Showing 69001 words to 72000 words out of 170049 words

Chapter 24 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7229

haka kuma ta gane shine saboda shi kadai tasan yana mata irin haka,

Cikin muryar mamaki tace Yaya!

Tafaɗa tana ɗora hannun ta akan nasa, tana milewa tsaye, sakin ta yayi ta ta ƙarasa juyowa,

Cike da farin ciki ta rungume shi tana cewa irina wannan zuwan bazatan haka, Ni ai nazata bazaka ƙara dawowa ba ai ka koma can,

Sakin shi tayi sai taƙara rungume sa duk ta rasa inda zata tsoma ranta saboda jin daɗin ganin sa,

Shima yana dariya yana jan hancinta yace "ya fitina da rashin ji andaina ko har yanzu tana nan,

itama dariyar tayi tace tofa kadawo kenan ko hutawa bakayi ba zaka fara halin naka,

Zaiyi magana taƴi saurin dakatar dashi tare da kamo hannun sa tace yanzu dai duk ba wannan ba muke kayi wanka kazo kaci abinci,

Kallon ta yayi yace ammaa dai abari infara gaisawa da masu gidan "ina Dady yake ko baya gari,

"Ɗan murmushi tayi tace yana gari amma dai ya fita tun ɗazu muje ka gaida mom tana ɗaki sai kazo kayi wanka ka huta nasan ka kwaso gajiya,

"To ƙanwata wai yaushe kika ƙara hankali haka kodan auren yazo kusa shiyasa kika ƙara nutsuwa fari tayi da ido tace haba yaya au baka da masaniya aure tun yaushe aka fasayi da wancen yanzu nagano wanda yafi dacewa dani kai yaya baka gansa ba kykkyawane sosai ga kuɗi,

",Uhm wai Rasheeda yaushe kika koma haka ko kunya na bakyaji kike gaya min wannan zance, to ni abar ni haka bari inje ma in fara sauke kayan nan da ko kitayani dasu amma sai zuba kika iya,

Rasheeda tace "to meye abun jin kunaya yaya kaine fa babban yaya
na idan ban gaya maka wa kake so infaɗawa, tsaka nina dakai ai ba wata kunya wallah............,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️

    'Rasheeda tace "to meye abun jin kunaya yaya kaine fa babban yaya
na idan ban gaya maka wa kake so infaɗawa, tsaka nina dakai ai ba wata kunya wallahi......,

   "Hmm to naji mai babban yaya, bari inshiga mugaisa da mom sai mu ɗora daga inda muka tsaya, ina fatan dai antanadar wani abun ko?

Ɗan turo baki tayi tace "haba yaya ai kasandai bansan da dawowar ka da na tanadar maka amma yanzu ka shiga kafin ka fito na tanadar maka ɗin, bari in shiga ciki, gurin lami, tasan yanda zatayi da babban baƙo,

Ɗan murmushi kawai yayi sannan yayi gaba zuwa wajen mom, ita kuma ta nufi kitchen cike da farin cikin ganin yayan nata,

yana zuwa ƙofar ɗakin mom yayi nocking daga ciki tace shigo,

Turawa yayi ya shiga ciki da sallama abakin sa, tana zaune gaban kayan tana duba wanda zata saka ya shigo, da sauri tajiyo jin muryar a bazata, ganin dai da gaske shine yasa ta ajiye sauran kayan ta juyo fuskar ta ɗauke da murmushi, tace "amma dai mafarki nake, dan nasan wannan ganin dai bada gaske bane saidai a mafarki, tana maganar tana ƙarasowa wajen sa,

Dariya yasaka tare da tsugunnawa a ƙasa yace "mom ba mafarki bane nine dai, suprise nayi muku shiyasa kuka ganni haka kamar na faɗo ta sama,

Itama dariyar tayi tace "gaskiya nidai bana son irin wannan zuwan haka kawai ba tarba mai kyau,

Ɗan shafa kansa yayi yana sakin murmushi yace "to mom tuba nake ayi haƙuri bazan ƙara hakan,

"gaskiya dai kar ka ƙara dan banji daɗi ba wallahi,

Haƙuri yaƙara bata sannan ta haƙura tare da samun waje ta zauna, daga kusa dashi a bakin gado, sannan ta ɗora da cewa "ya hanya ya gajiya?,

"Wallahi lafiya lau mom yana same ku, kuna lafiya?

Itama ta amsa masa da lafiya, nan suka shiga gaisawa ya daɗe agurin ta inda har ta ɗan basa wasu abubuwan da suke faruwa a gidan, sannan daga baya suka yi sallama yace bari ya watsa ruwa yaci abinci sai suce gaba da tattaunawa,

Bayan fitar sa, itama tayi saurin shirya wa ta fita taje ta samu su Rasheeda suna ta ƙoƙarin yi masa abin da zaici, ita da lami amma lami ce ƙarfin aikin, haka itama ta shiga suka haɗa hannu suka ci gaba da shirya masa abun da zaici mai ɗan daɗi..........,


************************


_____Shettima

'Tun ranar da abun nan ya faru ya koma gida bai ƙara samun wani sukuni ba, tunda ya dawo yake kwance a ɗaki ko abinci ma baya samu yaci sa sosai shima saidai indan hajiyar sa ta takura masa yake ci, dan tayi tayi yagaya mata abun da yake damun sa, sai yace mata babu komai daga baya ma kawai sai yace mata ai Sam ne baya gida yabata labarin abun da ya faru, sannan yace sai kiran wayar sa yake taƙi shiga duk ya kashe wayoyin sa, ga kuma halin da mahaifiyar sa take ciki na ƙarin abun da ke faruwa acikin gidan su, saobada suma labari yazo musu tuntuni sun san duk abun dake faruwa tundaga A har Z shiyasa abun yake damun sa, ya rasa inda zai samu sam ya sanar dashi abun dake faruwa dan yadawo wajen mahaifiyar sa, yayi mata ƙarya da fakewa da Sam,

Dalilin hakanne yasa ta rabu dashi itama ta taya sa neman Sam ɗin amma aduk loƙacin da takawo masa abin ci yaƙi ci sai tayi masa faɗa wataran kuma tayi masa nasiha da kwantar masa da hankali da hakan yake haƙura yaci,

Yauma kamar kullum yana zaune akan kujerar yasaka abincin agaba yana kallo a zahiri zaka ce abincin yake kallo amma a baɗine hankalin sa bama ya gurin, tunanin sa kawai yake yanzu ai suna can tare, ga taƙaici ya hana sa zuwa gidan su, dan har yanzu haushin yake ji, saboda duk laifin tane mai yasa da yace kada ta shiga ta shiga, shiyasa ya rabu da ita yayi alƙawarin bazai ƙara neman ta ba, indai ba ita tane me shiba, gashi kuma abun nema yake yayi masa illa yakasa jurewa,

Yana wannan tunanin wayar sa tayi ringing da kamar bazai dauka ba, sai kawai yaja tsaki tare da miƙa hannu ya ɗauke ta batare da ya duba number dake kiran shi ba, kawai ya ɗaga tare da kara wayar a kunne, sai yayi shiru baice komai ba, kamar daga sama ko a mafarki yaji saukar murya ta a cikin dodon kunnen sa, da sauri ya zaro wayar ya duba screen ɗin wayar da ya tabbatar da wai da gaske ne abun da yaji ko kuma kunnuwan sane sukayi masa ƙarya, zubawa number ido yayi cike da tabbatar wa kansa ganin sunan da yayi saving da number ta ɓaro ɓaro yana yawo akan screen ɗin wayar, mayar da wayar yayi kan kunne sa,

Stiil dai yaƙara jin muryar ta tana tayi masa sallama,

da ƙyar ta tattaro duk wata guntuwar nutsuwar sa da ta rage masa ajiki, yayi ƙoƙari ya amsa mata mata da wa'alaikissalam, a yanda yayi maganar dake awaya ne ita baza tace a cikin damuwa yake ba,

"Ina wuni, yaji ta ƙara cewa,

"Lfy qalau " shima ya amsa mata dashi tare da ƙara yin shiru,

Itama kuma sai tayi shirun ta rasa kuma me zatace masa,

Jin tayi shiru har tsawon wajen minti 2, sai kawai ya daure yace "baki da abun cewa ne inkashe kin kirani kuma, kinyi min shiru,

Azeema ma ana ta ɓangaren ma daurewar kawai take dan ko kiran ma ta gwada kiran sa yafi sau ashirin tana fasawa tun ba yauba sai dai yanzu ta rufe idon ta ta daure ta kirasa,

Tana kwance akan gadon ta jin abun da yace yasa ta runtse idon ta, kuma bata san maiyasa takasa katse kiran ba tunda ya riga ya ɗaga, da ƙyar ta buɗi baki, tace "uhmm daman akan maganar nanne daka turo min message kace in sameka a mota ni kuma da na fito bangan kaba shine yanzu na kira inji ko maiyasa kace haka, idan da wata maganar sai muyi ta nan,

jijjiga kansa yayi jin rainin hankalin da tayi masa maiyasa zatace wai bata gansa ba bayan kuma ƙarya take yana kallon ta ko inda yake ma bata kalla ba tana fitowa ta tafi gurin motar da zasu tafi amma shine yanzu zata raina masa hankali, wani haushin tane yaƙara zuwan masa wuya,

"Shikenan ai tunda baki zoba a loƙacin ai ya wuce sai kije kuci gaba daga inda kuma tsaya, ai bani yakamata ki kiraba kije ki ta kiransa ƙarewa duk inda zaki ku tafi tare har bacci ma kuringa yi tare kar ku rabu da juna ƙarewa daukan ki a mota, sannan dan Allah kar ki ƙara kirana banaso tunda bani da matsayin da zan miki magana kiji to kije na barki dashi ɗin kirabu dani da abun da yake damuna basai kin ƙara min da taki ba banaso, Allah yaba ku zaman..., yana kaiwa nan ta buɗi baki zatayi masa magana kenan yayi saurin kashe wayar tare da jefar da ita aƙasa yana jin zuciyar sa na wani irin ƙuna,

Kwantar da kansa yayi ajikin kujerar yana rufe idon sa,

kamar daga sama yajiyo muryar hajiyar sa tana cewa "daman nasan wannan damuwar ba iya ta rasa Sam bace akwai wani abun aƙasa, ashe sirika tace ta saka min yaro gaba, tana maganar tana ƙarasowa wajen sa sannan ta tsugunna ta ɗauko wayar tare da zama a kusa dashi,

Buɗe idanun sa yayi tare da gyara zaman sa yana mamakin ya akai tajisa shi yama manta a inda yake da yasani ya koma ɗakin sa,

"Haba babana, muryar ta, ta katse masa tunanin sa, tace "haba haba sai kace bana miji ba kai waya gaya maka ana soyayya a haka, ba 'a saurin yanke hukunci cikin fushi, gaya min maiye tsakanin ku kuma mai ya haɗaku?

shiru yayi na wasu ƴan sakanni sannan ya numfasa da farko yaso ɓoye mata amma daga baya da ya tuna ta riga tasan komai, kuma daman tsakanin sa da ita ba wata ƴar ɓoye ɓoye baya iya ɓoye mata komai, tunda aduniyar nan ita kaɗai ta rage masa idan da wanda zai iya gayawa damuwarsa bayan ita to saidai Sam su su biyun nan su kaɗai yake gayawa damuwarsa to yanzu Sam baya nan dole ita ce wacce zai gayawa abu dake damunsa dashi akaran kansa abun mamaki yake basa baisan ya akai sonta yakamasa haka ba loƙaci ɗaya, kuma bai ƙara tabbatar wa ba sai ranar da yagan su da Hamza,

Nan ya gyara zama yafara bata labarin duk wani abu da ya faru tsakanin sa da Azeema amma yana rage wasu abubuwan kamar loƙacin da yafara ganin ta a office ɗin sa Salim baya nan har ya ɓalle mata bra, da kuma gurin da ya riƙeta a ɗaki har ta fito ta shiga kitchen ya ƙara binta, har Fulani taso ta kamasu Allah ya taimake su, komai Saida yagaya mata, har loƙacin da wannan na ƙarshen yafaru yagan su da Hamza alamun dai suna soyayya tare...,


Hajiya yana gama bata labari tasaka masa dariya sannan tace "masa ai ba haka ake soyayya ba wannan ai duk laifin sane tunda batasan yanayi ba kuma bai taɓa gaya mata ba to taya zata san yana sonta, idan sonta yake yi ai gaya mata zaiyi sannan tasan dashi amma bai gaya mata ba taya zai ringajin haushinta, nan dai Hajiya ta tsaya da kanta ta nusar dashi kuskuren sa da ɗora sa a hanya har ta fahimta sannan tace yaje har gidan su ya shawo kanta kuma yabata haƙuri in kuma ba hakaba to komai ma zai iya faruwa, yana zaune wani zai aure ta,

Ai a loƙacin ma yagama fahimtar ta kuma yagano laifin sa, dan haka ko ɗaki bai koma ba yace yanzu zai tafi gidan su, tunda de yasani, gwanda yaje da wuri tun loƙaci bai ƙure masa ba, kar yaje yaji labarin aure bai shirya mutuwa ba, dan idan yarasata ji yake sai ya rasa ransa,

Sallama yayi Hajiyar sa sannan ya tafi tana ta tsokanar sa tanayi masa dariya, haka ya fice daga gidan tabi shi da addu'ar samun nasara.......,


'yana kan hanyar sa yana tasakin murmushi sai yanzu yagama ashe kansa ya ƙulle duk baiga abun shiga damuwa ba, akan ɗan wannan abun da bai taka kara ya karya ba, duk laifin sane ma amma yana tafaman jin haushin ta ashe shine ma abun haushin gashi har ta daure ta kirasa amma yayi mata rashin mutunci yanzu kuwa dole yaje ya bata haƙuri akan abun da bata sani ba ya hauta da faɗa da jin haushin ta,

yana daf da ƙarasawa unguwar tasu dan kwana zaiyi kawai sai yaga wata mota tayi kwana, motar kuma kamar dai yasanta,

Da sauri yayi rivers ya juya yabi motar, dan yana da tabbacin motar asibitin suce kuma babu wanda yake shiga inba Sam ba, dan haka ya ware yajata da gudu yabita saboda waccen ɗin ma gudu ake,

Haka sukaci gaba da tafiya suna tafiya yana bin bayan motar har suka ƙaraso kusa da wata unguwa sai yaga motar tafara slow tare da samun guri akayi parking ɗin motar,

Tsayawa yayi shima daga ɗan nesa dasu yana hango motar yana jiran mai fitowa,

Yana gurin kuwa saiga Sam yafito daga ciki fuskar sa ɗauke da face mask sai p cap Dan badan yayi masa farin sani bana bazai taɓa gane saba,

yana ganin fitowar sa shima ya fito da sauri ya nufo inda yake,

Sam yana fitowa ya zagayo ya buɗewa sumy tare da miƙa mata hannu ta ɗora nata akai tana kallon fuskar sa ta sakar masa murmushi wanda hakan kana gani kasan tsatstsan murmushin ƙauna ne,

Shima da murmushin ya mayar mata, yana ƙarasa fito da ita daga ciki,


Fuskar sa ɗauke da murmushi idon sa akan ta, yace "yarinyar nan kin raina ni wallahi ɗan kwali yaja riga ko kinsaka ni agaba saida burinki ya cika gashi munzo to kuma wallahi ƙafata ƙafarki tare zamu shiga kuma a haka dan ko sakin hannun ki bazanyi ba, ba ruwana da idon mutane,

Ƴar ƙaramar dariya ta saki tace "wallahi baka isaba muje dai bakin ƙofa sai ka dawo ka jirani bafa daɗewa zanyi ba yanzu zan fito wallahi,

(tun bayan barin su gida washe gari ya ɗauke ta ya kaita wani gida ya ɗauko mata wata tsohuwa su ringa kwana tare saboda tsaro badan tsoro ba a ɗan kwana biyun nan da sukayi ba ƙaramar shaƙuwa sukayi ba har suka ƙulla soyayya zuwa loƙacin kowa ya fahimci yana son ɗan uwansa, duk sun tattara komai da kowa sun ajiye gefe sun rungumi junan su, ba inda suke zuwa soyayyar su kawai suke yanzun ma dalilin fitowar su, itace ta takura musu wai ya kawota gidan wata ƙawar ta zata karɓi wani abu yayi yayi da itama tagaya masa mai zata karɓa amma taƙi gaya masa,

Shi kuma sai yace bazai zoba sai ta faɗa ita kuma tace bazata gaya masa ba saboda sirri ne, daga nan suka rigayi yace baza su zoba, sai da ƙyar ta shawo kansa tayi masa wayo ta lallaɓa sa da kalamai, sannan ya yarda suka shirya suka fito tana yi masa kwatance har suka ƙaraso)

Sam zai yi mata magana kenan saiga shettima ya ƙaraso wajen, tare dayin gyaran murya,

Juyowa Sam yayi da mamaki yake kallon Shettima dake tsaye agabansa shima yana masa kallon mamaki yana kallon hannun su dake riƙe da juna, kallo ɗaya yayi wa sumy yagano ta, amma ita bata gane saba ganin sa yasa ta fara jan hannun ta daga riƙon da yayi mata amma sai yaƙara riƙewa ƙam,

"Malam kallon fa daga ina haka? Sam ne ke yiwa Shettima tamaya da ya tsatsaresu da ido,

"Hmmm daga sama nake ɗan rainin hankali kai watakon kana nan hankalin ka kwance kabar mutane acan cikin tashin hankali,sai neman ka ake ka kashe wa mutane waya anrasa inda kake,

Sauya kalar fuskar Sam yayi cike da yanayin rashin daɗi yace "idan an nemeni mai za ayi min, bayan an kore ni to kuma mai zan tsaya inyiwa mutane kaga malam kaima idan ba gaisawa ce ta kawo kaba ka rabu dani dan Allah ina cikin farin cikina kar ka sanya min damuwa ina zaman zama na,

"Haba Sam ni kake gayawa haka, koda yake banga laifin ka ba, amma dai koma meye ya kamata ka ajiye komai agefe abun da ya faru ya riga ya faru saboda gida ba lafiya ya kamata ka dawo gida kodan saboda mahaifiyar ka, duk da ta yanke hukunci cikin fushi amma yakamata kayi mata uzuri, ni bata gaya mana ainahin abun da yafaruba kawai dai tace kun samu matsala, tace ka tafi kar ka ƙara dawowa inda take, to amma tun ka ayi nisa ta gane kuskuren hakan nemanka take kamar me tayi kuka ba adadi, ga kuma babbar matsalar da ta faru acikin gidan, abun ya matuƙar cutar da zuciyar ta abun ka tausaya mata ne yanzu tana cikin wani hali babu wanda take buƙata kamar kai tana buƙatar ka akusa da ita yakamata ka koma gida Sam,

"Shiru Sam yayi kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya kalli sumy da jikin ta gaba ɗaya yayi sanyi tayi shiru ta sunkuyar da kai tana taso yasakar mata amma yaƙi,

Ganin damuwa a fuskar ta, yasa ya ɗan saki fuskar sa saboda ita, sosai ya zuba mata tare da kiran sunan ta a hankali ɗan ɗagowa tayi ta kalle sa batare da tace komai ba,

janta yayi can baya sannan yace "maiye haka kuma ki saki fuskar ki kinsan dai banson ganin ki cikin damuwa ko,

Kai ta ɗaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login