Showing 153001 words to 156000 words out of 170049 words
kanta gefe kamar bata san me yake nufi ba, murya ciki ciki tace "kamataa in fito ai ko takan ka zanbi kawani babbake hanya,
"Idan kin shirya bi takan nawa bismillah ai hakan ba laifi bane girmanki ne, in tsugunna? yaƙarasa maganar cikin kwantar da murya, yana ɗan leƙen fuskar ta,
Shiru tayi masa dan bata da kuma baƙin da zata ƙara yi masa magana,
"LILY....
Da sauri ta juyo tana kallon sa jin sunan da ya kirata dashi,
Wani ƙayataccen murmushi ya ƙara saki har haƙoran sa na bayyana, tare da ɗaga mata gira yana girgiza kai...
Ita kam mamaki ne ya kusan kashe ta a a zaune dan bata taɓa tsammanin jin wannan sunan a bakin saba, domin akwai wanda yake kiran ta da sunan a makaranta, amma dai bata taɓa ganin saba, saidai yabada saƙo akawo mata ko kuma yaita turo mata saƙo ta waya, sau ɗaya ya taɓa kiran ta awaya kuma ya kirata da sunan tace ita bata son sunan meyasa zai ringa kiran ta da hakan, sai yace saboda ita yarinya ce kuma ƙyaƙƙyawa dan haka sunan yafi da cewa da ita, kuma hakan shi bazai iya kiran sunan taba kai tsaye dan haka tayi haƙuri zai ringa kiran ta da hakan, aranar sun daɗe suna waya tana taso yagaya mata ko shi waye amma yaƙi sai yace mata har sai sun saba kuma shi ba wai auren ta zaiyi ba saboda yasan ita matar aure ce, idan sun saba zaigaya mata, aranar itama ta ciccimasa mutunci tace kar ya sake kiran ta yasan tana da aure kuma yake kiran ta, kar ya sake turo kuma kar ya sake turo mata saƙo ko wane iri ko ta wata ko gift tana gama faɗa masa haka ta kashe wayar tundaga ranar bai kuma kiran ta ba, kuma bai kuma aiko mata da sakon ba kamar yanda ta buƙata, dan haka ita tama manta dashi kwata kwata arayuwar ta sai yau da Meer ya faɗi sunan tayi saurin tuna wancen ɗin,
"Lily magana fa nake.....
ƙara ɗagowa tayi ta kalle sa, so take ta tambaye sa a ina yasan sunan, amma takasa,
Hannun ya ƙara miƙa mata tare da cewa tunanin banaki bane idan kuma kina da tambaya mu fara shiga saikiyi, nagaji da tsayiwa,
Ɗan numfasawa tayi sannan tace "ka matsa dan Allah,
Kallon ta yayi sannan ya janye hannun sa tare da matsawa kamar yanda ta buƙata yana matsawa ta zuro ƙafafun ta, tare da jawo mayafin ta ta rufa a kanta, sannan ta ƙarasa fitowa gaba ɗaya kallon gurin tayi sai tagama ai ba part ɗin su yakai taba, juyawa tayi tana tunanin tantance ina ne,
Tana tsayen bata gama tantancewar ba, taji anyi sama da ita,
Riƙon jarire yayi mata sannan ya fara tafiya da ita,
tun tana ƙoƙarin sauka har ta haƙura dan tasan komai zatayi masa ba sauke ta zaiyi ba,
yana tafiya da ita yana kallon fuskar ta, har suka ƙarasa bakin wata ƙofa hannu yasa ya tura ƙofar tare da yin sallama ya shiga ciki, ɗaga ta yayi ya ɗorata akafaɗa sannan ya rufe ƙofar tare da saka mata muƙulli ya ƙulle ƙofar falon.............
*****************
A can ɓangaren ƴan denner guri ya cika tamƙam da muta ne ƴan mata da samari, inda MC yake ta koɗa amare da angwayen su, sannan yana kiran ƴan ɗayan kujerar da be gansu ba, akace suna ƙarasowa, tun ana jiran ɗayar amarya har aka gaji, nan su Azeema suka rikice aka fara neman inda amarya Ameesha take amma ba ganta ba, can gida suka jira ko tanan aka ce musu bata nan, dukan su mamaki ne ya kamasu da rashin zuwan ta gurin,
Saboda an riga an haɗa mutane ba ayi abun da za'aji kunya ba, dan wasu ma basu san ana cigiyar wata ba, gaba ɗaya babu kuzari ajikin su, hankalin duk sai ya rabu gida biyu,
Angwaye kam sai sharholiyar su suke, kowanne bakin sa kamar gonar auduga, saboda su a tunanin su ko fasa zuwa tayi saboda ita daman tana da auren ta tuntuni kuma mijin ta baya nan shiyasa sukayi zaton dalilin da ya hanata zuwa kena, dan haka babu wata damuwa atattare da su, sai murnar su kawai suke, nan aka fara gudanar da taro, yanda aka tsara sa, masu rawa sunyi, masu yin drama suma sunfito sunyi, sun tsara abubuwa da dama kuma duk saida aka gabatar dasu, sannan aka fara bawa ciki haƙƙin sa a kaci a kasha akai hani'an kowa ya cika tunbin sa, dam, daga nan kuma aka dawo aka ƙara cashewa, wajen ƙarfe shaɗaya aka rufe guri da addu'a aka sallami kowa da kowa,
Ga ba ɗaya aka tattara kowa ya ɗauki wacce ya kawo aka taho gida, a hanya wasu daga cikin su Azeema suke gaya wa mazan abun dake faruwa na rashin zuwan Ameesha kuma ance musu bata, gida barin dai zancen sukayi acewar su bari su koma gida inyaso sai a ƙara bincikawa ai baza ta ɓata ba,
Hakan yasa babu wanda ya ƙara tada maganar har suka ƙaraso gida.....,
Bayan sundawo an sauke su a ɓangaren da aka ɗauke su sannan suka ƙara kiran su Maama suka gaya musu bafa suga Ameesha ba har yanzu, nan suma suka shiga neman ta, tun abun ana ɗaukar sa kamar wasa har abun yazama anfara shiga damuwa,
Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, annemi Ameesha an rasa, har Meer aka kira amma wayoyin sa duk akashe ba wacce take shiga, daman zargi ne kawai sun sanma ba yanda za'ai yasan inda take tunda bai dawo garin bama bare ayi tunanin ko za'asame ta a gunsa, tunda aka kira kuma akaji a kashe aka ajiye batunsa...
Kowa ya shiga tashin hankali, su Dadda har anfara kuka, inda Allah ya taimaka ma Abban ta da maman suna asibiti Maman Ameesha ba lafiya tunda safe ta fara na ƙuda amma ba asanar da kowa ba aka ci gaba da shagalin biki,
Dadda abunne ya haɗar mata biyu, ga ɓatan mata, ga kuma tunanin ƴar ta da take cikin halin na ƙuda,
Har gurin ƴan sanda aka bada report ɗin gidan biki gaba ɗaya ya hargitse, amare suma harda kukan su, kuma an bincika duk moto cin da akake dasu an gansu babu wacce babu ita, ƙawar nan tata kuma da ta raka ta, ta bada shaidar a gaban ta ta shiga mota, saidai kawai batasan kallar motar ba bare kuma wanda yake cikin motar,
A bokan angoma duk antarasu, ana ta tuhumar su tare da tsoratar dasu idan ba a ganta ba zuwa gobe duk sai ankama su an ɗaure,
A bundai ba daɗin ji, daga murna an koma tashin hankali,
Wasu har sun fara danasanin zuwa dan suna mamakin yanda hakan ta faru,
Kuma duk wannan cigiyar da akeyi Khalid yana gun hasali ma yana cikin masu tuhumar abokan ango akan ɓatan ta, sai kace be san inda take ba, daman kuma suna sane suka shirya hakan da Meer.........,
Wajen ƙarfe sha ɗaya da rabi aka sanar dasu Maman Ameesha ta sauka lafiya da santaleliyar ƴar ta mace, amma tashin hankalin da suke ciki ya hanasu zuwa da ƙyar Maama ta daure, aka tafi da ita asibiti,
Su kuma sauran aka cigaba da fafatawa wajen neman Ameesha........
_____*MEER*
Bai sauke ta a ko ina ba saida ya shiga da ita wani ɗaki sannan ya sauke ta akan gadon dake cikin ɗakin, sannan ya koma shima ɗakin yasa ka masa muƙulli sannan ya dawo wajen ta,
Miƙewa tsaye tayi da sauri cike da tsoron abun da taga yanayi, yaza'ayi ya kawo ta nan gurin da batatasan ko ina bane sannan ya ringa ƙulle ƙofofi, me yake nufi da hakan....?
Ki tashi kije kiyi wanka ki wanke wannan abun fuskar ki,
Wani taƙaici ne ya taso mata, wai tayi wanka anan,
Kamar ta fashe haka take ji, cikin jin haushi tace "Ni ka mayar dani wajen Dadda, ba wankan da zanyi anan,
"Ok fine, sai ki zauna a haka, yana faɗar haka ya samu waje ya zauna, sai ya kuma cewa ga hanya nan fita,
Kallon sa tayi sannan ta kalli muƙullin hannun sa, tace "to ban muƙullin,
"Ƙwaci inkina da ƙarfi, na ƙarfi ne,
Rasa inda zata tsoma ranta tayi, har yanzu ta kasa gane kansa, duk waɗannan abubuwan bata san dalilin sa nayi mata su, bata san yaushe ya koyi magana ba har haka,
Ɗaga key ɗin yayi yana karkaɗa sa a sama, ta gefen idon sa take satar kallon so take ta shammace sa ta fisge,
Gani tayi kamar wani gurin yake kallo hakan yasa tayi saurin kai hannun ta zata fusge yayi saurin janye wa, yana cewa daman har yanzu ke yarinya ce, to ga dama ɗaya indai zaki iya ni kuma wallahi zan barki ki fita kinji na rantse,
Hararar sa tayi tana turo baki tare da ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa, tana harɗe hannun wanta akan ƙirjin ta alamun na shirya zanyi,
Jinjina kai yayi sannan yace "Alright, kin shirya kenan, shiri haka da sauri, to shikenan zan ɓoye muƙullin indai kin iya nemosa kuma kinɗakko to kije, sannan ina da sharaɗi idan baki yi ba ni kuma zan riƙeki daga nan har kwana biyu, kuma sai kinyi duk abun da nake so, kin yarda?
Ƙara haɗe rai tayi sannan ta ɗaga masa kai,
Sai yace "ba kai zaki ɗaga ba, ki amsa min da bakin ki, dan infi tabbatar wa,
A ƙufule tace "Eh na nayarda,
Sanin abun da ya shirya tunkan ya aiwatar da abun ya shiga yi mata dariyar mugun ta, amma duk da haka bata kawo komai arai ba,
Tana jiran taga ya tashi ya tafi inda zai boye ɗin sai kawai taga ya faɗa kan gadon yayi rigingine, sannan ya ɗaga muƙullin daman ƙaramar rigace a jikin sa sai kawai ya ɗaga wandon sa ya jefa muƙullin a cikin sannan yace "U can start,
Da sauri ta juyar da kanta, gaban ta na faɗuwa, daman wai abun da yake nufi kenan me yasa zaiyi mata haka,
zaune ya tashi yana kallon bayan ta, cikin wata iriyar murya yace "na baki nan da minti goma idan baki yi, ba ni kuma nawa zai fara, dan haka zaɓi ya rage naki kuma dai kinsan bazaki karya min alƙawari ba, sai kin cika min shi, dan haka zaɓi ya rage naki, loƙacin ki zai fara daga yanzu, agogon hannun sa ya kalla, yace "yanzu ƙarfe sha ɗaya saura minti biyar dan haka 11:05 biyar loƙacin ki zai ƙare nawa kuma zai fara,
Gaban ta taji ya fara faɗuwa, tunanin mafita ta shiga yi, tana tsaka me wuya yanzu yazatayi, ko za'atara mata duniya akai bazata taɓa saka hannun ta"a inda yasaka ba, kuma har ga Allah bazata taɓa bari ta zauna anan ba har tsawon kwana biyu...,
"Saura mintuna bakwai har kinci 3 minutes,
wayyo Allah na ta faɗa aran ta, wata dabara ce ta faɗo mata, dan haka sai ta juya tare da ɗan sakin fuskar ta, kamar ba ita ba, wai ita zatayi masa wayo,
"Cikin kwantar da murya harda ɗan karya kai tace "kasan me ni bazan iya ɗaukowa ba, na yarda zan zauna amma dan Allah kabarni inji in fara ɗauko kayana, sai in dawo kaga fa daman koda ace hakan bata faruba daman gobe za a kawo ni, kaga sai mita zama bama kwana biyu ba, ko kwana nawa kake so zanyi, amma kaga anan banda kaya, kabari inje indawo, Allah zan dawo ka yarda dani kaji yaya, ta ƙarasa maganar tana ƙara kwantar da kai, dan taga alamun inba hakan tayi masa ba ita zata sha wuya a banza,
Miƙewa tsaye yayi yana matsowa gaban ta, yana binta da kallon rainin hankali yace "oh dan Allah da gaske, sai kuma gashi ba kece babba na riga ki zuwa duniya, bare kiyi min wayo, waye zai kawo ki ai kin riga kin shigo kenan,
"Allah da gaske kaya zan ɗauko,
Girgiza mata kai yayi tare da cewa "no need akwai waɗan da zaki sauya ai duk wani abu ma dakike buƙata akwaishi, kar ki damu, amma idan kinaso kifita zaki iya ɗauka nima kuma nayi miki alƙawari da kaina ma zan mayar dake,
"kamar ya da kayan da zansaka bangane ba,
Bai bata amsa ba kawai ya jawo hannun ta sannan ya shiga janta ɗan wani lungu ya shiga da ita, suna shiga ya tsayar da ita a gaban wardrobe ɗin, tare da buɗe ta, da hannu yayi mata nuni da ta kalla,
kallon wardrobe ɗin tayi taga yanda take fal da kaya kuma duk na mata, mamaki ne ya kamata ta yanda akai ya tara kayan mata haka kuma duk ƙananun kaya ne aciki,
Murfin gaba ya buɗe shima duk kayane a ciki amma yanzu manya ne aciki, haka yai ta nuna mata kayayyaki, harda su takalma da, tayi mamaki sosai ganin kayyakin,
Bayan ya gama nuna mata, ya jawo ta suka fito daga gurin sai yace "kinga ba kayan da zaki fita ki ɗauka, ga sunan,
Shiru tayi dan tarasa amsar da zata basa, yagama kashe mata baki, ba wata dabara kuma da zata ƙara yi masa dole tayi haƙuri ta lallaɓasa ayi kwana biyun ya sallame ta tafi in bahaka ba kuwa tasan zatayi biyu babu ne,
"Hmmmm yanzu dai kije kiyi wanka zan ɗauko miki kayan da zaki saka,
"A'a basai ka ɗauko ba nima ina da da hannu, tana faɗa masa haka ta nufi inda suka, baro dan wankan take buƙata amma da bazatayi ba, kayan jikin ta duk sun takura mata bata saba zama da suba, ga kwalliyar da akayi mata itama duk jinta take wani iri,
Inda taga hijabai nan ta buɗe ta zaro ɗaya sannan ɗaya sannan ta fara sakasa, ta cikin hijabin ta cire rigar jikin ta ta ƙasa tare da cire komai na jikin ta daga ita sai hijabin haka, ta fito tana kakkare jikin ta batare da ta kalli inda yake ba ta wuce inda take da tabbacin shin bathroom ɗin,
binta yayi da kallo yana jinjina kai da kuma mamakin yanda take yin wasu abubuwan gana ɗaya ta sauya itama, kamar ba itaba, haka yake ganin ta idan yana tuna yanda take shekara huɗu baya, yana mamakin girman da ga ƙara, tashi yayi yafita daga ɗakin amma duk da haka saida ya rufe ta waje, kayan abincin da yasa aka kawo masa falo da yayi order tunkafin suzo, yasa Khalid ya kawo masa part ɗin, ɗaulo su yayi sannan yaje kitchen ya ɗauko plate da cups da spoon ya fito, ɗakin ya koma, har yanzu bata fito ba,
Bayan ya ajiye shima sai ya hau cire kayan jikin sa daga shi sai ɗan ƙaramin wando, shima cire sa yayi ya ɗaura towel sannan ya zauna a bakin gado yana jiran fitowar ta...
Bai daɗe da zama ba sai gata ta fito, tunda ta fito ya zuba mata ido, ita kam tana fitowa ta gansa babu riga tayi saurin janye kanta bata ƙara kallon inda yake ba ta nufi inda zata saka kaya,
Har lumshe ido yake loƙacin da ta juya baya yabi bombom ɗin ta da kallo, yaga yanda suke yawo ta cikin hijab ɗin ji yake kamar suna jansa, har saida ta wuce ciki sannan ya daina kallon ta, daurewa kawai yayi ya tashi ya shiga wankan.....
Koda Ameesha ta gama shiryawa kasa fitowa tayi daga gurin saida ta loƙa taga baya nan sai tayi sauri ta fita, dabarar neman muƙullin ta shiga yi,
Wajen tasa wardrobe ɗin taje ta fara bubbuɗe su tana dubawa amma bata gansa ba, ɗakin taci gaba da duddubawa,
Rasa inda ta ya ajiye tayi kamar ance mata ta ɗaga filon kujerar dake ɗakin tana ɗagawa ta gansa cike da murna takai hannun zata ɗauka taji anriga ta ɗaukewa,
"Kassh ta faɗa tana dafe goshin ta, cike da jin haushin rashin dubawar da batayi ba tun farko, da tuni ta ɗauka ta fita,
"Haka mukayi dake farautar sa kike daman, kasa ɗaugowa tayi ta kalle sa, saboda taji kunyar ka matan da yayi, ga kuma yanayin da yake daman bazata iya kallon sa ba,daga shi sai towel,
Hannu yasa zai ɗago fuskar ta tayi saurin matsawa baya,
"Hmmm kawai yace sannan ya nufi wajen drawer ɗin sa, jallabiya kawai ya ɗauka yasaka,
Sannan ya ɗauko prayer mat ya shimfiɗa musu, sannan ya hau, yace "kizo muyi sallah,
Daman tayi alawala sai kawai ta taho, sallar isha'i yafara jansu sannan ya ɗora da nafila bayan sunyi, yace ta matso gaba, ƙin motsawa tayi da farko Saida ya haɗe rai zai nuna mata asalin kalar sa da tafi sanin sa da ita, sannan tayi saurin matsowa, dafa kanta yayi kamar yanda yake a musilin ce yayi mata addu'o'i sannan ya ɗora mata sa wasu tambayoyin, tana ta kunbure kunbure da turo baki da haka take basa amsa har suka gama,
Ɗan satar kallon sa tayi taga dai har yanzu ransa a haɗe kamar de yanda tasan shi ada haka ya koma yanzu badan bama da tace yaso yafi daɗin, tana mamakin sa, mutum sai kace me aljanu kamar bashine ɗazu ba,
A bincin ya jawo musu a gaban ya ajiye su sannan ya buɗe ledar take away ɗin yafara buɗewa me ɗauke da fried rice da take ƙamshi, sai ya buɗe wata ledar me ɗauke da banƙararrun kaji, ɗauka yayi ya ɗora akan abincin sannan ya ɗauko holondia ya zuba shi a cikin cups ɗin, sannan ya tura mata su gaban ta, ko uffan baice mata ba,
Itama kuma bata ɗauko ba kuma bata ce komai ba,
Wayar sa ya ɗauka ya shiga daddanawa, wajen 5 minutes sannan ya ajiye wayar tare da ƙara kashe ta gaba ɗaya, sannan ya ɗago ya kalle ta, yana ɗagowa kuma suka haɗa ido, arashin sani itama ɗagowar ta kenan da niyar taga me yake sai kuma suka baɗa ido dashi, sai tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa, saboda wani banzan kallo da ya watsa mata loƙacin da suka haɗa idon,
Cike da muryar isa da taƙama irin dai tasa ta