Showing 141001 words to 144000 words out of 170049 words

Chapter 48 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7390

ya hanasa yarda dan gani yake kamar gizo ne shi kaɗai yake kallon abun dake faruwa,

Tana kuna ta kuma kiran sa, Sai yanzu yasamu damar ɗaga hannun sa a hankali ya ɗora duka hannu wansa akan ta, ganin bata ɓace bane yasa yafara tunanin to kode ba gizo bane,

Yana rungume ta suka sauke ajiyar zuciya a tare har cikin zuciyar sa saida yaje wani sanyi,

Shima cikin sanyin muryar yace "Norry, MY DEEYA!

Ɗagota yayi daga jikin sa, ido cikin ido suka zubawa junan su idanu sunayiwa juna kallon ƙurilla dan kowa ji yake kamar a mafarki,

Tattaro maganar sa yayi yace "Norry kece da gaske ko gizon da kika saba yi min ne,  Dan Allah kar ki kuma tafiya kibar Ni kitsaya ko a hakane ko ni kaɗai ne idan ka kallon ki, Please my Deeya kar ki tafi please......, yana faɗar haka yakuma jawota jikin sa ya rungume ta, shima yana sakin kukan,

Cikin kukan tace "Norry nice ba gizo bane, nuna gani nake kamar gizo kake nin, Norry a kace min ka mutu, ni daman nasan bazaka taɓa tafiya ka barni ba, dan Allah ka tsaya muci gaba da rayuwar mu kar ka ƙara yin nesa, dani nima ina tare da kai babu inda zan ƙara zuwa inbar ka,

Jikin sa har yana karkarwa wajen ɗagoya ya ƙara ganin ta da kyau jin tana magana hakan yasa yafara tabbatar wa kansa da ba gizo bane gaskiya ne,

fuskar ta ya kamo a tafi kan hannun sa ya shiga goge mata hawaye yana girgiza kai yace "nima haka aka ce min, kullum da tunanin nake kwan nake wuni komai baya min daɗi aduniyar nan, babban burina bai wuce ace nasanya ki a idona ba, ina taƙaici da baƙin ci aduk ranar da na wayi gari na wuni nakai dare ban sanya ki cikin idona ba, hakan ba ƙaramin ɓatan rai take ba, nima zuciyata bata taɓa bani kin tafi ba, ni nasan zaki dawo gare ni mu cigaba da rayuwar mu tare da Babyn mu,

Ɗan baya taja da sauri cike da jin daɗin tace Babyn mu, tace "Babyn mu fa kace kana nufin itama tana raye bata mutu ba,

Murmushi ne ya kuɓuce masa ganin yanda tayi tana tambayar, jinjina mata kai yayi, sannan ya juya ya kalli inda Ameesha take, tana gefen su amma ko lura da ita basuyi ba hankalin su yana kan na juna,

Da hannu yayi mata nuni da inda take yace "ga Ameeshan ki,

mayar da kallon ta tayi ga kan Ameesha, tabbas kallo ɗaya tayi mata ta gane hakan dan ga kamanni Norry ɗin tanan a fuskar ta, wani irin daɗi da farin ciki wanda tafi na farko shi taji ya ziyarci zuciyar ta,

Buɗa mata hannu tayi alamun tazo gare ta,

Hakan da tayi sai ya tunawa Ameesha loƙacin da mahaifin ta yadawo shima haka yayi mata,

Takawa ta fara yi hankali dan itama jikin ta duk a mace yake ga fuskar ta da tagama wankewa da hawaye, tana zuwa ta faɗa jikin ta suka rungume juna suna,

Kallon inda Abban Ameesha yake tayi sai shima tayi masa alamun da ya taho yazo,

Zuwa yayi ya haɗasu gaba ɗayan su ya rungume su Ameesha na tsakiyar su, sun daɗe a haka kafin suka saki juna kowa yana farin ciki da kuma mamakin yanda hakan ta kasan ce,

(Tsaya wa cigaba da bayyana muku tsatstsan halin da bayin Allahn nan suka kasance aciki ɓata loƙaci ne, andai yi abun da ya samu)

Nan suka ƙara riƙe juna suna shirin cigaba da ƙara wasu maganganun,

Meer ne yayi gyaran murya dan ya fahimci kamar idon su ya makan ce basa ganin kowa a gun, kansu kaɗai suke gani a cikin falon,

"Hmmm nace ba kunmanta da sauran ne?

Baba ne yace "a'a rabu dasu mu ai inajin duk ba ason ganin mu sai mu koma inda muka fito,

Sai loƙacin Abban Ameesha yaga Baba, dan shi har ga Allah bai kula dashi ba sai yanzu, kunya ce ta kamasa, ƙasa yayi da kansa yaje gurin Baba ya tsugunna har ƙasa yace "Ayi haƙuri Baba, ban kula bane, ashe duk tare kuke,

Baba ina kuka shiga tsawon loƙacin nan, duk munyi tunanin kun mutu ashe kuna raye,

Kamosa Baba yayi ya miƙar yace muna raye Babu abun da yasame mu, fatan munsame ku lafiya, nima banyi tunanin kana raye ba,

Dadda ba gefe sai faman zubar da ƙwalla take, loƙacin da Abban Ameesha ya tafi gurin Baba, ita kuma Ameesha sai taja maman ta zuwa gurin Dadda dan itama sai yanzu taga Daddar, farin cikin tane ya ƙaru da ta ƙara ganin mahaifiyar tata, anan ma sai da suka sake yin kuka duk wanda yagansu cikin halin da suka kasan ce sai ya tausaya musu,  dan abunne banma san yanda zan kwatanta muku, abunne ya zowa kowa unexpected basu taɓa tunanin saba,

Nan aka samu kowa ya zauna sannan aka fara gaggaisawa da su Maama, da Papa, a loƙacin kuma Meer ya fita yaje ya taho da Ummyn sa da sarki Abuuu, suma zuwa sukayi kowa da kalar nasa al'ajabin najin yanda abun ya kasance,

Duk wannan hidundumin da ake Baba da Dadda basuyi magana ba, sakamakon ɗauke kan da Baba yayi ya nuna kamar ma besan da ita agun ba, hakan kwa ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba, suyi shekar da shekaru basa tare amma yazo inda take ya nuna kamar ma besan ta ba, duk da tana ta kallon sa idan suka haɗa ido ma sai ya kuma haɗe rai ya juyar da kansa, abun ya tsaya mata arai duk sai taji takasa sukuni,

Nan suka sake buɗe sabon babin hira, tun ana koke koke har aka dawo murnar nuna farin cikin ganin juna,

Abban Ameesha kam ko kunya yabi ya tattare a jikin Norry ɗin sa, ya kamo hannun ta ya riƙe gam kamar ance masa za a kwace masa ita,

Dadda ce ta kasa jurewa, cikin ɗan hasala, tace "wai ni me ake nufi dani ne, malam ko nayi maka wani abunne naga sai wani haɗe rai kake yi sai kace baka san dani ba agun, 

kowa maida hankalin sa yayi kansu, ga mamakin su amma sai sukaga Baba ya kuma haɗe rai tare da ƙara kawar da kansa, suma kuma sai yanzu duk suka fahimci hakan tunda suka zauna basu ga sunyi magana ba, a tsakanin su,

Abban Ameesha ne yace "Baba lafiya me yake faruwa?

Shiru Baba yayi bai basa amsa ba, yana me ƙara jin abun dake ƙasan zuciyar sa na ƙara taso masa,

A gaba suka sakashi, akan ya faɗi dalilin sa amma yaƙi Dadda harda su kuka,

Dadda ce ta miƙe cike da haushi ta goge hawayen, tace "To sai me inbaka kulani, suɗin ma ai da kasani baka kulasu daka sani ma baka dawo yanzu ma zaka iya tafiya ai ba wani yace kazo ba, me yasa ma kadawo,

Miƙewa Baba yayi shima cike da hasala, yace "ai badan ke na dawo ba ko angaya miki duk tsawon loƙacin da muka ɗauka bansan inda kike ba,

Ke ko kunyar faɗin haka ma baki yi ba, koda yake banga laifin ki ba, daman munafukin mutum baka taɓa gane kansa, ai baza ki taɓa jin kunyar faɗar komai ba tunda bakiji tsoron Allahn kiba wa kuma zaki ji tsoro, Allah wadai da halin ki,

Tofa wata sabuwa kowa yayi saƙare yana jin wani sabon zancen, Dadda kam ai saura kaɗan numfashin ta ya sarƙe, da sauri tayi baya zata faɗi, Abban Ameesha ya riƙota,

Baba bai damu da halin da ta shiga yaci gaba da cewa, sai yanzu hankalin ki ya tashi kenan ko duk a tunanin ki bansan wace ce ke ba, nasan har yanzu kina mamakin ya a kai muka kasan ce araye ko?

To kisan........,

Da sauri Abban Ameesha ya tari numfashin sa, cike da shiga ruɗani yace "Baba wai dan Allah me kake son cewa ne, me Dadda ta aikata maka, me kuma tayi, ya kamata kayi mana bayani ka duba kaga halin da ka jefata saboda maganganun nan naka,

"Duk na munafurci ne ai, dan baku san ko wacece ita, nafi ku sanin ko wacece ita, duk wani abu dake faruwa, itace musabbabin sa, duk ita ta jefamu cikin wannan halin, kowa ya taso cikin mawuyacin halin,

Hmmm dukansu akusan tare suka sauke ajiyar zuciya, dan yana faɗin haka duk suka fahimci inda zancen nasa ya dosa,

Ita kanta Dadda loƙaci ɗaya taji kamar ankwashe mata wani abun me nauyi daga cikin zuciyar ta, amma da gaba ɗaya tunanin ta ya tsaya, ta rasa ma wane irin tunani zatayi gurin gano abun da tayi masa yake jifan ta da waɗannan maganganun haka,


"Allah sarki Baba, wallahi har ka tayar mana da hankali, a ina ka ganta, Baba wallahi ba ita bace ai,

Wani kallo Baba ya watsa Abban Ameesha tare da cewa "har kake rantsuwa ingan ta da ido na ƙiriri ranar da tasa aka kama mu, amma kace ba ita bace,

Abban Ameesha harda ɗan murmushi yace "Baba ka kwantar da hankalin ka ayi maka bayani, itama yanzu da kake ganin ta anan tsawon kwanaki bama tare da ita, jiya mukaje Gombe acan ma muka kwana, sai ɗazu muka dawo,

cike da kallon rashin fahimta Baba yake bin Abban Ameesha da kallo,

Papa ne da kansa ya ɗora da yi masa bayani, da ƙyar suka samu Baba ya haƙura akayi masa cikakken bayani, tundaga A har Z saida aka basa, labarin kowa da halin da kowa ya tsinci kansa, sannan aka ɗora masa da labarin ganin mahaifan Abban Ameesha, yanzu haka acikin gidan su yake zaune,

Baba yayi mamaki mutuƙa abun da yafi komai basa mamakin shine ƴar biyun Dadda da take waɗannan abubuwan,

Nan ya ɗora musu da nasa, labarin bayan mutanen nan sun kamasa sai suka kaisa wani guri kwanan shi biyu kuma suka kawo Nadeeya loƙacin da suka kawo ta bata cikin hayyacin ta, saboda alurar da sukayi mata loƙacin da ta haifi Ameesha, itace ta taɓa mata ƙwaƙwalwa, gaba ɗaya sai ta burki ce, ta fita daga hankalin ta, abun sai ya haɗar mata biyu ga zafin haihuwa ga allurar da sukayi mata gashi kuma da ta tashi sai ta ringa kiran yarinyar da ta haifa taitacewa a fito mata da ƴarta, da mijin ta,

Dade suka ga abun nata ba sauƙi sai suka kira likita yazo yayi mata allurar da zata sa ta bacci, dan ta rage kwakwazon da take yi musu, bayan kuma anyi mata, ɗaya daga cikin su yace su Baba su shirya zai fita dasu sai suyi wani wajen idan ba haka ba kuma suka ci gaba da zama agun zasu iya rasa ransu,

Bayan sunyi haka da kwana ɗaya suka zo su su biyu sai suka fito dasu da niyar zasuje su kashe su, agurin waɗancen amma su awajen su idan sun fita dasu ba kashe su zasuyi ba, shiyasa ma aka amince musu da su fita dasu ɗin, suyi nesa dasu da gari sannan su kashe su,to a wajen fitowar ne, shi kuma Baba yaga ƴar biyun Dadda a cikin mota, basu bar gurin ba kuma, yaga fitowar ta daga motar ya ƙara tabbatar wa kansa itace,

Amma duk da haka da suka shiga motar sai da ya tambayi mutanen yace dan Allah wacece waccen matar Yahaya masa ai itace tasa aka kamasu, kuma yanzu haka ma da suka ɗauko su itace tasa, duk wani abu da zaiga ya faru itace take sawa, tunda ga wannan loƙacin Baba yake ƙullace da Dadda saboda duk a tunanin sa itacen da gaske,

Bayan kuma waɗannan mutanen sun fita dasu, sai suka kaisu asibiti suka biya komai da za a dubata koda bata samu lafiya ba gaba ɗaya to a ɗan bata abun da zaisa ta rage,

Suka yi musu godiya sannan sukayi sallama, suka tafi suka barsu agun,

Satin su ɗaya a asibitin aka sallame su saboda kuɗin su ya ƙare amma sun basa maganin da zai ringa siya mata idan ya ƙare zai iya zuwa wani asibitin ya siya,

Daga nan Baba ya rasa inda zai dosa, haka ya riƙota a hannu suka ringa tafiya shikan sa baisan inda zasu ba,

a wata kasuwa suka tsaya, wanda shi kansa baisan wane gari bane, saidaga baya yake jin sunan garin Kano abun da zasu ci yafara tunani dan haka yana ganin ana dako shima yaje yace a taimaka masa, abashi aikin yi zasu siyi abinci,

Wani mutumine yaji yabasa tausayi, hakannan ya ɗauko dubu biyar yabasa, yace yaje basai yayi masa dakon ba,

Tun daga nan, Baba yake zama a cikin kasuwar, tare da ƴar sa, kuma har yanzu batadawo daidai ba, kawai dai ta dena sambatun da buge buge,

Wajen Satin su uku a haka suna kwana a ƙasan wata rumfar me tebur sai ya nemi ƙyallaye yake rufe musu ciki idan dare yayi zasu kwanta, daga baya kuma sai aka fara ankare wa dasu, wani mutum ya nemi yayi masa lalata ƴa, sai kawai ya tattara ina sa inasa suka bar kasuwar haka sukai ta garari daga can suyi can daga na su koma can, daga ƙarshedai da Baba yaga abun hakane sai kawai ya ɗauke ta suka koma daji da zama, ya haɗa musu bukka da komai da zasu ringa amfani dashi, sannan ya ringa shiga daji yana nemo wasu magungunan sai yanzu yake ganin amfanin sanin su, ada sana'ar mahaifin sace amma shi baitaɓa maida hankali akan suba, sai yanzu inda ma Allah ya taimake sa duk ya riƙe su, kwaso su yafarayi yana kaiwa cikin gari yana siyar wa, kuɗin kuma da yake samu sai yaringa siyo musu abinci da abun da yasan zasu buƙata daga baya kuma yama haɗa nurhu da kansa yake yi musu abin da zasu ci,

A wajen siyar da maganin ne, ya haɗu da waɗannan yaran su biyu da suka taimake su suka fito dasu, suna haɗuwa suka gaisa cikin mutunta juna, sannan suke basa labari sun shiryu sundena wannan harkar, suma duk kusan marayu ne basu san iyayen su, shiyasa suka faɗa irin harkar, daga baya kuma suka shiryu, nan suka tambaye sa ina ya koma yagaya musu harkar da yake, nan suka roƙashi shine suka haɗa kai gaba ɗayan su suka koma rayuwar da jin idan zai fito sai su fito tare kowa ya nemi nakan sa, a haka har suka tara kuɗi suka buɗe shago da taimakon wani Alhaji da yabasu jari, Alahamdulillah komai yana tafar musu yanda yakamata, a loƙacin ne Bello da Sulaiman suka buƙaci Baba da su koma cikin gari subar dajin tunda suna da kuɗi sai su kama gida...,

Amma baba yace a'a sude suje su kama inyaso kullum idan ya fito da ringa haɗuwa, babu yanda suka iya dan sunfi son zaman cikin garin akan dajin, badan suna so ba suka bar Baba ƴar sa suka koma cikin garin inda Baba yabasu shawarar su nemi shaguna biyu me daki a ciki sai sun ringa kwana a ciki sun samu kwanciyar hankali, ganin hakan yasa Baba yace su taya shi bincike akan matar agano masa inda take,

Nan suka shiga bincike akan Dadda shi yanayi suma sunayi masa har aka gano inda take da kuma komawar su gidan sarautar duk wani motsin su da labarin gidan babu wanda baya zuwa kunnen Baba, shima kuma yana nemo wani abun da kansa, abun da yasa yaƙi tona mata asiri kawai saboda yana so sai ya fara gano dalilin da yasa ta zaɓi yi musu haka, kuma ya bari sai ranar da asirin ta ya tonu yasan dole asirin ta ya tono ko badaɗe ko bajima, shi kuma agun tonuwar asirin zai bayyana kansa yazo yaƙara da tashi shaiɗar, daga nan ya ɗora musu har zuwa inda ta samu lafiya gaba ɗaya, tun buge tan da Meer yayi da mota tun loƙacin yakaita asibiti daga nan kuma akayi mata aikin matsalar ta gaba ɗaya ta dawo normal,

Yana gama bada labarin, duk sun fahimce sa, kuma basuga laifin sa ba, saboda daman duk wanda yaga haka indai ba bayani akayi maka ba baza ka taɓa yarda ba,

Haƙuri yabawa Dadda abisa zargin ta dayayi akan rashin sani, daga nan suka cigaba da tattaunawa, sai wajen ƙarfe shaɗaya na dare sannan kowa ya fara shirin kwanciya, Dadda da Ameesha da maman ta, akace su tafi ɗaki, shikuma Baba su tafi da Abban Ameesha, da farko Abban Ameesha ƙin yarda yayi wai saidai su tafi tare da Norry ɗin sa, akace masa ai bazai yiyu ba, dole sai an ƙara ɗaura musu aure saidai yayi haƙuri nan da sati ɗaya sai a ware musu part ɗinsu daban bayan an mayar da auren su,

Ba haka suka so ba, dande anfi ƙarfin sune kawai suka yarda daga nan sukayi sallama, kowa ya tafi makwancin sa, asuba ta gari..........,

Washe gari tunda wuri duk suka haɗu a cikin falon gurin breakfast daga nan kuma aka haɗa taro a cikin fada na gabatar da bayyanar matar Abban Ameesha, da kuma mutumin da ya tsinci Sameer tun yana yaro,

Kowa ya taya su farin ciki anayi, gwaggwo ma ba abarta a baya ba ta nuna farin cikin ta tsantsa, ga bayyanar ahalin ta gabaɗaya ƙwansu da kwarkwatar su babu wanda aka rasa, sannan anyi maganin duk wani makiri da mugu dake kusa dasu saidai kuma ayi fatan Allah ya kiyaye gaba,

Har ƴar ƙaramar walima aka haɗa akayi saukar Alqur'ani, aka ci aka sha, sannan akayi sada ka ga mabuƙatan wajen masu yawa,

A cikin sati ɗayan kamar yanda akace aka mayar da auren Abban Ameesha da Maman Ameesha, inda aka ware musu part ɗin su domin suje suci gaba da soyayyar su daga inda suka tsaya, part biyu akayi su da su Dadda da Baba, ƙofa ce kawai ta rabasu su da su, Ameesha tana ta murna wai zata koma part ɗin su Maman ta akace mata ai ga nata part ɗin can, suma can zasu koma ita da Meer tunda akayi maganar tayi shiru bata sake magana ba,

A ranar da zata koma can akayi rashin sa'a Bossay yakawo ziyara gurin ta, yasamu mummunan labari, bawan Allah harda su suma, koda ya farfaɗo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login