na gari,ameen*
*Pageâ–¶76*
Alkali baiyi kasa a gwiwa ba ya shiga aikin sa, ganin alert daga ashween tun acikin daren sai ya sa shi kira ya sanar sa mrs hidayat akan yana da muhimman baki kuma zaifi dacewa su daga case dinta sai nan da 14 days in sun tafi kar su jangwalo musu wani abun..
Ba musu ta amsa ta amince don dama a private conference room za'ayi ba asalin kotu ba enda daga shaidu sai shaharrarun newsmen da yan jarida na kasa.
Awajen in kotu tayi mata licenced ta mika mata transfer of will na zahida da su lateef sai ta sa a watsa a labarai cewa rodriguez ta dawo da kafarta ga abubuwan da kuma ta mallaka
Ta dade tana shirin wannan rana don haka bata son wani obstacle ko kadan ya shiga tsakanin ta da cimma burin rayuwar ta.
Tace na jira shekaru dayawa ma sai dan wannan kwanaki?
A gefe kuwa Zahida ta sha mamki ita da saminu don bata yarda an daga karar ba saida saminu yaje ya jiyo musu gulman da kansa.
Nan tace yanzu mun samu damar tara wasu evidence akan mrs rod kenan
Saminu yace gaskiya zai yi wahala kice zaki nuna papers kawae as shaidun mu, karki manta mrs rod bata fara harka sai ta sayi bakin shugaban harkan
Nan ma saminu ya sake sata cikin zullumi sai ta koma gida ta zauna ita kadai tana tunanin duniya...ta tsorata sossai amma sai ta sa aranta
Ta ce ko mutuwa zatayi bazata bari a karbe hakkin ta tana raye ba..
Wani bin kuma tace to how can she do it,? Gashi shi kansa saminu baida idea bare ita..
Cikin haka wayar ta yayi kara ganin ashweeen ne ya sata sauke smiles dan dole.
Nan Ta sanyaya murya tace sai yau akayi lokaci na ko?
Yayi murmushi mai sauti yace my lady,
Me kike yi ne ya dan shagwabe.
Cikin nishadi da ya ziyarce ta bazataTace enaa zaune ne so lonely.
Yace oya kizo ki sameni a yola yanzu ena jiran ki a gida
Tace are u seRious
Har ka koma ne?amma shine kamal yace kana abuja.
To bari dai na zo ta daka tsalle dan murna ta katse wayar,
Nan ta tattara komai tayi shiri that moment tayi hanyar airpot.
Ashween Ya iso karfe 1.30pm na rana ita kuma ta iso karfe 4pmsaura ta shigo garin
Ba laifi yau ashween ya sauke mata kai sukayi hira sosai kamar ba shi ba.
Taji dadi sosai ta kuma dada jin ta yadda da shi can cikin kokon ranta,
Sai dai Tai ta yi yafada mata meke damun sa taga bandage akai yace sam
Bazai fada mata ba sai ta gaya masa meyasa ta takura tana son magana da shi.
Nan mood dinta ya sauya, ta ce masa tana cikin babban matsala and she needed somone to talk to..
Tace kai kadai na yarda da shi a duniyan nan yanzu
Kaine kadai garkuwa na ash
Yace bangane ba?ko Ki kina samun matsala da project din ki ne?
What happen
Sai hawaye suka soma sauko mata ta riko hannun sa tace mumy ne kawai,
Yace ohhhh maam,
tace ehh, azzaluman nan,bakar muguwan ma