Showing 51001 words to 54000 words out of 170049 words

Chapter 18 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7236

da halina, kar kamin mummunar fahimta,

Kallon ta kawai yake bai iya furta mata komai ba saida takai ƙarshe sannan yace "mata shikenan kar ki damu kije kawai zamuji waya,

Wani murmushin dolen ta ƙara sakar masa duk da tasan ba lalle bane ya yarda, amma sai tace "nahode daka fahimce ni sai munyi waya tafaɗa tana buɗe murfin motar ta fita baya ta buɗe baya ta ɗauki kayan ta, sannan ta kuma ɗaga masa hannu ta nufi cikin gidan,

Yana gurin yana kallon har saida ta shige sannan ya juya ya koma ransa duk babu daɗi ba haka yaso ba yaso ace sunyi hirar sosai sun ƙara fahimtar juna amma sai akasin haka, haka yaringa tuƙin sa cike da tunani har ya ƙarasa gida......,


Su Ameesha ma basu dawo ba sai wajen magariba suka dawo shina tunda suka dawo suna tare da Bossay sai bayan sallar isha'i yabar gidan,

Ita kuma Ameesha tace bazata kwana ita kaɗai ba, tabi su Amra ta kwana acan....



Tunda Meer ya fita bai dawo ba sai da akayi sallar isha'i sannan ya shigo gidan yana shigowa kuma ya wuce part ɗin sa, saboda baiga kowa a falon ba yau da alamun duk sunyi barci da wuri,



***********************

11:pm

Cikin masarautar ta ɗau shiru da alamun kowa ya tafi makwancin sa, kamar haɗin baki babu kowa awaje,

Kamar yanda suka tsara ɗaya bayan ɗaya suka zo wajen a wajen fadar suka har haɗu, su biyar daman mutum bakwai ne to yanzu saura 5 babu guda 2,

tura ƙofar sukayi sai sukaji ta adatse da muƙilli, zaro muƙullin da sukazo dashi sukayi suka zurashi suka buɗe ƙofar sannan ɗaya bayan ɗaya suka fara danna kai ciki na ƙarshe ya rufo musu ƙofa, gurin daman ƙofa biyu ce dashi sai ka shiga farko gurine kamar ɗan corridor amma babba, sannan zaka buɗe main ƙofar cikin fadar, inda suka shiga da haske amma can cikin fadar duhu ne gaba ɗaya saboda ba shiga ake ba shiyasa ake kashe ƙwayayen gaba ɗaya,

Suna shiga ɗaya daga cikin namiji yace "bamai waya ya kunna mana haske nifa ba abun da nake gani,

Ɗaya tace kai kaman ta abun da boka yace ne mubuɗe ƙofar kawai ai hasken corridor ɗin nan zai shigo ko aduhuma ai zamu iya zuwa wajen kujerar tunda ba baƙuwar mu bace munsan inda take ,

"Eh to hakane kuma bari in buɗe ya buɗe ƙofar saikwa ga haske amma kaɗan bama agani sosai kawaidai yafi babu,

cike da murnar farin cikin su zai cika ko wanne da abun a hannun sa dan sun raba tundaga can, ɗiba suka fara yi suna watsawa asaitin kujerar da suka tabbatar da itace, haka sukai ta watsawa har suka gama sannan suka murnar,

ɗaya ne yayi dariya yace "wai wallahi har na tausaya musu fa wannan ai shi ake cewa ga samu ga rashi yanzu sunaji suna gani zasu bar kujerar nan, nifa wallahi dama har shi papan aka haɗa ni banga amfanin zaman sa ba, mu tarkata su gaba ɗaya su tafi subar mu shaƙata,

Wani yace kaifa wallahi baka da imani mai yayi maka zaman sa da rashin zaman ai duk ɗaya,

Murya mace tace kuna da loƙaci shiyasa kuka zauna kuke lugudar leɓe ni na tafi idan aka ritsa da mutum wallahi kar yace yasanni, tafaɗa tanayin gaba,

Wata macen ta ta kwashe da dariya tace haba shugaba da kanki tsoro ai banaki bane, ke da kike hanamu kina ƙarfafa mana gwiwa amma yanzu zaki gudu ki barmu, dariya suka sanya gaba ɗaya, suna cikin dariyar sai sukaji kamar ana taya su ba iya tasu muryoyin bane, dakatawa sukayi sai sukaji anyi shiru, sai kawai suka ɗauka tasun ce daman, suka juya suka nufi ƙofar saidai basu kai ga saka ƙafafun su waje ba, kawai suka ga wal wuta ta gauraye cikin fadar kamar haske ta ko ina,

da sauri suka juyo gaba ɗayan su dan ganin mai kunna fitilar ko ɗaya daga cikin sune,

Amma ina idanun su suka sauka akan tarin nutanen da suke cikin falon a zazzaune daga gefe, sai Meer dake tsaye awajen mukunnar ƙwai.....,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️


_Da farko Ina miƙa Godiya ta gareki *MAMAN FARUQ* da irin alkharin ki Allah yasaka da Alkairi yabiya miki buƙatunki na alkhari, ina godiya sosai da sosai Allah yabar zumun ci💞💞_

_Na 2 ina godiya *AUNTU MAI JIDDA* inajin daɗin comment ɗinki sosai much ƙauna♥️♥️,_

*Na 3 godiya ta gareku masu yin comment wani koƙacin (Mrs mai martaba, bajatu, maman Arman, 07036484180, 💝💞)
to da wanda ma yakeyi da wanda ma bayayi duk ina godiya, Allah yabar min ku, I love U wujiga wujiga♥️♥️♥️ komai wuya muna tare👩‍❤️‍💋‍👩🤝💝*


           *_Typing........✍️✍️_*


*🅿️ 19*
     
'Amma ina idanun su suka sauka akan tarin mutanen da suke cikin falon a zazzaune daga gefe, sai Meer dake tsaye awajen mukunnar ƙwai.....,

A kusan tare duk suka miƙe tsaye, Papa ne yafara miƙe tsaye cike da fargaban abun da idanun sa suka gane masa saura kaɗan zuciyar sa ta daina aiki a ɓangaren Maama haka, gwaggo kam tsabar mamaki ya kusan kashe ta azaune ta kasa tashi tsayen ma,

_Tsuru tsuru sukayi tare da jin bagawar zuciya da ta riske su cikin wani irin yanayi marar misaltuwa, ba ƙaramar razana sukayi ba, da ganin gaba ɗaya kusan a halin gidan acikin gurin to ya a kai haka ta faru taya akasan zasu shigo ciki da har aka kafa musu wannan tarkon ankamasu dumu dumu gashi anji magan ganun da sukayi yanzu da wane ido zasu kalle su, basu taɓa tunanin wannan ranar zata riske su ba,

Gaba ɗaya sun ma rasa abun yi sai kawai ɗaya daga cikinsu tasamu ƙarfin cewa kuzo mugudu kowa yayi takan sa,

Daman kowa mafita yake nemowa kansa jin abun da tace kuwa ba kunya ba tsoron Allah duk suka juya zasu gudu, har wasun su sun saka ƙafafun su awajen corridor ɗin sai kawai suka dakata saboda to zali da abun da ya kusan sanya su mutuwa agun dan ba ƙaramin razana sukayi ba da ganin sa da kuma tunanin mai yakawo sa gun acikin daren nan, kodai yazo yatona musu asiri ne,

Sanye yake da kayan da suka barsa ɗazu ga kwalliyar fuskar nan ta irin bokaye bai goge taba, ga abun kansa shima bai kunce sa ba,

Takowa yashiga zuwa inda suke hakan yasa suka fara ja da baya da baya cike da kiɗimewa da tashin hankali,tsoro da fargaba,

Dariya ya kwashe musu da ita irin wacce yasaba yi musu idan sukaje wajen sa, amma ta yanzu har tafi ta ko yaushe saboda ta yanzu da biyu yake yin ta harda ta mugunta yakeyi saboda yanda yaga sun tsure suna binsa da wani irin kallo,

Saida yagama dariyar sa son ransa sanan yadakata tare da kunce abun kansa, ya jefar dashi, abu yasa ya goge kwallin da ya ɓata fuskar sa dashi,

Nan duk saranda basu kaɗai ba har su Papa da suka tsaya suna kallon abun al'ajabi ganin fuskar yaron nan da yakawo matar Waziri yace ya tsince ta,

yana warewa ya juya ya kalli Meer sannan ya ɗaga masa hannu sama daidai saitin kunnen sa sannan ya sauke yayi salute ɗinshi kamar soja harda ƙamewa,

Shikuma Meera ya jinjina masa da babbar yatsan sa na hannu tare da furta good 👍 a hankali,

sai kallo ya koma kansu yanda sukayi abun dole ya burgeka idan kana gurin kenan daman duk shirine shi ya turosa loƙacin,

Mutanen kuwa ai ƙiris yarage wasu su haɗiyi zuciya su mutu ko sa huta da tashin hankalin da zasu fuskan ta,

shugaba kuwa wani irin tari ne ya sarƙeta atake agun nan tafara tari kamar numfashin ta zai ɗauke,

tana cikin yi taji anmiƙo nata ruwa karɓa ƙin karɓa tayi dan da so samun tane so take daga tarin ta ƙarasa daga nan,

Ƙin karɓar da tayi yasa Meer ya daka mata tsawa da cewa karɓi,

Hannu na karkarwa tasa ta karɓa ta fara kwankwaɗa saida ta shanye tas sannan ta ajiye robar, sai kuma tarin ya lafa duk azabar nan da tasha hakan bai sa wani yayi mata sannu ba duk kuwa girman da take dashi agun wasun su,

tsudum sai ga gwaggo da tasamu ƙwarin gwiwar tashi ta ƙaraso gurin "ai da kabar shegiya ta ƙarasa shegiya nuna fuka alugun guma, fir'auna ta biyu, sheɗaniya watakon kece ma shugaba ko shugaba kece silar tarwatsa komai kenan, wallahi*SA'ADATU* kin ban mamaki ashe kice ƙungurumar ana zargin wata can daban ashe ke kina gefe kina kitsa iya shegen ki munafuka alugunguma Allah tsine miki to wallahi ahir ɗinki kurwar ɗan tafi ƙarfin ki, yau Allah ya toni asirin ku munafukai,

Damƙe idanun ta tayi jin kalaman da aka ambaci mahaifiyar ta dashi saida taji shi har cikin ranta, a hankali ta buɗe rinanun idanun ta ta ɗorasu akan mahaifiyar tata, dan har yanzu ganin abun take kamar a mafarki mai yake shirin faruwa da ita, duk abun da yake faruwa ace komai daga ginshiƙin ta komai zai faru mai yasa rayuwa tazo mata ahaka mai yasa abubuwa suke shirin faruwa da ita,

Saura kaɗan jiri ya kwashe ta ta faɗi ƴar uwar ta tayi saurin riƙota duk da itama jurewa kawai take, saboda itama hawaye yagama wanke mata fuska,

Cikin kukan tace Munubiya (momma) ki nutsu dan Allah karki sa zuciyar ki bugawa kibi komai a hankali,

Ɗagowa tayi tana kallon ta da jajayen idanun ta tace mamy (twins sister ɗin ta wacce akasaka mata sunan gwaggo Karima kenan ƴaƴan ta suna cemata mamy shiyasa kowa ma yake ce mata haka) "nutsuwa kuma ahaka kike so insamu nutsuwa ni gwanda ma na mutu da wannan baƙin cikin da yasame ne mai yasa rayuwa zatazo min ahaka, mamy mahaifiyar mu fa ko bakiji mai tayi bane ko baki gane taba kingan taba bakiji mai aike ce mata ba itace fa tayi komai ita take sawa a cutar da mahainmu wannan wacce irin rayuwa ce, nashiga uku mahaifiya ta, (AMMAH kakar Sam kuma matar Papa) mijina (DADY baban Sam) ƙanin mahaifina(Waziri) ƙanwar mahaifiya ta (hajjaju, ƙanwar Ammah, wacce sam yaje gidan yakai sumy har sukayi mata muguntar nan)

Mamy mai suka tsare musu maiyasa zasuyi haka ga ƴan uwan su, sune duk sukayi komai wallahi suny ku kira min Sam yadawo yaji abu da mahaifin sa yake aikatawa kar yayi koyi dashi, ga kakannin sama duk yazo yagan su gasunan a tsaye wallahi sune ina zanga Sam Ku nemomin shi ku nemo min, yanda take maganar gaba ɗaya ba acikin hayyacin ta take ba wata maganar ma batasan tana faɗa ba,

Da sauri mamy ta jawota ta rungume ta itama tana kuka kamar ransu zai fita, ganin hakan yasa duk suka bawa kowa tausayi, ummy ce tace ta riƙe su tana basu haƙuri sannan tace momma tayi haƙuri yanzu za'a kira mata shi,
Ƙin shiru momma tayi ta cigaba da sun batunta saboda gaba ɗaya tagama susucewa bata cikin hayyacin ta daman ga damuwar Sam datake ciki kuma wannan yazo yaƙara faruwa shiyasa ta fice hayyacin loƙaci guda,

Da ƙyar da wayo da dabara akasa tayi shiru amma kallo ɗata zakayi mata kasan ba normal take ba.....,


"Papa da idanun sa suka kaɗa sukayi jawur tsabar tashin hankalin da yake ciki dan tashin hankali zai kira abun, yana zaune da mutane ashe duk da makiyan sa yake zaune kowa ashe da manufar sa akansa suna cin dunduniyar sa,


Kamar marar laka ajiki haka yake tafiya yazo har gaban ta ya tsugunna cikin wata iriyar murya da bazaka iya fassara tsantsar adadin damuwar da take tattare da ita ba, yace "me yasa SA'ADATU mai yasa me nayi miki arayuwa zaki cutar min da ahalina, daman duk zaman danke dake da zuciya ɗaya ke ba haka bane awajen ashe kina da mugun ƙudiri akaina, mai yasa zakuyi min haka mai na tsare muku, ɗan dakatawa yayi da maganar jin muryar sa na neman ɗauke wa,

Miƙewa tsaye yayi idanun sa na cikowa da ƙwalla cikin sanyin murya yace "mata ta wacce na muƙawa dukkannin yardata, ƙanina na wanda muke uwa ɗaya uba ɗaya, daku za ahaɗa baki a cutar dani wane irin son zuciya ne wannan,

Maama guri ta samuma ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido saboda daman tayi zargin wasu abubuwan da dama shiyasa koda hakan ta faru batayi wani mamaki ba abun da take zargine ya zama gaskiya dan haka yanzu saidai ta tazama ƴar kallo,

Itadai Ammah kanta na ƙasa bata ɗago ba bare tasan halin da wasu suke ciki saboda tsabar mutuwar zuciya ko ɗigon ƙwalla babu a idon ta,

Abdullah shima da kunya ta kamasa bai iya ɗagowa ba saidai shi yaji zuciyar sa ta karaya,

Hajjaju kuma ko akwalar rigar ta batayi nadama ba babban baƙin cikin ta shine rugujewar auren ƴarta da za ayi dan tasan babu shi tunda asiri ya tonu,

sauran mutum biyun kuma bata su ake ba daman babu wanda yayi musu magana saboda rashin matsayin su acikin gidan, ɗaya namiji ne wanda yake matsayin mai gadin gidan a zahiri a baɗini kuma su yakewa aiki, sai ɗayar macen kuma jakadiyar Maama ce (Gimbiya sabreena) wacce itama duk dangin su Ammah ne matar ƙanin tace da ya mutu sai kawai suka ɗauko ta suka ɗora ta tafara yiwa Maama aiki da da ita suke ta amfani gurin cikar buri kansu, shi kuma mai gadi saboda shige da fice shiyasa duk abun dake faruwa idan antambaye sa sai yace shi baiga fitar kowa ba alhalin kuma yasan komai, shi kuma amintaccen bawa ne agidan dan mahaifin sama anan ya mutu anan aka haifeshi son zuciya tasa shi suka rinjaye sa ya shiga cikin su akan idan komai ya kammala zasu ƴantashi kuma zasu bashi dama yafita yaje yayi rayuwar sa awani gurin tare da bashi maƙudan kuɗaɗe......,


"Meer ne ya tako zuwa tsakiyar falon ganin kowa baya cikin hayya cin sa saboda taɓa zociyoyin wasu da abun da yafaru kowa kagani ba nutsuwa a tare dashi,

Ɗan gyaran murya yayi tare da bin kowa da kallo, sannan yace "silent please, yanzu ba loƙacin kace nace bane yakamata kowa ya nutsu, zamu bar maganar zuwa gobe daman shiyasa na taraku anan saboda kowa yagani da idon sa, ba sai anyi masa dogon bayani ba, gani da ido yafi abaka labari,

"yanzu dare yayi ba loƙacin da zan baku zuwa gobe za'a sake zama, kowa zai iya tafiya yanzu sai zuwa gobe,

Da farko wasu sukace su zasu kwana anan saboda koda sun tafin ma ba iya baccin zasuyi ba gwanda kawai yai komai yanzu, saidai Meer yace musu hakan bazai yiyu ba kawai suyi yanda yace, basu san me yake shirya wa ba dole suka haƙura zama ya tashi, wasu suka kai kansu wasu kuwa saida aka kaisu dan bazasu iya tafiya su kaɗai ba,


Su Ammah na zaune a inda suke babu wanda ya iya motsawa saida suka ga kowa ya fita sannan suka ɗago zasu fara magana basu san Meer na gaban su ba hakan yasa sukayi shiru suka fasa faɗar abun da zasu faɗa,

Fadar ta rage daga shi sai a bokin nan nasa wanda yayi shigar boka, suka ɗaine aciki,

Meer nakan zaune akan kujerun daje ciki ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ɗagowa yayi ya kalli abokin nasa, da shi kuma hankalin sa yana kan waya,

Sunan sa yakira, yace "KHALID"

Ɗagowa yayi yana kallon sa tare da cewa "da girman kujerar ka,

Hararar sa yayi, baice masa komai ba yayi masa alama da ido kawai,

Hakan yasan ya Khalid miƙewa ya fita daga cikin fadar yana fita kuma ya ƙullo ƙofar ta waje, bai daɗe da fita ba sai gashi ya dawo,

Sai gashi yadawo tare da tiso ƙeyar Waziri da matar sa, turo su yayi ma suka ƙarasa ciki tare da faɗuwa aƙasa gaban su Ammah,

Yana zubesu yaƙarara fita, still dai bai daɗe ba yaƙara dawowa, hannu sa ɗauke da wata ƙatuwar jaka, ɗakin dake cikin masarautar ya shiga da jakar ciki zuge zif ɗinta yayi ya fito da wasu kwalabai ya ajiye su agefe, sannan yazaro wata leda da farin abu ajiki, sannan ya ɗauke jakar ya fito da ita tare da ledar mai farin abu aciki,

Yana fitowa yace "Sarauta gaba da baya sai kayi ko ba kaso, komai yazama daidai,

"Wai yaushe nafara wasa dakai ne bana son fa raini kasani ko,

Khalid yace "to sarki nayi shiru ayi haƙuri kar asa fadawa subi takaina,

"Hmmm kawai Meer yafaɗa yana miƙewa tsaye, yana naɗe hannun rigar sa,

Kallon sa yayi yace "step 1,

wasu mugayen bulale Meer ya ɗauko daga gefan sa wajen guda shida, sai ya jefawa Khalid guda uku ya ɗauki guda, uku cafewa Khalid yayi sannan ya ajiye ledar agefe,

Tun kan su ƙarasa kansu suka tarwatse cike da tsoron abun da zasuyi musu, amma tun kan suyi wani yunƙuri suka rafar musu,

kan kace mai kawai sun fara sauke musu kawai kan me uwa jawabi suka fara yi musu wankan jego da bulalen duk inda suka samu duka suke,

basu wani dake su sosai ba suka rabu dasu saboda a kwai step 2,

Khalid ne yace saura step 2 ko miƙo wannan ledar,

Wani kallo ya watsa masa mai kama da harara "yace waye zai taɓa wannan ledar bayan ka gama ban labarin ta kuma saikasaka ni in taɓa sude shiga daga ciki gaba ɗayan su sai ka aiwatar tunda kai kasan kan abun,

Dariya yayi masa yace matsoraci kawai, kuma wallahi idan baka bini

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login