Showing 36001 words to 39000 words out of 170049 words
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️xeemat...love❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
Da sauri yasha gabanta ya haɗe rai sai kuma yarasa abun cewa, tsayawa yayi yana kallonta itama shi take kallo da mamakin tare tan da yayi,
Ɗan shafa ƙeyarsa yayi sannan yaɗan tsugunna ya kawo daidai tsawon ta, sannan yace "am uhm naceba kiɗan je waje ganinan zuwa zan shirya kinji yayi maganar yana kafe ta da tare da kama hannun ta alamar zai fita da ita saboda daman bata shigo dakin ba gaba ɗaya tana bakin ƙofa,
Kallon sa ta tsaya yi tare da ɗan harararsa tace "au yanzu ingama yi maka gwanin ta inzo intashe ka amma shine zaka wani ce infita ka shirya so kake sumin dariya to wallahi baza kasa naji kunya ba inkaga na fita daga ɗakin to tare muka fita,
Ƙara riƙe hannun ya yayi yace "Wai a haka kike so na fita banfa yi wanka ba ni bacci ma nake ji jiya ban samu damar yin isasshe ba, idan na tashi namiki alƙawari zanzo har inda kike agabanki ma zanci komai kikaban amma a yanda nake nan yanzu ko mafita baci zanyiba kuma ma bazan taɓa iya fita a haka ba yayi maganar yana kallon jikin sa yana kallon ta,
Itama haɗe ran tayi tace wa zaka haɗewa rai to ko an gaya maka hakanne zai sa infita to ba inda zani nmin dariya ka wuce mutafi a haka ko kuma kashiga ka shirya injiraka zan zauna har ka gama mufita sai kazaɓi ɗaga ehe, ƙoƙarin ƙara yin gaba take ya sake tariyar, riƙe da hannun ta, ƙoƙarin kwacewa ta shiga yi,
Ganin hakan yasa shi Sakin hannun nata ya harɗe hannun wansa akan ƙirjinsa yana ɗage girarsa gaba ɗaya biyun, kawai yana jiran tagama maganar yaga iya ina kafiyar tata ta tsayan, har ta gotashi zata wuce,
Hannu wansa yasa ya ɗageta cak ɗn ta kafin tayi wani aune har ya fito da ita falon yana fito da ita ya ajiye ta akan idon su papa da suke jiran fitowar su sai gashi anfito da Maama ahannu yana direta ya juya ya koma ɗakin sa ya ƙulle,
Acikin su kuwa babu wanda baiyi mata dariya ba harda masu riƙe ciki irin su Ameesha,
Ummy kam miƙewa tayi tsaye ta ƙarasa gaban Maama, Maama da tunda ya direta takasa motsawa kuma takasa ɗaga ido ta kalli kowa dan tarasa ma da abun da zata ji da ɗaukar ta dayayi da girman ta ko kuma da watsa matan ƙasa da yayi ko kuma da dariyar da suke yi mata da wane zata ji lalle tunda suke bata taɓa tunanin iskanacin yaron nan yakai hakaba, yau ita zai tozarta a bainar nasi bayan kuma tagaya masa idan ta fita ita kaɗai zasu yi mata dariya amma yayi mata irin wannan cin mutuncin taƙaici da haushi da kunya kuma duk sun haɗar mata a loƙaci guda,
Ummy na ƙarasowa gabanta ta tsugunna inda take tana dariya tace "Maama ya akai ne wai mai yahaɗaku ɗan bamu labari naga ranki a ɓace yake gaya min waya taɓa mana ke yanzu mukaishi prison,
Taƙaici yasa Maama miƙewa tsaye tana sakin tsaki ta dashi ɗakin ta zata tafi dan bazata juri tsokanar da zasu yi mata kar su ƙara mata wani baƙin cikin,
Can ta tsikayo muryar Abu nacewa "kaɗan ma kika gani indai yaron nanne zai miki fiye da haka ma, bakisan halinsa bane daman shi yasa kike goyon bayan sa akan komai yanzu ga irin tanan kunfi kusa,
Dadda ma da bata saka baki ba sai yanzu itama ta ɗora da cewa "anyi walƙiya mungani, wasu arana tsudum tsudum wannan abin kunyar har ina Ni Hadiza to,
Nan kowa yashi tofa albarkacin bakin sa, Papa ba abun da yake sai dariya saida yaga abun nasu bamai ƙarewa bane sannan ya tashi ya nufi wajen matar sa,
gashi dai duk tsokanar tata suke amma taƙi tafiya tayi tsaye agun sai kace an kafeta saida papa yaje zaija hannun ta tayi saurin janyewa tana hararar sa cike da ɓacin rai tace "Ni kar ka taɓani ai kanajin su baka hanasu ba, tana faɗar haka ta wuce fuuu kamar wacce aka yiwa wani babban laifin,
Da sauri Papa yabi bayan ta, kuma still baidaina dariyar ba,
Haka ta wuce suna mata dariya saida sukayi mai isar su sannan waɗanda suka gama cin abinci su suka tashi waɗanda kuma basu ciba suka ci gaba da ci,
Ummy da Abu suka tashi suka fita daga part ɗin zuwa nasu part ɗin gurin ya rage daga Dadda sai Azeema da Ameesha basu daɗe ba kuma itama Azeema ta tashi tace zata je ta ɗan rage cikin ta taji yana tayi mata ƙugi,
Ameesha tana mata dariya tace "daman kinsaba ai daga ci sai banɗaki wallahi yakamata kije kiga likita wannan kashin naki yayi yawa,
Tsaki Azeema ta doka mata tana hararar ta tace "A'a kinmanta sarkin mayu zangani ba likita ba, mutum da lafiyar sa kiringa jawo min bala'i to inbaki sani ba kisani kashinma ai rahama ce da lafiya, idan bakayi ka......ƙurrr cikin ta yaƙara murɗawa hakan yasa tayi saurin barin wajen bata ƙarasa maganar da tayi niya ba,
Yanzu kam har Dadda saida tayi mata dariya yanda ta kwasa aguje doke abun yabaka dariya,
Ameesha tashi tayi ta koma kan kujera tare da ɗaukan remote ta kunna TV, tun kan takai tashar da take so takalla da Dadda ta kira sunan ta, loƙacin da take kan kujerar gefen ta,
Ajiye remote ɗin tayi ta juya tana fuskantar Daddar da taji ta kirata,
Itama Daddar ita take kallo saidaga baya tace "Khadijah wata magana nake so muyi,
Gyaran zamanta Ameesha tayi gabanta na faɗuwa jin da sunan da ta kirata,
Dadda tace "naga tunda muka dawo nan gaba ɗaya kin canza min kinfara mantawa dani, kamar bani da wani muhimmanci a wajen ki ko kodan kin samu waɗanda suka fini,
Da sauri Ameesha ta katseta da cewa "dan Allah Dadda ki daina wannan maganar ke kinsan kaf duniyar nan bani da wani wanda yafiki agurina indai ba mahaifina ne yadawo ba shine kaɗai zan haɗa sonki da nashi amma kinfiye min komai kuma ni wallahi banga wata canzawa danayi ba tare fa muke kwana dake guri ɗaya muke cin abinci indai bana tare dake saidai idan ko munje wajen su Amra ko kuma idan mun fita amma kullum fa muna tare dake wace irin kuma rashin kulaki ne banayi,
Jinjina kai Dadda tayi tace "indai har kin ɗaukeni da muhimmanci ai bazaki ringa ɓoye min wasu abubuwan dan na fahimci akwai abun da yake faruwa kike ɓoye min jiya zaki gaya min waccen yarinyar ta hanaki naganota sarai kawai rabuwa nayi daku, yanzu kigaya min jiya mai yasa naga kunshigo kowannen ku da damuwa afuskar ku kuma kunyi min shiru bakuce komai, kigaya min mai yake faruwa acikin gidan nan,
Shiru Ameesha tayi tana tunanin maganganun Dadda da kuma maganganun su Azeema tunanin tafara yi ta faɗa mata ko kuma kar tafaɗa mata, shiru bata bawa Dadda amsa ba har saida Dadda ta taɓo ta sannan ta ɗan numfasa tare da sakin murmushi tace Dadda ta takaina wai wannan abunne yasa kike tunanin na canza miki to ki kwantar da hankalin ki babu wani abu dake faruwa,
Abun dake faruwa daman rannanne muka fita da su hamra sai Amra taga motar nan da aka sace ni aciki muka haɗu da ita shine muka dawo gida muka gayawa yaya Meer shine muka ƙara komawa inda muka ganta amma sai mukaga bata nan anjanye ta, tunda nan shine muke ta neman inda take jiyama muka ƙara fita gaba ɗayan mu zamu raka yayan su Hamra shine wasu suka tare mu sukace mubasu duk abun da muke dashi, mu bamu da komai saidai kuɗin yayan nasu ya tafi dasu zaiyi mana siyayya shi suka ƙwace gaba ɗaya harda wayar sa ma da ƙyar suka barmu muka taho dalilin da yasa muka dawo gida ranmu duk a ɓace, bayan wannan kuma babu wabun da yake faruwa, saidai kuma ko ɓangaren su Maama bansani ba ko suna wani bincike akan abun da ya faru,
Kallon ta kawai Dadda take amma nadan ta yarda da itaba kawai dai zata bar zancen saboda tunda ta fahimce ba aso tasani sai ta rabu dasu idan tayi tsami taji,
A fili kuma sai tace "to shikenan Allah ya kiyaye gaba, ai ni nazata koda wani abun da ba aso insani, amma tunda hakane shikenan mubar maganar tana faɗa ta miƙe daga gurin tare da barin wajen,
Tashin ta kuma yayi daidai da fitowar Azeema daga ɗakin abakin ƙofar ɗakin sukayi karo da Dadda tayi saurin matsa mata ta bata damar wucewa,
Itadai Ameesha ta kasa ce mata komai dan bata san mai zatace mata ba abun yabata mamaki bata taɓa tunanin haka daga gare ta ba, tana cewa ta canza nata alhalin itace take neman canzawar, tana zaune agun ta zabga tagumi tana tunane tunane taji ana nocking ɗin ƙofar,
Tana shirin tashi sai Azeema ta riga ta ƙarasawa bakin ƙofar buɗe ƙofar tayi tare da leƙawa,
Wani bafade ne dake tsaron ƙofar yace mata "wai ana neman iso da Papa saƙo daga Waziri da kansa,
Da to ta amsa, masa sannan ta koma ciki, Ameesha tagayawa taje ta sanar da Papan,
Tashi tayi taje inda ɗakin Maama yake daga waje ta sanar dashi ana kiran sa, tunkafin ya fito ma yace mata tace "ya shigo falo,
zuwa tayi ta sanar da mai neman nasa, sannan ta dawo ciki ita da Azeema sukayi saurin barin falon saboda sun san ko waye shi,
Ba daɗewa Waziri ya shigo cikin falon cikin rashin nutsuwa kana ganin sa kasan ba nutsuwa a tattare dashi kamar ma a firgice yake haka ya shigo,
Papa ne ya fito shima daga ɗakin fuskar sa asake yaƙaraso gurin sa da ya gansa a tsaye ba a zaune ba, yana fitowa kuma Maama ta biyo bayan sa ta fito da falon itama,
"A'a Waziri da kansa ance inkaji kira samu ne amma banda kiran ƴan sanda Allah yasa labari mai daɗi ka kawo min,
Fuska kalar tausayi da take nuna tsantsar damuwa,
Kallon sa yayi da jajayen idanun sa yakasa magana,
Papa da yagan sa hakan a loƙaci ɗaya fara'ar sa ta ɗauke, cike da kulawa yace "subhanallahi mai yafaru na ganka haka me yake faruwa?
A fusace Waziri yace "yaya kana nufin bakasan maiyake faruwa ba acikin masarautar nan tun safiyar yau aka tashi da maganar amma bakasan komai ba,
Jin kamar faɗaɗa a muryar Waziri yasa su dadda ma suka fito saidai su Ameesha nadaga bakin ƙofar ɗakin su basu shigo cikin falon ba gaba ɗaya,
Waziri yace "Allah yaya mutanen nan yanzu bazan ƙyalesu ba dan sunga anyi musu shiri shine suke samun damar yiwa mutane wulaƙanci to wallahi anzo gaɓar da bazan yarda ba kamar ni mainayi musu maiye ruwana acikin abunsu, amma tunda har sukace haka zasuyi to muzuba mungani,
"Wai su waye suwa kake magana akai kuma mai akayi maka kamin bayani ya anda zan gane mana duk kabarni cikin duhu me yake faruwa acikin gidan nan,
Kallon sa Waziri yayi ido cikin Ido yace "yaya su rasa wanda zasu ɗauke sai Hindatu matar nan babu ruwanta saliha da ita tunda na aureta babu da wanda suka taɓa samun saɓani har yau saboda bata shiga sabgar kowa amma shine jiya daddare aka samu wani yaje ya sace ta agidan nan kuma anfita da ita kaf cikin gidan nan babu inda ba aduba amma ba aganta ba, wannan abun fa yayi yawa yakamata ayi gaggawar dakatar da komai akawo ƙarshen abun nan yanzu abun da zasu shigo dashi kenan sace sacen mutane,
Papa "yace wai da gaske kake an rasa Hindatu agidan nan amma to garin ya akai haka kai kana ina har kayi sake hakan ta faru,
Wazriri yace "ina wajen surayya mana, saida safen naje sashenta akece min wai ai bata kwana agidan ba kuma wayoyin ta duk na kira a kashe bataje gidaba gabaɗaya duk inda akasan zata iya zuwa anje ba asame taba,
Tun ɗazu ake bincike cikin gidan nan bata ciki,
Su Maama ma sallallami suka shiga yi suna jajan ta masa da mamakin irin satar da sukeyi ba akansu,
Papa ne yace "Subhanallah kai mutanen na me suke so ne da baza subar mu cikin kwanciyar hankali ba sudai burin su kullum suga kanmu a tarwatse to Allah ya toni asirin su a duk inda suke, yanzu muje aƙara bada cigiyar ta sannan a ƙarfafa bincike,
Maama tace "ni fa abunma kamar da ranin hankali ina mamakin ta yanda ake fita da mutum daga cikin gidan nan amma ace wai ba aga loƙacin da aka fita dashi ina masu tsaron gidanan kuma waye yake buɗe musu ƙofar fita wannan abunfa dole da sa hannun wasu daga cikin gidan nan, kuma da sannu zasu bayyana kansu da kansu, in sha Allah Allah ya kusan tonuwar asirin su,
Waziri jin addu'ar ta aransa saida ya dara saboda tuna maganganun bokan su, shinan wani irin kallon loƙacin tafiyar ku ya kusa dashi yake binsu,
Daganan Papa yasa suka fita har Maama Dadda ma saida ta bisu suna gama fita, su Azeema suka kwashe da dariya suna tafawa da cewa Allah yaƙara Allah yasama ta mutu, kowa ya huta sudai ɓatan ta ba ƙaramin daɗi yayi musuba,
Ameesha tace besty ai ba abarmu abaya ba muje muma muganewa kanmu kar show ya wuce mu, kinga yanda yake magana kamar zaiyi kuka ashe ba daɗi shi matar sa kawai ce amma ji yanda ya tashi hankalin sa ina kuma a ƙwace masa kowa nasa har ƴaƴan inajin da sai ya haukace,
Azeema tace ɗan isakan ba tsohon banza tsohon hofi ma yaudari waya sani ma ko yanzun ma haɗin nasu ne wata manaƙisar suka shirya, wannan mutumin wallahi ba mutumin arziƙi bane, ni har tsoroma yake bani wallahi,
Ameesha tace wallahi hakane ai babu abun da bazai iyaba tunda ya ci amanar ɗan uwansa ma wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya suka fito ciki ɗaga to waye ma bazai iya cutar wa ba,
Azeema tace "hmmm Allah dai ya kyauta ai asirin sa ya kusa tonuwar tunda de anada hujjar kamasa dumu dumu ai zance ya ƙare,
Ameesha tace wallahi hakane....., Nan dai sukaci gaba da tattaunawar su sannan suka fita waje,
Meer dake bakin ƙofa daman jiran fitar su yake, yana ganin kwa sun fita ya fito da sauri, yayi hanyar kitchen ɗin falon buɗe ƙofar barander yayi, sannan ya dawo cikin ɗakin sa, a bargo ya nannaɗe ta bayan ya yaƙara shaƙa mata abun suma, sannan ya ɗauko ta ta hanyar ya fito da ita yana fitowa inda yasa aka ajiye masa mota gurin babu kowa dan haka, yana zuwa aka buɗe masa gaba yasaka ta sannan ya shiga motar shima ɗayan da ya akawo masa motar wannan abokin nasane, shine yasa masu gadi suka barsa ya shigo da motar bayan yagaya musu tawaye sun san shine dan haka yana zuwa ya shigo kansa tsaye, ya tsaya a inda Meer yayi masa kwatance,
Yana sakata aciki Meer yace yaje zai zasu ƙarasa maganar a waya,
Jan motar yayi ya fita dake daman baidaɗe da zuwa ba kuma tun kan zuwan sa aka sanar da ɓatan nata dan haka babu wanda zaiyi zargin zai fita da wani abun,
Wunin ranar haka akai ta cigiyar matar Waziri,
Zuwa wajen ƙarfe sha biyu na dare Meer yagama setilling ɗin komai ya gyara video ɗin nan da yafara ɗaukar su dashi wanda sukayi masa abunnan har ya shaƙeta ta faɗi kamar ta mutu ashe duk shirin sune shine shi kuma zaiyi musu nasu shirin,
Yana gama sai tashi kawai yasake shi a social media sannan ya lalubo wasu nombobi da yasa aka nemo masa na ƴan cikin gidan har dashi Wazirin kansa saida ya lalubo number sa, da kuma wasu masu hannun akan lamarin duk ya haɗa nombobin su suma ya tura musu wasu ta WhatsApp wasu kuma ta message.......,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
_____Waziri yana zaune a cikin mutanen sa na ƙungiya acikin wani ƙaton falo inda daman yawanci haɗuwar da suke agurin suke to yauma ɓatan matar waziri yasa suka haɗa zaman tun wajen ƙarfe sha ɗaya,
Kowa yana mamakin ta yanda akayi ta ɓata dan basu yarda Meer ne ba saboda dashine dole zasu sani tunda sun saka ido akansa sosai da hakan ta faru da tuni sun samu labari to amma abun da yake ƙara basu mamaki waye zai ɗauke tan abun ba ƙaramin ɗaure musu mai yake ba, sunyi wajen minti talatin agun suna tattaunawa amma sun kasa samun mafita,
Suna cikin wannan halin Waziri yaji kira awayar da sa sauri ya zaro wayar tare da suba kan wayar yaga mai kiran da sauri ya ɗaga ganin sabuwar number ke kiran sa ne a tunanin sa ko wanine yake kiran sa ya gaya masa ansamu inda take,
Yana ɗagawa daga can ɓangeren