Showing 81001 words to 84000 words out of 170049 words
yayi,
Kallon kallo suka shiga yi a tsakanin su, Meer ne ya haɗiyi wani zafaffan yawu yaji ya haɗiye tare da jin wata faɗuwar gaba da saida tasa ya dafa jikin bango, yana shirin magana kenan Khalid ya rigasa da cewa, "Wai kaji kuwa abun da naji amma baka gaya min ba,
Tsaki Meer ya doka tare da cewa "naji mana ko ni kaɗai ne Sameer zaka wani tsare ni da ido ko ji kurma ne, idan nine mai zai hana kaji ko kaga nayi maka kama da wanda za'a ɗaurawa aure yanzu,
Cike da mamaki Khalid yace amma fa abun da mamaki gaskiya da alamar tambaya ya za'ayi ace komai naku iri ɗaya taya hakan zata faru Sameer Sameer Sameer nidai kai ka ɗai nasani amma kuma itama yarinyar sunan mahaifinta da kakanta Sameer Sameer to wacece ita,
Wannan baya nin na Khalid shine yaƙara sa Sameer karkata wani tunanin tabbas da mamaki ace suna iri ɗaya kuma akusa da nan gashi kuma yarinyar ma, to amma abun tambayar shima da ta ɗaure masa kai wacece Khadija iya tunanin sa ya gano wace Khadijah yakasa ganowa, saurin kawar da tunanin yayi yasawa ransa bama shi bane saboda yasan ba tayanda za' ayi hakan ta faru batare da sanin saba,
Juyawa yayi ya kalli Khalid da mamaki yagama kashewa gashi mutane har anfara fitowa wasu hannayen su ɗauke da goro da alawar daurin aure, wasu kuma na murmushi gashi yawancin mutane idan suka fito da fara'ar su idon wasu kuma akansu saidai babu wanda ya ƙaraso wajen su sai suga sunyi gaba mutane da yawa sun fito daga ciki ƴan waje kam daman wasu duk sun kama gaban su,
Meer ne yace"kaga idan kallon zaka tsaya ni inyi tafiya ta kasan dai bata yanda hakan zata faru za amin aure ne batare da sanina ba ko kuma akwai wanda ya isa yayi min auren dole ne,
Shiru Khalid yayi bai tanka masa ba har saida yaga Meer yayi gaba sannan yayi saurin binsa abaya zuciyar sa fal cike da mamaki saboda abun ba ƙaramin mamaki ya basa ba amma yaga shi Meer ko ajikin sa,
daman suna kusa da bakin gate ɗin saboda a ƙafa suka zo daman, dan haka saikawai suka shiga ciki, suna ƙarasawa gurin gate na biyu suka fara jiyo kiɗan ganga,
Shide Meer bai kawo komai ba, suka ƙara shiga, suna shiga suka fara bin mutanen gurin da kallo, ga mamakin su kuma sai kawai suka ga masu kiɗan nayowa wajen su tare da wasu mutanen, matsawa Meer yayi yabi ta gefe dan atunanin sa ko fita zasuyi amma yana yin gaba sai suka ƙara binsa abaya, cak ya tsaya yakasa ci gaba da tafiya jin abun da masu kiɗan suke cewa,
"Takawar ka lafiya mijin sarauniya Khadijah takawar ka lafiya ɗan sarki jikan sarkin gobe sarkin mu na gobe Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon kwana Allah yasa kafi haka, Allah ya kawar da fitina acikin auren ku Allah ya kawar da sarrin mutane maƙiya da mahassada Allah ya tsare ku.....,
Wani maroƙi ya ɗora da "kaga na kadi angon kadi Allah yabar ƙauna mai ɗoreawa Allah ya kawo zuri'a tagari Allah ya kawo ƙazantar ɗaki da wuri, a haifo mana magaji...., Nan gurin ya ƙara kaurewa da ihu masu jiɗa suka ɗora daga inda suka tsaya anayi ana masa waƙar kirari,
Khalid da Meer yabari abaya ya ƙaraso gurin ta cikin mutane ya ratsa ya ƙarasa gaban Meer sai kawai ya tsinci kansa cikin farin ciki dan yagama karantar komai daga gani anyi hakane batare da sanin saba, hakan kwa ba ƙaramin daɗi yayi masa,
Ganin yanda Meer ya haɗe rai idon sa sun fara canza kala ya gama cika fal ƙiris yake jira ya fashe,
Khalid da yasan halin kayan sa sai yayi haƙuri ya tattara farin cikin sa ya ɓoye sa aràn sa yaje gurin sa, tun kan yayi magana ma, cikin wata iriyar murya da shi kansa Khalid bai taɓa jinta ba daga gare sa duk da yasha yin ɓacin rai agaban sa amma bai taɓa ganin irin na yau ba,
Cikin daka musu tsawa da ɗaga murya Meer yace "YA ISAH!! "ENOUGH!!! I told you that everyone should visit this place before I kill you all..!!! yafaɗa yana tattoshe kunnu wansa yayin da idanun sa suke a rufe,
Kowa Saida ya tsorata ɗif kake ji babu wanda ya ƙara koda motsi,
Shiru wajen yayi na ƴan loƙuta sai kawai Meer ya ƙara jin wani kiɗan, a fusace ya buɗe ida nun sa da suka koma kamar garwashin wuta ya sauke su akan su da tunanin sa basuji garga ɗin da yayi musu ba shine suka ci gaba,
Amma sai da ya buɗe idon sa sai yaji kiɗan badaga su bane ta bayan sane, da sauri ya juya dan ganin wane isasshen da mai ne yake kuma yin kiɗan bayan yace baya so,
Wasu dandazon mutanen ne suke tunkaro inda suke waɗan nan kuma harda mata suna ta guɗa dan mutanen yanzu ma sunfi na nan gurin yawa,
Baigama ɗimaucewa ba saida yaga Maama ce akan gaba fuskar ta ɗauke da wanni sanyayyen murmushi, tunda ta taho kuma idon ta akansa,
Kamar meson gano wani abun ajikin ta ko kuma wanda bai taɓa ganin taba haka shima ya kafe ta da idanu ko kaɗan baya ƙiftawa, har ta ƙaraso inda yake,
Wani murmushin ta ƙara saki ba yanzu har haƙoran ta ake ganowa loƙacin da tazo daf dashi tare da kamo hannun wansa tace ango kasha kasha ƙamshi ko baka sa turare ba ƙamshi kakeyi,
wani irin kallon tuhuma ya ringa binta dashi, jin abun da take cewa,
Maama sarai tasan halin da yake ciki kuma tagane kallon tuhumar da yake mata,
Meer na so yayi maganar amma ta maƙale saboda tsabar ruɗanin da yake ciki zuciyar sa neman daina aiki take,
Maama data gama karantar sa gudun kar ya tona musu asiri agaban mutane ya basu kunya yasa ta ƙara faɗaɗa fa'ar ta ta kamo hannun sa batare da ta bari sun ƙara haɗa ido ba, sai kawai taja hannun sa, ta hanasa damar magana,
Suna juyawa ta juyo ta kalli mutane ta sakar musu murmushi tare da kaɗa kai tace sauti mana....,
Nan take makiɗan suka fara kiɗan suka ɗora daga inda suka tsaya sunma manta da wani kashedun da yayi musu suka bi bayan su masu kiɗa nayi masu rawa nayi,
Maimakon Meer yaga sun tafi part ɗin Maama sai yaga sun nufi part ɗin Ummy, kamar wani ƙara min yaro haka yake bin momma abaya har suka ƙarasa cikin falon, suna shiga Meer yaga su ummy acikin falon,
Suna shiga Meer ya fusge hannun sa daga hannun Maama, tsayawa Maama tayi tana kallon sa,
Cikin ɓacin rai yana kallon Maama ido cikin ido yace "Maama wai me yake faru mai kuke nufi dani kuyi min bayani waye ya shirya hakan, me yasa zakuyi min ni zakuyiwa auren dole aure kamar ni, ni zakuyi wa batare da sanina ba mai nayi muku da na fuskanci wannan hukuncin Maama Ummy! Ku gaya min mai yasa!?
yayi maganar kamar zaiyi kuka, saboda ransa yakai ƙololuwar ɓaci,
Suma kansu saida suka sha jinin jikin su dan sun san ba'a kyauta masa ba yakamata a gaya masa koda bayaso ayi da haka,
"Kunyi shiru gaba ɗayan ku ina muku magana ku ban amsa Maama wace kucakar kuka aura min daman harda kwai wacce ta kai matsayin da zaku iya aura min ita acikin garin nan,
To wallahi kuyi gaggawar kunce wannan auren da kuka ɗaura, idan na baku warware ba ni da kaina zan warware sa yanzun nan sai ku gayawa mutane kamar yanda kuka sanar da auren sai ku sanar da sakin koma wace jakar ce,
A zabure Maama ta ɗago tana kallon sa cikin tashin hankali tace "dan Allah kar kayi haka na roƙe ka kar kabari mutun cin mu yazube a cikin mutane mun san bamu kyauta maka ba amma nasan hakanne kawai mafita bamu da wata hanayar da ta wuce wannan ina mai baka haƙuri akan yin hakan batare da sanin ka ba amma dan Allah karka sake furta kalmar zaka sake ta dan Allah, ta ƙarasa maganar cike da raunin murya, dan muryar har karkarwa take tasan ayanda ya ɗauki abun da zafi zai iya yin komai ma, ga bata da iko dashi bare ta dakatar da shi ta hanyar tsoratar wa,
Juyawa tayi tana kallon Ummy da itama ranta baiyi mata daɗi saboda ko ita ba agayawa ba saida aka ɗaura, ita ba haɗin auren ne yabata haushi ba, kawai rashin sanar da itan da ba ayi ba tun farko, amma zuwa yanzu dake tana da saurin fahimta ta sauko, saidai bata da bakin da zatayi masa magana tasan daman hakan zai faru fiye da hakan na zai iya aikatawa shiyasa tayi shiru,
Maama ce tace "Ummu Kulsum (ummy) kiyi masa magana kar ya furta abun da yake shirin yi,
Tasowa Ummy tayi tazo kusa da Meer zata riƙo hannun sa da niyar rarrashin sa sai kawai ya kawar da hannun nasa yana ja baya, yace "kada wanda yaƙara cewa komai kuma babu wanda ya isa ya hanani sakin ta tunda de ba da ita zaku zaun, ni kuma a tsarina babu aure ban shirya aure yanzu ba dan haka babu wanda ya isa yayi min auren dole, auren ma irin wannan wanda ko a tarihi ban taɓa jin sa ba ina aka taɓa aure irin wannan, wannan wacce irin tsana ce zakuyi min haka, sai kace marar gata,
Ummy ce ta ƙara daurewa tace "Meer ba haka bane ka tsaya ka saurara kaji bazamu taɓa yi maka abun da zai cutar dakai ba, wacce aka aura maka baza ka taɓa yin da nasanin auren taba kadena kiran ta da wani sunan marar kyau, domin ita ɗin ƙan...., Da sauri Meer ya dakatar da ita da cewa "Ummy bana so bana so bana sonta kuma bazan taɓa son taba ban damu da sanin ko wace ita ba na tsane ta, kuma ku sanar da ita,
Ni Sameer na saki matar da kuka aura min saki......,
Tabb babbar magana Ameesha will be a widow oooo,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
*_🅿️30_*
'Ni Sameer na saki matar da kuka aura min saki......,
MEER..!!!!! Abuu ya daka masa tsawa hakan yasashi dakatawa daga shirin ƙarasa furu cin sa,
"Wallahi kana sakin ta ina tsine maka albarka kuma kai da zama anan har abada saidai ka tafi kaje ka nemi wani gurin ka canza iyaye amma bamu ba, daga yau babu kai babu mu mutiƙar kasaki yarinyar nan wallahi, marar mutunci kawai, Abuu ya ƙarasa maganar yana zazzaro masa ido yana nuna sa da yatsa,
Shima Meer ɗin ido cikin ido yake kallon Abbu ɗin, ko kalma ɗaya ta kasa fita daga bakin sa, saida ya jira abu yayi shiru sannan yace "tsinuwa tsinuwa fa kace to sai me idan kayi min nace sai me idan nabi duniyar ko daku ko baku zan iya cigaba da rayuwa ta, ni da wannan auren gwara tsinuwar ma dan banga bambanci ba,
Abuu ne ya ƙaraso kusa dashi baiyi aune ba kawai ya kwashe shi da mari cikin ɓacin rai yace "daman abun naka har ta kai haka to indai ka cika ɗan halak ka saketa kaga ni, nima zan nuna maka nawa ɓacin ran sai ka gwammce baka zo duniya ba wallahi, kaji ka sake ta nace!! Yana ɗaga masa murya tare da ƙara sauke masa wani marin, yana shirin kai masa wani Maama tayi saurin dakatar dashi,
Maama tace "dan Allah ya isa kabari abi komai a hankali kowa ya kwantar da hankalin sa ɗaga murya ko faɗa ce faɗace ba namu bane tunda de kunsan gidan cike yake da mutane, ku rufa mana asiri agama komai ma zauna daga baya,
Babana dan Allah badan halin muba kabar wannan maganar da kake ka taimaka, kaji babana,, haɗa hannu wanta tayi waje guda tana roƙon sa,
Hakan da tayi ne yasa Meer ya daina ikirarin sakin da zai yi,
Juyawa yayi ya fice daga ciki fuuu bai ƙara cewa komai ba kuma har zuwa loƙacin da ya fita baisan matar da aka ɗaura masa aure da ita ba, dan baya son sanin tama bazai taɓa bari yagan taba, yafasa sakin tane kawai saboda darajar roƙon da Maama tayi masa amma badan haka ba sai ya saketa yau, ya ɗaga mata ƙafa zuwa loƙacin da ya ɗibarwa kansa,
Yana fita gaba ɗayan su suka sauke ajiyar zuciya tare da hamdalah Allah yasa bai sake taba da ya zasuyi ayi aure yau kuma ace anyi saki a ranar, ina aka taɓa haka,
Bayan fitar sa, Papa ya shigo shima nan ya sanar dasu su shirya yanzu za afara naɗi angama shirya komai,
Nan suka bashi labarin abun da ya faru sannan suka ƙara runguma suka fita daga ciki,
Cikin masarauta damƙam da mutane kowa kagani yana cikin farin ciki kamar gonar auduga, wani ɓangaren suna kiɗa kiɗe wani ɓangaren ana raye raye ga dokuna ana ta shirya su ana musu kwaliya, kar mu ɓata loƙaci, komai ya tafi yanda aka tsara cikin kwanciyar hankali, kowa ya shaida naɗin sarki Sameer Muhammad Sameer, an ɗorasa akan kujerar mulki, bayan an canza komai na cikin fadar amma banda kujerar andai gyarata anyi mata kwaliya an gyara ko ina ya sha gyara,
Meer tunda ya bar cikin falon ko can sashen baije ba ya nufi hanyar parking space ya buɗe motar sa ya shiga, yana shiga Khalid ya taho gurin da gudu yana yi masa magana amma kafin ya ƙaraso Meer yaja motar da gudun tsiya ko horn bayayi kuma ga mutane amma da haka yake gudu saidai kafin ya ƙaraso wajen mutane suyi saurin matsawa, a haka ya fice daga cikin gidan,
A ɓangaren Ameesha kam har zuwa wannan loƙaci labari bai iske su ba domin tunda suka shiga ɗaki yin Sallah basu fito ba hira kawai suke kamar babu gobe abincin ma can aka kai musu suka ci, ko da aka fara gudanar da naɗin duk basu fito ba, daman kuma Maama bataso a sanar da su shiyasa ta ƙara bada umarnin idan bata nan kar abar kowa ya shiga cikin gurin saboda kar wani ya shiga da maganar ɗaurin auren ciki,
Meer nayin wannan mahaukacin gudun dan ko gaban sa baya gani yana cikin yi bai ankara ba yayi sama da wata mata yayin da ta shigo gaban sa cikin gudu,
Da sauri ya taka burki yana dukan steering ɗin motar yana cije baki sannan yayi saurin buɗe motar ya fito tun kan yaƙarasa gurin shima yaƙaraso gurin da gudu yana haki, tsayawa sukayi atare tare da kallon junan su,
Da sauri Meer ya tsugunna yana shirin ɗago matar tsohon yace Sameer barta karka ta ɓata kaje kawai Allah ya kiyaye gaba,
Sak Meer yayi saboda jin tsohon da bai sani ba ya kira sunan sa.......,
Kawar da tunanin yayi saurin yi atunanin sa kodai kunnuwansa ne basu jiyo masa daidai ba, dan haka sai ya ƙara yunƙurawa yakai hannu zai ɗauke ɗago da ita, sai tsohon yaƙara cewa bana son taurin kai Sameer ka barta nace kayi tafiyar ka kawai bata ji ciwo ba suma ne kawai......,
Da kallon mamaki Meer yake kallon sa dan mutumin baiyi kama da mutanan da yakamata su san saba, ko ba agaya masa ba kayan jikin sa sun nuna masa yafi kama da mafarauci domin kayan fata ne ajikin sa irin na masu zaman daji, wandon jikin sa yaɗan ɗage masa ba har ƙasa ba sai takalmin danƙo baƙi rigar jikin sa kuma doguwa ce har zuwa gwaiwar sa shap ɗin ta kamar irin ta mata saboda na ɗaurin da akayi mata a tsakiya sai ƙasan ya buɗe bazar,
Sai gashin kansa da ba'a aske shi da yawa shima yayi wani iri dashi ga kuma wani uban kwalli da ya damɓara a idon sa,
Saida Meer ya gama ƙare masa kallo tundaga sama har ƙasa,
Shima kuma tsohon shi yake kallo yana ganin yanda yake binsa da kallon ƙurlla, tsoho da yagade Meer bashi da niyar daina kallon sa sai kawai ya ɗanyi gyaran murya tare da cewa idan ka gama kallon nawa zaka iya tafiya ko,
Ɗan sunkuyar da kansa Meer yayi tare da saurke ajiyar zuciya ya furzar da iskar bakin sa yana ɗan karkaɗa kai, yana kallon gefen sa gurin shiru har yanzu babu mota ko ɗaya da tazo ta wuce daman gurin ba a fiye wucewa ba saidai kaga mutane jefi jefi,
Tsugunnnawa tsohon yayi zai ɗauko matar dake kwance aƙasa har yanzu ko motsi batayi,
Da ƙyar ya ɗagota ya cicciɓe ta ya rataya ta a kafaɗa yana shirin barin wajen,
Meer yace "dakata,
Cak tsohon ya tsaya batare da ya juyo ba,
Sai shi Meer ɗinne ya taka yaje ta gaban sa yatsaya yana ƙara kallon sa na ƴan sakanni, kafin daga bisani yace "waye kai?
"Bawan Allah" 'tsohon yabasa amsa,
"A ina kasanni? Meer ya ƙara tambayar sa,
"Hmmm saninka ai ba abune mai wahala ba, tunda gidan ku ba ɓoyayye bane yaro taya zakayi min wannan tambayar,
Ɗan jinjina kai Meer yayi sannan yace "amma ai kai bakai kalla da masu zama cikin mutane ba taya zaka sanni, kuma mai yasa ka hanani in taimake ta bayan kuma ni na kaɗai ta,
"A'a yaro kabari kawai zanyi mata magani saboda kai ango ne bai kamata kasha wahala ba gurin ɗaukar ta, kuma tabbas ni bamai zama acikin mutane bane kamar yanda kaga yana yina amma