Showing 84001 words to 87000 words out of 170049 words
kasani kaf mutanen gidan ku babu wanda bansani babu wanda bansan tarihin sa ba, dan haka kama daina mamaki, saboda gidan ku ba ɓoyayye bane kowa ma zai iya sanin ku da wanda yake zaune cikin mutane da wanda baya zaune saboda kimar ku da martabar ku dole kowa yasan ku,
Kallon sa kawai Meer yake har saida yajira yakai ƙarshen maganar sa sannan yace "ban yarda ba kagaya min gaskiya waye kai? kuma waye yabaka labarin tarihin kowanne mu taya hakan zata kasance,
Murmushi tsohon yasaki yace kana son sanin ko ni waye kabari duk sanda muka ƙara haɗuwa zaka san ko ni waye, shawara ta kuma agare ka ka riƙe Khadijatu da kyau domin itace hasken rayuwar ka idan kaje kace ina gaida ita, ita tasanni,
Haɗe rai yayi tuna masan da yayi amma sai ya danne saboda yanaso yaji a ina yasan ta kuma ya akai yasan da aure har yasan sunan wacce aka ɗaura masa aura da ita,
Sai kawai ya maze yace "ok wa zance mata, ya nuna masa ba komai kamar babu wani abun da yafaru,
Sai tsohon yace "kace mata wanda ya taimaka muku loƙacin da ruwan sama ya dake ka ka suma, ta shiga tashin hankali ta fito waje cikin daren tana neman taimako anan take gaya min abun da ya faru, ka tambaye ta zata baka labarin sauran labari na barka lafiya, tsohon yana kaiwa nan yayi gaba shi ko nauyin matar da ya ɗauka ma baya ji duk tsawon surutun nan yana tsaye da ita,
kafin yayi wani yunƙurin dakatar dashi har yayi masa nisa, saboda tunanin da yafaɗa saura kaɗan zuciyar sa ta buga saboda jin sunan da tsohon yace masa Khadija kuma yace ya taimake su loƙacin da ruwa ya dake sa, idan ya fahimci maganar tsohon ana nufin ace yarinyar nan ita aka aura masa itace Khadijan kenan, a hankali ya furta Impossible yarinyar da ta kusan haifa itace amatsayin matar sa taya ma zai yarda da hakan,
Dawowa yayi daga tunanin da yafaɗa ya fara dube dube inda zaiga tsohon amma sai ya neme sa ya rasa, kamar aljani haka yagani ko ƙyarsa bai bai gani ba,
Hannu ya ɗora aka kamar ya fasa ihu haka yake ji yama rasa wane tunani zaiyi, abun haushin shi ma shine da bai tsayar da tsohon ba, dole ya lalubo tsohon nan, kodan maganar da yayi ya taimakasa loƙacin da ya kwanta shiyasa yake ta mamakin ya akai ya tashi daga suman da yayi bayan idan hakan ta faru dashi baya farfaɗowa da wuri, to shi mai yayi masa da yatashi da wuri haka wane irin magani yayi masa, wata zuciyar ce tace masa anya ba aljani bane kuma, in ba hakaba taya akai yasan komai har maganar auren da akayi alhalin dudu auren ba ayi awa biyu da ɗaura saba, kashhhh ya ƙara faɗa da ƙarfi yana dafe kansa, juyawa kawai yayi da sauri ya koma gurin motar sa ya shiga maimakon yayi gaba sai kawai yaja rivers dan juyawa gida, yafasa zuwa inda yayi niya...,
Yana shiga ya ƙara kwasar motar aguje ya nufi gida.......,
************************
______wasu mutane ne guda biyu ne agaban wata ƙofar ɗaki, suna hirar su saiga wani mutumi ya shigo cikin gurin yana kallon su,
Yana shigowa duk suka shiga gaida shi amsawa yayi tare da cewa "yaci abin cin?
Ɗaya daga cikin su yace "a'a tunda muka kawo sa yaƙi cin komai ko ruwa yaƙi sha, jinjina kai mutumin yayi sannan yace "ku ɗauke sa ku mayar dashi inda kuka ɗauko sa kawai kuma kar ku bari kowa yagan ku,
Ɗagowa sukayi suna duban sa da kyau sannan, ɗaya yace sir mu maidashi fa kace amma fa za'a iya samun amatsala da ƙyar fa muka ɗauko sa, aganina idan ma babu abun da za'ayi masa to kawai mu sake sa ya tafi mana, dan a yanzu nasan ana can ana neman sa kaga kwa wajen maidashi ai akwai matsala,
"Eh to nima nayi wannan tunanin to amma dole amaida shi saboda ba wanda nake nema bane ansamu matsala bama anan gidan wancen ɗin yake ba, ni kuma nasa kuka je wannan gidan duk atunanina shine ashe bashi bane,
Ɗaya daga ciki yaƙara cewa to yanzu ya zamuyi meye mafita,
Mutumin yace nidai gaskiya kusan yanda zakuyi ku maidashi hakan shi kaɗai ne mafita dan bamu san waye shi ba,
Sir amma fa ni ana ganin gaskiya kar mu mayar dashi dan bama mayar dashi ɗinne matsala ba, matsalar shine a yanda muka same wannan mutumin yana cikin wani hali duk yanda akai ɓoye sa kuma ana yi masa azaba dan daga ganin sa yana cikin wani hali kagafa yanda kansa yayi gashi yayi masa yawa ga gemu duk ya rufe masa fuska da alamun ya daɗe agun baya samun gyara, ga hawayen dake fitowa daga idon sa, gaskiya akwai abun dake faruwa da wannan bawan Allahn,
Ɗayan ya karɓe sa da cewa wallahi nima abun da yaban mamaki kenan babban mutum kamar sa amma hawaye na fita daga idon sa, kasan kwa ai ba ƙaramin abu bane ke samun sa ga kayan jikin sa kai mutumin nan fa sai a hankali kamar ba mutum ba, danni wallahi da farko ma tsoro yaban ga yaƙi yin magana, daurewa kawai nayi muka ɗauko.....
Mutuminne ya gyara tsayuwar sa yana nazarin maganganun su shima kuma daman tun kan su faɗa duk ya lura da hakan amma saboda ba hurumin sa bane shiyasa baibi takan saba, amma yanzu maganganun su yaƙara sawa yafara dogon nazari akan mutumin,
Ɗan numfasawa yayi yasamu guri gefe dasu yace "to nima naga duk abun da kuka faɗa a tattare dashi kubar shi anan zanje inyi shawara duk yanda ake ciki zan sanar daku idan ma sakin sane zangaya muku sai ku sake sa saboda bazan dawo ba zuwa safiyar gobe zan wuce kano da sassafe kuma ina tunanin ma zanyi wajen sati biyu acan....
Yana faɗar haka ya miƙe tsaye tare da cewa bari in shiga in gansa kafin in wuce,
"Ok sir' suka basa amsa,
Tura ƙofar yayi ya shiga ciki, can ya hango sa wajen jikin bango a zaune ya haɗa kai da gwiwa,
Ƙarasawa mutumin yayi kusa dashi tare da tsugunnawa, amma har yanzu mutumin dake kwance bai ɗago yagan saba,
"Uhm bawan Allah,
A hankali ya shiga ɗagowa har ya ɗago gaba ɗaya ya zubawa mutumin rinanun idanun sa da suka koma kalar ja akoda yaushe ga hawaye da suke zubowa dan ma duk gemu ya cika masa fuska ba aganin shatin hawayen da suke zubowa saidai kawai ka gansa daga cikin idon sa,
Sosai mutumin ya tausaya masa, ƙura masa ido yayi kawai sai yaga kamar yasan shi kamar kuma baisan shiba kawai dai shape ɗin idon sa da kuma hancin sane suke masa kama da waɗanda yasani amma kuma yakasa tuna a inda yasan mai irin waɗannan kamannin, ajiye tunanin kamar yayi sannan daga bisani yace "zan iya jin ko kai waye?
Shiru babu amsa nan yashiga yana ta tambayar sa abubuwa amma bai samu amsa koɗaya ba daga gare sa, babu yanda ya iya dole ya miƙe daga gurin ya rabuda dashi ya fita daga ɗakin,
Yana fitowa ya samesu batare da ya kalle suba yace "na tafi kuci gaba da kula dashi kawai, zuwa gobe ku mayar dashi gida zan sanar da sarki duk abun dake faruwa, amma kafin ku kaishi ina son afara siyo masa kayan sakawa sannan a haɗa masa ruwa mai ɗumi yayi wanka ya canza kaya sai ku kira wanzami ko kuma ma abu mai sauƙi kukaishi gurin aski ayi masa acan, a sauke wannan sumar ta kansa ayi masa gyaran fuska, sai ku kaishi can gurin sarki amma ku bari sai nace ku kai shi dan ba lalle bane sarki ya amince da hakan ba,
Shiru sukayi gaba ɗayan su kowa na tunanin maganar sa komai dai zasu iya yi masa amma sun san sarki bazai taɓa yarda bama, sunyi mamaki ma da har yake faɗar abun da yasan ba mai yiyuwa bane, amma yake faɗa,
Shima jikin nasane yayi sanyi dan yasan abun da suke tunani, dan haka sai kawai yace musu, ya tafi zasuyi magana zuwa gobe, suka amsa da to sannan sukayi masa adawo lafiya, ya fita daga gidan.......,
***********************
Meer na ƙarasawa cikin masarautar yayi parking ya fito daga cikin motar tsabar saurin da yake ma da ƙafa ya tura murfin motar yayi gaba, sauri sauri haka yake tafiyar tsirarun mutanen da suka rage suke shawagin su aciki duk wanda yagansa a hanya ya gaidashi sai ya harare sa wasu kuma ya zage su, yana daf da zuwa ya wuce wasu mutum biyu gudun kar su gaidashi ya zagesu shiyasa sukayi shiru,
Ga mamakin su sai sukaga yana zuwa daf da su sai ya tsaya tare da juyawa afusace yayi kansu, yana zuwa ya kwashe su da mari saida yabawa kowanne su guda biyu sannan ya shiga nuna su da yatsa yana cewa "saboda tsabar mugunta da ɓacin rai na cin sa, "baku da tarbiya ko kuna ganin mutane baza ku gaida su ba, to in ƙara wucewa wani ɗan iskan yaja bakin sa yayi shiru mutum yaga yanda zanyi dashi, yana faɗa ya juya yaci gaba da tafiya,
Su kam babu me ƙarfin yin magana dan abun yabasu mamaki ace ka gaida mutum yaƙi amsawa ya zage ka ma amma kuma kaƙi gaidashi ya hauka da mari.....,
Tundaga bakin ƙofa Meer yake jiyo kuka mai sauti wanda loƙaci ɗaya ya daki dodon kunnen sa,
Da ƙarfi ya tura ƙofar ta buɗe,
Ameesha ce a tsakiyar falon tayi zaman dirshen aƙasa sai shure shure take tana wani irin kuka na fitar hayya ci, tunda maganar auren ta riske ta take faman koke koke duk yanda akai da ita tayi shiru ma ta saurari mutane taƙi yin shiru, muryar ta har dashe wa take duk tabi tayi jaga jaga da fuskar ta hawaye da majina, duk ta haɗasu,
"Ni maiyasa za aura min mugu wallahi banason sa na tsane sa ni yaya bossay nake so wallahi bazan zauna dashi ba na tsane sa bana son sa, irin maganganun da take ta faman yi kenan Maama sai rarrashin ta ita da dadda, harda papa, duk suna cikin falon kowa na kalar rarrashin ta,
Su Azeema ma suna ciki duk sunyi tsuru tsuru da su saboda suma abun ya taɓa jin abun suke kamar almara,
Cike da taƙaicin abun da take dan ji yake kamar ya kasheta agun saboda tsabar jin haushin ta da yake ji, ƙarasa shiga falon, duk babu wanda yaji shigowar sa sai ganin sa sukayi kawai agaban su,
Bai kalli kowa ba kuma baiyiwa kowa magana ba kawai yayi sama da ita da hannu biyu,
Ƙara volume ɗin kukan ta tayi cike da tsoro tafara ƙoƙarin ƙwace wa,
Suma duk a tsorace suke kallon sa kafin wani yayi yunƙurin yi masa magana, har ya shiga ɗakin sa da ita yana shiga kuma ya ƙulle ƙofar tare da sauke ta ƙasa yasakawa ƙofar muƙulli,
Fuskar nan a haɗe ya juyo yana kallon ta, itama wani irin mahaukacin tsoron sane yakamata tafara ja da baya tana kuka,
Binta ya farayi tana baya yana binta ganin hakan yasa ta kwasa aguje tayi hanyar banɗaki, taku biyu yayi ya cafkota ya dawo da ita baya, take ta saki wata mahaukaciyar ƙara da sai ka rantse wani mugun abun akayi mata,
Ƙarar tace tasa su Maama suka ƙara ɗaga hankalin su duk sun rikice suna tsoron abun da zai mata koma yake mata tunda suka ji ƙarar ta,
Dukan ƙofar suke suna kiran sunan sa yazo ya buɗe ƙofar kar yayi mata komai,
Maama da taga tashin hankali na neman yi mata yawa tace dan Allah ka buɗe kar ka cutar da ita mun yarda za'a raba auren tunda bakwa so,
Babana ka buɗe ƙofar nan wallahi idan kayi mata wani abun ranka sai yayi mummunan ɓaci, cewar Papa da shima ransa yafara dugunzuma, sauƙin tama Abuu baya gurin,
Wata ƙarar suka ƙara ji ta saki sai kuma shiru ya biyo baya ɗif sukaji ta babu motsin ta ko ɗaya, gaba ɗayan su sukayi saranda jin ta ɗauke loƙaci guda kowa da abun da yake tunani........✍️✍️
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
______tsaye tayi saboda tsabar mamakin da yagama kashe shi, bai taɓa tunanin abun nata yakai haka ba, tun kan ya taɓa ta tana kurma masa ihu kamar yayi mata wani abun, hannu ya ɗaga zai mare ta saboda tsabar tsoro da firgice yasa ta ƙara sakin wata ƙarar tare da sume wa, tayi luuu zata faɗi yayi saurin riƙota ta faɗa jikin sa,
Haushi ne yagama cika sa kawai ya tura ta kan gado yana dafe kansa shigaba ɗaya ma tunanin sa ya tsaya yama rasa mai zaiyi mata ya huce taƙaicin sa,
Ruwan dake kan bedside drawer ya ɗauko yaje ya watsa mata a fuska, take ta sauke wani numfashi mai ƙarfi, tana ware idon ta kuma takara sakin kuka ta yunƙura da sauri zata sauka daga kan gadon, sai yasa ka ƙafar sa guda ɗaya ya danne ɗayar ƙafar ta,
Tsorata ta ƙara yi zata fashe masa da kuka ya daka mata tsawa yace "ya isheki haka kiyi min shiru idan kika ƙara ɓuɗar bakin ki da sunan kuka sai kinga yanda zanyi dake anan gurin,
Ɗif tayi ta daina kukan a fili ta saka hannun ta ta toshe bakin ta saboda gudun kar ya fito dan tagama tsorata dashi, musamman da taga idon sa ya kaɗa yayi ja,
Jin tayi shiru yasa ya ɗauke ƙafar sa daga kan tata, sannan yasamu gefen gadon ya zauna, tare da cewa sauko kizo nan gabana,
Cikin sauri ga tsoro haka ta rarrafo ta sauko daga kan gadon inda ya nuna mata ta zauna ta sunkuyar da kanta tare da haɗe jikin ta guri ɗaya da yake ta faman karkarwa, saboda sanyin da take ji sakamakon kukan da tayi har ya fara haddasa mata zazzaɓi,
"Zan tambaye ki kuma kar kimin ƙarya maiye ya faru dani ranar da kika rufe ƙofa akayi ruwa ya dake ni, taya akai na dawo cikin falon,
Ji tayi gabanta ya faɗi tunawa da tsohon da suka haɗu sannan maganganun da yayi mata suka shiga yi mata yawo akai sosai wasu maganganun nasa suka bata mamaki dan ta fara ganin wasu,
"Ba magana nake miki ba, Meer ta katse mata tunanin da ta shiga,
Cikin dashesshiyar muryar ta da bata fita sosai, tace "loƙacin da na buɗe ƙofar ka faɗo cikin falon shine na tsorata da naga kamar ka mutu shine na fito waje ina neman abun hawa dannadawo gida na faɗa sai kuma na haɗu da wani tsoho, nagaya masa duk abun dake faruwa shine......nan dai ta kwashe komai ta basa labari har abun da yabata yace ta ɗaura masa, da kuma kar tasake tagayawa kowa duk abun da yagaya mata da su haɗa kansu ita dashi babu abun da ta rage masa,
Shiru yayi yana ƙara nazarin maganganun nata da kuma abun da shima tsohon yagaya masa, to waye wannan tsohon ne yaje nufi dasu indai har yasan su haka to me yasa yake ɓoye kansa indai kuma ba aljani bane duk taya hakan zata faru yasan su yasan sunayen su kuma harda wasu maganganun ma, gaskiya da alamar tambaya akan wannan mutumin ba hakannan ya tai make suba,
Zuwa yanzu tunanin Meer duk ya raja'a akan tunanin tsohon ya ajiye batun aure agefe, dan ya saduda da sakin da zai mata amma dai kuma bazai taɓa zaman da itaba amatsayin matar sa ba har abada zuciyar sa bazata taɓa aminta da hakan ba,
Gajiya ta fara yi da zaman gurin jin shirun nasa yayi yawa, yasa ta fara tunanin ko ta tashi ta tafi,
Kamar yasan tunanin da take kuwa sai yace " tashi kiban waje kuma kar ki ƙara zuwa inda nake ko a hanyar fakon nan banaso muhaɗu kinjini koh,
A hankali ta ɗaga kai tare da miƙewa, har zata bar wajen sai kuma ta dakata, tare da juyowa tana kallon sa murya can ƙasa dan har ta fara zubar da hawaye, sannan tace "dan Allah ka sake ni wallahi idan ban auri yaya bossay ba bazan iya auren kowa ba, bana son auren nan, ba'a tambaye ni ba hakan nan akayi min aure ko makaranta bangama ba, dan Allah ka taimake ni kasake ni inzauna da wanda nake s......, Shiru tayi takasa ƙaraswa saboda wani irin mugun kallo da taga yana yi mata gudun kar ya kawo mata duka yasata dakatawa,
Shi kam ba komai yasashi kallon taba sai mamakin, ba ƙaramin mamaki yayi ba dan bai taɓa tunanin irin wannan maganar ba ama tsayin ta na yarinya ƴar ƙarama har tasan meye saki kuma shi take gayawa haka harda cewa bazata iya rayuwa ba tare da wani ba a yanda take ɗinnan har tasan irin waɗannan maganganun,
dalilin da yasa yake yi mata irin kallon miƙewa yayi tsaye shima cike da mamakin ta da har yanzu bai gama sakin sa ba ya dawo gaban ta yana kallon ta tun daga up har down, sannan yace"kina cewa bakya sona nima kusani basonki nake ba kuma bani nace a aura min ke ba hasalima na tsane ki in baki sani ba ki sani daga yau banason ki kuma bazan taɓa sonki ba har abada kuma aure na da ke ki ƙaddara kamar ba ayi saba, kije ki kula duk