Showing 15001 words to 18000 words out of 170049 words
gani ba,
A hankali Sam ya sauke idanun sa akan ta, jiyayi gabansa yayi wata irin mummunar faɗuwar gaba, ji yayi zuciyar sa na barazanar tarwatsa masa ƙirji tafito, take idon sa suka fara canza launi ya zaro su suka firfitowaje, ba komai bane ya haddasa masa jin wannan abun ba face tozali da idanuwansa sukayi masa da yarinyar da akace masa ta ɓata ma'ana idanun sa sunyi masa mugun gani, da yake ganin abun kamar a mafarki kamar almara,
Ko kallon gabansa bayayi ya shiga takawa a hankali zuwa inda take,
Hamza tunda yaga irin kallon da yake mata yasamu amsoshin tambayoyin sa, sannan kuma tunanin sa da hasashen sa sun zama gaskiya dan haka yaja gefe ya zuba masa ido, bai ƙara cewa komai ba,
Sam yayi tafiya wajen rabi kafin yaƙarasa wajen ta, saboda akwai ɗan tazara tsakanin inda suke zuwa parking lot ɗin,
Tagama wanke tayar da take wankewa ta ɗago zata wanke ɗayar sai brush ɗin ya faɗi ƙasa, da sauri ta juya ta ɗauka saboda sauri take 10 minutes aka bata tagama wanke ta tas inba hakaba kuma jikinta yagaya mata, tana wankewa da hannu ɗaya take wankewa ɗayan hannun kuma tiyo ne tana wankewa tana ɗaurayewa,
tana ɗauka ta juya da sauri taci gaba cikin sauri tanayi tana Allah yasa loƙaci bai kusaba,
jitayi kamar su tafiya ta a bayan ta da sauri ta juya atunanin ta ko loƙaci yayi antaho dukanta,
Tana juyawa idon ta ya sauka akansa itama gabanta saida ya faɗi ganin sa da tayi, ɗan ƙifƙifta idon ta tayi dan ta tabbatar wa da kanta gaskene ko kuma mafarki ne ganin dai da gaske shine yake tunkarota,
Bata san loƙacin da tayi watsi da brush ɗin da tiyo ɗin kuma ta manta a inda take, ta kwasa aguje ta nufi wajensa tana zuwa tafaɗa jikin sa ta rungume sa ƙam tare da fashewa da kuka tana ƙara duƙunƙune sa, atare suka sauke ajiyar zuciya,
Sam tsaye yayi yakasa motsi ya damƙe idanun sa yana jin wani irin zafi da raɗaɗi acikin zuciyar sa, da ƙyar ya iya ɗaga hannun sa yayi croping ɗinta ya rungumeta shima,
A hankali ya shiga buɗe idanun sa ba zato ba tsammani abun mamaki saiga hawayen masu ɗumi sunfara saukowa daga idon sa.......✍️✍️✍️
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️xeemat...love❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
_______A hankali ya shiga buɗe idanun sa ba zato ba tsammani abun mamaki saiga hawayen masu ɗumi sunfara saukowa daga idon sa.......,
Hannun ɗaya yasa yayi saurin share hawayen sa, sannan yaƙara rungumota sosai kamar zai mayar da ita cikin jikinsa sai karkarwa yake,
Saosai take kuka dan ba ƙaramin jin daɗin ganin sa tayi ba yazo a loƙacin da take buƙatar sa,
Kasa jurar kukan nata yayi gashi ya kasa yi mata magana, duba gefe da gefen sa ya shiga kalla yaga yanda maza suke kallon ta abun da yafi ƙona masa rai kenan ganinta da wando da riga ga kanta ba ɗan kwali ga maza dake yawo awajen suna kallon ta a haka,
A hankali ya shiga rabata da jikin sa amma sai taƙara riƙeshi cikin kukan tace please don't go, kar ka tafi kabarni tana faɗar haka ta ƙara rungumesa tana sake fashewa da wani kukan,
Wani abune yazo masa wuya, baisan loƙacin da ya ɗagata ba gaba ɗayan ta yariƙe ta ƙam yafara tafiya da ita ajikin sa baibi takan shiga cikin gidan ba kuma ya manta da Hamza dake bayansa,
cikin ɓacin rai yake tafiya har yaƙarasa bakin gate ɗin ya fita da ita,
Hamza dake bayansu tunda yaga ya ɗauke ta yana niyar barin wajen shima ya ɗaga ƴan matan ƙafafun sa ya mara musu baya fuskar sa ɗauke da murmushi,
A kusan tare suka ƙaraso gurin motar da sauri Hamza ya buɗe masa ƙofa back seat shikuma yashigar da ita ciki da niyar ya ajiye ta ya fito, amma yana niyar fitowa tayi saurin riƙeshe saboda gani take idan ya tafi kamar tafiya zai yi yabar ta,
cikin motar ya koma kusa da ita sannan yajawota ya rungumeta ta gefe yafara bubbuga bayan ta, yayin da zuciyar sa take masa wani irin suya,
Kuka ta ƙara saki sakamakon taɓa mata bayan da yayi saboda zafin da taji,
Tana kukan tace, "Dan Allah karka
barni anan wallahi mutuwa zanyi kasheni zasuyi ka mayar dani gidan ka kaini wajen baba na dan Allah mitafi, duk tabi ta rikecemasa sai surutu kawai take kuma ta riƙeshi ƙamƙam kamar yaci mata bashi,
Wasu zafafan hawaye yaƙara ji sun cika masa ido loƙacin da idon sa suka sauka akan wuyan ta yaga wani baƙin shatin bulala jikin nata ya shiga kalla da tun ɗazu bai kulaba ashema gaba ɗaya jikin ta duk ya ɓaci da shatin bulala har su ƙafar ta da hannun ta,
Sosai ya shiga mamakin yanda akai hakan tafaru to daman hajjaju haka take mutuwa ce ko kuma dai akanta ta fara muguntar me yasa zataci amanar sa yakawo mata yarinya amana amma tayi mata haka ta mayar da ita ƴar aiki harda su duka wannan wane irin mugunta ce hajjaju take da ita, shi abun da yafi tsaya masa ma arai da tace wai yarinyar bata gidan ta gudu alhalin tana nan da baizo ba kenan kasheta suke shirin yi,
Kallon ta yaƙarayi yaga yanda take kuka kana gani kasan daga ƙasan zuciyar sa take yinsa,
Wani abu ya ƙaraji tundaga kan ƙafatsa har tsakiyar kansa ji yake wannnan shatin bulalar kamar ajikin ta kamar ajikinsa kamar shi aka daka kukan ta kwan har can ƙasan zuciyar sa yake jinsa, duk dauriyar sa nema yake yakasa jurewa, gashi yama kasa furta mata koda da kalma ɗaya ne, Daƙyar ya iya ɗago jajayen idanun sa dasukayi masa nauyi, ya kalli Hamza dake waje ya juya musu baya, ɗan dukan glass ɗin yayi dan bazai iya magana ba, Hamza na jin haka ya juyo da sauri, yana kallon sa ta cikin glass ɗin motar, da hannu yayi masa alamar da su tafi,
Zagayawa Hamza yayi ya buɗe driver seat yashiga tare da tayar da motar yafara janta Saida ya hau kan titi sannan yace "ina mukayi?
Daƙyar sam ya iya buɗar bakin sa yace "gida, daga nan kuma bai ƙara cewa komai ba, ya maida dubansa kan sumy dake jikin sa tana kuka har yanzu, ita kanta batasan me yasa takasa daina kukan ba har yanzu,
Hannu biyu yasa ya ɗagota ya zaunar da ita tare da riƙo fuskar ta da duka tafikan hannun sa,ya zuba mata jajayen idanunsa yana ƙarewa fuskarta kallo da tayi sharƙaf da hawaye, sannan ya shiga goge mata hawayen, amma yana goge mata wani na zubowa, kansa yashiga girgiza mata, yana ƙara goge mata, gannin dai hawayen nata sunƙi tsayawa baisan loƙacin da yaƙara jawota jikin sa ba ya ƙara rungume ta, murya cike da rauni dan shima ji yake dama yayi kukan ko zai samu sassaucin raɗaɗin da zuciyar sa take masa, cikin ƙasa ƙasa da murya da yakasa ɗagata yashiga cewa "plss ya isa haka kidaina kukan nan ko kinaso nima kisani kukan, da sauri ta ɗan girgiza masa kai, yace "to kiyi shiru ya isa haka,
itama cikin kukan tace baza ka ƙara tafiya kabarni ba kuma dan Allah ka kaini inda ka ajiye min mahaifina, ina son ganin sa,
"Tohm" kawai yace mata yaƙara yin shiru dan bayajin zai ƙara kaita wani wajen ko gidansu bazai mayar da itaba saboda ɗayar matar da yake kyautata zaton matar ubace shiyasa take gallaza mata azaba, dan haka babu inda zai kaita shima mahaifin nata idan yana sonta to saidai ya canza mata gida amma bazasu ƙara zama guri ɗaya da itaba,
Hajjaju kuwa shikaɗai yasan hukuncin da zai mata duk da tana matsayin kaka agurin sa, amma hakan bazai hanasa ya rufe ido ba yaci mutuncin ta idan batayi wasa bama idan yaji labarin abubuwan da tayi mata, wallahi sai yasa anƙulle masa ita sai yayi ƙarar ta ko kuma ya ɗauki ƙwaƙwaran hukunci da kansa, dan bazai taɓa barin taba, idan kuma yarinyar nan ce ƴar kenan (wacce akeso a haɗasu aure) idan itace sai ya ɓaɓɓalata yanda suka azabtar da ita duk sai yarama mata ninkin baninkin ma abun da sukayi mata, Ɗagowar da tayi ne daga jikin sa ya katse masa tunanin sa,
Da kumburarrun idanun ta take kallon sa shima itan yake kallo da idonsa da suka canza kala daga yanda suke zuwa baƙin ciki,
Janye nata idon tayi tana ƙoƙarin tashi daga kansa amma sai ya hanata hakan, bata takura ba akan dole sai ta tashin sai kawai ta haƙura, zuwa yanzu ta daina kukan, sai ajiyar zuciya da take saukewa akai akai,
"Wait Hamza, sam yafaɗa yana kallon Hamza, da sauri Hamza ya taka burki ya tsaya tare da juyowa yace "lafiya?
Sam yace "EH" yana faɗar haka ya zura hannu a aljihun sa ya zaro ATM card ɗin sa tare da miƙawa Hamza,
Karɓa Hamza yayi yana jiran karin bayani, Sam yace "kaje cikin nan......., Sai kuma ya katse maganar tare da ɗan sakin ƙaramin tsaki yace " Mtsw barshima kawai bani naje da kaina ya karɓi abunsa, sannan ta buɗe motar,
Rabata yayi da jikinsa, yana kallon ta itama shi take kallo, idonsa akanta yace "bari inje indawo kizauna, yanzu zan dawo,
Kamar tace masa a'a zata bishi sai kuma ta tuna da shigar da take jikin ta, dan haka sai kawai ta ɗaga masa kai tare Da kawar da kanta ta kwantar dashi ajikin kujera,
Tsayawa yayi yana kallon ta tsawon sakanni sannan ya kalli Hamza yace ka kula da ita kafin na dawo,Hamza yace "In sha Allah,
Sumayya jin maganar tasa yasa ta buɗe ido tare da juyawa ta kallesa, sai kawai ya ɗan sakar mata murmushi kaɗan yace "yanzu zan dawo, ji yake kamar kar yatafi, kai ta ƙara ɗaga masa tare da rufe idon ta taƙara komawa yanda take,
Daƙyar dai ya iya rufe motar ya tafi wani babban shagon sayar da kaya ya shiga, yana shiga ba ɓata loƙaci ya shiga kwaso mata kayan saka dogayen riguna riga da sket harda riga da wando da hijabai, da underwears su panties da bra, duk dai wani abu da yasan zata buƙata saida ya ɗauko mata sannan ya koma kan kayan ciye ciye da su choculate da sauran su abubuwa dai yasiya masu yawa sannan yaje wajen biya ya miƙa ATM ɗinsa aka ciri kuɗin aka basa abunsa sannan aka saka masa kayan a leda wasu suka ɗaukar masa sannan suka fita daga gurin har wajen motar aka kaimasa,
Hamza na ganin su tunkan su ƙaraso ma ya buɗe musu booth suka saka masa aciki aka rufe,
Buɗe motar yayi ya shiga yanda ya barta haka yazo ya same ta ko motsawa batayi ba,
Tayar da motar Hamza yayi suka cigaba da tafiya,
Sosai ya tsaya yana ƙarewa fuskarta kallo ganin haryanzu bata ce komai ba kuma bata buɗe idon ta ba duk da yasan taji shigowar sa, amma bata kulasaba,
Ƴar ƙaramar ledar da ya ɗauko a hannun sa yashigo da ita cikin motar ita ya buɗe ya zaro hijabi aciki, ahaka bata motsaba shima kuma baice mata komai ba ya ware hijab ɗin yafara ƙoƙarin saka mata sai aloƙacin tayi saurin buɗe idon ta tana kallon hijab ɗin, kallon ta tamayar kansa sannan ta ƙara kallon hijab ɗin sai kawai tasa hannu ta karɓa taƙarasa sakawa,
Ɗas yayi mata daman kalar da tafi so ya siyo mata maroon colour shikuma baisan shi tafiso ba kawaidai ya ɗaukar mata shi saboda irin shi yafara ganin ta ranar da suka fara haɗuwa, shiyasa ya ɗaukar mata kalar,
Wani Choculate Biscuit ya ɗauko mata tare da ɓare mata shi ya miƙa mata da farko ƙin karɓa tayi saida ya watsa mata wani kallo sannan tayi saurin saka hannu ta karɓa murya can ƙasa ƙasa ta ɗan kallesa tace thanks....,
Wani ƙayatacen murmushi yaƙara sakar mata, duk da bata gani ba hakannan yake jin daɗin godiyar da tayi masa, gashi abun da yake basa mamaki shine yanda ya zuba mata ido yake kallon ta ko ƙiftawa bayayi,
Aɓangaren ta kuma kallon da yake mata yafara isar ta, sai take jin duk ta takura dashi, gefe tayi da kanta tana kallon waje, ganin inda suke shirin shiga yasa tayi saurin juyowa tana kallon sa, daman shima ita yake kallo dan haka tana juyowa suka haɗa ido sai tayi saurin janye nata tare da cewa "naga munzo nan ba gida ba?
"Eh nan gidan mune, zan kaiki amma ba yauba,
Zata ƙara magana kenan yace "shiru karkice komai, yafaɗa yana ɗauke kansa daga gare ta,
Itama bata ce ɗinba kamar yanda ya buƙata, amma a ƙasan zuciyar ta tunanin ta shine karfa yaƙara kaita inda za a kuma cinzalinta irin gidan da yakaita dan baƙaramar wuya suka bata ba duk azabar da umman su Waleed take mata baikai irin wannan ba, ita iyakacin ta duka amma nasu yayi yawa ga aiki ga duka ga zagin cin mutunci, sai taji muguntar gidan su nafilace akan ta gidan da yakaita shiyasa take tsoron kar yaƙara kaita inda za' azabtar da ita, duk da taji yace gidan sune amma hakan baisa taji zuciyar ta kwanta ba, so take kawai ta ganta agaban mahaifin ta hakan sai yafiye mata fiye da duk inda zaikaita,
Hamza na shiga cikin masarautar Sam yace "yakaisu daidai ƙofar part ɗin fulani ta yanda suna fito zasu shiga ciki batare da kowa yaga shigar suba, haka kwa yayi ya kaisu daidai ƙofar shiga sannan yayi parking yana parking ɗin kuma ya buɗe motar ya fita yabasu waje,
Sam ne ya kalli Sumayya da gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta ya lura bama taga shigowar su ba ta tafi tunani,
Hannu yasa ya riƙo hancin ta, hakan yasata saurin dawowa daga duniyar tunanin da ta faɗa,
"Tunanin me kike ya jefa mata tambaya, kai ta girgiza masa tana kallon cikin gidan ashe har sun tsaya bata saniba, gaban motar ta kalla taga, mejan su ma har ya fita daga motar duk bataji ba tana tunani,
Buɗe ƙofar yayi ya fita sannan yace itama tafito, da ƙyar ta jawo jikin ta ta matso kusa da murfin sannan ya matsa mata ta fito,
Suna fitowa ya riko hannun ta ya buɗe kofar da ɗayan hannun sannan suka shiga ciki, ya mayar da ƙofar ya rufe, Hamza dake bayansu ya buɗe yafara fito da kayan da Sam ya siyo mata sannan ya bisu dashi ciki,
Yana shiga ya wuce ɓangaren Sam, abakin ƙofar ta tsaya ya kwanƙwasa jin shiru yasa ya tura kofar ya shiga kaitsaye,
Basa cikin falon sai kawai ya ajiye kayayyakin afalo sannan yajuya yabar falon,
Saida Sam ya shiga da ita ɗakin sannan ya sakar mata hannu kan gado ya nuna mata yace ta zauna, shikuma ya wuce bathroom, shiga yayi ya haɗa mata ruwan wanka me zafi sannan ya fito yace "taje tayi wanka,
"To tace masa saboda daman a buƙace take da son yin wankan saboda yau kwanan kwanan ta wajen huɗu batayi ba tunda taje gidan batayi wanka ba, sun hanata yi,
Ahaka yanda take ta tashi ta nufi banɗakin, da kallo kawai yabita baice mata komai ba, saboda bayaso ya takura mata,
fita yayi daga ɗakin, yana fita ya tadda kayan afalon sai kawai ya ɗauka ya shigar dasu ɗakin, ware su ya shiga yi sannan ya ɗauko mata wasu riga da sket da wata hula harda pant da bra, ya ajiye mata su akan gado,
sauran kuma ya haɗe su ahaka ya buɗe wardrobe ɗin sa yasaka su ya rufe, sannan yaƙara fita kitchen ɗinsa ya shiga ya ɗauko plate sannan ya buɗe frigh ya ɗauko holandiya me sanyi sosai tare cup sannan ya koma ɗakin har loƙacin bata fitoba,
Mamakine yakamasa ganin irin daɗewar da tayi, tunani yashiga yi kodai ba lafiya ba,
Banɗakin ya nufa yana zuwa yakara kunnen sa yanaso yaji da motsi ko ba motsi, saidai kuma yana kara kunnen nasa, ita kuma tana buɗe ƙofar, da sauri tayi baya cike da tsoro tare da sakin ɗan ƙaramin ihu, shima saida saida yaɗan tsoratan yanda tayi masane yasa ya tsorata,
Ajiyar zuciya ta sauke tana tace "wlh ka tsoratani,
"Sorry naji shirun yayi yawane shiyasa nabiyo inji ko lafiya, yana gama faɗar haka kuma yayi baya dan yabata damar fitowa,
Fitowa tayi tana faman sunnar dakai duk da hijabi ne ajikin ta amma sai kunya ta kamata,
bakin gado ya zauna yana jiran ƙarasowar ta, tana ƙarasowa ya ɗauki kayan ya nuna mata kayan yace gashi sai kisaka ɗaukar su tayi sannan ta juya zata bar wajen "yace ina zaki?
Tace "shiryawa zanje inyi,
miƙewa tsaye yayi yace "kiyi sauri kishirya, sannan ya fita waje,
Yana fita tacire hijab ɗin sannan ta ɗauki bra ɗin tunkan tasaka take mamakin yanda akai ya ɗauko size ɗin tana sakawa kuwa tayi mata cas kamar ya gwada ko tagaya masa size ɗin da take sakawa, pant ɗinma daidan ta, haka kayan ma komai daidai ita, saida tagama sakawa sannan ta ɗauki towel ɗin data cire ta ɗaure gashin ta da tawanke shiyasa ma ta daɗe saida ta ware kalbar kanta ta wanke kan,
Tana cikin tsane kannata ya shigo ciki, bakinsa ɗauke da sallama amsa masa tayi tana cigaba da goge ruwan kannata, ƙarasowa yayi gaban ta yana ganin abun da take yasa hannu ya karɓi towel ɗin, ya ajiye sa gefe yace "akwai draya gata can, yafaɗa yana nuna mata inda take, tare sukaje gurin, zatayi da kanta ma yayi saurin karba ya busar mata dashi ya gyara mata kan kamar mace harda yi mata oiling sannan ya ɗaure mata shi da wani zare saboda