Showing 63001 words to 66000 words out of 170049 words

Chapter 22 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7230

cikin ƙauyen nijar dan adaji ma suke kwana shida ɗan uwansa saboda ankashe musu iyayen su acikin dajin, bayan mutuwar su suka baro cikin dajin inda suka fara kasuwan ci tare suka tara kuɗi daga baya ɗayan ya mutu yarage sai shi kaɗai wani mutumi ya ɗauke shi gadi agidan sa, loƙacin baifi shekara goma sha takwas ba, mai gidan ya aura masa ƴarsa yabasa amana loƙacin da ƴan daba suka kawo musu hari suka kashe kowa saura shi da ƴar shima yana hanyar mutuwa ya bashi auren ta yace yaje a ɗaura musu aure,

daga nan yaƙara barin garin tare da yarinyar itama yarinya ce kamar yanda mahaifin ta yace mishi haka akayi yaje akayi musu aure,

Awajen haihuwata wahala ta kasheta itama, inda mahaifina yaci gaba da ɗawainiya dani, har nafara wayo, loƙacin da na cika shekara ɗaya loƙacin mahaifina yayi ashirin da biyu,

daga ƙasar Nijar ya ɗauko ni muka dawo nan garin inda yasamu aiki agidan sarki Gombe amma da akaga yana da ƴa sai aka ƙiyarda dashi aka kore shi acewar su sato yarinyar yayi, ni kuma suka ƙwace ni daman matar sarkin amaryar sa bata taɓa haihuwa ba, sai tasa aka ƙwato mata ni, tace zata riƙe ni, 

tundaga nan mahaifina ya canza inda ya fara aikata abubuwa marar sa kyau anan ya haɗu da gwaggo ya nuna yana sonta ita kuma sai tace bata sonsa haka yai ta fama da ita akan ta amince amma taƙi yarda dashi har kwana yake a ƙofar gidan su amma duk da haka bata taɓa tausaya masa ba,

Duk wulaƙancin da take masa baitaɓa haƙura da itaba yaci gaba da bibiyar ta ba irin wahalar da bai shaba, sai daga baya tace ta amin ce masa, suka fara soyayya ko sati basuyi ba ashe yaudarar sa take, sai kawai yaga katin ɗaurin auren ta, da yayi mata magana tace masa bata gaya masa bata sonsa ba yaƙi ji to yanzu tunda yagani da idon sa sai ya daina bibiyar ta, tayi masa cin mutunci ta kore sa, koren wulaƙanci,

Tunda ga loƙacin yaji yafara tsanar ta kuma ya ɗauki alƙawarin sai ya tarwatsa ta bazai taɓa bari tasamu farin ciki ba a gidan auren ta,

Bayan tayi auren ya dinga bincike akanta har ya gano a she ɗan sarki ta aura inda ya koma sarki bayan auren,

duk yanda yaso ya shiga gidan bai samuba saboda tsaron da gidan yake dashi dan a loƙacin kai inba wani bane baka isa ka shigaba,

sai kawai ya yanke shawarar da ni zaiyi aiki ni zai saka inshiga gidan inyi masa aiki, dan haka sai ya koma Gombe inda yabarni, kafin kuma ya shiga Masarautar saida yafara bibbiyar bokaye da malamai akan yana so yasamu sarautar gidan sarki, ta hanyar auren yarinyar gidan,

Ba samu matsala ba yagama haɗa komai ya shiga gidan a matsayin ɗan aiki daga nan kuma ya fara soyayyar ƙarya da yarinyar gidan har akazo akayi musu aure, sarkin garin loƙacin murabus ɗinsa baiyi ba mahaifina yaje gurin boka akasa ya sauka daga kan mulkin daman baida ɗa namiji dai mace sai yace yabawa yarsa sarautar ita kuma tabawa mijin ta,

burin mahaifina ya cika yazama sarki nima kuma loƙacin na girma kuma nasanshi saboda tunda na ɗan girma yasa aka sato mishi ni yagaya min duk wani abu dake faruwa yabani hujjoji, daman kuma tun kan yagaya min acan masarautar angaya min na ba ƴar gidan bace shiyasa da yagaya min na yarda,  kuma duk sanda yake son gani na ina zuwa mu haɗu dashi kuma duk halin da yake ciki yana gaya min, har zaman sa Sarkin gidan da nake Saida Yahaya min kuma na goyi bayan sa tare da basa wata gudunmawar ma tundaga nan komai muke yi tare har ya shigo gidan da yazama sarki kuma na koma hannun sa,

Bayan yazama sarki kowa ya shaida har yakan kawowa Sarkin nan ziyara amma basu taɓa haɗuwa da gwaggo ba  daga baya ma yadaina zuwa, tun a loƙacin yaso in shigo gidan inda ya kawowa sarki Sameer tayin aure na asirran ce batare da kowa yaji ba, amma sai yace ya za ayi yana tsofe tsofe dashi ga yara yafara tarawa taya zai auri ƴar ƙaramar yarinya ƴar cikin sa, saidai yabari idan ɗansa ya girma sai ahaɗasu auren,

Duk da haka mahaifina baiji daɗin ƙin karɓar tayin da yayi masa ba, nan ma sai yaƙara kullatar su yaji haushin su,

Bayan sunyi maganar tsawon loƙaci shiru shiru baiyi masa maganar ba, da yaga haka sai ya ƙara ɗaukata mukaje tare dashi ya ƙara tuna masa maganar auren amma sai yace masa ɗan sa makaranta yake sai ya gama saanna zai masa aure zuwa loƙacin kuma yayi murabus zai bashi sarauta sai a haɗa tare da auren sa, haka muka dawo,

Kwatsam mahaifina saiji yayi anyiwa ɗansa aure mata biyu ma kuma amma baiyi masa maganar ba,

Munzo taya murnar naɗin sarautar sai a nan nagansa tunda nagansa kuma naji ina sonsa, haka muka koma gida babu daɗi, bayan ƴan kwanaki naƙara yiwa mahaifina maganar aurenmu, sai yace ai yaƙara komawa shikaɗai sunyi magana yace masa bazai taɓa haɗa zuri'a dashi ba saboda yayi bincike akansa yagane baida asali dan haka indai da ransa aduniya bazai taɓa bari ya aurawa ɗansa niba indai yaga anyi auren nan saidai bayan ransa,

Mahaifina nagama bani labarin nima raina ya ɓaci na ɗauki alƙawarin ko ta halin ƙaƙa sai na aure shi kuma bazan taɓa bari su samu ƙaruwa ba da matayen sa,

Nida mahaifina muka fara shirya yanda za ayi, mahaifina yace indai yana raye sai ya tarwatsa masarautar nan gaba ɗayan ta, bazasu ƙara samun ci gaba ba, daga nan mahaifina yaje har masarautar azin yakawo ziyara kamar yanda yake, da ya shiga kuma sai yasaka masa abu a abun shansha bai tafi ba saidai ya tabbatar da yasha sannan yabar gidan, da yabar gidan kuma yasa aka rufe bakin kowa tayanda koda antashi bincike babu wanda zai zargi kashe shi akai ko guba asha ko kuma ace ai shine last ɗin zuwa wajen sa a bincike sa duk ba ɗaya da za ayi,

Bayan mutuwarsa ne nikuma nafara nawa aikin akan su naje gurin boka nasa aka juyar da mahaifar Maryama itakuma Sabreena aikin ta yaƙiyiyuwa amma dai yace zaiyi min abun da ko tana dashi babu wanda zai gani har ita kanta ni kuma sai insan yanda zan ringa bata magani tana sha yana zubewa batare da sanin kowa ba abun dake faruwa ba, ta wannan hanyar ne kaɗai za akarkato da hankalin gwaggo ta yarda ayi auren, idan taga sunƙi haihuwa,

Bayan an auro ni kuma ba daɗewa mahaifina ya rasu ta hanyar kamuwa da ciwon ƙoda anje yi masa dashe kuma aka samu matsala daga nan harasa ran sa,

Tundaga loƙacin na ajiye batun so agefe na ɗauki alƙawarin cikawa nahaifina ƙudurin sa na tarwatsa masarautar daɗin daɗawar ma kuma ta rashin haihuwar namiji da banyi bane yasa naƙara ɗaukar zafi na kori Sabreenan ita da yaranta sannan na kawo wanda ba jinin saba na ɗorasa a mulki ta hanyar yin amfani da fulani, kuɗin kuma da nacewa bokan yagaya mata yaringa kaiwa wani ɗaki daga baya nake sawa aje a kwaso min su so nake inƙara naksa masarautar ta hanyar kaɓe kuɗaden da take ajiye wa,

Nan dai ta ɗora musu zuwa inda Kande tabasu labari, sannan ta ɗora da cewa, tunda muke aduniya daga ni har mahaifina babu wanda yasan wannan labarin,

Amma ko su da nake tare dasu babu wanda yasan wacece ni, babu wanda zan cikawa burin su daga cikin su, dan bazan taɓa bari jinin Waziri yazama sarki ba shima, wannan kuma itama ba ƙanwa ta bace ba uwar mu ɗaya ba ba ubanmu ɗaya ba, ƴar wani bawace itama tana yarinya nasa mahaifina ya riƙe ta har ta girma dan haka itama bazan bari ƴarta tazama matar sarki ba, shima kuma Abdallah jinin Waziri ne dan haka idan nabar Sam yayi sarauta abundai ya koma hannun su kuma za a iya yin adalci wanda hakan kuma baya cikin tsari na, Ghali kuma kawai ina amfani dashine dan naga yana da kwaɗayi haka daman zan ta gara sa bazai taɓa samun cigaba ba, shima,

Ɗan tsagaitawa tayi sannan ta maida dubanta ga Kande sannan tace "ke kuma nasan daman bada zuciya ɗaya kike min aiki ba kinayi ne dan nabaki ƴaƴan ki ni kuma fuska biyun da kike nuna min itace ta hana inbaki su tsawon shekarun nan amma ban kashe suba saboda suna ƴaƴa nane bazan iya cutar dasu tunda ƴaƴan ƙanina ne, shima laifi yamin nasa aka kasheshi sannan nace kece daga nan aka kore ki, saboda bana sonki, amma saboda baki da tunani kika yarda ki ka kuma biyo ni akaro na biyu, duk abun da kike ai boka nagaya min, koda ka ƙi kashe ɗan da nasaki duk nasani kawaidai inda yake ne narasa inda ya shiga shiyasa ya zauna da ransa,

ni kuma na rama abun da kikayi min ta hanyar rabar da yaranki da niyar ke dasu har abada, sai gashi kinci sa'a yanzu zan gaya miki hanyoyin da zaki bi ki samosu suna nan araye kuma akusa dake amma ke kanki baki san da hakan ba, babban ɗanki shine wanda muka tura ya buge Sabreena kuma tun loƙacin nagaya masa ko shi waye amma na gargaɗe sa koda wasa ya nuna hakan sai na kasheki sannan nakashe masa matar sa da ƴaƴan sa da haka ya haƙura bai taɓa nuna komai ba kuma yasan ki yasan inda kike yanama ganinki kece dai bantaɓa yarda kingansa ba saboda yana nan yanda yake bai canza ba ƙaramin kuma da nasan baza ki gane saba, ɗaya kuma yana cikin gidan nan na kula miki dashi yanda yakamata komai yana yinsa cikin ƙoshin lafiya da isa da taƙama ba ƙarya jinin sarautar mahaifin sa yana aiki ajikin sa dan koman sa kamar sarki yake, yana ɗan aiki amma baisan da hakan ba shiyasa yaron yake burge ni bana bari komai ya taɓa sa acikin gidan nan, saboda inayi masa kallon ƙanina da muke uba ɗaya dashi a duniyar susu biyu suka rage min ƴan uwana sai kuma ƴaƴa na,

Dan haka nabaki gari kije ki nemosu bazaki sha wahala ba, sannan kafin inbar gurin nan, zan miki wani adalci da taimako shine karon farko da zanyi arayuwata, idan kinje masarautar mu ki nemi Alalu shaidun komai agurin ta, za asauke sarkin da yake kai kibawa ɗaya daga cikin ƴaƴan ki domin su kaɗai suka rage jinin sarautar gidan, idan kwa ba hakaba bazata taɓa gyaruwa ba har sai ɗaya daga cikin su ya hau da haka asirin zai karye komai ya dawo daidai,

Sannan abu nagaba da zan faɗa nagama gaya muku komai kuma gaskiya amma bansan inda ɗanku yake ba karma kuyi tunanin nice ko ku tuhume ni, kuje ku lalubo sa, abun dai da nasani shine yana raye har yanzu bai mutu ba kuma zai dawo gare ku, sai ku ƙarfafa bincike kuma tana nandai bata canza zani idan kun rabu bukar to zaku haifi habu nan gaba yana nan zuwa har gara wata wainar da bata wake ba, wata kusan tafi wata kusan, duniya ba tabbas........,

lasat ga saƙo zan baku kubawa Sam nasan bazan ƙara haɗuwa dashi ba, kuma amsar zatayi masa amfani nan gaba, kwanaki ya taɓa yi min wata tambaya yace, idan akace na kusan kusan ka wanda kuke shirin haɗa alaƙar jini dashi, ba fatana ku gane tambayar ba shi ya riga da yasanta, amsar kawai zaku basa,

Kuce masa amsar sa shine siriki duk wanda yagaya maka haka to yana nufin, sirikin amma ba ayi auren ba shine kuna shirin haɗa alaƙar jini, ma'ana shine baban wacce zaka aura, nakusan ta ita kuma matar zata zama ta kusan ka idan kunyi aure kuma kun hayyayafa daga nan kun zama jinin ɗaya,

Kar wanda yayi dogon tunanin wajen gano ko mai nake nufi wanda na faɗa danshi zairiƙe kuma zai gano ma'anar hakan..........,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*


________Tana gama faɗar haka ta miƙe tsaye, a harzuƙe Meer yayi kanta tayi saurin ɗaga masa hannu tace bance karka ƙara saka min baki ba, kabari idan nagama komai da kaina zanzo wajen ka, kayi yanda zakayi dani, mtswww taja tsaki ta wuce ta gaban sa,

Gurin Papa ta nufa tunkan ta ƙarasa Papa yayi saurin miƙewa tsaye tare da ɗaga mata hannu, yace "dakata kada ki sake ki raɓo inda nake bana son ganin ki, mai baƙar zuciya Allah ya isa tsakanin na dake dan kingama cutata mugaye kawai kuma wallahi bazan taɓa ƙyaleki ba,

"Da ina za a ƙyale ta dan uwar ta ashe daman mijina ba mutuwa yayi ba kune sanadi to wallahi sai na koya miki hankali yanzu nan sai kinsa wacce kikayiwa irin waɗannan abubuwan Allah ya tsine muku ke da ubanku tsinannu kawai, gwaggo ce ke wannan maganar yayin da ya tashi daga inda take ta koma kusa da ita ta tari gaban ta tana masifa tana duddun gure mata kai dataga dungurin bazai yi mata ba sai kawai tasaka hannuwa biyu ta shaƙeta tana jijjigata tana kuka idan saboda abun yayi mata ciwo inta tuna wai duk dan saboda da ita ake musu wannan abun gashi kuma sanadin ta mijin ta ya rasa ransa gashi gaba ɗaya sun ruguza Masarautar kamar yanda sukayi alkawari, ƙarin wani taƙaicin natama da akace ya mutu ba damar ɗaukan fansa akan sa,

ƙwace jikin ta tayi daga riƙon da tayi mata sannan ta maida nata hannun kan wuyan gwaggo tace "Ni kafin kolashe ni bari in kashe ki sai afi jin daɗin yi min hukun ci, 

Da sauri Abu yayi kanta yana ƙoƙarin cire hannun ta daga kan wuyan gwaggo amma taƙi saki, ganin hakan yasa Meer ƙarasowa gurin cikin ɓacin rai,

Yana zuwa itama yakaiwa wuyanta damƙa mai kyau, take tafara kakarin mutuwa, Saida ta fara jin ƙanshin mutuwa sai ta sannan ta saki gwaggo tana ƙoƙarin ƙwatar kanta, ran Meer ya ɓaci dan haka yaƙi sakin ta saida yaga numfashin gafara sama da ƙasa jikin ta yafara sanyi alamun numfashin ta yana daf da ɗaukewa gaba ɗaya sannan yasake ta tare da tura ta baya tafaɗi a ƙasa tunda ta faɗi kwa bata iya motsawa ba, sai farfar da ido take can kuma tari ya turnuƙe ta tafara yinsa babu wanda yayi ƙoƙarin tai maka mata bare yabata ruwa daga kwancen tana cikin tarin kuma sai taji amai ya taho mata tana ɗagowa zatayi sai taga  jini ya fito harda guda guda,

Meer ne yaje gabanta tare da tsugunnawa agabanta, yasaka hannu ya ɗagota kamar abun arziƙi yakamata yayi hanyar waje da ita yana zuwa bakin ƙofa yace "Khalid follow me,

Da sauri Khalid ya tashi yabi bayan sa babu wanda ya dakatar dashi,

Momma kam fashewa tayi da wani irin kuka mai tsuma zuciya, kowa na gurin su kaɗai yake tausayawa Papa da kansa ya tashi yaje gurin su ya fara rarrashin su, shima duk da daurayewa kawai yake, duk wanda ke cikin gurin nan Saida ya tausaya musu wasu harda taya su kuka, kowa yana Allah wadai da halin ta, wasu suna mamaki, irin su Waziri dan suma abun ya matuƙar bugar su jin ashe suma duk shiri take akan su ta mayar dasu wawaye,

Su Meera na fitowa waje, Meer ya cillata gaba ta faɗi a ƙasa kafin ta ɗago yayi kanta yaɗata kai mata duka fuskar ta ya kama ya ringa nausa har saida yaga haƙoran ta na fitowa ya zubar mata dasu jini kuwa ba'a magana duk yagama ɓata masa hannu amma da haka yake dukan ta  sai ya ɗan rabu da ita sai yaga kamar dai bata daku ba sai yaci gaba da dukan ta, saida ya karya mata hannu ɗaya yatsun ta kuwa saida duk suka saki basa motsi sannan duk yasagar nata da duk wata gaɓa,

Ƴan ciki duk basu san abun dake faruwa ba wajen kuma mutane duk wasu sun fara zuwa kallo annan wasu daga cikin jiko kin gidan suka fara sanin abun da yake faruwa, daman wasu sun sani tun ajiya amma dai ba komai suka sani ba,

Ajita jita su Amra da suke tare da Ameesha suka ji suna suka fito su bama su san wacce ake duka ba saida suka zo wajen, ganin wacce ake duka yasa su Amra fashe wa da kuka, suna zuwa har gaban sa inda yake dukan ta,

Meer bama ya cikin hayyacin sa dan kawai dukan ta yaje kamar mahaukaci gashi ko motsi batayi azaba tasa ta suma,

Khalid ne yafara hange hangen inda zai samu ruwa bai gani ba sai ya matsa kusa da wani da yake da tabbacin ma'aikacin gidan ne, sai yace "dan Allah ruwan danyi nake buƙata ina zan samu, da sauri yace bari akawo maka, ba daɗewa yakawo masa ruwan sanyin dake shima mugunne ba tausayi a tattare dashi sai ya samo ruwan a botiki mai yawa wanda suke sha,

Yana kawowa kuwa ya karɓa yayi masa godiya yaje gurin Meer tare da cewa wait idan ta farfaɗo sai kaci gaba....,

Yana faɗar haka ya ɗaga ruwan ya juye mata shi take kwa takawo numfashi saida ba ƙwarin da zata iya yin motsi, azabar da taji ji tayi dama mutuwa tayi ta huta da wannan abun da yake mata,

Zuwa yanzu babu abun da take gani saboda tafara fita hayya cin ta, ga bakin ta da ya juye gefe guda ga jini da ya ɓata mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login