Showing 18001 words to 21000 words out of 170049 words
babu reboon akanta shima kuma basiyo mata ba,
Dawo da ita bakin gadon abubuwan da ya shigo dasu ya dawo dasu gabanta ya ware ledar snaks ɗin ciki ya zuba a plate ɗin ya zuba mata holandiyan aciki, sannan yace ta sauko ƙasa,
Ba musu ta sauko ta zauna duk abun da yace mata yi take takasa yi masa musu,
Hannu tasa zata ci ya dakatar da ita ya ɗauko zai bata ta girgiza masa kai tare da cewa "nagode amma kabarni zanci da kaina, rabuwa yayi da ita,
Yana gurin zaune a gabanta har tagama ci tace masa ta ƙoshi, saida ya tabbatar ta ƙoshin sannan ya haɗe kayan, ya fita dasu ya dawo,
kan kujerar ɗakin ya koma ya zauna yace itama ta dawo ta zauna ba musu ta tashi ta dawo ta zauna gefen sa, tare da sunkuyar da kanta ƙasa, tana kallon yatsun hannun ta ranta cike da tambayoyi,
Gyara zaman sa yayi yana facing ɗinta da kyau yace "kibani hankalin nan, itama juyowa tayi tana kallon nasa, cike da haɗo duk wata nutsuwar ta gare sa,
Ɗan gyaran murya yayi sannan yace "ko bantambaya ba nasan abun da yafaru dake agidan da nakaiki ina mai baki haƙuri nima bansan haka zai faru ba bantaɓa tunanin halinta haka yake ba ƙanwar kaka tace, yanda na ɗauki Ammah haka na ɗauke ta bansan muguwa bace banyi haka dan na cutar da rayuwar kiba na ɗauko kine dan na taimaka miki kiyi haƙuri da duk abun da sukayi miki kuma nayi miki alƙawari zan ramamiki duk abun da sukayi miki babu wanda zan ƙyale daga cikin su, kigaya min duk abubuwan da sukayi miki,
Amma kafin inji abun da sukayi miki inason kifara bani labarin ki kuma ina mahaifiyar ki take nasan matar da naganki da ita ba itace ta haife kiba, kuma shi mahaifinki baya ɗaukan mataki akan abun da take ne ko kuma shima bashi ya haife kiba,
shiru tayi na ɗan wasu loƙuta tana tunanin tagaya masa ko karta gaya masa sai kuma tayi tunanin inbata gaya masa ba watake dashi aduk faɗin duniyar nan da yafishi kulawar da yabata a iya haɗuwar su ko mahaifinta baya bata irin ta bare kuma mahaifiyar ta da kallo ne kawai yake gaɗata da ita,
Cikin sanyin murya tace "shine ya haifeni ubanane kuma uwata bani da kowa da ta wuce, duk da kasancewar mahaifiyata tana raye amma da ita da babu duk ɗaya ne awajena bata da wani amfani awajena nayi danasanin kasancewa ta ƴa agare ta ko a hanya banason anuna min ita ko a kirata amatsayin mahaifiyata bana so banaso kuma bazan taɓa so da kasancewar ta araye gwara intaso acemin bata raye gwara intaso akirani da tsintacciya wacce ba asan ko wacece ba, bana son ta bana son ganin ta bana son zancen ta bana son tunata kukane yaci ƙarfinta yasata dakatawa da zancen da take..........✍️✍️
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️xeemat...love❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
Agurguje naji wata tace anbawa sumayya muhuimmanci da yawa to bari ayi komai ataƙaice yazama dole ne abayar shiyasa, amma bari intaƙaitashi, inkunlura da yanayin tsarin rubutuna ban iya taƙaita labari bane yadawo ɗan kaɗan shiyasa kukaga haka kowa idan nazo kan abu sai na fayyace sa nafiso inyi komai dalla dalla, amma dai kar ku damu zanyi ƙoƙari inkoyi taƙaita labari. yanda zamu fi saurin gamawa da wuri, ina ganin hakan sai yafi ko ya kukace???????????
"""""""""""""""""""""""""""""""""""""
__________Ahaka yaci gaba da rainon ƴarsa wajen watansa ɗaya shine yayi samu yayi aure inda ya auri matar da take wahalar da a yanzu,
Tunda ta girma tafara hankali take fuskantar ƙalubale kala kala, harmahaifin ta yabata labarin ta inda ta nemi nahaifiyar ta har inda take take tasame ta amma taƙi kulata tayi mata korar cin mutunci tundaga nan bata ƙara zuwa inda take ba, itama kuma bata ƙara neman taba, har yauɗin nan,
Gashi matar mahaifin nata bata ƙaunarta, ko kaɗan, kuma ta asirce mahaifin nata, dan haka ita yanzu gatan da mahaifinta yake mata sai yaragu sosai wataran ma agabansa za adaketa amma baya iya hanawa, shima kansa abun na damun sa amma yarasa yanda zaiyi, matar sa ta gaje komai, gaba ɗaya ta canza masa halayen sa,
Haka kuma ɓangaren mahaifiyar sa baisamun rangwame indai akan sumayya ne, kuma halinta ma yana nan bata canza ba, ina fatan kun fahimci kowacece mahaifiyar mahaifin sumayya (RABI'U) wacce ta riƙe ABU (mahaifin Meer), tare suka taso da mahaifin sumayya, azaba iya azaba tayiwa Abu loƙacin da yake hannun ta,
Sumy ta ɗora da cewa, tun ina ƙarana nake aikin gidan mu ina da ƙanne maza biyu mace ɗaya amma basa komai acikin gidan ni kaɗai nake komai na gidan harda wankin su da na mahaifiyar su, duk wata wahala Ni nake yin ta acikin gidan idan kuma taga dama hakanan sai ta kamani da duka da zagin iri iri da ni da mahaifiyata, banda wani kwanciyar hankali acikin gidan nan, makaran tama da ƙyar nasamu na kammala secondry ƙanwata har ta shiga University amma ni ina zaune ina yi musu bauta,
Ranar da kuma ta koreni daga gidan saboda mahaifina ya ɓata shine ta koroni tace inje duk inda yake innemo mata shi, ina tsoron sanar da ita halin da yake ciki shiyasa nace mata bansan inda yake ba, shine ta koroni sai naje na nemoshi, zan dawo gidan,
Kuka ta fashe dashi tace wannan wacce irin rayuwa ce nake fuskan ta a rayuwa ta duk inda naje bana sa'a babu wanda yake sona, nayi tunanin da kaɗauke ni ka kaini gidan nan zan samu sassauci daga wahalar da nake sha saidai kuma tasu wahalar ma tafi wacce nabaro ni yanzu babu inda zanje inji daɗi arayuwata, Ni nasan da bakaje ba na tabbatar da wahalar su zan mutu, domin sunce sai sun kash......, Shiru tayi bata ƙarasa ba ta sunkuyar da kai saboda tuna gargaɗin da sukayi mata idan tasake ta faɗawa wani ko da wasa,
Cikin ɓacin rai Sam yace "kashe ki!? SU WAYE SU!!! Ya miƙe tsaye cikin ɓacin, riƙota yayi yace mai sukayi miki gaya min,
Ta tsorata da yanayin sa sai kawai ta dakata da kukan da take tace, "calm down plss ka bar maganar tundade yanzu komai ya wuce gashi na samu ka kuɓutar dani daga hannun sa babu abun da zance maka sai godiya sannan in godewa Allah da yakawo min kai cikin rayuwa ta,
ƙwace hannun sa yayi yace " I can' kigaya min!! yafaɗa cikin ɗaga Maurya,
Cikin sanyi murya tace "matar da kakeni tun aranar da kakaini......nan ta bashi labarin abun da yafaru ranar da yakaita, sannan ta ɗora dacewa a ranar ma a waje suka turo ni na kwana, sannan kayan jikin na da naje dasu suka saka nacire su suka bani wannan riga da wandon na saka, suka sallami mai aikin su ni nake komai na gidan sai abani aiki mai yawa ace kuma a ƴan mintina kaɗan zanyi sa idan banyi ba kuma ita da ƴarta su haɗar min suna duka, jiya kuma ina yima yarinyar gidan tana dukana, ahaka nagama aikin ga wankin motocin su gaba ɗaya ni nake da bawa fulawowi ruwa, da sharar compound ɗin gidan sau uku arana,
Wai so suke idan nakai sati biyu ina aikin daga ƙarshe kuma sai su kashe ni, wai na haɗu dakai acan saboda suna tunanin da kwai wani abun a tsakanin mu, musamman yarinyar gidan tana kishi dani hakanne yasa take min muguntar ma fiye da ta mahaifiyar ta, amma dan Allah na roƙeka ka rabu dasu su da Allah, yanda sukace maka na ɓata kawai kabisu a hakan kar ka bari wannan abun ya shafi family ɗin ku dan wata ta waje, banason yazamana ta sanadin taimakon da kayi min yaza nice silar ruguza muku zumunci, ni komai ya wuce agurina, zan koma inda na fito,
Kallon ta kawai yake yana kasa buɗar bakin sa saboda yanda tabasa labarin wuyar da suka bata, amma wai take cewa ya rabu dasu hakan ba ƙaramin sagar masa da gwiwa, amma duk da haka sai yabi mata haƙƙin ta,
cike da rashin karsashi yace, ko mai zai faru saidai yafaru amma bazan taɓa barin su ba sai sun gane kuren su,
Shiru tayi takasa basa amsa saboda batasan me kuma zata ƙara ce masa ba,
Shiru yayi shima yana tunanin labaran da tabasa dalla dalla yashiga yi musu yana nazarin ta ina zai fara nemo mata mafita, ya tausayawa rayuwar ta sosai kamata yayi daga tsayen da suke ya zaunar da ita agefen sa,
Shiru sukayi gaba ɗayan su na ƴan daƙiƙu saidaga baya Sam ya ɗan nufasa yana kallon ta sannan yace "kiyi haƙuri komai mai wucewa ne, wataran sai labari, kuma nayi miki alƙawari sai na bi miki haƙƙin ki akan duk wanda ya zalince ki kuma in sha Allah zan sasan ta tsakanin ki da mahaifiyar ki duk inda take zam nemota kuma zata dawo gareki sai ta baki haƙirin duk abun datayi miki sannan zakiyi rayuwa da mahaifiyar ki kamar yanda kowa ne ɗa yake in Allah ya yarda zata dawo gareki nan bada daɗewa ba kinji ki kwantar da hankalin ki manta da komai,
Sosai taji daɗin kala mansa ta fara jinsa aran ta, cikin kuka tashiga karkaɗa masa kai tace, dan Allah kabarni kawai ka rabu da ita nayi alƙawarin bazan ƙara zuwa inda take ba tunda har bata buƙatar gani na, Ni yanzu hakama bansan inda take ba dan haka mubar maganar kawai yanzu kakaini gidan mu zanci gaba da rayuwa ta kamar yanda nake ada nagode da taimakon ka agareni, tunda nake bantaɓa haɗuwa da wanda ya kula dani ba kamar kai uwar sa ta tsugunna ma ta haifeni ta tafi ta barni amma kai ka tsaya ka kula dani, a loƙacin da nake buƙatar hakan, Nagode Nagode Nagode....,
Hannu ya ɗaga ya dakatar da ita yace "kiyi shiru kawai ya isa haka maƙarasa maganar anjima ni yanzu zan fita, ki kwanta zanje na dawo, yana kaiwa nan ya miƙe tsaye, itama tsanyen ta tashi tasha gabansa da sauri, tace dan Allah ka mayar dani gidan bazan iya zama anan ba ina son ganin mahaifina,
kallon ta ya tsaya yi saida ta gama sannan yace "nace miki ba yanzu ba kiyi abun da nace miki kawai ina dawowa, ja da baya tayi ƙwalla naƙara cika mata, saboda ba haka taso ba so take kawai ta ganta agidan su,
Baibi takan taba yayi gaba saboda bayaso tagane gazawar sa dan labarin ta baƙaramin dakar sa yayi ba, ya taɓa masa zuciya sosai, kuma aransa yayi alƙawarin daga rana irin tayau bazata ƙara kukan wani abun ta rasa ba, sai yazame mata gatan ta, babu inda zata ƙara zuwa batare dashi ba, duk inda take zai kasance da ita yabata kulawa fiye da tunanin me tunani...... A haka ya fice daga ɗakin cike da tunane tunane.......,
************************
_________MeeshMeer
Batare da Meer ya kalli Ameesha ba yace "gaya min me yake faruwa ke kika turon video awayata ba,
Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke jin maganar da yayi daman tarasa ta inda zata fara yi masa bayani ashe ya gani ko shiyasa yayi mata shiru duk abun da take masa bai hukun tataba,
"Magana nake miki...,
Ta ƙara jin maganar sa ta dake ta da sauri ta dawo da dubanta gare sa tare da gyara zama, saida ta tattaro nutsuwarta gaba ɗaya ta nutsu sosai sannan ta shiga basa labarin duk abun da yafaru, loƙacin da sukaje kiransa suka tarar da abun da kuma ɗaukar da sukayi har suka zo ɗakin sa suka tura masa,
Tana gama basa labarin duk wani abun da yafaru ya shiga dawo masa akai atake agun ya tuna komai,
Dafe kansa yayi yana girgiza kai sannan yana jinjina irin wannan lamarin nasu, ashe yanda yake ɗaukar abun yafi haka,
"Suna dayawa kenan?
yafaɗa afili tare da ɗagowa yana kallon Ameesha, itama da shiɗin take kallo, kai ta ɗaga nasa, sannan tace yanzu ya kake ganin za ayi, maiye mafita dan nifa wallahi mutanen nan sun fara ban tsoro kodai mu sanar da su maama kar suje batare da kowa yasani ba su ƙara yi mana wani abun musamman ma idan sukaji munɗauki muryoyin su, baza su barmu ba,
Jinjina kai yayi, yace "babu abun da suka isa suyi, amma dai kar kuƙara fita daga part ɗin har sai nace ku fita daga ke har ita ɗin, yanzu ki tashi kije zan nemeku gobe, kafin wannan binciken inason inyi wani binciken ne dan wannan nagama dashi komai yazo ƙarshe tunda aka samu hujjoji basu da wani abu da zasu iyayi,
sannan kuma koda sun nemi da ku basu memoryn ku basu har wayar ma, amma kafin nan kikawo min wayar zanyi wani abu da ita inbaku,
Cike da gamsuwa da maganar sa tace to shikenan yanzu inje in kawo maka wayar ko itama sai a'a yanzu zaki kawo min,
Tashi tayi da sauri tace "Tom bari inkaɓo ta, tana faɗa bata jira amsar sa ba ta fita daga ɗakin cikin sauri,
Bayan ta fita ba daɗewa ta dawo da wayar a hannun ta, gabanshi tazo ta miƙa masa sannan ta koma inda ta tashi ta zauna,
Daddana wayar ya shiga yi sannan yace ta dauko memoryn inda suka ɓiye nan ma dai tashi tayi ta duba inda suka ajiye ta ɗauko ta bashi, yana karɓa yasaka awayar yagama danne dannen sa sannan ya miƙa mata wayar yace zaku iya fitama duk sanda kuka ga dama sannan inaso anjima da daddare zansa wani daga cikin ƴan gidan nan zai fita daku zaku karɓo min saƙo awani waje idan kun fita zan gaya masa inda zakuje, kuma baku biyu ba har sauran yaran nan twins kuje ku taho dashi kuma banason kowa yasan da fitarku karkigayawa kowa ma zaku fita kawai kisan yanda zakiyi kifito dasu har gurin motar cikin dabara batare da wani yaji zaku fita ba kin gane?
"Eh tace masa, amma ina zamu baka ganin zasu iya binmu karfa su sa a kashe mu, nidai wallahi tsoro nake ji,
Taƙasan ido yake binta da kallo sannan ya girgiza kai, yace "banason shashanci ke kaɗai ce dazasu kashe ki kuma taya ma za ayi su san da fitar ku saidai idan faɗawa wani kikayi, amma in ba hakaba babu wani abu ni banason fitane kuma saƙon yana da muhimmanci ne daga yamen aka kawo min bazai yiyu in aiki wani bare ba daban za a iya samun matsala, shiyasa na aike ku, kuje kawai kiyi addu'a babu abun da zai faru,
Itadai har ga Allah batayi na'am da fitar nan yau ba kuma yauɗin ma da daddare dama zai bari sai zuwa gobe da safe ido na ganin ido yanda duk ma wanda yabi bayansu zasu gansa ta cikin ido amma ya za 'ayi yanda a kasan sunsan komai ɗin nan kuma yace su fita sukaɗai,
A fili kuma sai tace masa to shikenan Allah ya kaimu anjiman, zan iya tafiya, ɗaga mata kai yayi kawai loƙacin wayar sa tana hannun sa yana daddan nawa,
Miƙewa tayi idon ta yana kansa, ji take kamar tace masa dan Allah yayi haƙuri basai sun fita amma tana jin tsoron kar ya fusata ya mammagare ta tasan kaɗan daga cikin aikin sa kenan,
Ganin yana shirin ɗagowa yasa tayi saurin ɗauke idon ta akan sa ta juya ta fice daga ɗakin, bin bayanta yayi da kallo yana girgiza kai, sannan ya jawo laptop ɗinsa ya buɗeta yafara aiki......,
_____Waziri ne tsaye a cikin ɗakin sa yana ya kaiwa da kawowa yayin da matar sa ke zaune kan gado itama ta zabga tagumi,
Miƙewa tsaye tayi ta taka taje gaban sa, sannan tace "Wai har yanzu ka kasa samo mana mafita, idan fa muka bari waɗannan yaran suka nuna videon nan akwai fa matsala yakamata muyi gaggawar katse su ayau ɗin nan duk wata hanya da zatasa su nuna videon nan mubi mu tosheta kafin wankin hula yakaimu rana, dankwa duk wanda yagani bamu da bakin kare kanmu tunda mune kuma muryoyin mune, amma kai yakake gani,
Shiru yayi bai bata amsaba sai daga bisani ya ɗan numfasa tare da furzar da iska mai ɗumi daga bakin sa, yace "Anzo wajen Anzo wajen dole kowa yayi ta kansa ɗan ƙaramin zaki ya girma, ko ince ƙananun zakuna sungirma, indai har abun da shu'aibu yafaɗa gaskiya ne abun da yace sunfaɗa ɗin to bamu da hanyar da zamu kuɓutar da wannan videon da suka ɗauka, tunda suka ɗauka dole sai sun fallasa sa, amma dai zamuyi ƙoƙarin karɓe wayar tasu wannan aikin kine kisaka adaren nan a ɗauko mana yaran idan muka tsorata su zasu faɗi inda yake zasu bamu,
Cike da zaro idanu tana rarrabasu tace "bangane maganar ka ba kana nufin dole sai ansan da videon nan to ya kake so inyi da rayuwa ta kuma shikenan burinmu bazai cika ba ko mai kake so kace min, ko kana ganin idan videon ya fita, za'a rabu damu baranta na har mucika burin mu na shekara da shekaru da muka ɗauka muna ɓata loƙacin mu,
Bakin gado ya samu ya zauna yace "kusan hakan amma dai da yardar Allah ma hakan bazata faruba, saidai rashin faruwar sa ne abun da kamar wuya,
Itama cike da ɓacin rai ta ƙaraso gaban sa tace mai kake nufi mai yasa kace haka, mai yasa baza ku koma gurin boka mai yi ba, ya kamata kuje a ƙara rufe bakin kowa