Showing 15001 words to 18000 words out of 219669 words

Chapter 6 - So Makamin Cuta Complete Hausa Novels Compelet By Surayyams.txt

14 Mar 2026

4106

yanzu tana kyrma hannun ta da ya kankame rigar sa sai karkrwa yake
Tsintar kansa yayi da shafo sumar kanta data bari ba dankwali a hankali yana saisaitata batare da yace uffan ba
' saida ta sauke wani nanauyan ajiyan zuciya sannan ta soma kokarin kwace kanta daga kan kafadar sa
Baiyi gardama wajen sake ta ba
Sai Binta da yake da kallo kamr wanda yake so ya tambayeta wani abun
' y'am sorrry ""tafada kamr zatayi kuka tana kallon kasa yadda plate suka farfasahe suka watsu

Binta kawai yyi da ido yace" Its ok..meyasa baki daura dankwali ba ?

Cikin Hanzari ta dago ta kallesa dan batayi xpecting wannan tambayr ba

Uhm dama zan kai wayyanan kitchen ne sai na sauya kayan jiki na

'har kin gama naki hidimar kenan? Ya tambaye ta kamr baisan bataje ba

Dan shiru tayi sannan tace
Ai ammy ce ta hanani zuwa

Ok dats good
Yace a takaice..yana kallon yadda ta shgwabe ta marairaice fuska lokaci guda

Yaya ni kenan an tsame ni ko? Dinner ma kar nazo ko
Sai karamin hawayen ta ya soma saukowa gwanin tausayi
" kallo ya bita da shi baice komai ba haka ma fuskan sa bai nuna alamn komai ba
" kiyi hakuri princess ure too precious i cant gamble with you agaban kowani jick and jack bazai yuwa ba" ya raya cikin ransa
Jin ya mata shiru ya sata juyawa da niyyar tafiya
Cikin hanzari ya damko hannun ta ya dawo da ita daf da shi' tsammanin ta wani abun ne

' murya kasa kasa yace shine akace kiyi kuka
Wai ke yaushe zaki girma ne?
Shiru tayi dan harga Allah salon daya mata maganar ya kashe mata jiki sosai
Sai zare ido take

Lura da hakan ya sa yace "Kin duba abun da na baki jiya?
Gyada kai tayi alamn eh

And i ques you unlike it ko?
Sake gyda kai tayi alaman ah 'a

Ok toh in bahaka bane shi zaki sa anjima
Sai kizo wajena kar ki fita fa, If not in aka sake hanaki zuwa dinner ba ruwa na
Dan karamin Murmushi ne ya kufce mata
Ta daga ta kallesa a dabaran ce
Na gode yayah"

Baice komai ba ya ja hannun ta suka zaga chan sama
Sannan ya sauko ya kaita har bakin rum din ta bawanda yace uffan tsakanin su....murmushi kawai suka sakar ma juna ya juya ya koma hotel cikk
In taro abunsa

Kamr ancillo ta tafado dakin rigif sai akan gado
Tsaye Salma tayi tana salati hannun dauke da wayar datake famar chats tuntuni
Me haka jasmine meya faru kuma ?
Kan ta kara cewa wani abu jitayi jasmine ta rungume tana wani kyalkywlewa da dariya har tana jan shauki

Galala salma tayi "Wht? Wtf..kifada min mana
Kin fa daure min kai

Nan ta dago tace
Just forget ,wallhy fita nane nayi babban samuwa
kinsan me ? ya faran ta min raina sosai' tafada tana kankame pillow cikin jin dadi

Mswwt whteva, intayi tsami dai dole naji
Cewar salma tana dada gyara zaman ta
Bata fasa ba ta fauce wayr salman fuskan ta dauke da annuri

Ke ki tashi kibar wannan aBun mufara shirin zuwa dinner

Uhh i seee abun kenan dama
Baki da dama jasmine
Ni ki ban wayata kar sugar ya ji haushi

Dan tabe baki tayi tace kaji manya
Wai sugar? Kin manta chokolate ne

Oho dai ni ki bani tafada tana fauce abun ta

Bayan sallahr isha'i
Lokacin yawancin an ragu sai baifi tsirrarun manyan bakin ba da suka rage ba

Gida ya koma shida kamal
Anan Bayan ya kammala dukan sallolin sa ne ya zame ya nufi dakin ammyn sa
Nan suka dan taba hira kadan
Sannan ya rufe ta cikin kulawa ya mata sai da safe
"
Surutu sosai sukeyi a farfajiyan gidan su da saura abokan sa da suka biyo Suma zasu wuce "

bro,mutumiyar ka tana nan tana shiri fa"
cikin rada kamal yafada masa a
Gefen kunne

Hmm ' tania ma tace min tana hanyar hotel din yanzu,
nafiso su hadu kafin nan komai yayi set sai muje ko?

Yh ..kamal yace a takaice


Zaune take rike da gown din tana jiran taga kirar ashween kafin ta sa ajikin ta
don tun Karfe 10 saura suka kammala shirin su tsaf sunyi kyu har sun gaji
' salma baifa kirani ba naga kinata wani sauri sauri
Tafiya zakiyi?

Ahh ni nace miki ? Nifa waje zAnje ma aalman tafada tana gyra make up

Uhmm ,ta tabe baki tayi shiru

Cikin arabian gown din ta mike ta sabi clutch purse din ta "bye babe kinga ya sake kira

zumbut jasmine ta mike "dama wajen sugar mu ne jira ni muje mugaisa

Ah a ba enda zakije ..ai mun gama magana nace randa kika nuna min shi ruhin naki ranar xaku gaisa da sugar

Haba salma meye wulknci yanzu saiki barni ni kadai tafada kamr mai shirin kuka

Whateva! ba ke kadai bane akwai ruhi tare dake
Ta karashe cikin dariya ta fice abunta

Daga gefe akayi parking mota
Cikin simple catwalk ta isa ta bude front seat ta zauna
Qamshi ne ya gauraye wajen ga snyin ac da ke buga su
Murmushi ya sakar mata ganin yadda ta sunkuyar da kai yace
Mrs shyness "to ni baki kalleni ba sai wa xaki kalla in mukaje dinner?
Cikin rangwadi ta kallesa "toh ai nasan ba wanda zai na min irin wannan kallon naka awajen , in akwai kuma kaga kenan bazan kalle sa ba..
Hmm
Salma ta kenan ,i like dat yafada yana murmushi
Shall we ?

Mine, jasmine fah? Da kyr fa tabar ni na fito ita kadaice
In Taji na tafi na barta ai she will be mad

She wont ,ash yana ciki zasu zo tare "kamal din yace

So,mu tafi?
Gyada kai kawai tayi tana murmushi bata ce komai ba
Bai bata lokaci ba ya tada mota nan suka fice

Chan sama daga window ya ga wulgawar motar wanda ya tabbatr masa kamal yayi gaba
Tare da sauke ajiyan zuciya ya zari car key dinsa ya sauko karamin palour ya zauna yana jiran ta
Cikin minti 10 sai gata ta fito gaba daya fuskan ta a murde sai juye juye take don jin shiru Yayi yawa a gidan
Tsoro ne tam cikin ranta bata ma kula da shi ba

Shiko tuni yayi nisa wajen kallon yadda tayi kywu cikin gown din tamkar domin ta a kayi shi
' wayar ta ta daga da niyyar kallon sakon tex daya shiga lokacin
" most bautiful queen,alwys looking gorgeous "taga an rubuta da wani sabon number
Dan tabe fuska tayi da niyyar kiran layin sai ji tayi an fauce wayar"
' kau da kanta ta kasa yi akansa shima haka
Kusan minti 5 ba wanda yace komai
Sai sanyi da jikin ta ya soma yi
Wato kin ajiye ni ena jiran ki kinata shirmen ki da wayar ki ko
Da sauri ta dago tace ' ah a yaya,, m sorry tafada a marairaice
Toh muje ..

Sai kuma ta tsaya bata kara gaba ba batayi baya ba
Har ya soma kaiwa baki ya tsaya "baki ji bane in kin fasa sai ki koma ko?
Da sauri ta tari numfashin sa tace
Dama ena so na kira salma ne ta karashe a dan tsorace

Baice komai ba ya dawo ya mika mata wayar ya fice abun sa
Cikin sauri sauri ta dialling
Kusan sau biyu ba a daga ba gashi ta na tsoron kar ya tafi ya barta
Sai da takai Karo na hudu akayi picking
Hello" toh sarauniyar soyayya ai sai ki fito mutafi ko

Sai da takai minti biyu kafin ta amsa
Gashi ba ta jinta sosai
Ki taho kawai karki jirani..sai gyat wayr ya yanke

Zare ido waje tayi cikin rashin fahimta
Ta sake dialing " switchd off
Dan karamin tsuka taja tayi waje ranta a dagule

Gum taja ta tsaya
Zuciyan ta na fat fat shi kadai
Waigawa ta sake yi taga takusan kaiwa tsakiyar farfajiyan gidan bata gansa ba bare motar sa
Take wasu zafafan hawaye suka kunno kai zasu zubo a fuskn ta

Wayyo Allah na yaya yatafi ya barni tafada cikin shgwaba tana dan bubbuga kafarta a kasa kamr karamar yarinya

' dariya yake yi ciki ciki yana videon duk abunda takeyi daga gefe
Ita ko sai dada bori take tana maganganu ita kadai ga hawaye har ya soma saukowa kan face dinta
' kuma wallhy ba zan ma kowa magana ba agidan nan ba
a zuciye tafadi hakan tana goge hawayen ta cikin fushi da niyyar komawa ciki

Tana juyo wa suka hada ido
Cikin Sauri ta juya cike da kunya 'wayyoh tafada tana cije bakin ta hade da rufe ido gam" kar dai yaya yaji abunda na fada
Na shiga magana ya zAn yi na kalle sa yanzu..


Jasmine...yafada yana dariya ciki ciki
ita kam
Bata sani ba tuni ta bashi baya sai make kafadar ta take

Toh shikenan bye
Yace ya juya abunsa jin ya danyi nisa ya sata juyowa da gudu tabi bayan sa
Yana shiga motar itama ta karaso ta shige ciki

Ko ya kula ta ya kunna motar suka fice sai kicin kicin take tana famar waswasi a zUciyar ta

Suna kaiwa wajen ya juya ya kalleta a dabaran ce tare da sauke wani kasallalen murmushi

Bude kofar tayi ta biyo bayan sa daf da daf
Daga ganin ta kasan ba a sake take ba
" ko ena cike take fam da guys and ladies
Wajen yayi haske sosai sakamakon komai na wajen da white aka decorating din sa
Sai da suka iso daf shiga ciki taga mai aiki yazo ya karbe haddaden jacket dinsa daya sanya akan kayar sa

Nan Haddadiyar white wengers shirt dinsa ya bayyana fara kal..
A hankali ta dago ta sake kallon sa
sai gani tayi ya sake sauyawa ya dada yin kywu fiye da yadda ta gansa dazin a gida
Wani murmushi mai dauke da cunkusashhen kishi ta sake bazata
Charaf suka hada ido amma ta kasa dauke kai
Duk da hasken camera dake kansu
Tun daga nan sai pics ake musu
Dan giran sa ya daga mata kafin ta fahimci cewa yana nufin wani abu
Tana daga idon ta ta ga hannun sa alaman ta rike nasa
Ba musu ta mika masa gam taji ya rike
Sun soma shiga ciki tare
A rude take ta rasa yadda zata sa kanta duk da ma jinta ta take complete har zUciya..
Wani bangeren kuma inba dan taji hannun ta baya ko motsi cikin nasa ba da sai dai ta tsaya chak a wajen dan fargaban idon mutane
Musamman yadda wajen yayi haske

Ga white party snow burbles da aka hura wanda ya ke zuba akan su sai slow blue music da aka sanya a background din "

Daga gefe tania tafito ta
Karaso wajen su da kawataccen murmushin ta "Hey baby ..tafada tana dan jingina da shi kadan

Wani mugun kallo ta mata "don Hakan ne ya sa ta farga ganin ashe ma sunkai kusan rabin hall din
Dayan Hannu yasa ya riko na tania da ba karya itama tayi kywu sosai
Domin kuwa asalin yar brazill ce ita

So cute ' ta sake cewa shikam baice uffan ba sai Murmushi da ya mayar mata

Kicin kicin ta somayi da hannun ta amma taji gam yaki sakewa
Cikin sauri ta kau da kanta gefe
Har suka isa wani rumfa da aka zagaye da white
bonquet '

C'mon zo muje.. cewar tania data zare hannun sa cikin na jasmine
Cikin hanzari ta ja shi suka bar wajen

Da kyr ta saita kanta ta daina kallon su din kamar ana kunce mata kai haka take ji
Tsaki kawai take ja ,fuskan ta dam ya cika

Ganin idon mutane ya sa ta kane tayi kokarin kauda yanayin face dinta yayin da ta juya zata bar wajen
Salma ce a gefe tana tsaye alaman tuntuni tazo ta labe

Uhhh ufff ,,,jasmine ta kalleta ta ja tsaki
wanda yasa salman fashewa da dariya
Ta ja hannun ta sukayi gefe..



🤪.


*Surriem*
[23/08, 03:02] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*



💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_


_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥



*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.


*Salam sisters*
```Kullum ki kasance bayan kowani sallahr farillah kina karanta kulakulan nan guda uku(surah nas,falaq,da nas)
Babban kariya ne daga mahassada daga cikin mutum ko aljani,makiya,mugaye, sannan kana cikin gadin malaikun tsaro daga duk wani cutar wa da zai shafe ka``` ,

*Yadda ake yi*

```Sallahn safiya wato fajr da magrib, zaka karanta ko wanne sau uku uku,

Sauran (zuhr,asr da ishai)kafa daddaya

Allah ya taimake mu baki daya ameen```






*Pageâ–¶7*





Bori sosai jasmine ta shigayi, ita kanta tasan harda fushin abun da take ji a ranta ta hada take ma salma
Wacce tuni ta gama fahimtar ta
'to jasmine in magana bai kare kema sai ki rama tunda duk hakurin dana ke baki baida ma'ana awajen ki

Shiru tayi ta kau da kai

Nan itama ta mike da niyyar barin waje
Da sauri ta damke ta
Ta shaqwabe fuska tana dada marairacewa

Salma tayi "msww tace,
Iskanci
To meye kuma? ba fushin zaki cigaba da yi ba

Ah ah..tace" sannan ta kalle salman a sanyaye
Amma kun ganni lokacin da muka shigo da yaya ?

Gyada kai salma tayi alaman eh'"

Kuma kinga
Wacce tazo daga baya ta same mu?
Eh mana salma tace tana kallon ta

Dan shiru tayi tana sake sake aranta "can tace Uhhm na tambayeki mana salma'
Zama salma tayi kafin tace ena jin ki '
Ki fadi tsakani da Allah
Dani da budurwan yaya wayafi kywu ?

Wani boyayyen murmushi tayi na mamaki tace
Are you ok? Lpya kike wannan tamvayar jasmine

Ni dai kawai ki fada min.. Tace fuska a shake

Tabe baki kawai salma tayi
Ganin yadda jasmine ta daure fuska snnan tace"
" tsakani da Allah aunty tania tana da kyau sosai .

Harara masu zafi ta watsa ma salma bazata ta Kau da kai gefe tun kan ta sake cewa wani abu
" wacece kuma aunty tania ?
Salma ko Kamr bata san meta keyi ba
Ta sake cewa girlfriend din yaya ash mana

Dum taji kanta ya sara
Sai ta yi shiru batace komai ba
Itama salman shirun tayi tana binta da kallo
Cikin kula ta kamo hannun ta
"jasmine' kywu irin naki ba za a hada da nata ba..ke ta daban ce"
Kin gan ki kuwa da kuka shigo tamkar wata angel kowa ke yake kallo
So its obviius kin fita kyawu ki dena hada kanki da ita ..
Duk maganan da salman take
Ji take kamar karya ne
Don gaba daya taji
ta tsani komai a lokacin
Ga zuciyan ta sai maimaita sunan tania yake idon ta kuma yaki dena nuna mata smiles din da suke
Xchanging da yaya ash dazun

Dan buga table a hankali salma tayi "ke, Ohhh kin tambaye ni na baki amsa kin wani share ni ko
Ba laifin ki bane jasmine ni kinga tafiya ta ma .
Tsaye ta muke zumbut itama kamr mai jinnu

Sai yanzu salman ke lura da yadda idanun ta suka sauya sosai
kallo daya zaka mata kasan tana cike da damuwa '

Zauna jasmine ta fada a sanyaye
Ruwa ta tsiyaya mai sanyi 'ta mika mata' ga shi pls take

Ba musu ta karba ta sha
Tana ajiye cup din ta sauke numfashi a hankali ta kife kanta kan tebur
Whts wrong ?
Salma ta tambaye ta cikin kulawa
Tana dafa ta

Da kyar ta amsa tare da cewa babu komai salma
Kawai raina ne ke baci
Musamman en naga wannan gf din yayan
Ni wallhy bana son shi da ita

Murmushi kawai salma tayi tace gf dinsan kuma? To meye a ciki

Dagowa tayi ta dan harare ta
Ita wannan Tania?

Eh aunt taniar fa,

Mswww wai yaushe tadawo auntyn ki ne s ta karashe a fusace tare da dan buga table din

Huh? Calm down mana jasmine chill
Toh kedin Shi yace miki gf dinsa ne
Ena dai don nafada ne kika hau kai.

Shiru tayi batace komai ba in banda dada daure fuska da tayi

Hmm jasmine kenan to fa ba ruwa na Nifa bance miki gf din sa bane
Kawai nafadi ra'ayi na ne...
To Jasmine wai ma me laifin ta ?
Kafin ta dago ta amsa
ji tayi mutum akan su bazata
' murmushi ta sakar musu
Yayin da Lokaci guda zuciyar jasmine ke harbawa kamar zai fita

Hi gurls ....

Hy.. salma tace tana binta da ido da karamun murmushi

Jazmine ku taho yayan ki na kira
Banza tayi da ita fuskn ta a daure
Batace uffan ba
Tania ko da ke tsaye tana kallon su bata ko nuna alaman wani abun aranta ba
Sai ma kure su da ido
Tashi muje salma tace tana tappin dinta

Kamr ta kwalla ihu haka taji
Da kyr ta mike a fusace
Ta kama hanya
Suna bin tania
Chan cikin wani wajen ta musu jagorA tace musu tana zuwa zata masa magana
Enda sukayi tozali da wata secndry schl friends dinsu zaune da wasu yan mata su biyu wanda daga ganin su kaga turawa
Da sauri salma Ta karasa suka rungume juna
Marriam ?
Jasmine,salma, duka suka kwashe da dariyaa

Yaushe kika dawo nija maryam ? Jasmine tace ..
'Kafin kace wani abu Zama sukayi nan aka bude shafin hira
Wanda Har ya sa ta soma samun saukin nauyin da zuciyan ta ke mata
a haka suna wajen a zaune masu aiki sai safaran kayan makulashe suke musu wanda
Hakan ya dada debe musu kewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login