Showing 144001 words to 147000 words out of 170049 words

Chapter 49 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7225

kam sunbatun ya shigayi akan me yasa za'ayi masa haka bayan ansan shi yake sonta amma shine za'a aura mata, shikenan ancuce sa ankashe shi bazai taɓa aure ba, yasan ƙarshen sa yazo mutuwa zaiyi idan bai rayu da ita ba, kuka kam kamar ƙaramin yaro haka yaringa yi,

itama kuma antaɓo mata inda yake mata ƙaiƙayi nan ta shiga daru itama akan sai ansa Meer ya sake ta dan baza ta zauna da shi ba, da suna rufawa juna asiri akan sun sa santa junan su, yau sai asiri ya tonu, kowa saida ya shaida rashin son da basuyi,

Dadda da batasan da auren ba daman tace meyasa za'ayiwa jikar ta auren dole to kuwa sai an sake ta tunda bataso, rikici yaso ya ɓalle Dadda itama ta dage sai an sakar mata jika,

Sude su Maama Abban Ameesha basu iya cewa komai ba kowa jan bakin sa yayi yai shiru,

Papa da yaga yarinyar bata so kuka take kamar ranta zai fita, kuma shi yafi son kwanciyar hankali baya son tashin hankali dan shi tun farko ma yaso yace asoke auren sai kuma yaji ance sun sa santa junan su shiyasa ma kawai tabar maganar sai kuma yanzu yaji aka sun haka, da haka sai yace.....

To shikenan indai basa so za'a warware auren dan haka Meer ya sake ta, kowa ta amin ce, Meer yana kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana danna wayar sa inka kalle sa sai ka rantse baya cikin falon duk wannan abun dake faruwa, ko a jikin sa,

Papa ne ya kalle sa yace "babana kaji meke faruwa ko ka sake ta dan Allah ko hankalin ta zai kwanta, kaga yanda take kuka,

Ai baba kamar yayi magana da gini, har saida ya kuma yi masa magana, Maama tayi masa, dan itama yanzu ta saduda ta haƙura da auren, baki tasa itama tace "Babana magana ake ma kasaƙe tan kawai tunda nasan kaima bakaso, kar mushiga haƙƙin ku,

Abuu ne yace "Haba Maama wannan wacce irin magana ce kuke yi, ai ba ayi haka ba, ni ina ganin kawai abarsu, idan akace su rabu su suke gaba damu ma kenan, bamu isa muyi musu abu ba suyi mana biyayya ba,

"A'a fa Abu kaman ta a yanda ka auro ni ko kamanta nima iyayena basa so na biyo ka, kaga kwa tunda banyuwa nawa biyayya ba, kar kaga laifin wani in yaƙi yi, daman abun haka yake kama tudeeni tudaan, duk abun da kayi sai anyi maka, duk dani da dalilin su na hanani auren ka, amma duk da haka banyi musu biyayyar ba, tunda akan gaskiya suka hanani dan haka, nima na goyi baya ina ganin kawai kabar kowa ya auri wanda yake so....

Harar ta Abuu yayi hakan yasa tayi shiru tana juyar da kanta gefe,

Sai yanzu Meer ya kashe wayar sa tare da mayar da wayar sa, aljihu yana miƙewa tsaye,

Cikin isa da taƙama yace "Ni zan wuce, wannan maganar taku ce, loƙacin da kuka ɗaura auren jin sa nayi kawai a masallaci, dan haka idan kun yanke shawara, idan anje sallar asuba gobe sai ku sanar da cewa an warware auren da kuka ƙulla kun aura kuma zaku saki matar, shikenan a wuce wajen, kowa sai ya huta, sai da safen ku yafaɗa yana ficewa daga cikin falon, dan tafiya sabon part ɗin sa, dan baiga dalilin da zai hanasa komawa ba tunda yagama kai komai nasa can,

Kamar ruwa ya shanye su haka suka koma harya fice babu wanda tasamu ƙwarin gwiwar dakatar dashi,

Abban Ameesha ne yace "shikenan ta faru ta ƙare sai kowa yayi haƙuri wanda bazai haƙura ba yakashe kansa, tunda de miji bashi da niyar sakin matar sa, in kuma zaku iya sakin ta kamar yanda yace batare da yawun bakin sa ya furta hakan ba, to bismillah nima de bacci nake ji, Norry muje ko yaja hannun matar sa suka bar galon zuwa nasu part ɗin dan su daman basu da bakin cewa akan wanna maganar duk abun da suka yanke daidai ne agurin su,

Abuu ma niƙewa yayi yace "to nimade babu abun da zance, masu so sai ku saketa, nima nayi nan, ya tashi ya tafi cike da jin daɗin rashin sakin da ba ayi ba, yaude Meer ya faranta masa,


Duk sun fice sun bar su Maama da jin kunya, Maama tasan halin Meer tunda yayi hakafa to sai ta Allah saidai suyi haƙuri ko su lallaɓasa,

Gurin ya rage daga Maama sa Dadda da Papa, sai Ameesha da tunda taji abun da Meer yace kukan nata ya tsaya cak, sai hawaye kawai dake sauko mata,

Papa ne yace to Allah ya kyauta ke kiyi haƙuri yanzu ki tashi kije kawai a san yanda za ayi daga baya, kinji ko, yana faɗa shima ya tashi ya tafi,

Suma duk miƙewa sukayi da niyar gobe kawai sai suyi mata nasiha su mayar da ita cen tunda bazai sake taba,

Tun daga wannan rana babu wanda ya sake maganar kuma har sati ya kusan zagayowa, Ameesha kam inbanda zaman ɗaki ba inda take zuwa saboda sun gama exam ɗin su, ga shi Azeema ma ta tafi gida,

Sai ta ɗan faki ido ta tabbatar bazata haɗu dashi ba, sannan take fitowa shima tana fitowa zata ƙara komawa, su Maama na sane da ita amma babu wanda ya kulata, sun bata zuwa nan da wani loƙacinne,

Shima a ɓangaren Meer ma bai ƙara bi takan ta ba hasalima harhaɗa kayan sa yake zai tafi ƙasar sa yamen, kuma baya tunanin ma zai dawo nan kusa, dan zaiyi wani muhimmin abu,

Bayan satin su uku da faruwar abun....., yagama shirya komai saida ya fito ma yace zaiyi tafiya akace masa matar saba, yace ai ba daɗewa zaiyi ba, ita kuma karatu zatayi da ya tafi da ita,

Ba yanda aka iya dashi anaji ana gani ya tafiyar sa, ko neman inda take beyi ba,

Tunda ya tafi Ameesha ta samu freedom dan ji take ma kamar babu wani aure akan ta, har gwada kiran Bossay take amma baya ɗagawa danshi tun ranar bai ƙara zuwa gidan ba, kuma aranar da ya tafi ma saida aka kwantar dashi a asibiti kusan sati yayi a asibiti, kafin yaɗan samu lafiya, saboda yanda ya ƙwallafa rai akanta da tunanin ta, har ciwon zuciya ne yakama sa, tunda ya haɗu da ita bai taɓa tunanin zai rasa taba, tun ranar da yaganta ya fara sonta kuma yake hasaso musu rayuwar kasancewa da juna, shima a can ɗin har yanzu baya zuwa ko ina, kullum yana gida, duk yazama wani iri ga rama da yayi da duhu saboda yawan sakawa kansa damuwa,


Ameesha tun tana kiransa har ta daina ta fara fawwalawa Allah, satin Meer ɗaya, su Ameesha suka samu admission a Bez University dake Abuja, da ƙyar aka bar Ameesha zata tafi, dan cewa akayi saidai ta canza tayi nata ana amma ta dage da roƙo da magiya, sai akace saidai ta kira mijin ta idan ya amince sai taje idan kuma bai amince ba sai ta haƙura,

Babu yanda ta iya dole ta rufe ido ta kirasa da sabuwar wayar da Maama taba ta, saida yagama yi mata rainin hankali sannan ya amsa sallamar, daga nan ta gaya masa abun dake tafe da ita, dan rashin mutun sai kawai yace mata zamana kike, ko nace miki inzakiyi abu sai kin tambaye ni, yana faɗar haka ya kashe, kamar tayi kuka haka ta danne baƙin cikin, taje tace ya amince,

Nan suka fara shirye shiryen tafiya, acikin sati ɗaya ka gama shirya, komai har hostel ɗin da zasu zauna, an tanadar musu, kasancewar Abu yayi zaman Abuja kuma yasan mutane da yawa yana da alfarma, sai hakan ba basu wahala ba, suka samu komai cikin ƙanƙanan loƙaci,

Ranar Lahadi aka tafi akai kaisu, su su biyar, Ameesha, Azeema, Sumayya, sai twins Amra da Hamra,

Sumayya da Azeema suma da ƙyar Sam da Shettima suka bari, suka tafi dan su a tsarin su suna gama level 1, za a ɗaura musu aure, loƙaci ɗaya, a hakan ma saida su momma suka saka baki, sannan suka haƙura, amma sunce ana dawowa za a ɗaura auren,

Koda aka tashi kaisu ma tare dasu aka tafi, kowanne ya ɗauki tasa budurwar suka ce a mota zasu tafi, su kuma su Ameesha suka shiga wata motar tare da Dadda da Maama, suka tafi, saida suka kaisu sukayi sallama dasu, sannan suka juyo gida, tundaga kan hanya suka fara missing ɗin juna,


BAYAN SHEKARA 2,

A cikin shekara biyun nan, baifi sau uku su Ameesha suka zo gida ba, domin karatu soke sosai, kowa karatun sa, me wuya ne shiyasa basu tsaya wasa ba, dan ko samarin makaran ta basa kula kowa, duk da irin harin da ake kawo musu amma basa shiga harkar kowa,

Kuma duk dawowar nan Ameesha bata taɓa haɗuwa da Meer ba, abun har mamaki yaɗan bata, tanaso taji tun tafiyar da yayi baidawo ba ko kuma yana dawowa haɗuwa ce basa yi,

Haka suke komawa, tare da ƙara wata rakiyar,

A cikin masarauta ma komai yana tafiya yanda yakama yanzu babu wata matsala, ana mulki yanda ya kamata, mutane da yawa suna kawo kukan su, kuma ana share musu kukan su, duk wanda zai zo neman buƙatar wani abun ana biya masa, kowa dake garin yasan anyi sabon sarki, saboda yanda aka gudanar da mulkin cikin tsari da adalci, babu me cewa anyi masa wani abun daga cikin masarautar,

Dadda da malam suma Yanzu hankalin su kwance babu wani abu da zasu nema su rasa, saidai godiya kawai,

Su Noory da Norry kam sai soyayya ake sha inda har aka samo mana little Ameesha ko little Sameer, sai wata kulawa ta musamman Abban Ameesha yake bata,

A ɓangaren gidan su Azeema, ɗan su sarki Salahudeen ya gina musu wani gidan yayi musu part part shima ya tattara nasa iyalin duk da Papa ya hanasa amma haka yabawa Papa haƙuri ya kwashi iyalen sa suka bar cikin masarautar, ya koma can, ga iyalen sa ga iyayen sa hakan yafi masa daɗi da kwanciyar hankali.. amma yana shigowa sosai ya gaida su Papa, sa Fulani,

Saleema yana nan ƙalau inda yake ta aikin sa a hospital ɗin su, Sam wanda zuwa yanzu yaƙara samun babban matsayi, yana samun albashin sa me tsoka, gashi yayan sa ya ɗauke masa nauyin gidan su babu abun da yake siya, shiyasa kuɗin sa suke ta ta ruwa har yafara gina tamfatsetsen gidan sa na kansa, wanda ko matar da zai saka bai gama samu ba, amma ya kusan gama gida,


*********************

A ɓangaren su Rasheeda suna cikin wani hali na rayuwa, dan duk wani abu da Dady ya mallaka anƙwace sa, babu abuda suka tsira dashi, gashi sun koma gida amma saboda halin su yasa kowa sai janye abun da yake daga zarar sunzo zasu raɓe ka kowa sai yace ai da suna dashi wulaƙanci take musu, alhalin ba haka bane, batada hali dai me kyau amma kuma bata da rowa ko kaɗan,

Rayuwa kenan, gashi daman mahaifayar ta ta rasu, sai abun da tagani, daga ƙarshe ma da tsangwamar tasu tayi yawa, dan duk wannan ƙibar tata saida ta zazzage,

Rasheeda ta lallaɓa suka tafi ƙauye dan tana ganin can sai yafi musu daɗi akan nan, hatta wayoyin hannun su saida ƴan sanda suka kwace kayan jikin su kawai aka barsu dashi,

Rasheeda duk wannan gayun yanzu kamar ba ita ba, duk ta fara canza kamanni, satin su ɗaya a ƙauyen ta cewa uwar ta bazata iya zama ba, ƙauyen fa ko ruwan arziƙi babu, idan ma ansamu wata kala ne jajawur me ƙasa, ga ba wutar nefa indare yayi sauro ya ta cizon su ga wani irin zafi da akeyi a ƙauyen, da ƙyar mahaifiyar ta ta lallaɓata tayi satin shima wai a hakan akwai wani saurayi agidan yana zuwa cikin gari ya siyo mata ruwa da abin ci da yayi na kwana biyar kuwa yace ya gaji indai tanaso yaci gaba da siya mata saidai ta yarda ayi musu, aure shikuma zai siya mata kome take so,

Tunda ga ranar ko kallon inda yake bata ƙara yi ba, banda tsabar ya raina mata hankali wani gaja da shi baki duk kore ƙazami dashi zai wani haɗa kansa da ita, abincin hannun nasa ma da ƙyar take iya ci, dan akwai loƙacin ma da take ci abin ci kawai ya shigo yana ware mata baki yazo inda take taji warin jikin sa ya dakar mata hanci ta kalli bakin sa, ai saida ta dawo da abin nan gaba ɗaya, babu wanda ya iya zama acikin ta, da ƙyar taƙara kwana biyu a daddafe tana yi kuwa tace wallahi idan ta ci gaba da zama mutuwa zatayi haka ta tattaro ƴan kayayyakin ta ta dawo gidan su mahaifayar ta, gashi dangin mahaifin tama intace zata suma duk ɗaya ƴan ƙauyen ne hasalima bata taɓa ganin suba batama san garin da suke ba, ɗan uwansu ɗaya ta sani mahaifin Khalid kuma shima ya rasu, Khalid kuma ya tattara kayan sa yabar gidan batasan ma sanda ya tafi ba bare ta bisa......

Shikuma yana sane yayi musu haka sai yake sai ta horu sosai, dan duk yasan halin da suke ciki yana tausaya musu, kawai dai yafiso sai sun fara gane kuren su, da kuma abun da mahaifin su yake aikatawa, sai yazama izna akansu,

Gidan ɗaya daga cikin ƙawayen take ta bata labarin duk abun dake faruwa tace ta taimaka mata, ta kira mata sauran su san yanda zasuyi da ita, amma koda ta kirasu kowa sai yanuna mata bashida kuɗi wasuma ƙarya sukayi mata wai basa gida saboda karma taje,

Wacce taje gidan suce ta barta tayi kwana har biyu, daga nan tace taso ta tafi iyayen sunyi mata magana, da zata tafi ta bata kaya kala biyu, ta bata dubu ɗaya tace ta hau mota,

Haka Rasheeda ta tafi har da su kuka tana ta tuna rayuwar da tayi dasu wasuma ita take biya musu kuɗin makaranta babu abun da suke nema agurin ta su rasa komai yi musu take, idan bikine ya tashi ita zatayi musu anko duk wani abu idan ya tashi ita take ɗaukar nauyin su, ko kayan ankon bikin ta saida ta ɗinka musu set biyar biyar, amma yanzu saboda rayuwa tayi mata haka suka yi mata haka,

Nan gidan su mahaifayar tata ta dawo kawai ta kama ɗaki ta ci gaba da zaman kaɗai ci gashi bata gama makaranta ba batasan ya zatayi ba, haka take wuni a ɗaki tana kuka daga nan bacci ya ɗauke ta, idan ta tashi ta fito cikin gidan, haka wanda yaga dama ya tsakura mata abin ci wasuma ko kallo bata ishe su, wataran kuma kakan ta yabata haka take rayuwa cikin ƙunci da damuwa........,


*********************

A ɓangaren su Dadyn Bossay, tunda Ayuba ya samu sauƙi suka ƙara komawa garin Abuja inda aka tattauna maganar karagar mulki,

Nan suka sauka akaje harda su Papa akan maganar wanda ya dace a ɗora da farko baban Bossay suka ce ya hau, amma sai yace shi gaskiya bazai iya barin kasuwancin sa ba saida abawa Hamza tunda shima ai ya riga da ya manyanta, sai kuma akayi maganar aure sai yace shi gaskiya yanzu baida matar da zai aura wacce kuma yake jin zai aura ɗin karatu take saidai in za ajira nan da shekara biyu, sai ayi inkwa ba kaba saidai a naɗasa da haka, dan bazai taɓa auren matar da baya so ba,

Rasa yanda za ayi dashi akayi saboda taurin kansa ya riga ya kafe yace shi wallahi baza'a aura masa wata ba, sai ita akace yafaɗi wacce yake so acikin waɗanda suka tafi makarantar yace abari idan sun dawo aji, Hamza taurin kan sa yayi yawa, in ya kafe akan abu babu wanda ya isa yasa shi, ga kuma isa da taƙama da kai, ko dayake jinin sarauta dole saida hakan,

Papa ne yace abari to yanzu kawai wanda yake kai ya hau shima daman nan da shekara biyun shima akwai abun da ya shirya in sa rai da lafiya, sai ayi naɗin masa tare da aura masa, kuma ya lalubo ɗayar kafin loƙacin dan mata biyu zai aura,

Daga nan suka juyo suka dawo gida, shima Hamza yanzu ba sosai yake zaman can masarautar ba, yafi zama anan gidan yayan sa gurin Bossay, zaman sa kuma yasa Bossay yaɗan fara sakin jiki ba kamar da, dan har yanzu sonta bai fita aransa ba, dan kawai ranar ma da yaji ita yake son gani kawai ya shirya ya tafi har can Abujan yaje ya tsaya a wajen makarantar su,tun safe, saida yaga zuwan ta sannan shima ya fito ya shiga cikin makarantar fuskar sa arufe ya ringa binta daga nesa yana kallon har suka tashi saida yaga tafiyar ta sannan ya haƙura ya juyo gida, batare da tasan da zuwan nasa ba har ya tafi.....


Meer kam ko shekara baiyi ba a ƙasar su yadawo suka ƙara shiri tare da su Ummy da Abu harda Maama Papa ne kaɗai bai tafi ba saboda kula da fadar,

Tun kafin suje Ummy ta kira ta sanar da gidan su inda akai ta ɗokin zuwan ta bayan shekaru da suka ɗauka basu ganta ba,

Koda taje sun samu tarba me kyau harda gurin mahainta, daman yace sai ya kawo dangin sa sannan zai kulata, yanzu kama ta cika, ta kawo masa, kowa sai nan da nan yake dasu, tare da zuwa gurin dangi dangi ana gaisawa,

Saida aukayi sati biyu sannan suka juyo cike da kewar juna, tare da farin ciki, fal ranta ta na ganin ƴanuwan ta,

Suna dawowa kuma Meer yaƙara komawa amma watan sa uku ya juyo maimakon ya dawo gida sai kawai ya wuce Abuja, aje yaci gaba da gudanar da aikin sa, bare da sanin kowa ba, duk sunyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login