Showing 24001 words to 27000 words out of 170049 words

Chapter 9 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7222

zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                        
_______RASHEEDA

Tun ranar da abunnan ya faru ake cigiyar Meer har yau ba basu gano inda yake ba, (Ranar da Meer ya haɗa mata jikin ta ya haɗu😜😂😂😂)

Zaune suke da ita da dadyn ta sai mom ɗin ta agefe tana kallon su,

Rasheeda na kan dadyn ta akwance tace "dady wai haka za arabu dashi ya daki banza kenan nifa wallahi bazan taɓa yarda ba indaj ba aramamin abun da yayi min ba,

Tashi tayi daga kansa ta mayar da dubanta ga mom ɗin ta, tace "mom nifa abun da yafi ban mamaki ganin sa da matsiyaciyar yarinyar nan wai tana ma ina ita da wannan shegiyar tsohuwar wallahi na tsane su, kuma ta hanayar sune kaɗai zamu iya gano inda mutumin nan yake,

Da sauri dady yace "wacce yarinyar kike magana?

Rasheeda tace "wannan mai aikin tamu marar asali wacce tabar gidan nan ka gane ta?

Jijjiga kai Dady yayi tare da sakin wani shu'umin murmushi  da shi kaɗai yasan ma'anar sa yace "tabbas nagane ta ai baki faɗa min ba da kin faɗa tun wuri ai da andaɗe da nemomiki shi, kar kidamu ayau ɗin nan zaki gansa agabanki sai ya durƙusa ya nemi yafiyar ki sannan ki faɗi duk irin hukuncin da za ayimasa agabanki zan saka a lallasa shi,

Cike da murna har tana tsale ta ƙara faɗawa jikin sa tana dariyar farin ciki tace "Dady dan Allah dagaske kasan inda suke,

Kai ya ɗaga mata tare da cewa "of course"

Rungumeshi tayi sosai tana cewa "shiyasa nafi sonka Dadyna Allah yabarmin kai, ai Dady nifa ba wani abu nakeso ayi masa ba kawai kasa ya aure ni, ni kuma zana rama abun da yayi min idan ya shigo hannuna, burina kawai kashiga gaba ayi aurennan nan da sati ɗaya idan kayimin haka Dady ka gama biyana duniya da lahira, sai nasa yayi da nasanin dukana da yayi, sai naga inda iya ƙarfin nasa ya tsaya, please Dady nasan zaka iya,

Zaro ido yayi jin ƙudurin sa akansa, cike da rashin gamsuwa da baya nan ta, yace "baby kinsan kwa me kike cewa aure fa naji kina magana da wani kin manta da batun naki auren gaskiya kibar wannan maganar ki auri wanda kikeso tun farko tunda dai anriga angama magana, biki saura kwana goma har anfara shirye shirye kuma kizo da wannan batun kidai bari kawai ayi basai kin aure shi ba zaki iya ɗaukar fansar abun da yayi miki, na miki alƙawarin duk abun da kikeso zansa ayi masa ke inda kanki ma kikeso kiyi masa nagaya miki zan kawo miki shi har gaban ki ayau ɗin nan, amma batun auren sa ni hakan baimin ba, saboda nasan yaron bai da asali shima ɗan talakawa, shiyasa ma kikagansu tare da yarinyar nan,

Zaro ido tayi tana mamakin abun da yace wai ɗan talakawa ne mutumin da tagani kalar nera amma yace mata ɗan talakawa ne, cike da rashin yarda da maganar sa, tace "Dady anya kuwa kasanshi da gaske baka gansa bane ɗan gidan masu kuɗi ne fa, taya ma za ayi su haɗa dangi da wannan yarinyar,

Shafa kanta yayi, yana sakin ƴar ƙaramar dariya, yace "nikwa nasan shi bayan barin yarinyar nan ai gidan marayu ta koma shima kuma ɗan gidan marayun ne acan yataso, naje ziyara na tadda yarinyar acan shima kuma acan yake shiyasa nasan su, kinsan kwa samun shi bazai min wuya ba inacewa ina buƙatar sa za abani shi dan haka karki wani damu ki kwantar da hankalin ki, kuma maganar auren ki dashi ki haƙura saboda bana son ki auri wanda baida asali ko so kike ƙawayen ki su yi miki dariya kin auri ɗan gidan marayu,

Da sauri ta girgiza kai tace "dagaske Maraya ne Allah sarki wallahi Dady ya ban tausayi sai naji na ƙara sonshi Dady ni na yarda duk ma abun da zasuce suce zan aure shi da haka tundade yana da ƙyau idan kuma kuɗi ne basai kabashi ka ɗau nauyin mu kawai tunda de Kai kana da kuɗi amma nidai bazan iya rayuwa babu shiba,

Mom ɗin tama dake zaune tana sauraron su bata saka musu baki ba saboda tun farkon maganar tasu, da tasaka baki Dady ya yanka mata magana shiyasa bata sake saka musu baki ba, itama  ba ƙaramin mamaki tayi ba jin wai marayane agidan marayu yake bayan kuma ƙawarta ta gaya musu ko shi waye, to kodai bashi Dady yake nufi ba,

Ɗan gyaran murya tayi tana kallon su tace, anya kuwa kasan wanda ake magana gaskiya wannan ba ɗan gidan marayu bane ɗan gidan marayunne zai zo yanayiwa mutane rashin mutunci son ransa, Fatima ma fa (momy) tace a Abuja yake yana da babban asibiti nasa nakan sa asalin suma ba ƴan ƙasar nan bane, a ƙasar Yamen ne, kuma na yarda dan kaf faɗin garin nan bana mijin da na taɓa ji yakama ƴan mata yana duka kamar Allah ya kawosa duk kuɗin uban mutum kuwa, amma tunda kaji yana aikata haka ai kasan da abun da ya taƙala shiyasa yake rashin mutun cinsa,

Wata wawuyar harara ya watsa mata mai cike da gargaɗi da yasa loƙaci ɗaya ta fahimce sa ta kuma gane yaren masa, dan haka taja bakin ta tayi shiru bata ƙara tanka masa ba, tasan dawar garin idan taƙara saka baki,

Rasheeda tace "nima dai haka nagani mom wallahi baiyi kama da wanda yasan wata wahala ba ko marar gata, nidai Dady ina tunanin baka san kowa ake magana akai ba,

Kamo hannun ta yayi yace "Baby kina ja da magana tane?

Shiru tayi bata basa amsa ba, hakan yasashi cigaba da cewa "bani minti biyu ina zuwa, tashi yayi daga gurin ya zaro wayar sa yana ƙarasa fita daga ɗakin,

Zama sukayi suna jiran sa shiru shiru baidawo ba, Rasheeda tace mom kina ganin kwa da gaske Dady yagane wanda muke nufi,

Mom ta gyara zama tare da kishin giɗa akan gado tace "tunda kikaji haka ai yasanshi ɗin amma dai kibari yadawo ɗin muji mai zaice,

Bata gama rufe bakin taba sai gashi ya shigo hannun sa ɗauke da waya, yana sakin murmushi yaƙaraso kusa da ita yace "baby zangoge miki tantamar ki yanzu akan yaron nan, 

"Ba shine wannan ba yafaɗa yana nuna mata screen ɗin wayar sa,

Da sauri ta karɓi wayar tana kalla ta ɗago ta kalle sa tace "Dady wallahi shine a ina kasamu hoton shi Wallahi shine amma kuma Dady ai nan kamar ba gidan marayu bane kaga fa wani zane kamar irin na gidan sarauta ko mom kingan saba, karɓa itama tayi tace "au shine ni daman bantaɓa ganin saba, gaskiya dai nan gidan sarauta ne gama mutane nan agaban sa, hoton Meer ne zaune akan kujera loƙacin da yake zaune akan kujera loƙacin da ya tara mutanen nan acikin masarauta ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya bisa ga dukkan alamu kuma anyi hotonne batare da sanin saba,

Karkaɗa kai Rasheeda tayi tare da karɓe wayar daga hannun ta, tana kallon Dady, cike da jiran ƙarin bayani,

"Kidaina ko kwanto akan duk abun da zangaya miki, kedai kijira zuwa anjima kuma zaki gansa agaban ki, kinji ko, yana faɗa ya miƙe tsaye yace kijirani,

Cike da murna tana washe baki tace Dady ina sonka kuma na yarda da maganar ka, duk abun da zaka faɗa nayarda kawai ina buƙatar ganin sa, zan shirya ina jiran dawowar ka,

Fita yayi yana ƙara sakin dariyar manya yana sakin murmushi yana cewa "don't worry my baby duk abun da kike so afaɗin duniyar nan sai namiki shi komeye kinfi ƙarfin komai awajena, ƙiƙara dawowa ta yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin bai jira amsar taba,

Tashi ta tsaye tana tsalle tsalle har da zuwa ta rungume mom ɗinta tace mom yau zangan sa agabana, bari inyi sauri inkira su momy da Zeee suzo dan afiyin komai agaban su gani da ido yafi abaka labari, daman nasan suna can suna min dariyar kun kasa nemomin shi, shiyasa ma na korasu amma yanzu zan kirasu in antaya musu wannan sweer story ɗin, tana maganar tana wani juyi tana dariya, ta fita daga ɗakin,

Itadai mom na inda take bata tanka mataba, saboda tana mamakin mijin ta, ta yanda yake kashe ta da mamaki kamar aljani sai kaga abu kamar bazai taɓa yiyuwa ba amma sai kaga yaje shi ya lalubo yanzu a ina yasamo wannan hoton nasa, dan ta fahimci duk ƙarya yayi ƴar tasa nacewa wai ɗan gidan marayu ne yayi hakane kawai dan ya cire mata son yaron to amma meye dalilin sa nayin hakan tunda harta nuna tanaso ai kamata yayi ya shige mata gaba amma shine da kansa yake mata ƙarya yana mata zame zame dan ta haƙura dashi, dole akwai ƙwaƙƙwaran dalilin sa nayin hakan, akwai abun da ya hango ko kuma yasani akan yaron da baya so su sani,

Tashi tayi zaune bayan fitar Rasheedan, a fili ta furta koma maikake shiryawa zan gano kane, na lura akwai abun da kake ɓoye min da baka son nasani tunda daɗewa amma yanzu take taken ka yafara yin yawa dole insaka maka ido aduk wani takun ka zan ganoka ne tayi maganar tana miƙewa tsaye tafara zagaye ɗakin tana saƙe saƙe a cikin zuciyar ta,

Rasheeda na zuwa ɗakin ta, ta ɗauki wayar ta, Zee tafara dannawa kira nan ta antaya mata labarin duk abun da yafaru sannan tace ko mai take ta bari tazo gidan su yanzu yanzun nan, bayan sunyi sallama haka tabi sauran ƙawayen ma gaba ɗayan su ta sanar dasu komai sannan tabasu umarnin zuwa, duk suka amsa mata da zasu zo amma duk sai zuwa dare zasu iso, itadai momy dariyar mugunta kawai take mata, dole tazo tagane wa kanta wannan labarin ƙanzon kuraigen, inda rabon ya haɗasu gaba ɗayan su ya ci ubansu, sudai nasu kallo ne suna daga baya.....,

Bayan tagama wayar ta ajiye ta, haka ta wuni tana farin ciki har zuwa dare jim kaɗan sai ta leƙa window tana jiran dawowar mahaifin ta, amma shiru da taga har takwas tawuce ƙawayen nata basu zoba sai kawai ta hau cire kaya, ta shiga wanka ba daɗewa ta fito nan ta fara zubo da kayan ta dan ta zaɓi wanda suka fi kowanne kyau dan ganawa da abin alfaharin ta dan zuciyar ta tabata duk inda Dady yake yana hanyar ƙarasowa gida tare dashi ,

Tana cikin zaɓar kayan wayar ta tayi ringing da sauri ta tashi ta nufi inda ta ajiye ta dan duk atunanin ta sune suka ƙaraso, saidai tana ɗauka tasaki wani wawan tsaki tare da sakin wayar ta faɗi kan gado,

Tana jin kiran har ya katsa wani yaƙara shigowa ahaka saida akayi mata kira huɗu bata ɗaga ba ana biyar ɗinne ta ɗaga tana jan tsaki tare da kara wayar a kunnen ta, tayi shiru shima daga can ɓangaren shirun akayi, saida ta daɗe ahaka har tana shirin katse kiran, yace "mai yasa baki ɗaga ba ina ta kiran ki tun ɗazu,

Taɓe baki tayi tana ya tsina fuska tace "saboda banda ra'ayin hakan,

Bossay dake kwance akan gadon sa riƙe da waya, jin amsar da tabasa yasashi saurin tashi zaune yana bin wayar da kallon mamaki ƙin aminta yayi da abun da yaji, hakan yasa ya ƙara cewa ko baki ji abun da nace miki bane,

Abun da ta gaya masa da farko haka ta ƙara maimai ta masa,

Yace "ok haka kika ce ko fine, ya faɗa yana shirin kashe wayar shi daman baiyi niyar kiran taba Ammi ce ta haɗasa da Allah ya kirata yaji yanda zatayi tsare tsaren bikin tunda biki na matsowa, dalilin kiran kenan,

Jin kamar zai kashe yasa tayi saurin cewa "Aliyu dakata kaji abun da zan gaya maka ka buɗi kunnuwan ka kajini da kyau kagane ko, bata jira cewar saba, taci gaba da cewa, yanzu bada bace kagane yanzu nafi ƙarfin ka nafi ƙarfin ajinka banda loƙacin ka nasan bikin mu yakusa to amma kasani nayi counselling ɗin sa babu maganar aure tsakanin dakai nasamu wanda nake so wanda yafika komai yanzu shine agabana bakai ba maganar auren babu ita zaka iya sanar da ƴan gidan ku ni nagama yanke shawara saduwar alkhairi please don't call me again and delete my contact, if not sai kayi regretting ɗin ƙara kirana da zakayi arayuwar ka poor boy kawai ni banma san tsiyar da nagani ajikin ka ba da har nasoka wallahi nayi da nasanin saninka ma bare har inyi soyayya dakai nake shirin haɗa alaƙar jini dakai gwanda da Allah ya ganar dani tun wuri yabani irin wanda nakeso cikar mafarkina......, Nayi da nasanin....., Shiru tayi bata ƙara saba sakamakon nocking ɗin da taji anayi mata, yasata yin shiru tace "who is?

Muryar Dadyn ta tajiyo ta waje, yace "Baby angama aiki ke kaɗai ake jiran fitowar ki gashi a falo ke yake jira,

Da sauri ta saki wayar aƙasa tace Dady dagaske!?

Turo ƙofar yayi ya shigo cikin ɗakin yana binta da kallo, yace "kina mamaki ne zo muje ki ganewa idonki,

Tsalle tayi ta rungume sa cike da murna da farin ciki da ya kusan kashe ta ta shiga manna masa kiss a kumatu tace "Dady nagode Nagode kagama yi min komai yanda ka faranta min kaima Allah ya baka abun da kakeso,

"Baby ya isa haka kibar min godiya kinsan banaso yi sauri ki saka kayanki mufita,

Sakin shi tayi da sauri ta ɗauki kayan da ta fito da su ta hau shiryawa agaban sa, cikin hanzarin tagama kimtsa kanta cikin riga da wando saidai rigar ta ɗan sauko mata ta rufe mata ɗuwaiwai, ta ɗauki hula ta ɗora akanta sannan ta kalli Dady tace "Dady komai normal?

Hannu ya jinjina mata yace "yesss fine girl muje ko, riƙo hannun sa tayi suka nufo ƙofar fita ranta fal cike da farin ciki, duk da farin cikin da take zuciyar ta takasa yarda ɗari bisa ɗari dagaske ne inta fita zata gansa, amma dai bata nunawa Dadyn nata ba a fuska saboda kar yaga kamar tana ƙarya tasa shiyasa kawai tayi shiru tabishi a yanda yake so,

Buɗe ƙofar Dady yayi suka fito daga ɗakin sannan suka fara takowa benan da zai sauko dasu falon, tunda suka fara saukowa take rarraba ido ta inda zata gansa amma bata gansa ba har suka ƙarasa fitowa tsakiyar falon,

Ɗagowa tayi ta kalle sa da alamar tambaya,

Murmushi ya sakar mata tare da shafa gefen fuskar ta, yace "kin karaya ko?

Kai kawai ta samu damar ɗaga masa,

Sai yaƙara wani murmushin tare da kallon ƙofar shigowa yace "Come in...

Turo ƙofar akayi tare da shigowa ciki, da sauri taja baya ganin abun da bata taɓa tunanin ba duk atunanin Dadyn ta wani zai kawo mata daban amma sai taga da gaskennen murya na rawa ta kalli Dady tace "Da...dy wai da gaske ne abun da nake gani ba mafarki bane Dady shine fa wallahi shine..... Gaba ɗaya ta fita hayyacin ta duk son da take ta gansa amma ganin sa sai ya ɗaga mata hankali gaba ɗaya ta tsorata da ganin sa musamman ma da suka haɗa ido dashi taga idon sa ya juye kamar bana mutane ba.......✍️✍️✍️

Wayyo Allah na mai yake shirin faruwa Meer har cikin gidan su Rasheeda tabbb, lalle Dadyn Rasheeda na jinjinama ƙarfin halin ka kayi namijin ƙoƙari dole mu tsorata dakai........,

         
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

     
            _*BAYA*_

_____ Abun da yafaru  har ya samu ya ɗauko Meer....,

Loƙacin da Meer yacewa Ameesha ta shirya zasu fita da daddare, ita kuma bayan ta fita daga ɗakin sa, tana fitowa direct ta wuce ɗakin dadda saboda Azeema ma tana can tana jiran ta,

Tana shiga ta tarar da Azeema kwance akan gado amma ba bacci take ba shigar ta yasa ta tashi zaune tana mata dariya tace matsoraciya to yanzu ba gashi angama komai ba amma da kin tsaya wani jin tsoro sai kace kin haɗu da dodo,

Itama dariyar tayi ta ƙarasa gurin ta zauna agefen ta, tace ba wani nan aidai nayi ƙoƙari ahakan, ni abun da yafi ban tsoro ma, kin san mai yace,

Kai Azeema ta girgiza mata tace sai kin faɗa,

"Wai yace mu shirya anjiman zai aike mu gaba ɗayan mu wai harda su Amra, wai zaisa wani daga cikin gidan nan yakaimu a mota mukarɓo masa saƙo,

Azeema tace to kuma maiye abun tsoro aciki naji daɗin hakan ma, ke ai wannan dama ce kika samu da zaku ƙara sabawa sosai yanda zaku ringa fahimtar juna, duk wani abu da zai kusantaku ai mu dama ce agurin mu, ba wani abu wallahi kar ki damu ai yasan mai yake kindai san bazai taɓa sawa akaimu inda za'a cutar damu ba,

Ameesha tayi jugum tayi tagumi saida Azeema tagama maganar ta sannan tace "besty nifa bawai wani abun nake tsoro ba, abun da yafi tsaya min arai kinsan dai mutanen nan sunganmu kuma nasan yanzu dole idon su a kanmu yake duk wani motsin mu zasu saka mana ido kinga kwa suna ganin fitar mu zasu iya binmu, gashi kuma yace wai mutafi da wayar yama mayar da memoryn ciki, bansan dalilin sa nason aiken namu ba, kumafa da farko haka yace kar musake mufita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login