Showing 126001 words to 129000 words out of 170049 words

Chapter 43 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7204

tare da kwasar ta aguje, suka fice daga cikin airport ɗin,

Tunda suka ɗauki hanya babu wanda ya iya furta koda da kalma ɗaya kowa yagama mutuwa da mamaki da al'ajabi musamman ma, Bossay abun yafi taɓasa, shi kuma Meer baiyi mamaki ba sosai, saboda daman tun kan loƙacin yana zargin hakan, sai kuma zargin sa yazama gaskiya dan haka abun bai wani ɗaɗasa da ƙasa ba,

Saida Meer yasa suka fara biya Hospital ɗin sa, ya ɗanyi dube duben sa ya duba wasu abubuwan, saboda kasan cewar ya kwan biyu bai zo ba, sai yaga komai yana tafiya yanda yakama ya, saboda wanda ya ɗora akai baya wasa wajen aikin sa, komai yana gudana yanda ake so, sai abun da ba'a rasa ba,

ya daɗe a cikin sannan ya fito, mai makon su ɗauki hanyar gida, sai ya kuma kaisu can gidan su, dake garin Abujan,

Nan suka je saida suka ƙara yin wanka, Meer yabawa Bossay wasu kayan, sannan yasa akayo musu order abinci sukaci suka ƙoshi, suka kuma hutawa suna tattaunawa akan wannan babban abun al'ajabin da ya daure musu kai, saida suka jira sukayi sallar Az'har sannan suka shirya sai hanayar kano, kuma duk wannan loƙacin da suka ɓata bayin Allahn nan cikin booth itama kuma ɗayar tun loƙacin da suka tsaya a hospital suka fito da ita suka mayar da ita wajen sauran,


Da farko Meer yayi niyar kawai ta wuce dasu station sai kuma, yafasa yaga ai sai yafi ace yakai su can kowa da kowa yagansu, kamar yanda aka saba tara mutane idan ankama masu laifi suma ayi musu haka sannan su faɗi abubuwan da suka aikata da bakin su kowa sai yafi yarda, gani da ido yafi abaka labari,

Tun suna kana hanya kamar yanda yayi loƙacin da zaikai Abban Ameesha gida, yace kowa ya hallara a fada, yanzu ma haka yayi ya kira yace a haɗa taro, kuma wannan taron yafi na koda yaushe ma domin shine taron ƙarshe yana so kowa yakasance yana nan, a haɗa kowa yara da manya, kar a cikre kowa,

Sunyi mamakin jin hakan shiyasa saida aka takura sa akan yanzu me yake tafe dashi yace adai jira dawowar sa, haka kuwa akai nan aka fara shelar sanar da taron a kasaka shi ƙarfe huɗu zuwa sama, kowa ya hallara,

Basu sauka a Kano ba sai wajen ƙarfe shida, dan koda suka ƙaraso cikin masarautar basu fito dasu ba, akace kawai abari sai anyi sallar magriba dan kar afara zama loƙacin sallah yayi,


(Todai loƙaci baya ƙarya komai ya zo ƙarshe yau zata faru ta ƙare............🙅,


____Damƙam aka cika cikin fadar dan kamar yanda Meer yace hakan kwa akai kowa saida ya hallara harda ƴan sa ido ma saida suka shigo cikin gurin,

Kowa yayi jigum jigum yana jiran yau kuma da wane abun al'ajabin Meer ya kuma zo musu dashi,


......Turo ƙofar akayi yayin da kowa ya maida idon ga ƙofar ana jiran me shigowa,

Meer ne ya shigo cikin takunsa da yasaba yi a koda yaushe,

Shi kaɗai ya shigo hannayen sa sanye cikin aljihu, fuskar nan tasa a ɗaure kamar yanda take, abun mamakin da mutane basu taɓa gani ba, har da glass a idon kuma baƙi yanda babu wanda yake ganin ƙwayar idon sa, amma daga yanayin sa ya isa yasa ka gane kamar ba lafiya ran maza ya ɓaci duk da shi daman koda yaushe a bacen yake, amma ma yau yasha bambam da sauran,

A tsakiyar mutanen dake cikin fadar ya tsaya yana bin kowa da kallo sannan ya gyara tsayuwar sa da kyau, tare da zare glass ɗin, yayi two eyes da wasu,

Daga ya kalli wannan sai ya kalli wancen, yayi wajen minti uku yana haka ya rasa ta inda zai fara yi musu bayani,

Ɗan gyaran murya yayi, yana ƙara kallon kowa sannan yace "nasan wasun ku sun san abun dake faruwa game da abun da yafaru a asibiti na kama yana ƙara ƙoƙarin kashe Uncle akaro na biyu mukayi nasarar kamasa bayan kuma ya ɗan samu duka, hartakai saida aka kwantar dashi a asibiti aranar kuma da muka kwantar da shi aka shiga har cikin asibitin aka ɗauke sa, todai tun jiya muke bincike akan sa, inda kuma Allah yabamu Sa'a mukayi ram dasu yayin da suke shirin barin ƙasar ma gaba ɗaya, ɗan dakatawa yayi sannan yaci gaba da cewa........

"Todai shi wannan da muka kama tunfarko shine ya kama Uncle nasan kunsan da haka, to amma abun duban shine da mukayi bincike shima a ƙarƙashin wata yake aiki bashi kaɗai bane yana da ogar sa, wacce kuma itace maƙasudin faruwar komai dan badan itaba da tuni abubuwa da dama basu faru ba, kuma shima da baishiga halin da ya shiga ba, da iyalen sa basu faɗa mawuyacin hali ba, duk wani abu da ya faru ya faru ne ta ƙasan ta ita take shirya komai, zamu iya cewa itace muguwar kuma munafuka me fuska biyu,

"Hmmm karde in cika ku da surutu, yanzu zaku gansu kowa ya gani da idon sa, sannan daga ƙarshe ina me bawa wasu haƙuri bisa abun da zasu gani idan ya ɓata musu rai ko ya taɓa zuciyar su to suyi saurin miƙa lamarun su ga Allah kar su bari sujawo wa kansu wata matsalar dan kan iya kaisu lahira, kaɗan daga cikin ku zasu iya kasancewa hakan, kudai yi haƙuri kubi komai a sannu, yana kaiwa nan yace...

"Bismillah shigo da su.....,

Bossay ne ya shigo tare da matar nan ƴar gayu, itace ta fara shigowa kanta a ƙasa, domin duk rashin kunyar ta ganin ɗunbin mutane sai yasa taji bazata iya ɗaga ido ta kalle su ba,

Tunda ya shigo da ita kowa yake bin matar da kallo babu wanda yasan suna ta mamakin daga inda take, can suka jiyo muryar mace tana cewa, Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, Dan Allah ku fita da ita bana son ganin ta zata iya aikata koma meye dan Allah ku fita da ita, bata da imani,

Da sauri Sam ya miƙe yaje kusa da ita, ya riƙota, tunda yaji furucin da take yagama fahimtar inda yaren nata ya dosa dan yana kallon matar yaga kamannin da suke,

A tsorace matar nan take kallon yarinyar da take cewa a fita da ita, tana me mamakin abun da ya kawota nan, tayi maganar a zuciyar ta tare da sakin ɗan ƙaramin tsakin ta ƙaicin ganin ta....

Kallo sai ya koma kansu.

Meer ne yace "wacece wannan ɗin ya faɗa yana kallon Sam da yaga ya riƙeta,

cike da ɗan damuwa Meer yace "Mahaifiyar tace, kar ku damu da wannan kuci gaba da abun da kuke,

yana gama maganar yajawo ta suka zauna yana toshe mata baki yana bata haƙuri da cewa tayi shiru,



Meer ne ya kalli Bossay yace "shigo da sauran,

Komawa Bossay yayi sai gashi ya shigo dasu kamar yanda suka samesu acan airport haka ya shigo dasu, Dadyn Rasheeda sanye cikin wasu kayan da Meer yasa ya sauya su, saboda waɗancan wani gurin duk ya fara yagewa saboda jan da yayi masa aƙasa,
Ɗayar matar kuma sanye take cikin niƙab ɗinta, kamar yanda tayi acan,

Daram...Daram Daram gaban wasu yabada sauti loƙacin da suka shigo ciki kollo ɗaya wasu sukayi mata suka gane ta amma kokonta da rashin yarda yasa basu gasgata hakan ba,

A tsakiya suma suka tsaya Bossay sai ya koma bayan su, Meer kuma ya ƙaraso gaba inda suke,

Sunkuyar da kai matar tayi dan ita kanta ta gama shan jinin jikin ta,

Zagayawa Meer yayi ta bayan ta dan yabawa kowa damar samun ganin ta da kyau,

A hankali ya ɗora hannun sa akan niƙab ɗin, a hankali ya shiga ɗaga niƙab ɗin har yagama yaye sa gaba ɗaya fuskar ta ta bayyana a bainan nasi,

"NOOOO........!!!!! ya faɗa tare da yanke jiki ya faɗi agun,

Cike da tashin hankali da mamakin da yagama kashe ta a tsayen da ta miƙe, loƙaci ɗaya jikin ta ya ɗauki ɓari, hawaye har yagama wanke mata fuska dan kamar famfo haka suke sauka daga idon ta😭😭😭😭😭😭😭

Hannu ta ta ɗaga tashiga nuna ta cikin wata iriyar murya da kanaji kasan tana cikin tsantsar damuwa da tashin hankali,

Muryar ta har saƙewa take ga kuma karkarwa da take ba iya muryar bama har jikin karkarwa suke,🥺

Cikin sarƙarƙiyar muryar ta wacce da ƙyar ta iya buɗe baki, ta tattaro kalmomin da suka maƙale mata a maƙogaro cikin rarraba sunan tace... "D..D...DA...D...DDAA...!!!!!!!

Tana faɗa ta saki wata iriyar ƙara tare da zubewa agun, ɗif ta ɗauke wuta tare da zama sumammiya,🥺🥺.........

To nima dai dole in ɗauke wuta anan gurin dan al'ajabi bazai bari in iya ci gaba da ɗauko muku rahotan nan ba, sai an kawon ɗauki da yayyafin ruwan sanyi ko zan samu in farfaɗo, zuwa gobe........,, Kuma Allah yasa idan na farfaɗo acemin abun da naji ba gaskiya bane mafarki nake, kunji dan Allah ku gayan gaskiya kodai nice banjiyo daidai ba ne..🥺🥺😭




  
[19/11, 10:23 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                    *_🅿️46_*
                  

...Cikin sarƙarƙiyar muryar ta wacce da ƙyar ta iya buɗe baki, ta tattaro kalmomin da suka maƙale mata a maƙogaro cikin rarraba sunan tace... "D..D...DA...D...DDAA...!!!!!!!

Tana faɗa ta saki wata iriyar ƙara tare da zubewa agun, ɗif ta ɗauke wuta tare da zama sumammiya,🥺🥺.........,

Da sauri Dadda tayi kanta zata taɓata, Meer yayi saurin tare ta, yana binta da wani mugun kallo yace "kar ki kuskura ki taɓata, ko kinaso ki ƙarasa kashe tane?

Yayi maganar yana juyawa yayi saurin ƙarasa wa gurin Ameesha ya ɗago ta, ya ɗorata ajijikin sa,

Can ɓangaren kuma Abuu da Papa sukayi saurin komawa gurin Abban Ameesha da shima yake a sume,

Da sauri wasu daga cikin fadar sukayi saurin miƙawa Meer ruwa, da su Papa,

Meer ne ya yayyafawa Ameesha amma bata farfaɗo ba, su Papa kuma suna yayyafawa, Abban Ameesha ya farfaɗo,

Yana farfaɗowa ya fara bin su Papa dake tsatstsaye akan sa, yana kallon su ɗaya bayan ɗaya, can kuma saiga hawaye  ya fara sakkowa ta gefen idon sa, ko motsi yakasayi, ya ƙame kawai a kwancen,  yana kallon su, yadai farfaɗo daga suman da yayi amma har yanzu bai dawo daga shock ɗin da ya shiga ba,

Ganin kamar baya cikin hayyacin sa yasa, Papa ya fara yi masa addu'a yana tofa masa, sannan ya kamo sa ya zaunar da shi, da kyar aka samu ya dawo cikin hayyacin sa, amma yana dawowa ya fashe da kuka, yana cewa dan Allah idan mafarki nake ku tasheni daga wannan mummunan mafarkin,

Dan Allah kuce min abun da naji nagani ba gaskiya bane, dan Allah ku taimake ni ku gaya min gaskiyar abun dake faruwa, danna san ba daidai nake jin komai ba, ƙwaƙwalwa ta tafara samun matsala, ta fara jiyo min wasu abubuwan da ba daidai ba,

Shiiiiit... Ya isa haka ka kwantar da hankalin ka dan Allah kadaina waɗannnan maganganun duk abun da kaji kuma ka gani, babu ƙarya aciki, komai gaskiya ne dan haka ka kwantar da hankalin ka kar ka sanyawa kanka wani ciwon. Cewar Abuu yafaɗa yana me rarrashin ƙanin nasa,

Ameesha kam har zuwa yanzu bata dawo hayyacin taba, Meer yana kanta amma taƙi ɗaukan ta yayi yamaida ita can bayan kujerar karagar mulki, ya kwantar da ita agun,

Sannan yaƙara yayyafa mata ruwan tare da kamo hannun ta, cikin tafin hannun ta ya ɗora nasa yafara murza mata yana hura iska ajiki, har da su tafin ƙafarta yana murzawa amma duk da haka tayi nisa bata motsa ba,

Cikin ɓacin rai ya ɗago daga gurin daga inda yake ya nuna DADDA da hannu cikin ɗaga murya yace wallahi idan wani mugun abun yasamera ko kuma ta rasa ranta ta sanadinki, wallahi wallahi sai na kashe ki da hannu nagaya miki, duk abun da yasame su sai kingane kuranki,

Wani irin kuka me tsuma zuciya Dadda ta fashe dashi, tare da tsugunnawa agun, cikin kukan tace wallahi ni ban aikata komai ba, babu abun da nayi musu, ku barni inje wajen jikata, wallahi ina ƙaunar ta,

wani irin ƙaton abu Meer yaji wani abu yazo masa wuya, ya tsaya watakon ɗan rainin hankali tasan me ta aikata amma take irin wannan maganar kodan taga bai taɓa ta bane har yanzu shiyasa tasamu bakin yin magana,

A fusace ya dawo wajen yazo gaban ta, yana binta da wani irin matsiyacin kallo,

Ɗan tsugunnawa yayi tare da ɗago kanta cikin wata iriyar murya yace "bakiyi musu komai ba, kike faɗa ko,

Yanda yayi mata maganar a hankali yasa tayi tunanin ko ya yarda da abun da ta faɗa,

Sai kawai ta ɗaga masa kai, tare da cewa "EH...

Girgiza kai yayi kawai tare da miƙewa tsaye, cikin yanayin rainin hankali da gatse, yace mata,

"Ok taso kike to, na yarda,

Da saurin ta ta miƙe, saidai tana gama miƙewa bazato ba tsammani taji wani irin gigitaccen mari wanda saida yasa tayi juyi ta dawo,

Zai ƙara mata wani kenan, Abban Ameesha yayi saurin riƙe shi yace "dan Allah kar rabu da ita, bakaji me tace ba, bafa ita bace ni nasan daman umma bazata taɓa yi mana haka ba, kundai saɓa bincike ne amma ni nasan ba ita bace,

Cikin kuka Dadda tace "Eh, Eh bazan taɓa yi muku haka ba, ka ganar dashi gaskiya kagaya masa ko ni wacece, nice mahaifayar ka, da na riƙeka, tun kana yaro, nice uwar Nooryn ka, taya zan iya cutar daku, kaifa sirirkina ne, da zan cutar daku ai duk da bankasan ce cikin wannan halin ba, amma tsawon loƙaci nakasance cikin talauci na zauna, daga ni sai ƴarka, sanadin ka narasa ƴata na rasa mijina, na rasa dangina, duk san saboda, saboda shigowar ka rayuwar mu, amma duk hakan bai isaba, sai kun zargeni me yasa zaku min haka ne yasa? Ta faɗa tana fashewa da kuka mai ban tausayi,

Rungume ta Abban Ameesha yayi cike da tausayin ta, yace ni nasani, bazaki yi hakan ba, ni bazan taɓa yarda ba,

Raba jikin sa yayi danata, yana kallon Meer yace "dan idan danni ake wannan tuhumar tata, abar wannan maganar koma itance na yafe komai da komai tunda na haɗu daku ni yanzu duk wata dukiya bata da amfani awajena burina kawai inkasan ce tare daku cikin farin ciki,  dan Allah abar maganar nan,

Haɗe rai Meer yayi, yace "Uncle wannan wace irin magana ce kake, taya kake tunanin sharri ake mata ko ƙazafi,

Idan sharri akeyi mata, me ya fitar da ita daga cikin gidan nan? sannan me yasa zata bar ƙasar? Meye haɗin ta da wannan mutumin, kuɗaɗen dake cikin jakar ta, waya bata su?

Uncle kayi tunani, naji indai ta amsa duk waɗannan tambayoyin da nayi mata, ni kuma zan yarda za'abar ta babu wanda zai kuma tada zacen tunda haka kace,

Shiru Abban Ameesha yayi amma duk da haka zuciyar sa takasa gasgata hakan,

Cikin kuka tace, "wallahi ni banyi haka dan saboda wannan case ɗin ba, daman tuntuni ina da shirin barin gidan nan dan banga me nake muku ba shi yasa na yanke shawarar nesan ta kaina da ku, nasan idan nagaya muku baza ku taɓa bari na in tafi, ni kuma nagaji da rayuwar gidan, sannan wannan mutumin ni bansan me ya aikata muku ba, bansan shine wanda kuke nema, maƙocin mune shine yake taimaka mana loƙacin da bamu dashi, shiyasa yanzu da natashi tafiyar naje na samesa nagaya masa matsalata yace zai taimakamin, sannan ya haɗani da wannan matar yace idan nashirya inyi mata magana, shiyasa ka ganmu tare amma ni bansan shine akwance a asibiti ba, kawai nagansu tare shiyasa muka shirya tafiyar tare,

"Kaji ko? kaji abun da tace rashin fahimta ce kawai,

"Oh da gaske, gaskiya ne na yabawa ƙoƙarin ki,

"Tom aje mun yarda da hakan, kafin a bar maganar ina zuwa,

Wata waya ya zaro tare da nunawa Abban Ameesha yace "zaka iya faɗo min number ka, ta layinka da ka taɓa yi,

"Cike da fara gajiyawa da tambayoyin da yake tayi, yace masa "Eh, yafaɗa tare da karanto masa,

Nuna masa wata number yayi da akayi saving ɗin ta da Ummana, yace wannan number waye,

Kaɓa yayi yana dubawa tare da ɗan karantatawa, sai ya ɗago yace wannan number tace mana gashi nan nasaka Ummana, a ina kasamu Sim ɗin,

Karɓa Meer yayi tare da dannawa number kira saikwa ga ringing a cikin aljihun sa, sai ya zaro wayar yace ka gani, to number ta har yanzu tana aiki, mu kuma anan ta nuna mana ko wayar ma bata da ita alhalin tana sarrafa ta a ɓoye,

Sosai Abban Ameesha ya shiga wasiwasi, amma bai nuna hakan ba a fili yunƙurawa yayi zaiyi magana,

Meer yayi saurin dakatar dashi, sannan yace "Uncle kayi shiru ka saurare ni da kyau duk wannan maganar kake yi bamai yiyuwa bace, dan baza'a taɓa barin taba kamar yanda kake so, kabari zangaya maka hujjoji na, idan nagama sai ka yanke hukuncin da kaga ya kamata..

"Da farko a labarin da ka bamu da kuma yanda kazo kana tambayar ina sauran suke, alamu sun nuna bakasan da mutuwar matar kaba, saɓanin nata labarin da ta bayar tace loƙacin da ake neman ka za'akashe ka, loƙacin haihuwar yarinyar ku ta rasa ranta wajen haihuwa,

A zabure Dadda ta ɗago zatayi magana yace "kimin shiru kar nasake jin bakin ki, har sai nagama faɗar abun da zan faɗa idan kuma ba haka ranki zaiyi mummunan ɓaci,

Yanzu kam Abban Ameesha kasa cewa komai yayi,

Meer yaci gaba da cewa, "na farko kenan, sannan na biyu, me yasa mutanen da tace suna neman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login