Showing 123001 words to 126000 words out of 170049 words
za'a iya canzawa amma idan bada nawa ba, saidai kawai a buɗe ta idan ansan password,
Meer yace "to bari in sake gwadawa, yafaɗa yana duba inda M da Y take yadanna su sannan ya kuma duba D take sai ya danna ta tare da furtawa a fili yace D ko?
Abban Ameesha yace "Eh.
Sannan Meer ya kuma cewa E ko?
nan shima Abban Ameesha yace "Eh,
Sai Meer yace "A, R ko?
"A'a ba haka bane, kaida wai wannan DEAR kasaka daman, ai ba wannan DEAR ɗin nake nufi ba,
"Meer yace "oh to ai naji kana cemata Noori ne shiyasa nayi tunani ko da turanci ne shiyasa kake ce mata My Dear,
Ɗan murmushi Abban Ameesha yayi tare da saurin goge hawayen da yaji yana neman zubo masa, idan ya tuna mutuwar ta ba ƙaramin kuka yake shaba, ko zancen ta akayi sai ta zubar da hawaye, jin mutuwar ta tafi komai tsaya masa arai, danji yake da yasan idan ya dawo bazai ganta ba, da ya roƙi Allah tun wuri ya ɗauki ransa, tunda suka faɗa masa daurewa kawai yake saboda bayaso suma su shiga damuwa, shiyasa sai yaje kwanciya yake kukan sa, shi kaɗai yasan halin da yake ciki na rashin ta, amma baya bari kowa yagane hakan,
"Hello, Uncle kanaji na kuwa, Meer ya katse masa tunanin sa....,
Da sauri ya dawo daga tunanin da yatafi tare da saurin daidai nutsuwar sa, yace "Eh, ina jinka.
"To Uncle me zan saka?
Abban Ameesha saida yaƙara sakin wani murmushin da direct zamu kira murmushin da murmushin yaƙe,
Sannan yace "Kasan sunan ta NADEEYA. To ni kuma sai nacire mata NA ɗin nake kiran ta da DEEYA, sai kuma kowa ma ya koma kiran ta da hakan bayan kuma munyi aure, sai ni na ƙara mata da MY, nakece mata MY DEEYA, ko kuma ince mata Noory,
jin hakan yasa Meer yayi saurin saka yanda yaji Uncle ɗin nasa yafaɗa,
yana sakawa kuwa akwatin ta buɗu,
"yauwa Uncle ta buɗu,
"Dan Allah dagaske meye a ciki komai yana ciki ko ankwashe su,
cike da damuwa Meer yace "Uncle da akwai amma kamar duk banaka bane aciki duk an canzasu an zuba wasu abubuwan acikin, amma baridai zuwa gobe zamu yi maganar sai da safe ka kwana lafiya,
Abban Ameesha yana yunƙurin yin magana kenan Meer yayi saurin kashe wayar saboda idon sane ya sauka akan wani dake cikin akwatin shiyasa yayi saurin katse kiran,
Zaro wata takadda yayi wacce take manne da wani passport ajiki, hoton ya ƙurawa ido, cike da ɗunbin mamaki da ya kusan kashe shi a zaune agun, duk da yana zargin hakan amma kuma ƙara samun tabbacin ba ƙaramin mamaki hakan yabasa ba,
Ameesha ce ta taso ta zauna agun dan ganin abun dake ciki saboda taki duk wayar da akayi da mahaifin ta kuma ta fahimci inda suka dosa, inda itama, ta fara wani tunanin,
Ganin tazo wajen yasa yayi saurin lanƙwas takaddar saboda baya so, ta gani,
Abun da baisani ba kuma tuni ta gani amma sai ta barsa a bata gani ba, kawai dai tunanin ta bai gama tantance mata hoton waye ba, tanade so tagane hakan,
Cigaba yayi da zaro takaddun ɗaya bayan ɗaya yana ganin adadin su da kuma canjin wasu da akayi, harda kamfanunnuwa, ga kuma na Uncle ɗin waɗanda suka shafi gurin aikin sa ma banki, su ba a canza su ba, saboda baiyi singning ɗin su ba,
sai kuma can ƙasa yaga wasu suma sumai, da sauri ya ɗauki suma suman yana miƙewa daga gurin, ya nufi inda Bossay yake ta aiki har yanzu yakasa gano inda location ɗin yake, ana tayi masa yawo da hankali sai ya gano inda yake sai kuma yaga har ya canza wani garin ma da ban, sai yagan sa a can sai ya gansa acan, haka a ke tayi masa yawo da hankali, sai kuma yaga anma sauke layin daga kan waya gaba, ɗaya,
wata wayar ya ɗauka acikin wayoyin ya fara gwada sims ɗin a ciki guda biyu ne daman sai yasaka,
Yana sakawa saiga message from bank, alart kawai ya fara ji, yana dubawa yaga anata zarar kuɗi, a ciki, da sauri yayi check balance yaga milyoyin kuɗaɗen daka ciki,
Mamaki ne yakama sa, duba daitals ɗin SIM ɗin yayi nan yagano ashe ma Sim ɗin Uncle ɗin nasane,
contact ɗin ya shiga dubawa yafara ganin numbers ɗin dake kan layin waɗanda akayi saving ɗin su,
Number wayar ya zaro yasaka wata number dan yaƙara tabbatar da zargin sa yazama gaskiya,
Yana sakata yayi dailing nan take ta fito masa da wani suna, da saura kaɗan ya saki wayar sai yayi saurin riƙota,
Maida duban sa yayi ha Bossay yace "ka gano inda location ɗin yake,
"Eh nagano, amma kuma matsala yake ban, sai gurare yake kaini da yawa amma dai yanzu naga ya tsaya agu ɗaya, saidai kuma ina tunanin ba gaskiya bane saboda wai yanda ya nuna min anan unguwar ne, kuma acikin gidan nan, a cikin gidan ma, kamar anan wajejen take, saidai mufita mu duba daidai inda take dan ina ganin har yanzu kamar wasa ake min da hankali,
Meer ne yace "ba ƙar ya bane tashi ka gani,
Tashi yayi yabasa guri,
Nan Meer ya zauna ya ƙara gyara zaman sa da kyau, wayar sa ya ɗauka yayi typing me tsawo sannan ya kira Ameesha yace "ungo karan ta kuma kiyi min sauri kar ki ɓatan loƙacin,
Tana karɓa ta fara karantawa, tunkan taƙarasa karantawa, ta juya ta fita daga ɗakin cikin sauri,
Shi kuma yaci gaba da dubawa, yaga dai tabbas location ɗin yana inda Bossay yace, sai can kuma, yaga baya gurin shima, saida ƙyar ya iya gano inda abun yake,
A wata unguwa yagani nan take yace wa Bossay su tafi,,
Kafin su fita saida Ameesha ta kawo masa saƙon sa, sannan suka fice daga gidan, loƙacin tara har ta kusa,
Gudu kawai Meer yake dasu, kamar suyi tsuntsu haka yake ji, saboda suna tafiya shima abun yana nuna musu gaba akeyi, kuma tazarar su da nisa,
Haka sukai ta tafiya cikin gudu tun suna ganin abun yana tafiya sai kuma sukaga ya tsaya, inda yake sukaci gaba da bibiya,
Suna zuwa inda abun yake sukagan su abakin wani babban hospital, dake unguwar kanada, parking sukayi tare da fitowa suna ƙara duba daidai saitin da yake, daga can gefen asibitin suka ga abun ya nuna musu, gurin suka bi, suna zuwa kuwa saiga waya a yashe a ƙasa harma ta farfashe alamun jifa akayi da ita,
Da sauri Bossay ya ɗauko ta, Meer shima yayi saurin karɓa suna duddubata, wayace me tsadar gaske amma har aka iya jefar da ita,
Kamar Meer yayi ihu haka, yaji cike da ɓacin rai "yace ƙarya kuke wallahi baku isa ba, duk inda kuka sai na nemoku,
Bossay ne yace "Please calm down zamu nemosu, tunda kaga haka jefar da ita akayi kuma ina me tabbacin barin garin za'ayi shiyasa aka jefar da ita, dan aƙara raba mana hankali,
Gaba Meer yayi yabar Bossay agun shima sai yayi saurin binsa, abaya, me gadin suka fara sannan meer yace nuna masa hoton Dady yace ko kaga me kammanin a cikin gurin nan,
A'a me gadin yabasa amsa,
Ciki suka shiga inda sukai ta tambayar mutane, da ƙyar suka samu wata likita aciki, tace ai tasan su itace ma ta rakasu bakin tati suka hau motar, dan mutumin ma baiji sauƙi sosai ba, suka sa aka sallame su,
Tambayar ta sukayi tasan unguwar da suka tafi, da har tace musu a'a sai kuma tayi saurin tunawa tace ta sani taji sun tambayar me keke napep tashar da ake hawa motar abuja zai kaisu, kuma basu daɗe da tafiya, dan yanzu bama suyi nisa ba,
Ai tun kan takai ƙarshen zancen suka baro gurin ta suka fito da gudun su,
Mota suka ƙara faɗawa Meer ya kuma janta da gudu sannan yacewa Bossay ya duba wayar da kyau sannan ya duba last kiran da akayi da ita,
Wayar ce taki kawo yayi yayi taƙi kawowa saida ƙyar ta kawo amma taci rabin screen, kuma babu security ajiki, da haka Bossay yafara duddubata amma tajikin System ya shiga,
Nan yaga wani saƙo anturo, shima kuma angoge sa, amma saida ya shiga ya gano inda yake, message akayi a kace,
_komai yazama ready jirgin ku zai tashi gobe da safe ƙarfe takwas, sai ku hanzarta ku shigo a yau, kayan kuma duk nagama haɗa muku kuma zuwa ɗauka zakuyi_
Da sauri Bossay yabi diddigin layin shima yagano daga can abujan yake,
Cike da murna da farin ciki yace "na gano karma musha wahalar binsu bazamu same su ba, yanzu, zasuje Abuja acan zasu kwana jirgin su zai tashi ƙarfe takwas na safe,
Da sauri Meer yaja burki ya tsaya, tare da juyawa ya kalli sa, sannan yace ka tabbata, taya akai ka gano hakan,
Nan Bossay yayi masa bayanin yanda yayi,
Da ƙarfi "Meer yace Good..!
Agogon hannun sa ya duba yaga ƙarfe goma harda rabi lissafi yafara yanzu idan suka tafi ƙarfe nawa zasu isa,
juya kan motar yayi kawai yace "zan sauke ka agida ko mu wuce can gida,
Kallon sa Bossay yayi, sannan yace"ni ina ganin ai gwanda mu wuce Abujan yanzu, idan muka bari sai gobe ai kafin muje jirgin su zai iya tashi,
"Kar ka damu yanzu dare yayi sosai, gwanda mu koma gida, muhuta ƙarfe Huɗu zan shirya intafi, kuma inada mutane acan zansa a bincika min jirgin da zai tashi ƙarfe takwas ba abune me wahala ba, ko banje ba, zan sa a riƙe min su,
To shikenan muje amma tare zamu tafi, yanda muka fara tare inason mu gamasa atare, dan ina son inga ƙwararrunnan da suka ƙware wajen yi mana wasa da hankali,
Saura kaɗan Meer yasaki murmushi sai kawai ya girgiza kai, yace "shikenan zaka gansu kuwa,
Yana faɗar haka ya juya kan motar suka koma gida,
Loƙacin da suka koma shaɗaya har ta wuce dan haka suna komawa wanka kawai sukayi sukayi sallah sannan, Meer ya fita da kansa yaje har kitchen ya nemowa Bossey abinci dan shi baci zaiyi ba,
Bayan sungama komai suka kwanta,
Basu suka tashi ba sai wajen ƙarfe biyar da wani sai kawai suka jira akayi sallar sunayi ma daga masallaci suka wuce batare da kowa yasan da tafiyar tasu ba,
Suna kan hanya Meer ya kira wasu mutanen daka hospital ɗin sa, yana basu aikin da zasuyi ba a sha ma wata hawahala ba aka gano jirgin, dan haka Meer yasa akaje har can airport aka sanar dasu abun dake faruwa akace dan Allah suyi haƙuri su bari sai ƙarfe tara su tashi yasan zuwa loƙacin sun zasu isa gurin,
An amince masa amma duk da haka saida yabiyasu sannan suka amince, da kuma gargaɗin tara nayi bazsu ƙara jiraba, zasu tashi,
sai loƙacin Meer ya samu kwanciyar hankali, da Bossay ne yake tuƙin daga baya kuma sukayi exchanging saboda sai yafisa gudu,
Suna kan hayan takwas ta buga gudu Meer yaƙara gudun yake amma ji yake kamar ba tafiya suke ba,
08:45 da biyar sauran su minti shabiyar su ƙarasa, sosai yaƙara ƙure wuta dan yakai ƙarshe a gudu,
Bossay ne ya kalli agogon sa yace saura minti biyar wayyo Meer ji yayi kamar ya kashe motar ya fito yayi gudu gani yake hakan sai yafi masa sauri,
8:58, saura minti biyu ya rage yayin da adaidai loƙacin suka shawo kwanar cikin airport ɗin, 9:00 na cika sukuma na tsaya wa a cikin airport ɗin, ko kashe motar Meer baiyi ba ya buɗe murfin motar da sauri ya fito aguje ya nufi wajen jirgin,
Yayin da jirgi kuma shima yake shirin tashi, dan kowa ya shiga ya zauna tashin sa kawai ake jira, dan da tunima ya tashi sai aka ƙara samun wani neman taimakon daga wajen wasu passengers ɗin da basu samu damar ƙarasowa ba, amma dake suma suna da uwar kuɗin su kuma ta hanyar da suka biyo dole a jirasu, duk da aƙa'idar su babu jira, amma su sai yazamana dole ajirasu,
shiyasa suma su Meer suka zo suka same sa, amma da dan ta sune da tuni sun tafi,
Da sauri Meer yaƙarasa wajen jirgin, yana zuwa ya shiga da tsallen sa, yana shiga kuma shima Bossay ya shigo,
tsaye sukayi a tsakiyar mutanen dake cikin jirgin, suka fara kallon mutanen ɗaya bayan ɗaya,
Can suka hango wasu kujeru guda biyu duk babu mutane, akai, tsoro da firgice ne suka rufar musu, da sauri Meer yace "ina masu gurin nan,
Kafin ma abasa amsa, Bossay yace gasu can, ya faɗa yana nuna waje ta jikin window,
Meer na ɗaga kansa ya hango su suna tunkaro wajen jirgin cikin sauri,
Wata sanyayyar ajiyar zuciya Meer ya sauke tare da furzar da iska me zafi daga bakin sa,
Ɗaya daga cikin ma'aikatanne yace "daman sune ai to ai saboda su ma muka tsaya bamu tafi ba, kuna nufin duk jiran nan, da mukayi a banza,
Wani wawan kallo Meer ya jefamasa yana ƙoƙarin dunƙulle hannun sa, dan maganar da yafaɗa ba ƙaramin ƙona masa rai tayi ba wata kon suna nufin daman badan su suka tsaya ba, duk uban kuɗaɗen da ya tura musu,
Bossay da ya riga yasan halin sa, sai yayi saurin riƙo hannun sa, yace muje mana,
Dadyn Rasheeda ne agaba sanye cikin manyan kaya kamar bashine ya taso daga gadon asibiti ba, kafaɗar su kuma ya saƙalo wata jaka, sai wata mata agefen sa ita kuma taci uban ɗamammun kaya, ta zubo da ƙarin gashin ta gefe,
Hannun ta ɗauko da wata ƙatuwar trolley tana janta, yayin da ta ƙwama wani ƙaton glass a idon ta, ga takalmi me tsini, haka take tafiya ɗaiɗai, da dogayen takalman masu tsini,
Daga bayan su kuma wata mata ce sanye da baƙar riga har ƙasa sai baƙin hijabi ɗan ƙaramin me haɗe da niƙab ta rufe rabin fuskar ta dashi, ita kuma babu komai a hannun ta, sai wata ƴar ƙaramar jaka da ta saƙalo ta akafaɗa,
Haka suke tafiya ɗaiɗai batare da suna kallon gaban su ba, har suka fara taka step ɗin jirgin Dadyn Rasheeda da ɗayar matar ƴar gayu su suka fara hawa kan step ɗin sannan ɗayar matar ta tako tayi taku ɗaya taga su Dady sun dawo da baya da baya,
Ɗaga idon da zatayi yayi daidai da fitowar Meer daga cikin jirgin tare da Bossay agefen sa, Meer yana fitowa ya sauke idon sa anata, dan shi yafi ji da ita akan kowa, tunda itace humman leader ɗin,
Ido cikin ido ta tsaya tana kallon sa, kana kallon ƙwayar idon ta zakaga zallar tsoro da furgici da tashin hankalin da bata taɓa tsammani saba adaidai wannan loƙacin,
Bata ankaraba ta garin juyawa ta take rigarta daga kan step ta wuntsila baya,
Dadyn Rasheeda ya juya zai gudu Meer yayi saurin damƙo sa, ɗayar kuma batayi yunƙurin guduwa ba ta tsaya, saboda bata san su waye suba,
Meer na riƙe sa ya haɗa masa da wani kyakkyawan naushi tare da turo sa shima ya faɗo daga kan step ɗin, su kuma sukayi tsalle suka duro shi da Bossay,
Meer da yayi tsalle akan ƙafar Dady ya dira yana dirawa kuwa ta bada sautin ƙara,
Shi kuma Bossay kan matar yayi da yaga tana niyar tashi caƙumo wuyan ta yayi da hannu biyu ya miƙar da ita tsaye,
Yana ɗagota yasa hannu ɗaya ya fusge abun niƙeb, take fuskar ta ta bayyana a fili, Bossay na tozali da fuska ta, bai san loƙacin da ya sake ta ba yayi baya yana niyar faɗuwa,
Ganin ya saketa yasa ta juyawa zata gudu domin tsiratar da ranta, ai ko taku uku batayi ba,
Meer yayi wata irin sufa daga inda yake yaƙarasa bayan ta tare da buga kanta gaba, ta kifa da fuska,
Bossay na tsaye har karkara yake saboda ɗimaucewar da yayi, bakin sane ya shiga karkawa zai kira sunan ta amma halin da ya tsinci kansa ya hanasa furta koda da kalmar farko ta harafin sunan ta...............,
[18/11, 7:34 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
*_🅿️45_*
______Meer ne ya ƙara saka hannu ya kuma ɗagota, yana ɗagoya ga kwashe ta da marin da saida jinta ya ɗauke loƙaci guda,
saidai ya farfasa mata baki da suka sannan ya fara janta da hannu ɗaya,
Lura da yayi Bossay baya cikin hankalin sa sai baibi ta kansa ba, gaban Dady ya ƙarasa hannu ɗaya yasaka ya riƙo ƙafar sa guda ɗaya, sannan ya shiga jansa a haka, har ya ɗanyi gaba sai ya dakata tare da juyawa ya kalli Bossay yana watsa masa harara,
Sannan yace "har yanzu baka dawo daidai bane in tafi inbar kane,
Duk da haka Bossay baida wani kuzari ajikin sa, haka yaje gurin ɗayar ma da yaga tana niyar guduwa, yana zuwa itama saida ya kwashe ta da mari, sannan yasaka ta agaba suka nufi wajen mota a tare Meer ya riƙe ɗayar matar da hannu ɗaya yayin da ɗayan hannun nasa kuma yana jan Dadyn Rasheeda aƙasa, jikin sa duk yafara kurjewa amma da haka yake jansa a ƙasa,
Sai bayan su kuma Bossay da ya tiso ƙeyar ɗayar matar,
Suna ƙarasowa gurin motar, bayan motar Meer ya buɗe ya saka su a ciki duk da gurin yayi musu kaɗan amma haka ya turasu a gwamutse, ɗayar kuma Bossay yasaka ta a baya,
komawa sukayi suka tattaro jakunkunan suka dawo suka zuba su a cikin motar sannan Meer ya shiga gaba, mazaunin me zaman banza, shi kuma Bossay ya shiga driver seat, ya tayar da motar