Showing 96001 words to 99000 words out of 170049 words
ya koma ya zuba na mujiya aɗan ta ƙaice Hamza yabasa labarin ko waye shi jin labarin sa kam ba ƙaramin girgiza Ayuba yayi ba bama shi kaɗai ba har shi mutumin dan har aka gama bada labarin bai yarda ba yama za ayi ace shi wai ɗan sarki ne kuma anga iyayen sa hakan ai kamar bamai yiyuwa bane dan haka yace musu shifa su Dadda yasani sune iyayen sa dan gani yake kamar duk ƙarya su Hamza sukayi masa, saboda sun basu labarin duk abun da suka sani aɗan taƙaice saboda ba komai suka sani ba,
A ɗan taƙaice dai adaren ranar suka gama komai, Abban Ameesha tun yana kukan baƙin ciki da na danuwa har yafara na farin ciki tare da ƙaguwa yaje yaga a hankalin sa da ya ɗauke shekaru masu yawa batare da gansu ba, duk ya ƙosa ta gansu dan gaba ɗayan su babu wanda bai damu da ganin saba, amma duk labarin da suka basa basu gaya masa babu malam babu matar saba, saboda basa son suƙara rikitashi, sai wajen ƙarfe ɗaya da wani abun na dare sannan suka kwanta da niyar gobe zasu juya su koma Kano dan zama bai kamasu ba,
Duk sun kwanta suna bacci amma banda shi yana kan sallaya yana ta jero salloli nafila dan daidai da ɗigon bacci bayajin sa'a idon sa, burin sa kawai gobe tayi sutafi.......,
***********************
Dadyn Rasheeda, kusan kwana yayi acikin garin Gombe suna neman mutumin, gaba ɗaya ya tashi hankalin ma'aikatan gidan akan sai sunje duk inda yake acikin garin suje su samosa, harda ikirarin inbasu samo sa ba sai ya kashe su gaba ɗayan su,
Da ƙyar suka gano waɗanda suka fita da shi ta hanyar CCTV camera dake bakin titin kusa da gidan tanan sukaga loƙacin da mutane suka shiga gidan suka fito dashi suka sakasa amotar su, number motar suka ɗauka sannan yaƙara mutane wajen lalubo inda motar take, dan haka tun wajen magariba suka bazama suna neman ta, sai kuma aka ci sa'a suka haɗu dasu loƙacin da suka fito daga wajen su Ayuba bayan sunkai Abban Ameesha akan hanyar su ta dawowa sukaci karo a hanya aka kamasu....,
Sunyi sunyi su faɗa musu inda yake amma sunƙi faɗa sai gana musu azaba ake amma har cikin dare basu faɗa ba, sai gaba da asuba da suka ga suna daf da rasa ransu ɗaya daga cikin su ya faɗi inda yake,
sai loƙacin aka rabu dasu, sannan suka fara shirin tare da mutanen da suka kama,
Washe gari....
yanda Abban Ameesha yaga rana haka yaga dare bai rintsaba ko kaɗan yana ibada da roƙon Allah da miƙa godiyar sa ga mahallici,
Ana kiran sallar farko ya tashi ya ƙara yin wasu nafilfilun sannan, da aka kira sallah kuma ya tashi Bossay da Ayuba sukayi alwala suka tafi masallaci,
Bayan an idar saida suka zauna gari yafara haske sannan suka fito suka nufi hanyar gida da zunmmar suna zuwa zasu shirya su ɗauki hanya,
tundaga nesa suka ga wata motoci a ƙofar gidan da ɗan mamaki suka tsaya suna kallon motoci biyu dasuke ƙofar gidan, ƙarasawa sukayi suna shirin shiga kenan saiga Dadyn Ameesha nan yayi saurin fitowa daga motar da fara'ar sa, yana cewa "ashedai kaiɗinne nagani ɗazu da zan tafi masallaci naga kunfito naga kamar kuna sauri shiyasa banyi maka magana ba, nace bari in aka idar ma haɗu da na fito kuma sai na rasaku shiyasa nace bari inzo inda naga kafito.....
Shima Bossay da fara'ar sa ya ƙarasa tare da tsugunnawa har ƙasa ya gaida shi su Hamza ma duk suka gaidashi,
Sannan Bossay ya ɗora da cewa "Allah sarki ashe da rabon zamu haɗu dan wallahi yanzu muke shirin barin garin muma,
wani yaƙen Dady ya kuma saki sannan yace shikenan ma kaga sai mutafi tare waɗannan fa bansan suba, ko daman kuna da ƴan uwane anan garin bantaɓa sani ba, kasan nan garin mune babu inda bansani ba,
ɗan murmushi Bossay yayi sannan yace "Eh Dady amma muɗan shiga daga ciki ka zauna, duk ƴan uwanane,
Suna maganar suna ƙarasa shiga cikin gidan,
Sauran mutanen da duk suka ɓuya saboda tunkan su Bossay su gansu shi Dady yagan su dan haka da yaga Bossay acikin su gudun yin abun kunya agaban sirikin sa, kuma yana so yagano meye alaƙarsa da shi da yagan sa agunsu su suka saka a ɗauko sa kokuwa duk yana buƙatar amsoshin sa agun Bossay,
sai kawai yacewa yaran suyi sauri ɓuya idan kuma sunshiga ciki su fito su kama gaban su kar yafito yaga wani, idan wani abun ya faru zai kirasu kar suyi nisa,
suna shiga cikin falon Abban Ameesha bai zauna ba yace to me kuma zasuyi yakamata su tafi ai,
Nan suma suka ɗan kintsa jikin su Hamza ya fara shiga wanka, kafin kuma ya fito Bossay ya bawa Dady labarin a gurguje yanda zai fahimta,
Yana gama bashi labarin kuwa Dady harda ƙara gaisawa da Abban Ameesha, cike da nuna alamun tausayi yace "Allah sarki gaskiya ancuceka Allah yasaka maka duk waɗanda sukayi maka haka, wallahi bakaga yanda ƴarka ta zama ba ai agida na take aikatau yarinyar tana da matuƙar hankali gata kamar ku ɗaya babu inda ta barka har yanayin maganar ku iri ɗaya,
Yana ɗan fakar idon sa yaƙara cewa 'ai ni iyalina basu taɓa gaya min ainahin tarihin suba sundai ce su kaɗai suke rayuwar su bayin Allah, bansani ba wallahi da ban bari tayi aiki ba da na taimake ta,
Wani iri Abban Ameesha yaji jin ƴarsa wai aikatau take to duk ina kuɗin da ya barmusu ko kuma cincinye tunda shekarun da yawa, sosai tausayin su yakamasa jikin sa yayi mugun sanyi,
Bossay ne yayi saurin canza maganar gudun kar yaje yayo musu ɓarima Abban Ameesha ya fahimci sauran sun mutu ya ɗaga musu hankali tun anan yafiso idan yaje yaji komai,
Inda yaci sa'a ma suna cikin haka Hamza yafito da shirin sa tare da ɗan kayan da sukazo dasu Bossay sai yace "ai bama da sai yayi wankan ba su tafi kawai duk dan gudun kada hirar tasu tayi zurfi ya tono wasu abubuwan, dan haka ba ɓata loƙaci suka gama komai suka fito, sai Dady yace "kawai ma su tafi a motar sa tunda shi kaɗai ne dan shima yana so ayi wannan aikin ladan dashi ba'a barshi abaya ba dole yaje har inda zasu,
To daman Ayuba ba dashi zasuyi tafiyar ba dan mahaifiyar sa na neman sa da gaggawa saboda baigaya mata zuwan nasu ba, dan haka sai kawai yace dasu suje a motar tasa inyaso shi ya biyo su daga baya yana da wata motar, daman haka suka tsara, to Dady ya nemi hakan sai kawai suka amince da hakan suna ganin hakan sai yafi musu sauƙi ma, akan su tafar masa da mota,
Haka suka shiga motar Dadyn Rasheeda a driver site sai yace Abban Ameesha ya shiga gaba, Bossay da Hamza kuma suka shiga baya, ba ɓata loƙaci suka ɗauki hanyar kano........
tunda suka fara tafiya kowa yayi tsit da abun da yake saƙawa aransa, gudu kawai suke shararawa daman akan titi sakamakon safiya ce babu kowa akan titin......
Bayan tafiyar su da ɗan minti na Ayuba baibar gidan ba saida ya koma cikin gidan yayi wanka shima sannan ya shirya ya fita daga gidan, aƙaladai zaiyi wajen minti ashirin haka sanan ya fito,
yana cikin tafiya ya tuna da yaransa da sukayi masa aiki yace zai tura musu kuɗi dan haka sai kawai ya zaro wayar sa daman yana da account number ɗinsu yana tafiya duk ya tura musu, sannan ya kira Ɗan Ladi dan yagaya masa ya tura musu sannan yaƙara yi musu godiya, yana ɗagawa bayan sungaisa ya gaya masa ya tura musu har zai kashe wayar Ɗan ladi yayi saurin dakatar da shi,
"Sir akwai matsala fa, kai kaɗai ne?
Ayuba yace "Eh ni kaɗai ne me ya faru?
Murya ƙasa ƙasa yace "sir kunyi baƙo ɗazu ko?
"Eh, Ayuba yaƙara bashi amsa.
"Yauwa to wallahi karku yarda dashi shine mutumin da ya ɗauke wannan mutumin da muka kawo muku, tunjiya yakama mu yanzu haka muna wani waje a ƙulle shine yasa akayi mana duka har saida muka faɗi inda kuke, loƙacin ma da kuka dawo daga masallaci muna tare dashi da yagankune yace duk muɓuya kada wanda ya fito,
Saida kuka shiga mutanen sa suka ƙara kamomu suka kawo mu wani wajen daban yanzu haka muna nan angarƙamemu a ɗaki wayarnan ma basu san tana jikina ba,
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un, Inna lillahi wa'inna ilaihi Ɗan ladi, waye wannan mutumin shikenan ai yanzu haka duk ma abun da zai musu ya musu dan suntafi kano tare a motar sama suka tafi,
Shima Dan Ladi cike da damuwa yashiga yin sallati, yace yanzu dai yanda za'ayi ka kirasu kagaya musu tunkan suyi nisa, dan wallahi mutumin nan bashida imani ko kaɗan babu abun da bazai iya yi musu ba bakaga yanda yasa akay......, bamm yaji anturo kofa hakan yasa yayi saurin sauke wayar zai ɓoye amma ina anriga angansa da sauri suka ƙwace wayar suka shiga dukan sa dan sunji wata maganar tasa saboda suna kallon sa ta CCTV camera dake ɗakin,
Dan haka tuni suka hau dukansa ɗaya kuma yace "bari insanar da Oga...... yafaɗa yana zaro wayar sa tare da barin ɗakin......
"Hello, hello Ɗan ladi Ɗan ladi kana jina yanzu kuna ina? kana jina, yana ta magana baima san ankashe ba, saida yazaro wayar yagan ta akashe, kiran number tasa yakuma yi sai yaji anɗaga.,.
Ana ɗagawa yace "Hello kasan unguwar da kuke yanzu kaga yamin zan turo a fito daku ni yanzu zankira su kafin inbi bayan su nasan zan cinmasu dan basu daɗe da tafiya ba, maimakon yaji muryar Ɗan ladi sai kawai yaji ankwashe da dariya tare da cewa muna wajen gidan uwarka ka, ana faɗar haka kuma yaji ƙit ankashe wayar,
Ayuba ji yake kamar yayi hauka gefen titin yasamu yayi parking, tare da saurin lalubo number Dadyn Bossay, saboda bashi da ta su gaba ɗayan su,
saidai kuma sau uku yana kira ba'a ɗaga ba, da yaga ma ɓatawa kansa loƙaci kawai ya yanke shawarar gwanda ma yabi bayan nasu tun kan loƙaci yaƙara ƙurewa yanzu dai yasan duk inda suke yanzu basu fita daga garin Gombe ba idan yayi sauri zai iya kamosu....
A 360 ya kwashi motar shima ya ɗauki hanya yana gudun kuma yana ƙara gwada kiran layin Dadyn Bossay har yanzu kuma ba'aɗaga ba, gudu yake sosai kamar zai tashi sama haka yake jan motar nan,
yana daf zai fita daga garin wata ƙatuwar mota ta tunkaro sa gashi a ɓarin hannun sa take gurin sa take tunkaro wa gadan gadan kuma ta cike hanya amma duk da haka sai yayi ƙoƙari ya daina gudun yabi gefen ta zai sauka daga kan titin, amma ina kafin yakai ga sauka motar har ta ƙaraso kusa dashi tare da dakar gaban motar sa take yafara juyawa aka ƙara buga masa ya motar ta wuntsila can gefen titin, masu babar motar kuma sukayi tafiyar su, suka barsa agun........
***********************
Gudu suke shararawa suma kamar akan titi dan ba ƙaramin gudu Dadyn Rasheeda yake yi ba, sai gashi tafiyar da zasuyi wajen awa biyar ko shida amma baifi suyi awa huɗu ba,
Suna cikin tafiyar kuwa dan ina tunanin ma sun kusa shigowa kano saboda ko awa ɗaya ba lalle su ƙara ba,
kawai basu san ta inda mota ta fito ba sai gani sukayi kawai tasha gaban su sai kuma wasu ta bayan su, dan haka da sauri Dadyn Rasheeda yaja burki ya tsaya,
mutane ne zabga zabga suka fara fitowa daga cikin motacin fusko kin su duk a ɗaure, sunkai wajen su goma sha biyar haka suka zagaye motar, da sauri Dadyn Rasheeda ya buɗe motar ya fito Abban Ameesha ma cike da tsoro da fargaban abun da zai faru ya fito dan yagane mutanen masu gadin sane irin kayan da suke sakawa kenan kuma daman kullum ahaka yake ganin su, shiyasa yayi saurin fitowa dan yasan ma shi suka biyo,
Bossay zai buɗe ya fito shima Hamza yayi saurin riƙeshi yace "ɗau ko wayar ka, kafin su ankare kayi sauri ka turawa Dadyn ka message kagaya musu kawai wasu mutane sun tare mu a akan hanya a biyo tracking ɗin mu, dan waɗannan mutane baza su barmu ba, kayi sauri ni kuma bari in gayawa su Sam duk wanda ya riga gani sai azo a taimakawa bawan Allahn dan bana son wani abun yasame shi, duk wannan zancen yayi sane cikin sauri ƴan sakanni tare da fara rubuawa, shi Bossay harma yagama rubuta nasa ya tura, kuma saida sukayi sharing ɗin message ɗin ga wasu ta yanda za abasu taimakon gaggawa,
Ganin sun rirriƙe Abban Ameesha yasa sukayi saurin fitowa suma, duk wannan bataliyar mutanen kan Abban Ameesha sukayi suna ƙoƙarin jansa amma ya hana kowa dama dake yana da ƙarfi ga kuma zuciyar sa da yazo kusa yagama kaiwa ƙarshe ji yake babu abun da bazai iyaba ga duk wanda ya kuma yunƙurin rabasa da ƴan uwansa iya ka ƙarfin sa yake sawa wajen kaiwa duk wanda yazo zai taɓasa duka,
Su Hamza kuma suna fitowa tuni wasu mutum biyu sukayi ran dasu suka hanasu ƙarasawa inda yake, Dadyn Rasheeda ma riƙe shi akayi,
Sauran kuma duk suka tararwa Abban Ameesha tun yana yi da jiki har jikin sa yafara gajiyawa yadawo kai dukan a hankali daga ƙarshe ma sai ya kasa kawai ya zube awajen ga gajiya ga baƙin ciki sai kawai yasa kuka, cikin kuka yace dan Allah ku kasheni ku huta ku kasheni burin ku ya cika wai me nayi muku me nayi muku kuka zaɓi ƙuntatawa rayuwata, baigama rufe baki suka rufe sa da duka...
Dadyn Rasheeda har da su kuka, yazo kusa da su yana tsugunnawa dan Allah ku rabu dashi me yayi muku idan kuɗi kuke so kufaɗi ko nawane ni zan baku amma ku rabu dashi kada ku cutar na roƙeku kunji dan Allah ku rabu dashi,
Babu wanda ya saurare sa da suka gaji da dukan nasa sai kawai suka fara jansa, zasu sakasu a mota,
Hamza ne ya gama kaiwa ƙarshe shima tuni ya turar da wanda ta riƙeshe yayi kan su yana zuwa ya shiga sauke musu naushi duk wanda ya nausa sai yaja baya dan ba ƙaramin bugu yake kaimu su Bossay ma da yaga haka sai yasamu ƙarfin gwiwa, daidai tsinin gwiwar sa ya saita adaidai wajen alulun wanda ya riƙe shi ya taƙarƙare ya buga masa agabansa take azaba tasa mutumin yasake sa yasaka hannu akai yana tsalle dan yaji zafi ji yayi kamar ransa zai fita,
Nan faɗa ya kauraye tsakanin su kowa nayin iyaka ƙarfinsa, suna ƙoƙarin ɗauke Abban Ameesha, su Bossay kuma na ƙoƙarin hanasu........,
[15/11, 10:53 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
*_🅿️36_*
___'Nan faɗa ya kauraye tsakanin su kowa nayin iyaka ƙarfinsa, suna ƙoƙarin ɗauke Abban Ameesha, su Bossay kuma na ƙoƙarin hanasu........,
.......haka sukai ta kokawa, zuwa yanzu kuma su Hamza jikin su yafara sanyi duk ƙoƙarin su amma dake sunfisu yawa dole suci galaba akansu.
"babu yanda suka iya suna gani aka aka ɗauki Abban Ameesha aka saka amota suma kuma ɗaya bayan ɗaya duk suka kwashe su suka zubasu amotar gaba ɗaya suka tattara su amotar su,.
Dadyn Rasheeda kuma suka sakashi a motar sa, wasu mutum biyu suka shiga ɗaya yaja motar ɗaya kuma ya zauna a gefe motar suce tafara yin gaba, sannan ta sauran suka bi bayan su,
Wani shu'umin murmushi Dady yake ta saki, kwantar da kansa yayi ajikin kujerar, sannan ya zaro wayar sa yayi danne danne ya dannawa wata number kira, ana ɗaga yasaki dariya yace "angama komai dan ma sunɗan bamu wahala da tuni mun taho tun ɗazu yaran akwai ƙarfi bakiga yanda suka wahalar da kansu ba, Allah ya taimake mu dai yanzu munci nasarar ƙwamishe su. Kina ina ne yanzu? shiru yayi yana sauraron ansar da ake basa..
"To shikenan muma yanzu zamu shigo cikin garin, amma fa gaskiya bazan ƙara sakaci ba asirina ya tonu dan indai suka gansa kinsan sai asirin mu ya tonu dan haka muna zuwa zansa akashe shi, ni bansan dalilin da yasa kika hana akashe shi, yanzu gashinan barin sa yana neman yajawo mana matsala, shiru yayi yana jin maganar da akeyi daga can ɓangaren,
Tsaki yaja sannan yace "wallahi baki isa ba mu zuba mugani ni zaki kawowa maganar banza bari zanzo insame ki, kuma kisa aranaki ina muashigowa garin Kano zai mutu dole ya mutu dan bazan taɓa barin sa yaci gaba da zama ba a duniyar nan, kina gani tunda waɗancan yaran sun gansa kina tunanin zasu shiru da maganar inba ganin gawar sa sukayi ba, baza suyi shiru da bakin su ba, dan haka nagama yanke shawara yauce ranar mutuwar sa. Yana kaiwa nan baima jira amsar taba ya kashe wayar gaba ɗayan tama saboda karma ta kirasa,
sukaci gaba da tafiya yana ta saƙe saƙe kala kala na yanda zai tsara komai yatafar masa yanda yake so,
***********************
Baban Bossay fitowar sa daga wanka kenan yaji ƙarar text ya shigo wayar sa shareta yayi babi takan taba, ya wuce ya cigaba da shirin sa, har yagama kintsawa, ya ɗauki wayar sa, yama manta da jin