Showing 3001 words to 6000 words out of 170049 words
ba yin kanmu bane Allah ne ya aiko mu, dan ya taimake kune shiyasa mukazo gurin, ki godewa Allah yanzu da bamu zoba da shikenan kamar yanda yace yaga samu yaga rashi hakan zai kasance saidai kuma gashi ta Allah ba tasu ba samun ya tabbata kamar yanda yace sai da ƙwaƙwarar hujja za a yarda dashi to gata munsa mu duk wanda yaji wannan maganganun nasu ai dole ya yarda, ko ya kikace kamata yayima kiyi murna ba kuka ba, please besty kiyi shiru kiban hankalin ki mu tattauna akan maganar nan kinji,
Shiru tayi tana nazarin maganganun ta atake kuma maganganun tsohonnan suka shiga dawo mata ƙwaƙwalwa tabbas yanzu ta yadda wanda zai nuna maka soyayya a fili ba lalle yazama masoyin ka abaɗini ba idan tayi la"a kari da Waziri da suke uwa ɗaya uba ɗaya da papa amma ji yanda yake da mugun nufi akansa da iyalen sa, alhalin a zahiri nunawa yake babu wani abu to ɗan uwanka ma da kuka fito ciki ɗaya ma yana zalintar ka ina kuma ga wanda ba haɗin iya bare na baba, babu abunma da bazai iya aikata maka ba,
Azeema ce ta ta taɓota ganin tayi shiru bata ce komai ba, yasa ta ɗan dafa kafaɗar ta tare da kiran sunan ta,
Hakan yasa Ameesha katse tunanin da take tare da ɗagowa tana kallon Azeema, Hannu Azeema tasa tashiga yi goge mata hawayen ta, tace "tunanin me kike?
Ɗan murmushin yaƙe Ameesha tayi ta girgiza kai tace "ba komai.
Ita ma Azeema murmushin ta mayar mata dashi sannan tace "ko kefa haka nake son gani ke da zaki zama babbar lauya jaruma ki ƙwatowa ahalin ki fansa da mahaifinki ko kin manta labarin da kika ban kince mahaifin ki yace kiyi karatu kiyi shari'a da maƙiyan sa ki fito dashi daga gidan yari kin tuna?
Kai ta ɗaga mata tana ɗan sakin fuskarta harda murmushi tunawa da tayi zata haɗu da mahaifin ta wataran gashi ana cewa suna kama sai taji kawai ta fara hasaso shi, ta ƙosa ta gansa, sosai tuna hakan yaɗan sata farin ciki, haƙoranta har suna fitowa waje ta gyara zama tana fuskantar bestyn tata da kyau tace "na tuna bestyna Allah ya barmin ke inajinki yanzu ya kike ganin zumuyi da videon nan,
Azeema itama cike da farin cikin ganin ta saki ranta, ta zauna kusa da ita tace yauwa haka nake sonji ƙawalli ta kuma ƙanwata,
Ɗan hararar ta Ameeaha tayi jin tace ƙanwata, tace "a ina nazama ƙanwarki mutaso tare da ke ki wani cemin ƙanwar ki ko wata ɗaya fa baki ban ba..,
Azeema tace "Allah ko Aunty babba to bari kiji loƙacin da aka haife ki da wayona har goya ki nayi abayana nida yaya saleem har faɗa muke akan goyaki, ke har wanka ma namiki kawai maleji nake ƙawance dake amma ruwa ba sa'an kwando bane yarinya,
Dukan wasa Ameesha ta kai mata a kafaɗa tace "wallahi banyarda besty ƙarya kike Allah kuwa amma bari zamu raba musu muje gurin dadd....., Kasa ƙatasawa tayi sakamakon tunawa da ita da tayi ashefa bata nan yanzu Allah ne kaɗai yasan halin da take ciki yanzu jikin ta taji yayi sanyi,
Lura da hakan yasa Azeema saurin kawar da zancen tace besty kinsan me?
kai ta iya girga za mata kawai, Daman Azeema tasan bazata samu amsar baki ba daga gare ta dan haka saikawai ta share ta,
Ta ɗora da cewa "besty kina saurare na, dole ki tashi tsaye ko ince ku tashi tsaye dake da ɗan uwanki domin ku kaɗai me da zaku iya taimakon dangin ku dole ku haɗa kai wajen yin binciken ku yazama na bakin ku tare duk abun da ɗata yasani ya sanar da ɗaya tsintaiya ɗaya bata shara dole ku haɗa kanku, duk wani wanda zai taimake ku ba kamar yanda zakuyi ba mu namu kawai mu baku wata gudun mawar a wajen binciken ku bamu da ikon shiga wasu hurumin domin bamu ya shafa ba, kune zaku tsaya tsayin daka kuma kuna da damar shiga lungu da saƙo na cikin gidan nan wajen aiwatar da binciken ku, ku taka wanda kukaga dama ba kamar muba duba da yanda yayi ya tara duka mutanen awane ɗaya yana da iko dasu shiyasa yayi musu haka kuma dolen su suje koda ace da makiran acikin su amma mutum bai isa yayi jayayya dashi ba, dole yabi umarnin sa, amma idan bashi ba akwai wanda ya isa yasa su suyi haka idan kika cire manyan gidan, ɗan dakatawa tayi da maganar batare da ta jira amsar taba ta ci gaba,
Yanzu nidai a shawarar da zan baki itace wannan videon da muka ɗauka kar mubar kowa yasan dashi ko zuwa gobe ki sameshi a ɗaki kar kiji tsoran sa kiman ta da wannan babun ki ɗauki babun taimakon junan ku zakuyi naka sai naka dole zai fahimce sa kiyi masa bayanin komai sannan ki bada videon shi zaifi adana Sa akan yana wajen mu, daga nan kuma sai mufara sa ido akan kowa bincike mutane da yawa ganganci ne saboda zuciya bata da ƙashi wataƙil za a iya samun mai ruɓaɓɓiyar zuciya yana cikin ku yagama sanin sirrin ku daga baya kuma azo asiye sa da kuɗi ya canza ra'ayi to irin haka sai kiga ana ta abu amma ankasa cimma nasara akai arasa a inda matsalar take kiga duk abun da aka ƙulla sai ana fatan nasara sai kiga ya warware, amma idan yazamana muhimman abun yakasan ce agurin ku inyaso sauran da zasu taimaka muku kuma irin mu baiwuce na muje wani waje ko mu nemo muku kaza ko mu tsaya muku awaje kaza irin haka duk zai iya faruwa kuma zamu taimaka muku zai zamana ana taimaka muku amma su kansu waɗanda suke taimaka mukun basusan taƙamaimai inda kuma dosa ba ina fatan kina fahimtar inda zance na ya dosa,
Cike da gamsuwa Ameesha ta gyaɗa mata kai aranta tana mamakin yanda akai tunanin ta yazo ɗaga dana tsohon nan,
Azeema taci gaba da cewa"bari in barki haka kar tunkina fahimta ki daina ganewa yanzu dai abun da zakiyi shine kiyi masa bayanin kuma ki basa sannan abu nagaba shine dole asan abunyi a shekarar nan mu zana jarrabawa gaba ɗayan mu, mu haƙura da sss 3 ɗinnan muyi gaba sannan mudage da karatu musamu result me kyau mushiga University ta yanda zakiyi sauri ki gama karatunki idan Allah ya taimakeki kisamu kifara aiki da wuri kinga koda hanya ne sai ayi mana nima can zantafi ƙafarki ƙafata, nasan tunda akwai kuɗi hakan bazai bamu wahala ba ko jinkirin rashin samun aiki, kinga komai zaizo mana da sauƙi ana tunanin fa amma ke ya kika ce,
Ɗan jimm Ameesha tayi tace "eh to banƙi ta takiba maganar gaskiya ce amma dai bari muyi maganar da maama inji me zasu yanke akai sai ayi komai da wuri, amma ba kya ganin kuma yanzu idan na surfafa da karatu taya zamu iya yin wani bincike hakan kamar zai raba min hankalina biyu ne daga ƙarshe inzo inkasa yin ɗaya, ga karatun low da wahala ga kuma tsawon shekarun da zamu ɗauka duk da bansan shekara nawa bane amma dai ina ganin kamar za aɗau loƙacin kafin nan kuma su ai tuni sun aiwatar da ƙudurin su akan mu,
"Haba besty kar ki damu da wannan bakisan ana iya shekara goma ba ana case ɗaya yaƙi kammaluwa saboda rashin shedu da hujjoji sai kiga ana ta ɗaga ƙara, ai babu abun da za afasa na bincike acikin gidan nan karfa ki manta bake kaɗai bace ga yayanki ga maama ga su Abu da ummy ga kuma su sam da su bossay kowafa yana kan bakansa na binciken abun da nake miki magana koda an kamasu kinga dole sai an shigar da ƙara to idan aka shigar da ƙarar kuma babu wanda zai tsaya muku duk da hujjojin da kuka tanada dan ganin sunyi nasara akanku zasu iya biyan ko nawane wajen kawar da waɗannan hujjojin naku su zama basu da amfani ko kuma asiye lauyan da zaku danƙawa case ɗin naku daga ƙarshe a watsar da shari'ar ke duniya fa yanzu cin hanci yayi yawa babu abun da baza a iya yiba mutuƙar aka bawa mutum kuɗi yanzu zaki ga mutum yacanza daga nagari ya koma na wiwi saboda kuɗi,
Ameesha tace "kuma fa hakane to shikenan duk da hakadai zamuyi magana amma ba yanzu ba saboda halin da ake ciki yanzu bata makaranta ake ba ga dadda da ta ɓata kinga hankalin su duk ba akwance yake ba amma da zarar anɗan samu nutsuwa zanyi musu maganar kar kidamu mudai ci gaba da addu'a Allah ya taimake mu ya dafa mana,
"Ameen" Azeema ta amsa mata sannan suka miƙe daga gurin zasu bar gurin juyawar da Ameesha zatayi taga wani ya juyawa da sauri shima yabar gurin gaban ta taji yayi wata irin faɗuwa, cike da fargaba hawaye har sunfara taruwa a idon ta tace besty mun shiga uku wai meyasa abubuwa suke zuwar min a haka,
Cike da rashin gamsuwa Azeema take kallon ta tace "me kuma ya faru?
Cike da rashin nutsuwa bakin ta har yana harɗewa Ameesha tace "besty kingan sa can yanzu yabar wajen nan shikenan asirin mu ya tonu yagama jin duk tattaunawar da mukayi zaije ya faɗa musu nasan baza su barmu da rai ba besty ya zamuyi yanzu,
Azeema ma ba ƙaramin razana tayi ba da ganin mutumin basuga fuskar shiba kawai dai sunga bayan sa, dan haka bazasu iya sanin ko waye ba,
Da ƙyar Azeema ta iya aro jarumta da nutsuwar ta ta dawo da ita jikin ta sannan tayi saurin riƙe hannun Ameesha tace zama ko jinkiri ko maida yanda akayi bai taso ba mayi daga baya muyi sauri mutafi muje can tunkan su cinma mu a harabar gidan nan muje mu ɓoye wayar nan kafin ya farfaɗo ayi gaggawar sanar dashi nasandai ai ƙaryar su su shiga ciki suce zasu ƙwata kuma koda sun kama mu ai bazasu taɓa samun abun da suke nema ba, yanzu abu na gaba da zasuyi shine yanda zasuyi su samu wayar nan, tana maganar cikin sauri kuma tana jan Ameeaha suna sauri kamar zasu tashi sama ko gabansu ma basa kallo tafiya kawai suke,
Ameesha ce ta juya bayan ta ɗan ji take kamar ana binta amma da ta juya bata ga kowa ba hakan yasa taƙara ɗaga ƙafa suka cigaba da saurin Allah ya taimake su har suka ƙarasa inda Meer yatara mutanen nan, nanɗinma basu tsaya bi takan kowa ba suka wuce part ɗin maama Saida suka shiga sannan suka samu damar dakatawa da tafiyar da suke,
Loƙacin da suka shiga babu kowa afalon daman sunsan hakan zata faru baza su tadda kowa ba,saboda loƙacin da suke waje azaune su maama suka fito da shirin fita dalilin zuwan su wajen Meer kenan maama ce tace suke su kirashi yazo ya sallami mutanen nan yabari sai zuwa gobe yanzu fitar sauri takama su yadawo ya zauna a part ɗin tare da su Ameesha, suna ai kansu kuma suka fita daga gidan, su Amra kuma daman tunkafin loƙacin momma ta kirasu ahiyasa basu tafi tare da su ba, loƙacin sukaɗai ne, shine su kuma sukaje kiransa daga nan kuma kunnuwan su suka jiyo musu maganganun da Waziri yake Azeema tayi saurin ɗauko ƴar ƙaramar wayar ta tayi musu video da ita, duk da ba agani sosai amma dai ana iya gane fuskokin su,
da suka ga ba kowa a falon suka juya suka ƙulle ƙofar da muƙulli duk da akwai masu tsaro a wajen babu ta yanda za ayi su bari wani ya shigo amma Saida suka saka muƙulli ajiki sannan suka nufi ɗakin Meer suka shiga neman inda zasu ɓoye wayar har sun buɗe jakar kayan sa zasu saka wayar sai, Ameesha tace besty muke ta wahalar ɓoye waya me zai hana mu zare memoryn daga jiki mu ɓoye shi inyaso sai mu fita da wayar mu barta a hannun mu ma koda zasu ganta idan ma sun ƙwata bamu da matsala da hakan,
Azeema tace "eh kumafa hakane tana daf da zarewa idon ta ya sauka akan wayar dake kan bedside drowar da sauri take ta ɗauka tana dannawa taga ba password ajiki tace bari mu fara turawa duk incase dai duk da nasan bamai shigowa nan amma dai mutura take suka buɗe Bluetooth suka tura masa a wayar sa sannan suka zare memoryn suka nemi wani waje suka ɓoye shi yanda inba su da suka ɓoye ba babu wanda ya isa yaga gurin da suka ɓoye, sannan suka fito daga ɗakin, tunkan su ƙaraso falon sukaji ana bugawa, saida suka tsorata gaba ɗayan su sannan suka ƙarasa bakin ƙofar jin muryar su maama yasa sukayi saurin buɗe ƙofar suna buɗewa suka ga dadda shame shame ummy ta riƙota akafaɗa maama ta riƙo ɗayan hannun kamar bata numfashi ga jini da yake zubowa ta hancinta, kana ganinta kasan ba ƙaramin jigata tayi ba jikin ta ko mayafi babu ɗan kwalinma duk ya sukurkuce yayi gefe..........✍️✍️
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️xeemat...love❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
______Ganin halin da dadda take ciki yasa Ameesha sakin kuka tana ƙarasawa gabanta zata taɓa ta, Azeema tayi saurin janta gefe, tana bata haƙuri, Su kuma su ummy suka ƙarasa shigowa da ita akan kujera suka kwantar da ita,
Abu ne ya shigo shima da saurin sa yace "Ina Meer yake yazo ya dubata, yayi mata treatment abata magani,
Kuka sosai Ameesha ta ƙara saki tana zuwa gaban dadda tana cewa "me yasami dadda ta waye yayi mata haka kamar fa bata numfashi dadda dan Allah kar ki mutu kibar ni dadda kitashi dadda kitashi duk tabi ta rikice ganin dadda bata motsi girgizar tafara yi tana kiran sunan ta saida ƙyar Maama ta kamo ta ta shiga rarrashin ta tace "babu wani abu ki kwantar da hankalinki daddar ki ba mutuwa tayi ba yanzu zata tashi kiyi mata addu'a kinji kukan ya isa haka yi haƙuri kidaina kar haddasawa kanki ciwon kai, yanzu za adubata ta tashi suma ne kawai tayi shima bata daɗe da suma ba da ranta muka sameta muna daf da shigowa ne ta suma amma yanzu zata farfaɗo kinji yarinyar arziƙi ke da nasanki da dauriya kidaina ɗaga hankalin itama ummy Saida ta zauna kusa da ita tana bata baki duk dai dan su kwantar mata da hankali,
Maama tana gama faɗa mata haka ta shiga goge mata hawayen ta amma itadai Ameesha bata iya cewa komai ba kawai dai tayi shiru tana sauraron ta hankalin ta kuma gaba ɗaya yana kan dadda dan batajin zata iya kwantar da hankalin ta kamar yanda Maama take buƙata,
Ganin tayi shiru ya sa Maama ta kalli Azeeama tace "ke je ki kirashi yi sauri ko yana waje ko yana ciki dan naga mutanen da nace ya sallama suna gurin ko baku gaya masa saƙona bane,
Azeema kasa asma mata tayi duk sai ta ɗan dubur buce sai ta kalli Ameesha itama Ameesha ta kalle ta maama na niyar ta ƙara magana Ameesha tayi saurin tarar nufashin tace "eh da mukaje bamu gansa ba shiyasa muka dawo saidai aduba wajen ko yanzu yadawo,
Maama ta kalli Abu "tace to ko zaka dubama wajen nan nasan idan yaganka zaifi zuwa da gaggawa,
Abu yace "to bari naje amma kamar ba ya wajenan nidai da nashigo kamar bansame shiba, amma dai bari induba ko saurin da nake yasa ban lura dashi ba, yana kaiwa nan ya fita daga falon,
Sudai su Ameesha sai kallon kallo sukeyi su da suka san gaskiyar lamarin amma bazasu iya faɗaba, dole suyi shiru suga yanda abun zai kasance, ga mamakin su sai suka ga Abu ya shigo tare dashi Abu agaba shi abayansa abun yabasu mamaki sosai ko taya su Waziri suka fito dashi daga ɓangaren nasu batare da wata matsala ta faru ba, kawar da tunanin sukayi ganin ba mai basu amsar da suke buƙata a halin yanzu,
Maama ce ta kalle su tace "yauwa a ina kasamo shi?
Abu yace can na hango sa yana niyar kaiwa bakin gate ko ina zashi na tambaye sa kuma yamin halin nasa na raini da yasaba yayi min shiru da muka ƙaraso ma nace masa ya sallami mutanen da yatara sai yace mun ai shi bashi ya tara suba tsabar wulaƙanci da rashin mutunci irin nasa da acikin mutane nayi masa maganar shikenan ya kunyata ni ya maidani ɗan iska, Sai yace "wai insunga dama su kwana agun tunda bashi yasa su zauna ba, sai ni na sallame su,
Da mamakin kalaman Abu Maama take kallon sa tace "anya kuwa lafiya yake,
Cike da taƙaici Abu yace lafiyar sa lau daman irin wannan abun ai ba sabon abu bane awajen sa rainawa mutane hankali ai yadaɗe da yin degree akansa,
Ummy ma duk da tayi mamakin jin hakan amma itama sanin halinsa sai yasa tayi tunanin zai aikata fiye da haka ma indai Meer ne wataƙil yanzu wani dalilin yasa shi faɗar haka ko kuma zuciyar tasa ta masifa ce yasa tun abun da ga haɗasu yake jin haushin mahaifin nasa shiyasa yagaya masa haka dan yarama, tasan kaɗan daga cikin aikin sa, Da haka tabarwa kanta yarda tayi na'am da abun da yazo mata rai,shiyasa itama ta ɗora dacewa wallahi Maama iskanci ne kawai sarai yana sane wulaƙanci ne irin nasa,
Itadai Maama jinsu kawai take amma zuciyar ta bata yarda da abun da suke faɗa ba akansa tana tunanin something is wrong da yaje part ɗin