Showing 12001 words to 15000 words out of 170049 words
ni, nayi tunanin kana da mutunci idan na bika zaka ƙara taimakamin ka mayar dani gida sai kuma naga ashe baka da mutunci, mugune kai,
Buge mata baki yayi da ɗayan hannun yace "kar kisake cemin mugu kuma kitashi kibar min ɗaki tunda na baki amsarki ki rabu dani kifita,
Dafe bakin tayi saida ta daina jin zafin sannan tace "To kuma badan niɗin ba ai da ba tuni yanzu bakasan inda dangin ka suke ba da ka koreni na tafi da tuni ka kori danginka kaifa wallahi kamata ma yayi ka gode min tunda na taimake ka, kuma wallahi kayi na farko wallahi ka ƙara taɓani daga nan sai wajen Abu Allah in kuma kana wasa ka ƙara,
Meer fa yafara fusata, da ƙarfi yaƙara ɗaga hannun nasa zai ɗauke ta da mari sai kuma komai ya tuna sai yadakata baikai hannun nasa kan fuskar tata ba,
Ita kuma har ta rufe ido tana jiran taji saukar marin sai kuma taji ɗif, a hankali ta fara buɗe ido ɗaya tana kallon sa taga abun da yahanasa marin nata,
Ƙwace hannun sa yayi gada riƙon da tayi masa yana miƙewa tsaye cikin daka mata tsawa yace tashi ki fita ga mamakin sa sai kawai tama faɗa kan gadon nasa ta kwanta daga bayama ta ɗora duka ƙafafun ta akai, sannan ta ƙara da cewa "bacci nakeji kabari idan natashi zan barmaka ɗakin ka ba ci zanyi ba wai kai meyesama bazaka barni ba kake kora duk duniyar nan kana da wata ƴar uwa kamata baka da ya baka da ƙanwa sai ni kaɗai kai da zaka lallaɓa ni amma ba abun da ka iya sai yimun mununta da cin zalina, Allah ya shiryeka ka gane gaskiya, nasiha nake ma amatsayi na ƙanwar ka wallahi kadena abun da kake ka shiryu kuma kadena yiwa iyayen ka rashin kunya, inba hakaba kajefa kanka cikin wutar jahannama yakamata ka ringa jin maganar iyayen ka kaga ni da ace agaban iyayen na taso ace mahaifiya ta da ranta bata mutuba da sunga biyayya da kulawar da zanringayi dasu, Allah yasa mahaifina yana raye Allah ya bayayya na min shi ko shikaɗai inyi masa biyayyar tanayin maganar kuma sai jikin ta yayi sanyi ta ƙarasata a hankali,
Loƙaci guda taji hawaye ya cika mata ido tunawa da tayi ayanda mahaifiyar ta ta rasu wani irin kuka ne ya taho mata me ƙarfi dan sosai zuciyar ta ta karaya, da sauri ta tashi daga kan gadon ta kwasa aguje saboda bataso tayi kukan anan gabansa,
Saidai kuma ko taku uku batayi ba taji an riƙo hannun ta tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba tana ƙoƙarin ƙwace hannun ta, shikuma ya ruƙe da ƙarfi tare da jawota ta dawo baya agaban sa ta tsaya suna facing ɗin juna yayin da kukan ta kuɓuce mata tasake shi me ciwo,
Tsayawa yayi yana kallon ta yanda take kukan kamar ranta zai fita akaro na farko arayuwar sa da yaji ya tausaya wa mace har yaji shima jikinsa yayi sanyi yaji bayason ganin irin wannan kukan da take,
Ƙoƙarin ƙwacewa taƙara yi zata fita daga ɗakin sai shima yayi saurin ƙara riƙota ya fisgota ya haɗata da ƙirjinsa ya rungumeta tare da kwantar da kanta akan ƙirjinsa saboda bata da tsawo gaba ɗayan ta a ƙirjinsa ta tsaya,
Shafa kanta ya shiga yi cikin son rarrashinta saidai kuma shima yanda zuciyar sa ta karaya yasa yakasa furta koda da kalma ɗaya wajen kwantar mata da hankali ta dena kukan,
Aɓangaren ta kuwa hakan da yayi mata sai taji kamar yace taƙara volum haka taƙara fashe masa da wani irin kuka da ita kanta batasan ta yanda akai take irin wannan kukan ba......
✍️✍️✍️
_Afuwa jiya banyi ba bansamu damar yi ba ina shirin yi data ta taƙare bansamu nasaka ba sai yanzu shiyasa banyi ba jiya_
_Sai kuma ranar asabar kamar yanda nace zanringa hutun kwana biyu Alhamis da juma'a ba update, sai asabar idan Allah yakaimu,_
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️xeemat...love❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
_______kuka ne sosai yaci ƙarfinta tana ƙara gyara shigewa jikin sa,
ganin taƙi yin shirun kuma yakasa ce mata komai saboda baisan ma ta ina zai fara rarrashin taba, daga ƙarshedai da yarasa mafita sai kawai yafara tafiya tana jikin nasa ya ƙarasa bakin gadon sannan ya zauna ya ɗorata akansa kamar wata baby haka ya riƙeta sannan yasaka hannun akan sumar kanta yana shafawa a hankali ɗayan hannun kuma ya shiga bubbuga bayan ta dashi,
Daidai saitin kunnen ta yakai bakinsa sannan a hankali yasamu damar furta mata sorry, stop crying, ya isa haka,
Duk da tajishi amma sai taji ta kasa daina kukan ita kanta tanaso tayi shirun but she can't, ba yau ta fara tunawa da suba amma bata taɓa yin irin kuka makamacin irin na yau ba bata san me yasa ba,
Meer dai yau yaga ta kansa bai iya rarrashi ba amma yau saida ya koya ya rarrashi tilon ƙanwar sa, haka yayi ta rarrashin ta har saida yaga tayi shiru ta fara ajiyar zuciya,
Tunda tayi shiru tayi lamo ajikin sa ko motsawa batayi kawai tayi shiru sai taji wata nutsuwa tafara saukar mata,
Shima shiru yayi yana sauraron bugun zuciyar ta da take bugawa a hankali a bankali, sunkai wajen minti ashirin ahaka kafin daga bisani Ameesha ta raba jikin ta da nasa ta sauka daga kan cinyar sa zata tafi ya riƙo hannun ta tare da dawo da ita gefen sa ya zaunar da ita batare da yace da ita komai ba, itama shirun tayi batayi yunkurin tashiba kuma batace komai ba bata kalle saba ta sunkuyar da kai kawai tana sauke ajiyar zuciya,
Saida ya tabbatar da tadawo daidai, yasa ta goge hawayen, duk da idon ta sunɗan kunbura amma amma saida ta samu nutsuwa sosai kamar batayi kukan ba, kallon ta kawai yake ita kuma bata iya ɗagowa ta kalle sa ba duk da sakayau take jinta ba wata damuwa ammadai takasa sakewa dashi yanzu kamar yanda tasake dashi ɗazu,
Sakin hannun nata yayi sannan ya zaro choculate ɗin da yasa a aljihun sa ɗazu, ɓare ta ya shigayi saida yagama buɗeta gaba ɗaya sannan ya miƙa mata,
Ɗagowa tayi ta kalle sa duk son da takewa choculate ɗin sai taji ta fitar mata arai, dan haka sai kawai ta girgiza masa kai alamun bazata shaba, yayi mamakin hakan tunda yaga yanda ta nuna tanason sha amma yanzu kuma tace bazata shaba, ƙara miƙa mata yaƙara yi akaro na biyu,
Sai taji nauyi ta ƙara cemasa a'a sai kawai ta miƙa hannu zata karɓa badan tana soba saidan kawai kar tamayar da hannun kyauta baya, ga mamakin ta sai taga kawai ya janye daga miƙo hannun da tayi sai ya nufi bakin ta dashi, ƙin buɗe bakin tayi sai da taga ya haɗe rai yana wurga mata harara sannan ta buɗe small mouth ɗin shikuma ya saka mata abakin tana shirin gutsirar ƴar kaɗan kawai ya danna mata ita abaki gaba ɗaya,
Waro ido tayi tana ƙoƙarin cire hannun sa ta ciro ta saboda ta cika mata baki bazata taɓa iya taunawa,
Hannu yasa ya rufe mata bakin yanda bazata iya fito da iyaba, da taga dai ba sarki sai Allah haka ta shiga taunawa da ƙyar harda ƙwallar wahala haka Meer yasata ta cinye ta tas sannan ya sakar mata bakin, yana saki kuma yaƙara dauko wata yashiga ɓare ta, ai tana ganin haka tayi saurin miƙewa zata gudu saidai bataje ko ina ba ya cafkota, yana miƙewa tsaye yace "ina zaki ai sai kinyi maganar da ta kawoki kamar kuma yanda kikace mufara shanye choculate ɗin zakiyi maganar to sai ki zauna sai kin shanye su duka sannan kiyi maganar idan kinason fita daga ɗakin nan,
Zaro ido ta shiga yi tana faman rarraba ido tace Allah kuwa na ƙoshi kuma ai mungama magana daman itace ta kawo ni kuma mungama, choculate kuma kasha kayarka na ƙoshi tunfar ko da nace kaban ai rowa kamin dan haka wacce kaban da mugunta ta isheni, daman nace mug...., Da sauri tasa hannu ta toshe bakin ta, bata ƙarasa kalmar mugun ba tunawa da tayi yace kar tasake ce masa mugu,
Wani mugun kallo kawai ya watsa mata sannan ya koma ya zauna yace "dawo ki zauna,
Ganin yayi maganar serious ba wasa, yasa ta dawo da baya ta zauna a inda ta tashi................,
*************************
___________ *SAM*
Tun ranar da yaje gidan da yakai sumy akace masa ta gudu tun loƙacin baiƙara samun nutsuwa, ya dawo gida ya rasa inda zai tsoma ransa, yaji daɗi, ga shettima abokin shawarar sa tunda ya tafi gida shima bai ƙara dawowa masarautar ba, kuma yafiso suyi maganar face to face shiyasa bai kirasa ba....,
Yanzuma yana zaune akan gado ya zabga tagumi yana tunanin samun mafita da ta inda zai fara nemanta gashi kuma ƙarewa ma babu wanda yasan ya ɗauko ta, baisan ta inda zai fara tunkarar wani da maganar ba,
Jiyayi andafasa da sauri ya ɗago yazuba rinannun idanuwansa akan fuskar sa kallo ɗaya kuma yayi masa ya janye saboda bayaso ya karanci halin da yake ciki,
Me yake damunka? Hamza ya jefa masa tambayar,
Batare da ya kallesaba yace ba komai kawaidai kainane yake ɗanyi min ciwo, kuma nasha magani yanzu zai daina kar kadamu, yana faɗar haka yaɗan gyara zaman sa ya kishingiɗa, yana dafe kansa,
Gefensa Hamza ya samu ya zauna yana kallon sa cike da nazartar sa, saboda tun loƙacin da abu yafaru sam yajasa ajiki tun bayaso har ya ɗan fara sakin jiki dashi, kuma sam yasa ya tattaro kayan sa yadawo part ɗin sa da zama amma duk da haka Hamza ba kullum yake zama ba a part ɗin kullum yana waje bayan gidan yana zagaye dan yafi son ya ringa keɓewa shikaɗai hakan yafi masa daɗi dan ko abinci ma bai fiya zama ya ciba wani loƙacin ma sai Sam yayi masa dole yake ci,
Cikin sanyin murya Hamza yace "kayi haƙuri zan shiga hurumin da banawa ba na fahimci kana cikin damuwa, bankai matsayin da zan san damuwar kaba, dan haka basai ka gaya min matsalar kaba, shawara zan baka yakamata kasamowa kanka mafita zaman ɗaki ba abun da zai haifar maka sai wani ciwon, kamata yayi kaje kasanar da mahaifiyar ka ko kasamu wanda kafi kusanci dashi kasanar dashi faɗar damuwa koda baza ayi maka maganin taba idan ka fitar da ita zaka ɗan samu sassauci akan yanda kakeji, duk wanda yaganka zai gane kana cikin matsananciyar damuwa, ba iya ciwon kai ke damunka tun ba yauba na lura dakai, dan Allah ka daure ko abokin kane ka sanar dashi matsalar ka kar kabari tayi maka illa a ɗaki, Sosai Hamza yashiga nusar dashi illar riƙe damuwa batare da ka fitar da ita ba hakan na ƙaramin cutar da ɗan adam take ba,
Kalaman sa kam sunyi aiki akan Sam sosai yaji maganar sa, kuma sai yaji ba daɗi da yace yasan baikai matsayin da zai san damuwar sa, hakan ba ƙaramin kashe mishi jiki yayi ba bayaso yaringa tunani wani iri da zai ringa sakashi damuwa shiyasa yake jansa ajiki dan ya manta da duk abun da yafaru, amma furucinsa na yanzu kwata kwata baiyi masa daɗi ba,
Dan haka yayi saurin tashi zaune yana fuskantar Hamza da kyau, yace "ko ɗaya ba abun da kake tunani bane indai har zan iya sanar da mahaifiyata ko abokina ko wanda nake da kusanci dashi to dole kaima kana cikin ɗaya daga cikin su, yanda zan ɗaukesu kaima haka zan ɗauke, Nagode da nuna kulawar ka agare ni tabbas akwai abun da yake damuna amma narasa mafita kuma bana tunanin ko na gayawa wani zai iya samamin ita, tunanin ya tsaya gaba ɗaya narasa yanda zanyi Hamza, yaƙarasa maganar cikin sanyin jiki,
Hamza ma jikin sane yayi sanyi kuma yaji daɗi sosai jin matsayin da yabasa mai girma haka duk da laifin da mahaifiyar sa ta aikata musu amma babu wani wanda yake nuna masa kyara da tsangwama, musamman Sam da yafi kowa jansa ajiki hakan ba ƙaramin daɗi yake masa ba,
A hankali shima yafara magana da cewa "indai har dagaske ne abun da kafaɗa to ina mai roƙonka da kagaya min nikuma in sha Allah zanne ma maka mafita da yardar Allah zan taimaka mana,
Ɗan murmushin yaƙe Sam tare da jinjina kai batare da yace masa komai ba, yakai wajen minti bakwai kafin yaɗanyi gyaran murya sannan ya shiga basa labarin abun da yafara tsakanin sa da sumy ɗin tundaga farkon haɗuwar su har ƙarshe, inda yakaita gidan ƙanwar kakar sa, (Ammah) yace kuma yaje amma ta sanar dashi suma tashi sukayi suka nemeta suka rasa.....,
Hamza najin haka yasaki murmushi mai ƙayatarwa da ya daɗe baiyi irinsa ba, da hakan har saida ya bawa Sam mamaki, danshi tunda suka zauna na bai taɓa ganin murmushin saba,
Batare da ya daina murmushin ba yace "ashe ƙanin nawa soyayya ya faɗa, kace munkusa shan biki, macece daman tasaka gaba haka ka kama damuwa har da su rama, tokwa dole intashi tsaye karka damu zamu nemo maka ita duk inda ta shiga afaɗin duniyar nan, bare ma nasan ba wani nisa tayi, tana kusa,
Tunda yafara magana sam yake kallon sa cike da mamakin kalaman sa shi yana masa maganar serious amma shi yazo yana masa wata irin magana marar ma'ana, haushi yaje yakamasa take ya shiga yi masa wani irin kallo saida yabari yayi shiru sannan yace "kaga nifa ba abun da kake tunani bane kanajin yanda nabaka labarin yanda take rayuwa abun tausayi kuma kana min wata maganar daban inma wasa kake Please mubar wanann maganar banaso inbaza ka taimake ni dan Allah ba to kabarshi yana faɗar haka ya miƙe cike da jin haushin Hamza,
Da sauri Hamza ya miƙe yana ƙumshe dariyar sa da take shirin fitowa, sannan yace "tuba nake kayi haƙuri bazan ƙara ba, yanzudai abar ko wane zance muje neman yanzu nan basai anjima ba, amma zamu fara zuwa gidan kakar taka kuma kar kasanar da ita muje kawai yana faɗar haka ya kamo hannun sa yana ƙara cewa muje,
Sam kamar wani soko haka yake kallon Hamza cikin rashin fahimtar inda zancen sa ya dosa, yana buɗe baki zaiyi magana Hamza yayi saurin da katar dashi yace "karkace komai pls muje kawai, haka kwa Sam yayi shirun ya shiga binsa tunani fal cikin sa shiyasa ma yakasa tantance wane iri zaiyi, bashi da zaɓi da ga wuce ya bisa ɗin,
a haka suka fito daga ɗakin har suka wuce falo suka fito part ɗin fulani suna fitowa sukaga anfita da gudu daga cikin falon,
Ai Hamza baijira wata wata ba ya kwasa aguje yabi bayan wanda ya fita daga ciki, yana fita ya hango wata mace, ta shiga wani part ɗin, girgiza kai yayi yace "zaki ci ubanki Ubaira, duk ma wanda ya aiko ki zakiyi bayani, yana cikin wanann maganar Sam yaƙaraso gurin yace "wacece wacce ta fito ɗin ka ganta ina tayi,
Ɗan dafa kafaɗar sa yayi ya bubbuga yace "muje kawai komai yana da loƙaci yanzu ba wancen loƙacin bane, zamuyi maganar idan mungama waccen, wata mata ce kuma nasanta naganeta naga kuma inda ta shiga ai anyi mai wuyar, dan haka kar kadamu da wannan kaji da abun da yake gabanka, muje yafaɗa yana yin gaba,
Yaudai Sam ya zama ɗan kallo sai yanda Hamza yayi dashi haka, yabi bayansa har suka ƙarasa inda motar sa yake, driver yazo zai buɗe masa ƙofa Hamza ya dakatar dashi yace "yaje sannan ya buɗewa Sam motar da kansa ya shiga shikuma ya shiga driver seat yashiga tare da tayar da motar yajasu suka fice daga masarautar Sam yana masa kwatance, ahaka har suka ƙarasa unguwar abakin gate ɗin gidan Hamza yayi parking,
Sam ne ya ɗago ya kalle sa ganin yayi parking a waje yace "naga ka tsaya anan mushiga mana,
Batare da Hamza ga kallesa ba ya girgiza masa kai, sannan ya buɗe motar ya fita ya zagayo ya buɗewa Sam, shima Sam bai ƙara magana ba, ya fito kawai atare suka nufi gate ɗin gidan, suna zuwa bakin gate ɗin Hamza ya kwanƙwasa, daga ciki mai gadin yace "waye,
Hamza yace "mune,
Buɗe ƙofar akayi, mai gadin yana ganin Sam ya washe baki yana gaida su bayan sun amsa yabasu guri suka shiga,
Suna shiga suka fara tafiya masu aikin gidan kama daga masu bawa fulawoyi ruwa zuwa ga drivers ɗin daman duk sun sanshi dan haka suma suka shiga gaidashi, amma halin da yake ciki ya hanasa amsa musu, kawai sukayi gaba basuyi nisa ba, suka ƙaraso suna daf da shiga ciki idon Hamza yakai wajen parking lot ɗin su inda yake yaga wata mace da gajeran wando da riga kanta ko ɗan kwali babu badan gashin kanta ba ma zakayi tunanin namiji ne, saboda yanda ta gwame tana ta wanko ƙasan tayar mota gashi duk ta jiƙa jikin ta, ƙafarta ma babu takalmi,
A iya sanin sa yasan mata basa wankin mota ko acan masarauta bare kuma waje ga kuma maza da suke zaune babu abun da suke amma mace na wankin mota,
Sam har yasaka ƙafar sa ɗaya zai tura ƙofar falon Hamza yayi saurin jawo sa baya, Sam har tsorata yayi jin irin jawowar da Hamza yayi masa, ransa har yana ɓaci ya ɗago zai sauke masa kwandon masifa,
Hamza yayi saurin ɗaga hannun sa yana masa nuni da inda yarinyar take tare da cewa kai nan gidan wai har mata ma suna wankin motoci abun da ko amasarauta bantaɓa