Showing 105001 words to 108000 words out of 170049 words

Chapter 36 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7207

yake yayi kuka ma ko yasamu sassauci amma yakasa zuciyar sa ta bushe,

"Kayi haƙuri Babana addu'a zakayi musu, tunda kaidai kadawo lafiya shikenan abun da nake fata kenan, babu da zance sai dai inyiwa Allah da ya nuna min ranar da zaka haɗu da iyayen ka da raina da lafiya ta wannan abun yafimin komai farin ciki,

Girgiza kai ya shiga yi sai yanzu hawayen suka samu damar zubowa, "a'a Umma kidaina wannan maganar dan Allah kar ki kuma cewa su mutu ina son ganin Noori a raye dan kice min bata mutu ba, yama miƙe tsaye dan ji yayi duk wani farin cikin da yake ciki ya neman gushe mishi burin sa kawai yasa ta a idon sa dan ji yake in ba ita bazai iya rayuwa ba idan babu ita saboda tsananin son da yake mata,

Da ƙyar aka samu ya koma ya zauna aka shiga rarrashin sa da basa haƙuri kowa saida yasa baki, sannan ya daina surutan da take ya kamo Ameesha ya rungume ta yana ƙara jin ƙaunar ta aransa dan ita yake gani kamar Norri ɗin sa, duk wanda yagan sa a wannan loƙacin sai ya tausaya masa,

Cikin tsananin damuwa Abban Ameesha yace "duk wanda yakashe su bazan taɓa yafe masa ba sun cutar da rayuwata sannan kuma sunje sun cutar da wasu akan meyasa zasu kashe su bayan inma laifi ne ai ni nayi musu binne yasa basu kashe ni ba, ni da rayuwar da suka nayi ai da kashe ni sukayi, sun kaini waje guda sun ajiye ni, tunda suka fito dani daga prison ban ƙara ganin kowa ba nayi rayuwa cikin wani irin hali wallahi da rayuwar nan gwanda mutuwa gashi bansan su waye sukayi min haka ba, bansan me nayi musu ba, kuma abun ya wuce kaina ya koma kan matata da babana bawan Allahn da baiji ba bai gani ba,

Maganar yake cikin ɓacin rai da damuwa dan shi abun duk da yafi ɓata masa rai kashe sun da a'kayi inya tuna duk dan saboda dashi suka shiga wannan halin sai yaji yama tsani rayuwar gaba ɗaya,

Itama Dadda tana kuka tana basa haƙuri da nuna masa haka Allah ya tsara bashi yaja ba, daman ko dashi ko bashi Allah yayi Nadeeya da malam bama su tsawon rayuwa bane, ka manta da komai, yanzu babu abun da ka rasa, ga ƴarka ga iyayen ka babu wanda ya rasa ransa, gaka acikin dangin ka martaba kima daraja mulki duk ka haɗa, dan haka kaman ta da wata damuwa,

Saboda halin da yake ciki ma ko amsa bai bata ba dan maganar tama so tayi ta ɓata masa rai taya za'ai ta manta da matar sa, dafe kansa kawai yayi shi kaɗai yasan halin da yake ciki...

Ran Meer ba ƙaramin ɓaci yayi ba ganin halin da Uncle ɗin sa ya shiga atake a loƙacin yanayin sa yafara dayawa daga farin ciki zuwa baƙin ciki har hannun sa yake damƙewa saboda yanda zuciyar sa take tafarfasa. Sai yanzu ma abun yake ta ƙara dawo masa suka ɗauke shi tsawon loƙaci suka rabasa da komai nasa sun kashe masa mata, ya ɗauki alƙawarin koma waye yayi masa haka bazai taɓa ƙyale saba sai yayi masa hukunci me tsananin kuma yanda suka sa yayi rayuwa batare da kowa nasa ba, suma baza su ƙara rayuwa awaje sai sun ƙare rayuwar su a gidan yari, (life in prison)

Saida komai yaƙara lafawa dan har ana shirin atashi daga zaman, Meer yace wa Abban Ameesha zai iya sanin prison ɗin da aka kai shi, da mutanen da suke zuwa gurin sa ko kuma babu wanda yake zargin zai iya aikata masa haka, ko agurin aikin nasu babu wanda suka taɓa samun saɓani dashi,

Nan yace masa shi babu wanda wani abun yataɓa haɗasu, kawai mugun tace amma babu abun da yayiwa kowa,

Nan Meer yace to zuwa gobe zai fara bincike dan bazai bari wannan binciken ya ɗaukar masa loƙaci ba dan inbai hukunta su ba zuciyar sa baza ta taɓa samun sukuni ba,

saida suka ɗan tattauna sosai akan yanda zasu ɓullowa lamarin sannan aka sallami kowa yakama gaban sa, saboda dare yayi sosai wajen ƙarfe shaɗaya,

Dadyn Rasheeda akace akaishi part ɗin baƙi saboda yanzu dare yayi, amma sai yace gida zai tafi da haka, tare da Bossay da Khalid suka tafi, idan su ka kai shi sai su wuce,

Abuu ne yace Abban Ameesha a part ɗin sa zai zauna, daman kuma in ba nan ɗin ba babu inda zai zauna a part ɗin Maama, Meer yace ma su zauna a ɗaki ɗaya akace bazai yiyu ba gwanda kawai yaje ya zauna shima ana sa ɗakin,

gaba ɗayan su a part ɗin Su Papa suka ƙara taruwa saida suka ci abinci sannan suka tashi kowa ya nufi makwancin sa yau ansamu har Meer akaci abinci, ba sabun ba yau sunci darajar Abban Ameesha, kafin kuma su tashi saida aka sanar da Abban Ameesha, auren da aka ɗaura tsakanin Meer da Ameesha, yaji daɗi kuwa dan ko basu haɗa ba shi da kansa sai ya haɗa dan yaron yagama yi masa, yasan idan ya aure ta zata samu kulawa(tabb jama'a Abban Ameesha baisan ɗayar kalar Meer ba, kallon ba ruwan sa yake masa)

Ameesha ce ta nace wai sai ta bishi sun kwanta tare amma sai Maama tace mata a'a ga ɗakin mijin ta ina zata ta kwanta, kunya ma bata barta tabawa Maama amsa ba, shiyasa tayi shiru, dan a yanda aka gayawa Abban ta ba agaya masa basa so ba, shiyasa bata so tayi wani abu da zaisa ya fahimci bata so tunda taga yaji daɗin hakan tunda aka gaya masa yake ta faman murmushin jin daɗi.....,

Abuu da Ummy da Abban Ameesha sun ka miƙe zasu tafi, har sunkai bakin ƙofa Ameesha ta miƙe tace bari ta rakasu, Abban ta yace to ta taho amma
kyataho ke kaɗai dawowa fa wazai dawo dake kiyi zaman ki kawai, maƙe kafaɗa tayi tana turo baki tace ai zan iya dawowa abun da ko ina da mutane,

Maama ce tayi caraf tace"A'a baga wani ɗan rakiyar ba tashi kuje sai ku dawo tare tunda ta nace sai tayi rakiyar,

Ba musu Meer ya miƙe yace "muje, tare suka fita ajere gwanin sha'awa Ameesha da Meer suna gefe gefen sa, sai su Abbu da Ummy a bayan su, haka suke tafiya har suka ƙarasa part ɗin dan saboda daman ba wata tafiya zuwa canɗin,

Saida suka kai Abban Ameesha har ɗakin da zai kwanta sannan sukayi masa sallama, kamar kar su rabu haka suke ji dole suka barsa suka fito yana ta tsokanar su wai su kula da junan su kar wani abun yakama su kafin suje, bayan fitar su yakasa zaune yakasa tsaye, har yanzu ganin abubuwan da suke faruwa kamar mafarki kamar ba gaske ba,

Suna fitowa suka yiwa su Abuu sallama sannan suka fita, da sauri Ameesha tayi gaba ta saɓa tafiyar tasu dan bataso su haɗa hanya dashi, bare kuma su haɗa kafaɗa da kafaɗa suna tafiya tare, gashi haushin abun da yayi mata ɗazu take ji har yanzu,

Yana kallon ta yanda take ta faman sauri zuba mata ido kawai yayi yana ci gaba da tafiyar sa hankalin sa kwance,

tana ƙarasawa part ɗin ta tura ƙofar ta shiga tana shiga bata tsaya ko ina ba ta nufi ɗakin su, tura ƙofar tayi sai tajita arufe ƙwanƙwasawa ta shiga yi, amma bataji an amsa ba, sai ta fara kiran Dadda, Dadda Dadda Dadda ki buɗe mundawo nan ma dai shiru,

Tana cikin haka Maama ta fito daga nasu ɗakin, tace "ya akai ne kina ta bugu wataƙil tayi bacci kinsan tagaji yau da yawa saboda fitar da tayi ɗazu ga kuma abun da yafaru kinsan ta da baccin wuri yau kuma batayi ba shiyasa bata jiki ba, ya kamata ki rabu da ita kar kitashi ta kije ɗakin sa kawai kiyi kwanciyar ki inyaso gobe sai ki dawo,

Turo baki tayi kamar zatayi kuka tana shirin yin magana, Maama tace kinga wallahi kar ki sake ki tashe ta idan kuma bazakije ba sai ki kwana anan gurin kar kiƙara damun mu da bugun ƙofa kinga tafiya ta, tana faɗa mata haka tayi tafiyar ta,

Baƙin ciki kamar ya kashe Ameesha haka take ji, babu yanda ta iya dole ta haƙura da bugun, amma ta ƙudurci bazata kwana a ɗakin sa saidai ta kwana a falo,

tana juyowa tayi karo da Meer dake tsaye agun, duk maganar da sukai da akan kunnen sa, suna haɗa ido da ita ya wurga mata harara ya girgiza kai, bai gama janye idon sa ba, kawai yaga ta rama hararar da yayi mata harda murguɗa masa baki,

Zaro ido yayi yana kallon ta da mamaki, ita kuma sai tayi saurin canza fuska zuwa kalar dan batayi tunanin zai kamata tana ba, tayi tunanin yana hararar ta zai juya,

Girgiza kai yayi shikaɗai yasan me zaiyi mata dan haka sai ya rabu da ita a loƙacin ya juya ya tafi ɗakin sa,

Hamdalah tayi a zuciyar ta harda sakin murmushi jin daɗin baiyi mata komai ba,

Kan kujera tazo ta zauna sai kuma taƙaici ya kuma kamata yanzu duk ɗakunan gidan nan a falo zata kwana ita kaɗai ita da bata saba kwana ma ita kaɗai ba, anya kuwa zata iya, sai wata zuciyar tace to in baki kwana ba a ina zaki kwana, a fili kuma sai tace ai wallahi da dai in kwana aɗakin sa gwanda ingwammace na kwana anan ɗin,

kwashe fulillikan tayi daga kan kujerar da zata kwanta gashi abun taƙaicin lace ne ajikin ta kuma bata iya kwana da manyan kaya ba, haka ta kwanta ta ɗan rufe fuska ta da mayafin jikin ta, shima kuma ɗan yalolo ne baida kauri, bazai tare mata sanyin da take jiba,,

Haɗe jikinta tayi ta kwanta ahaka bata daɗe ba kuma bacci ya ɗauke ta,

Meer da ya shiga wanka yayo yayi Sallah sannan ya saka kayan bacci, har ya hau kan gado ya kwan ta sai kuma ya tuna da ita, saukowa yayi ya fito wajen falon yana ganin yanda ta haɗe guri guda da alamun sanyi take ji daman kuma yasan hakan zata faru,

Aransa yana jinjina taurin kai irin nata yanzu tana ganin da ta shiga ta kwanta gwanda ta kwanta anan ko tsoro ma bataji, rasa me zai yi mata yayi yasan inma ya tashe ta ba shiga zatayi ba kuma ma baya son raini kar taga kamar ya damu da ita dan haka sai kawai ya fasa, dan mugun ta ma sai yaje ya kunna mata fanka sannan ya ƙure Ac yakaita har ƙarshe, sannan yayi tafiyar sa, harda ɓiye remote ɗin Ac,

Yana shiga ɗakin sa ya haye gado ya kashe ƙwai yayi kwanciyar sa,

Can cikin dare Ameesha ta farka sanyin yayi mata yawa har karkarwa take zaune ta tashi tana haɗe jikin guri ɗaya sai kawai ta fashe da kuka,

Haka taita kuka babu me jinta bare yazo wajen ta...,


Yana cikin bacci ya ringajin kamar sautin kuka tun yana jin sa abun har yafara yi masa yawa, saboda kujerar da ta kwanta akusa da ɗakin sa take, buɗe idon sa yayi still yaci gaba da jin kukan ashedai da gaske ne kukan da yake ji ba 'a mafarki bane,

Tsaki yaja kawai ya sauko dan yasan itace, cike da zafin rai ya fito zai sauke mata masifa, amma yana taka ƙafar sa a falon yaji wani irin sanyi ya ratsa masa jiki, shi kansa falon gaba ɗaya ya ɗau sanyi,

Yanda yaga ta takure tana ta kuka da karkarwa, sai kuma yaji tabasa tausay, tsigar jikin sa ce ta miƙe gaba ɗaya loƙaci ɗaya saboda sanyi da ya ratsa sa,

Gurin ta ya ƙara sa, saboda sanyin ma da yake ji bazai iya tsayawa a falon ba yayi mata magana sai kawai yajawo hannun ya miƙar da ita tsaye ya fara janta dan yasan idan yace ma zaiyi mata magana zata iya ɓata masa loƙaci,

yana shiga ɗakin ya rufo tare da sakin ta, kukan taci gaba dayi, yadaka mata tsawa yace "malama kimin shiru ko kuma ki fita idan bazaki iya yi ba,

Shiru tayi saboda ta daddara yanzu ta zaɓi nan akan can saboda zazzaɓi har yafara rufe ta,

wardrobe ya buɗe ya ɗauko wani bargo ya wulla mata yace gashi nan ki shinfiɗa,

kan gadon ya wuce kan gadon ya kwanta,

Jikinta na karkarwa ta ɗauka ta koma kan capet ta kwanta tare da lullaɓa abun bargon amma ina duk da haka bata daina jin sanyin ba saboda zazzaɓin da take ji, tana cikin bargon amma tana karkarwa bakin tane yafara fidda sautin kaf kaf kaf na jin sanyi,

Yana jiyo ta yayi mata banza da yayi biyar ya share ta amma sai yaji abun nata yayi yawa, fitowa yayi daga cikin bargon sa yana kallon ta ganin yayi kamar rawa take,

"Ke!!

shiru ba amsa haka yaita kiran ta amma bata iya amsa masa ba, tashi ya kuma yi yana jan tsaki yazo gurin da take, hannu yasa ya yaye bargon nan karkarwar tata ta kuma ƙaruwa,

hannu yakai ya taɓa jikin ta rau yaji zafin zazzaɓi me ƙarfi ajikin ta, a hankali ya furta ya salam, yana mamakin yanda akai zazzaɓi ya rufeta haka loƙaci guda,

Hannu yasa duka biyun ya ɗagota zaune amma sai ta kasa zama saboda yanda jikin ta yaci gaba da ɓari,

Tausayi ta bashi baiyi zaton hakan dayayi zai cutar da ita har haka ba, da bai kunna mata ba,

Riƙota yayi gaba ɗayan ta ya haɗata da jikin sa ya miƙar da ita jan gadon ya koma ya kwantar da ita, magani yaje ya ɗauko mata tare da ruwa yadawo kan gadon sai ya ajiye su a gefe yaƙara ɗagota amma duk da haka takasa zama,

kuka ta fara raira masa, tana zazzame wa zata kwanta ya hanata, gaba ɗayan ta ya ɗago ta ga ɗora ta akan cinyar sa, sannan ya ɗauko maganin da ruwan ya ɓallo mata ya nufi bakin ta dashi yana cewa, "ungo kimin shiru kar ranki yaɓaci ki karɓa ki sha,

Bakin ta yanufa dashi yanda bakin ta yake ta karkarwa yasa maganin yaƙi shiga saida ya riƙo haɓarta sannan ya tura mata maganin da ƙyar ya dauko ruwa yabata ta kora tana damƙe ido,

Ƙoƙarin zamawa ta kumayi zata kwanta yaƙara riƙota da kyau ya haɗata da ƙirjin yayi mata rumfa da ɗayan hannun, so yake ta daina karkarwar gaba ɗaya, dan haka yanda suke a zaune yajawo bargon ya rufe su gaba ɗayan su,

A hankali a hankali yafara jin karkarwar tata na raguwa, can kuma sai yaji ta ƙara nauyi alamun bacci ya ɗauke ta,

Ɗaga bargon yayi ya sauke shi daga jikin su tare da ɗagota sai yaji tayi saurin riƙosa ƙam, ƙara yunƙurin ɗagota ya kuma yi sai yaƙara ji taƙara riƙeshi, rubuwa yayi da ita kawai ya gyara kwanciyar sa tana kansa sannan ya kuma jawo bargon ya rufe su a haka kanta na kan ƙirjin sa, hannun wansa kuma ya haɗe su guri ɗaya ya ɗora kansa akan su bai taɓata ba,

Shiru yayi yana jin yanda zuciyar ta take bugawa da sauri da sauri, rufe idon sa yayi yana jiran bacci ya ɗauke sa amma yakasa, duk haushin kansa ne yakamsa da bai kunna mata ba da tuni yanzu yana baccin sa cikin kwanciyar hankali amma yanzu duk tabi ta addabi rayuwar sa,

juyi ya gwada yi zai turata gefe amma sai tama kuma ƙara gyara kwanciyar ta garin kuma gyara kwanciyar ta motsa ƙafar, inda gwiwar ƙafar ta taɓo masa saitin alulun sa take yaji zut zut jikin sa ya amsa har saida ya ɗan zabura kaɗan,

Ai ba shiri yayi juyi ta koma gefe, amma ina duk da haka ta riga ta gama cutar sa dan take yafara jin wannan azabar ciwon cikin yafara taso masa tun yanayi masa kaɗan kaɗan har ya fara yi da yawa juyi ya fara yi yayi rub daciki yana dafe cikin sa yana damdamƙe ido, so yake ma ya tashi yaje ya ɗauko magani yasha amma yakasa dan ciwon nema ma yake yafi masa na ranar farko da yafara jin sa........W✍️✍️
[15/11, 10:53 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                         *_🅿️39_*

.........sosai yake juyi akan gadon ya rasa inda zai tsoma ransa dan ba ƙaramin murɗawa cikin sa yake ba, maganganun Khalid ne suka shiga dawo masa loƙacin da yake basa labarin abun da ya faru dashi, a wancen ciwon cikin da yayi, 

Yace masa ai ba ciwon ciki bane ciwon mara ne da wasu mazan kanyi idan suka daɗe basuyi aure ba, kuma indai ya riga ya kama mutum bazai taɓa barinsa gaba ɗaya ba, har sai yayi aure zai samu lafiya, tunanin mafita yafara yi dan yanajin indai ko sai yayi aure to bazai taɓa samun lafiya ba kenan dan shide baiga macen da ta isa ya nemeta ba har ya wani iya haɗa jiki da ita, shiyasa ma bazai yi aure ba, dan agininsa duk macen da yayi haka da ita rsinasa zatayi, kuma ya zubar da ajinsa da girmansa,

Wani dogon tsaki yaja yana runtse idon sa sosai yana ƙara jin yanda azabar take ratsashi, juyi ya kuma yi yana komawa rigingine, idanun sa arufe, jiyayi ankamo hannun sa, sai yayi asaurin buɗe rinanun idanun sa da suka koma wata iriyar kala, hannun sa ya shiga bi da kallo har zuwa kan nata da ta riƙe nasa hannun,

Kallon sa ya kuma mayarwa kan fuskar ta sai yaga baccin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login