Showing 99001 words to 102000 words out of 170049 words

Chapter 34 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7227

ƙarar saƙo. Sai kawai ya zurata a aljihu ya fice daga ɗakin,

har yabar gidan bai duba ba, yana cikin mota aka kirasa daga can inda ake jiran sa, da sauri ya zaro ta daga aljihu yayi picking, bayan ya gama wayar har zai ƙara ajiye wayar kuma sai ya tuna da saƙon da ta shigo masa ɗazu, fasa ajiyewar yayi, ya shiga messages ɗinsa nan idon sa suka sauka akan message ɗin da Bossay ya tur masa ga kuma tarin maiss call ɗin da Ayuba yayi masa, nan da nan hankalin sa ya tashi matuƙa, yayi saurin taka burki, yashiga kiran wasu mutanen yana sanar dasu, harda police a waɗanda ya kira, sannan ya nufi police station dan su tafi tare.......,

Haka saƙon ma ɓangaren su Sam da Shettima da wasudai da Hamza shima ya turawa, kan kace me wasu daga cikin masarautar sunji labari, inda magana takai kunnen Papa shima ya sanar da wasu amma abun cikin sirri akayi sa,

Papa yana gayawa Meer yace abar masa komai a hannun sa shida kansa zaiyi tracking basai anhaɗa da wasu ƴan sanda ba,

Sam da Shettima tare suka shirya suka tafi suma a mota ɗaya, sannan suka doshi hanyar Gombe,

Meer kam shi kaɗai ya tafi amotar sa babu, gudu yake kamar zai tashi sama Saida gafara dubawa yaga tazarar mita ɗin da zata haɗasa dasu, dan haka yasan inbaiyi gudu ba dole za'a iya samun matsala......,


A kusan tare police ɗin Dadyn Bossay da su Sam suka ƙarasa gurin saidai kuma suna ƙarasawa basu samu kowa agun ba kuma gashi location ɗin ya nuna suna gurin, gurin suka ci gaba da bincika wa, har ɗan cikin dajikan wajen sai da suka duba amma basu gansu ba, saida ƙyar suka gano wayar dake faɗe aƙasan motar su ashe loƙacin da suke faɗan nan wayar Bossay ta faɗi agun bai tafi da ita, su kuma diddigin tasa number suka bi bata Hamza ba. Ɗaukar wayar sukayi cike da taƙaici,

......A kiɗime Dady ya fara salati sai can kuma kamar wanda aka tsikara yayi saurin cewa bari mugwada wannan number ya lalubo number Ayuba yace gashi kubi daddigin wannan number tare suke duk suna guri ɗaya,

karɓar number sukayi suka fara bincike akan number nan suka gano sai sun ƙara tafiya sosai kafin su same su...,

Mota suka ƙara shiga gaba ɗayan su suka kuma bin hanyar sukaci gaba sa tafiya......,


Meer bai ankara ba kawai yana dubawa sai yaga location ɗin ya canza daga hanayar da ya gansu, canza hanya yayi shima, sai kawai yaga kamar ma kusanto shi ake.....,

Gurima yasamu yayi parking ɗin motar sa ya zaro laptop ɗinsa yana ƙara saita location ɗin da kyau, yaƙara tabbatar wa nan suke yowa suna hanya ɗaya ma dasu kuma tazarar su babu yawa baifi kilo mita biyar ba, dan haka sai yafasa cigaba da tafiya, yaɗan ƙara nesa da titin sannan ya juya kan motar sa kamar zai koma, sai yayi parking ɗin ta ta yanda zai fara gano su ta mudubi,

Tun tazarar su na wajen kilo mita biyar har tazo uku ta dawo biyu ta dawo ɗaya ana daf da zuwa inda yake sai kawai yaga anyi kwana da sauri ya tayar da motar ya juya, baisha wahala ba yaga kwanar da sukayi, shima kwanar yayi, yana shiga kwanar ya hango motoci agaban sa duba location ɗin yayi dan yaƙara tabbatar wa kansa suɗinne,

Yanda suke gudu shima haka yake gudu saidai kuma baibari ya ƙure suba yadai yi yanda bazasu guje masa ba, haka suka ringa tafiya,

Wayar sa yazaro ya kira Khalid sannan ya sanar dashi abun dake faruwa, (daman Khalid ɗan sanda ne mai babban matsayi dan haka dandanan shima ya haɗo tasa tawagar,

Amma Meera yace masa ba yanzu ba kawai dai ya zauna cikin ready idan yaga inda suka tsaya zaiyi masa magana....,

sunɗau loƙaci mai tsawo suna tafiya kafin daga bisani suka shiga wata unguwa, kuma duk wannan tafiyar da suke babu wanda ya kula da Meer na biye dasu domin basu taɓa sawa aransu ba za'a biyo su dan haka babu wani kula dasu ke tafiya kawai suke, babu wani tsoro ko fargaba, bare su lura da meke bayan su,

Ba wata kwana kwana hanyar suka ƙarasa wani tafkeken gida amma daga ganin sa kasan ba zamansa ake ba kamar ma tsoho, saida mutanen suka fito suka buɗe gate ɗin sannan suka shiga da motocin, Meer naganin su yayi sauri ya kira Khalid ya kwatanta masa inda suke,

Bayan shigar sune shima Meer ya fito daga tasa motat, lallaɓawa yayi ya ƙarasa jikin gate ɗin wani irin luky da yayi baitaɓa tunanin haka ba,yana taɓa gate ɗin sai yaji sa ba'a datse yake, kuma basu rufe ta ba gaba ɗaya, dan haka yana hango su daga inda yake yana gani suka fito da su Bossay ''sai Kum wani da bai sanshi ba, abun da yafi komai basa mamaki sai kawai yaga anfito da Dadyn Rasheeda, shima kuma hannun nasa a ɗaure kamar yanda sauran ma duk aka ɗaure musu nasu....,

Shiga dasu aka yiyi gaba ɗayansu, sannan wasu daga cikin mutanenn suka shiga suma, wasu kuma suka tsaya daga bakin ƙofa,


Suna shiga suka ɗaɗɗaure Abban Ameesha da igiya suka saƙale hannuwan sa sama ƙafafun sa suka ɗaure, sannan suka fara dukan sa, wani ya zaro wuƙa zai caka masa Bossay ya ƙwalla ƙara yana No! kar ku kashe kar kushe shi dan Allah idan kuna so kugama da duniya lafiya ku rabudashi.

Sunbatun Bossay ne ya dakatar da wanda yayi niyar caka masa wuƙar saboda ƙarar da yasaki ta tsorata sa,

Ɗaga ido yayi ya kalli Dadyn Rasheeda da ido yayi masa alamun ya rabu dashi ɗin, amma sai Dadyn Rasheeda ta haɗe rai da ido ya gargaɗe sa dan haka sai yaƙara juyawa ya saita daidai cikin sa zai caka masa, amma baikai ga saukewa ba ya kuma dakatawa sakamakon wata uwar jiniyar ƴan sanda fata karaɗe gidan yanda kasan acikin falon aka kunna ta,

Aruɗe suka shiga kallon kallo da idanu wasu suka fara neman hanyar fita wanda ya riƙe wuƙar kuma da sauri yayi cilli da ita,

Kafin suyi wani kyakkyawan yunƙuri tuni ƴan sandan nan sun turo kai cikin gurin kowanne hannun sa ɗauke da bindiga suna saita kan bindigar akan wasu, Khalid ne da Meer suka shigo daga baya,

Nan Khalid yabasu umarni aka kama su gaba ɗayan su aka fita dasu waje daga cikin wajen,

Abban Ameesha kuma Dadyn Rasheeda yayi sauri yaje ya kunce sa, yana ɗan matsar hawaye yace "Allah shine abun godiya da baku zo ba da tuni sun kashe shi Allah ya tsallakar dashi, mun gode muku da kuka taimake mu, sai wani kalar tausayi yake nuna a fili amma a zuciyar sa fal take da taƙaicin ya akai hakan ta faru, abun ya matuƙar ɗaure masa kai ta yanda wannan lamarin yakasan ce, kuma duk haukan nan da yake idon sa bai sauka akan na Meer ba ko ince bai gane saba, saboda yasaka p cap ga kuma face mask shiyasa baisan waye ba,

Nan ya koma kan Khalid yana cewa Khalid kaga abun da fitar jiya ta jawo min da tuni na rasa raina daga taimako najefa kaina cikin bala'i Allah yasa kazo akan loƙaci da tuni saidai kuji mutuwa ta wasu mugayen sun kashe mu,

Cike da tausayawa Uncle ɗin nasa Khalid yashiga bashi haƙuri da kwantar masa da hankali,

Shi kuma Meer tunda ya shigo yake kallon sa abun da mamaki yanda yake nunawa sai ya nemi ya raba masa tunani gida biyu,

Meer ne yace "ya akai suka kamaku me kukayi musu nan Bossay ya shiga bawa Meer labarin duk abun da ya faru tundaga farkon zuwansu jiya har zuwa labarin da Ayuba yabasu akan mutumin da yazo kuma suka gansa yabashi labarin bai rage masa komai ba,

A hankali Meer ya shiga zare hular kansa tare da cire face mask ɗin cikin wani irin yanayi shi bazai ce farin ciki ba shi bazai kirasa da baƙin ciki ba, zamu iya kiran abun kawai tsantsan mamaki da al'ajabi ne yakama Meer wanda ya daɗe baiyi irin saba,

Da sauri Meer yaƙarasa kusa da Abban Ameesha yana zuwa kawai ya rungume sa, kallo ɗaya yayi masa yaji mutumin ya mugun kwanta masa arai kwarjini da ganin girman sa duk suka rufar masa loƙaci guda dan yana tunanin yanda yake ji akansa ko Abu bai taɓa jin irin yanayin akan saba,

Shima Abban Ameesha duk da baisan waye ba amma sai kawai ya ƙara rungume sa hawaye na sintirin saukowa daga idon sa,

Meer kamar zai maidashi ciki haka yake ji saida suka daɗe ahaka sannan Meer ta sakesa, tare da saka hannu ya shiga goge masa hawayen,

Meer baisan loƙacin da sunan yazo masa baki ba, ji yayi kawai yace UNCLE please stop crying ya faɗa cike da tsantsar damuwa a fuskar sa, hakan da yayi kuma sai ya kuma tunzura Abban Ameesha hawaye suka ci gaba da zubowa dan ji yayi zuciyar sa ta karaya,

Meer kamar zaiyi kuka haka ya cigaba da basa haƙuri kamar shi yayi masa laifin,

Shima Khalid saka baki yayi akaci gaba da rarrashin Abban Ameesha,

Dadyn Rasheeda kam tunda yayi ido huɗu da Meer ya haɗa hankalin sa guri guda bai ƙara gangancin ƙara yin magana ba,

Saida suka daɗe sosai acikin gidan sannan suka fito, ga katarar Abban Ameesha ga katarar Meer abaya suka zauna sai Bossay dazai tuƙasu agaba Khalid da Hamza da Dadyn Rasheeda suma suka shiga motar ɗaya,

Kafin su tafi gida saida Meer yasa suka siyawa Abban Ameesha kaya masu kyau manyan kaya, sannan sukaje wani Hotel ɗin yasa yayi wanka ya canza kayan jikin sa yasa shi agaba ya kuma cin abinci mai rai da lafiya, sannan yace ya kwanta ya huta sai zuwa dare zasu tafi gida shide Abban Ameesha ba haka yaso ba saida ya haɗasa da Allah ma shi bazai iya bacci ba su tafi kawai ya matsu yaga sauran, amma shima Meer ɗin ya hanasa tafiya, dan acewar sa yafiso yaje musu cikin ƙoshin lafiya yanda bazasu tashi hankalin su ba musamman ƴar sa, da ta matsu ta gansa bai kamata ta gansa cikin wani hali ba hankalin ta zai tashi da yawa, (tofa kunji ni da wanga mutum meye damuwarsa da ita bayan cin zalinta da yake")

Babu yanda Abban Ameesha ya iya dole ya haƙura ya kwanta cike da jin daɗin kulawar da Meer yabasa a iya yau,(hmmm bari dai inyi shiru da nace kodai neman fada ake ne Ale Meer na sirikan taka agun siriki) ba shiri kuwa bacci me daɗi ya ɗibesa,

bai tashiba sai bayan sallar magriba sannan ya tashi bayan duk suka haɗu sukayi sallah dan ko masallaci basu je ba, da suka idar Meer yaƙara bashi wasu manyan kayan masu mugun kyau ya saka yasake cin abinci saida ya tabbatar da komai need need sannan suka baro Hotel ɗin,

Dadyn Rasheeda fa jini fara ɗurar ruwa dan ganin yanda Meer yake nunawa bawan Allahn nan kulawa da so, yasan idan yagane da saka hannun sa, kashin sa ya bushe dan yasan halin sa sarai baiyi gadon mutunci ba, duk wanda ya shiga hannun sa zai ɗanɗana kuɗar sa, dan haka ya fara tunanin guduwa tunda wuri amma yasan idan ya gudu ayau za'a iya zargin sa shiyasa kawai yayi ta wannan zaman a Hotel badan son ransa ba, saidan ba yanda zaiyi,


Meer tun suna hanya yace "a haɗa zama a fada kowa da kowa ya hallara akwai zama gagarumi da za'ayi yana kan hanya yanzu zasu ƙaraso da wani muhimmin abu, anyi anyi yafaɗa yace shide ayi masa wannan alfarma kafin ya ƙaraso dole, Abu da Papa suka amince masa,

Nan danan suka sa aka fara haɗa kan muta ne acikin fada,


Ba jimawa motar su meer ta iso cikin masarautar, adaidai wajen fada Meer yasa akayi parking ɗin motar, loƙacin kowa ya hallara acikin fadar zuwansa kawai ake jira,

Meer ne ya fara fitowa sannan yace subari sai yace su fito zai shiga ciki yagani kowa yana ciki.....

Yana shiga cikin fadar kowa ya zuba masa ido mutanen ciki ya shiga bi da kallo ɗaya bayan ɗaya amma har hagama baigan taba, dan haka saikawai yace afuwa ina dawowa kowa ya ƙara shiryawa wanda bai wanke ido ba ya wanke wanda kuma ya wanke ya ƙara wankewa yanda zaifi gani da ƙyau, yana kaiwa nan ya juya ya fita yabar su da surutu....,

Koda ya fita bai yi musu magana ba hasalima ba su gansa ba, saboda bata gaban su yabiyo ba,

Can part ɗin ya nufa yana shiga direct ɗakin da yake kyautata zaton nanne ɗakin da take kwana nan ya nufa yana zuwa kuma ya tura ƙofar,

Yana saka ƙafar sa ita kuma tana sako tata daga banɗaki jikin ta ɗaure da towel iya gwiwa, dake ƙarar tata ƙofar baisa taji tasa ba dan haka bata san ma da shigowar saba, ta ƙarasa fitowa daga ciki,

gaba wardrobe ɗin ta taje dake sauri take tagama shiryawa ta fita cikin fada saboda farko cewa tayi bazata ba sai kuma daga baya kawai taji tana son zuwa gashi rabonta da wanka tun jiya shiyasa ta shiga tayi yanzu da niyar tana fitowa sai taje taga uwar da zaiyiwa mutane da yasa aka haɗasu,

Sanin ita laɗai ce babu kowa a part ɗin bare kuma ɗakin sai kawai ta saki towel ɗin ya faɗi ƙasa yanda zata fi saurin shiryawa...,

Pant ta ɗauka ta fara sakawa sannan ta ɗauko bra tana zurota ta baya zata fara saka maɓallan ta sai ta suɓuce ta faɗi ta bayan ta saboda saurin da take cike da sakin tsaki ta juyowa a fusace ta tsugunna takai hannun ta zata ɗauka kenan sai taga bra ɗin akan ƙafar mutum a razane ta ɗago dan batama ɗauki bra ɗin ba,

Tana tozali dashi ta wangame ɗan ƙaramin bakin ta zata kurma wani mahaucin ihu saboda razanar da tayi,,

Sauri yayi ya riƙota ya ɗora hannun sa akan bakin ta ya toshe mata baki tare da haɗeta da jikin wardrobe ɗin ya hanata koda motsi bare kuma ta samu damar yin ihu......,✍️✍️

(Wayyo Allahn mu yau ina zamu saka ranmu angane mana komai😭😭)
[15/11, 10:53 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                         *_🅿️37_*

____
Sauri yayi ya riƙota ya ɗora hannun sa akan bakin ta ya toshe mata baki tare da haɗeta da jikin wardrobe ɗin ya hanata koda motsi bare kuma ta samu damar yin ihu...


........ido yagama raina fata dan ƙafarta ma neman kasa ɗaukar ta take, dan ji tayi gaba ɗaya jikin ta ya ɗauki ɓari, ta shiga karkarwa,

yana jin yanda jikin ta yake shaking sai kawai ƙara riƙeta da kyau, yana bin fuskar ta da kallo ga kuma hannu sa dake kan bakin ta sai mutsul mutsul take dashi tana son ƙwace wa amma ya hanata damar yin hakan,

Ƙafar sa ya miƙa ya jawo bra ɗin da yatsun ƙafar sa ya ɗauko ta, ya ɗago ya riƙe da ɗayan hannun sa da ya rufe mata baki,

yunƙurin ƙara yin magana tayi sai yasa ya tsansa ya ɗannan mata baki, take hawaye suka fara saukowa daman sun cika idon ƙiris suke jira,

Ɗan matsawa yayi kaɗan daga kusa da ita hakan yabata damar saurin tsugunnawa tasa hannuwan ta duka biyu tana rufe ƙirjin ta gashi babu wani abu da zata ja ta rufe jikin, wani irin haushin shine yakama ta ji take kamar ta rufe da duka, aranta take ayyana ashe bayan mugunta harda iskanci inbanda ɗan iska waye zaishigo guri yaga mutum ba kaya kuma ya tsaya yaci gaba da kallon sa,

Ganin bashi da niyar barin wajen yasa ta rufe idon ta tace "dan Allah ka fita tafaɗa tare da sakin kuka dan baƙaramin taƙaicin hakan take ji ba,

Shikam harɗe hannuwan sa ma yayi yana watsa mata wani irin kallo, ga kuma bra ɗin a hannun sa, maganar da tayi ce ta dawo dashi cikin hayyacin sa, shi abun ma kusan dariya yaso yabashi yanda duk tabi ta tsorata kanta sai wani faman karkarwa take tana wani rurrufe ƙirji shi baiga ma abun rufewa dan tunda ya shigo ma shi baiga abun kalla ba kodan idon sa bai sauka akai bane oho, wani tunanin ne ya faɗo masa sai kawai ya canza fuska tare da gyaran murya yace "ke!!!

"Ni dan Allah ka fita wai wannan wane irin iskanc..., Saurin rufe bakin ta tayi tunawa da wanda take magana dashi ba sa'anta bane,

jinjina kai yayi ganin zata wuce gona da iri, aransa yake ta maimaita kalamar wane irin iskanci ne watakon shi take kira da ɗan iska aikwa badan yanayin da yake ciki ba da ya koya mata hankali da wannan kalmar, taci darajar mahaifin ta kawai yanzu yana cikin farin ciki bayason abun da zai ɓata masa rai, amma zaiyi saving ɗin kalmar nan tata,

miƙa mata bra ɗin yayi yace "tashi kisaka, kasa karɓa tayi dan batajin zata iya ɗagowa bare kuma ta karɓi brazia a hannun sa,


"In saka miki kenan?

Da sauri ta girgiza kai amma duk da haka bata ɗago ba,

"Ok oya ungo. Ya faɗa yana ƙara miƙa mata amma taƙi karɓa,

tsugunnawa yayi a gaban ta, suna facinɗin juna, ƙasa ƙasa yace "bazan ƙara yi miki magana ba idan baki sakaba zakisan sauran,

Jin furucin sa yasa tayi sauri zuro hannu zata karɓa sai kawai ya janye tare da riƙo hannun nata, bazato ba tsammani kawai taga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login