Showing 60001 words to 63000 words out of 170049 words
aiki za'a canza da wannan in tabbatar da nasaka mata shi ayau sai na nuna mata zanyi hakan, ina fitowa kuwa na zubar dashi nayi tafiya ta,
Da tagadai da gaske cikin yaƙi zubewa yana ta fitowa kuma ta tabbatar da zubawa ne banyi ba, sai yasa tafara yi min barazana in bansaka ba, nima sai nayi mata, nace wallahi idan bata rabu dani ba sai na tona mata asiri kuma sai nagayawa mahaifiyar ta dan batasan tanayi ba, saidai duk abun da zatayi min tayi min, sai loƙacin ta rabu dani da taga haka, shine har aka samu gimbiya ta haifi Sameer na farko shima kuma bayan haihuwar sa da ƴan kwanaki........ Kuka ta fashe dashi taka sa ƙarasawa, duk ido suka zuba mata da mamakin abun da yasata kuka haka,
Saida tayi kuka sosai sannan ta tsagaita ta goge hawayen ta tace "kuyi haƙuri a kullum na tuna abunnan sai na zubar da hawaye, SA'ADATU bata da imani muguwa ce acikin mugayen azzaluma ce, tsakanina da ita saidai Allah yasaka min,
Bayan haihuwar sa tasa aka kamani aka kaini wani waje aka daure ni ga kuma yarana suma tasa aka kawo su agabana tasa akayi musu dukan tsiya, sannan tace min wannan shine somin taɓi idan banyi abun da zata sakani ba, sai tasa ankashe mu gaba ɗayan mu daga ni har su,
Nace mata mai take so kuma inyi mata bayan haihuwa anriga anyi ta mai kuma yarage, sai tace indai inason in kasance araye tare da yarana, to insan yanda zanyi in ɗauke yaron in fita dashi daga cikin gidan in kashe shi in jefar da gawar saboda gawar sama bata son ta zauna a cikin gidan,
Duk yanda naso ince bazan yi ba ya gagara domin har wuƙa tasa aka sakawa yarana a wuya tace za akashe su, sannan tsoro da tausayin su yasa nace mata zanyi, sannan ta rabu dani amma bata sakar min yara ba, tace har sai nagama zata sake su,
Haka tasa aka dawo dani nikaɗai nasan halin da nake ciki gashi ina tsoron ingayawa wani ƴaƴana suna gurin ta,
A haka nayi kwana biyu ban aiwatar da abun da takeso ba,
Saida ta ƙara kirana sannan dai da naga bani da mafita, ranar gimbiya ta shiga wanka na shiga jikina na karkarwa na ɗauko shi nakai shi ɗakin nasamu abu na nannaɗe shi aciki nasaka shi a botiki sannan nakai shi can baya na ɓoye shi,
Loƙacin da ake rububin nemansa ni kuma na fita da yaron nafara ajiye sa awani waje sannan na dawo, can cikin dare na faki ido na fita, naje inda na ɓoye sa, sai na rasa inda zan dosa dashi saboda har ga Allah bazan iya kashe shi ba nadai fito dashi ne kawai saboda kar ta cutar damu,
Ina cikin tafiya na haɗu da wani mutumi daga ganin sa nasan ma buƙaci ne, sai na nemi alfarmar sa da ya karɓi yaron nan na basa labarin komai sannan nace masa duk daren daɗewa zan dawo in karɓe sa bayan ya girma in kuma bana raye yakawo sa cikin masarautar ya faɗi abun da ya faru,
Da ƙyar nasamu ya karɓe sa adaren na tattara duka abun da na tara da wanda taban da kuma na aikina, mukaje wani shago na tura musu gaba ɗaya na basa nace yayi nesa da garin sannan kar ya taɓa dawowa har sai yaron ya girma ya mallaki hankalin sa, ya riƙesa amana ya riƙesa kamar ɗansa kar ya bari yasan bashine ya haife sa ba har sai ya gama girma,
Da haka mukayi sallama dashi nikuma na dawo gida raina duk babu daɗi har rashin lafiya nayi na halin da nake ciki,
Tunda ga wannan rana ban ƙara saka shi a idona ba nadai san yana raye amma neman duniya na rasa inda yake , sai nima nasa aka fara yi min binciken inda zan same sa, aranar da aka kawo min labarin angansa na shirya na bar masarauta da ƙaryar zanje inga yara na,
Saidai kuma wani ikon Allah ko da naje sai akace min ai a ranar suka tashi daga unguwar kuma babu wanda yasan inda suke, haka na ƙara dawowa bansame shiba, tundaga nan nake addu'ar Allah ya bayyana sa idan yana raye,
Daga nan nace mata taban ƴaƴana sai tace min ai suna nan cikin ƙoshin lafiya , na nemi ingansu amma ta hanani damar hakan, bansan me tayi musu ba dan tun aloƙacin jikina yabani ba hakannan ta barsu ba, tunda taƙi faɗar inda suke, har yau kuma bata gaya min ba,
Daga nan kuma kwatsam sai naji maganar auren Sa'adatu da sarki, nayi mamaki banyi mamaki ba dan nasan babu abun da bazata iya aikatawa ba saboda saidaga baya nagane son sarki take shiyasa take ta ƙulla abubuwa bataso ya rayu da kowacce kuma bata so ya haihu daga ɗaya daga cikin su gaba ɗaya,
Ni kuma bayan shigowar ta gidan sai nafara shiga jikin ta saboda inaso insan duk wani shiri da take sai na nuna mata komai ya wuce zanci gaba da yi mata duk abun da take so, sannan kuma nayi mata banza da maganar ƴaƴa na ban ƙara yi mata maganar suba,
Haka mukaci gaba da kasancewa muna shirya abubuwa tare, anan nake sanin wai tun kan ta shigo gidan ta saka anjuyar mata da mahaifar fulani bazata taɓa haihuwa ba, ita kuma gimbiya anyi anyi anjuyar da tata amma taƙi juyuwa shiyasa ita kuma take bata magani dan cikin ta ya zube kar tahaihu saboda tace baza ta taɓa bari wani daga cikin su ba ɗansa ya gaji sarki, saidai ɗanta,
Ana haka kuma sai bata haifi namiji ba sai mata, basu daɗe ba kuma itama gimbiya ta ƙara haihuwa, da taga namiji ne sai tace kawai zatasan yanda zatayi,
Tabbas da haɗin baki na aka fita da gimbiya amma nima duk tarko nakeyi mata dan so nake na ɗauki fansa akan yarana, sannan in tona mata asiri bayan nagama sanin duk wani shirin ta,
Bayan an fita da gimbiya ita da ɗanta, ita kuma fulani sai muka haɗa baki da ƙawarta aka tasata agaba akan maganae ciki har ta shawo kanta ta amince zatayi abun da ƙawar tata tace, saboda Sa'adatu tace indai jinin ta baiyi mulki ba to babu wanda ya isa yayi mulki indai kwa wani zaiyi saidai ba jinin gidan ba kuma mugunta kawai za aringa yi dan sai ta tarwatsa masarautar bansan dalilin taba nayin hakan dande ayanda na fahimta kamar akwai wani abu da take ɓoye mana, nida su Waziri, kamar yanda Ghali yabaku labari zuwa loƙacin duk bakin mu, ɗaya,
daga nan aka sanar da mutane cewa gimbiya ta mutu kawai da mutuwar aka sanar dan wata gawa muka samu a asibiti da ta mutu aka rasa dangin ta mukuma mukayi amfani da ita sai aka hana kowa ganin ta, tare da ƙullewa kowa baki, har aka manta da maganar ta,
Bayan munfitar da gimbiya muka ƙara samun wani muka ce yabita ya buge ta ta mutu ita da yaron, shine ya karɓi kwangilar, kamar yanda muka tsara yaje ya bugetan daga nan kuma ya kira motar asibiti su ɗauke ta saida yace mana ta mutu loƙacin da yakaita asibitin daman kuma bai tsaya ba muka ce yana kaita ya gudu kar ya tsaya yabar ta anan,,
Tundaga nan hankalin mu ya kwanta ko ince hankalin su ya kwanta danni har loƙacin bawai da zuciya ɗaya nake zaune dasu ba, inayi ne kawai dan ingano inda ƴaƴana suke, inda nayi tawa son zuciyar kenan,
Bayan komai ya lafa kuma ta ɓangaren gimbiya an fara mantawa da babun ta ma a masarauta saboda asirin da akayiwa kowa, na mantar dasu,
daga nan kuma ɗan Fulani ya girma inda sa'adatu tasa aka sanyawa kowa mugunta a zuƙantan su ita da ɗan nata, tunda sarki ya sauka daga mulki yabawa Salahudeen aranar da ya zauna akan karagar mulki aranar komai ya fara canzawa masarautar ma ta canza aka fara gudanar da mulki marar kai da ma'ana mugunta zalunci rashin tausayi rashin imani har kisan kai ma idan takama ana iya yi,
Haka ake ta gudanar da mulkin yayin da cikar burin kowanne mu ya gabato loƙacin kuma asiri yafara warwarewa,
Cikar burin Waziri da matar sa jikan su yazama sarki daga nan sarauta ta dawo hannun su gaba ɗaya, cikar burin Ghali shine a ƴantasa abasa kuɗaɗe da yawa ya koma ƙasar waje, cikar burin hajjaju shine ƴar ta zata auri Sam zata zama gimbiyar masarauta, cikar burin Abdallah (Dady) shine ɗansa zai zama sarki, cikar burin Adama kuma shine ta gano inda ƴaƴan ta suke sannan ta tona asiri a shirmen ta, To cikar burin Ammah (Sa'adatu) kuma ita anata lissafin ma babu duk cikar burin sauran babu wanda zata cikawa burin su acikin su, nata burin kawai taga komai na masarautar ta lalace komai ya tarwatse bata son wani cigaba ko kaɗan da zaizo yasamu cikin masarautar tafi so kullum akasan ce cikin bala'i da masifa da mugunta da zalinci, shine nata shirin.......,✍️✍️✍️
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
________Shiru tayi bayan ta gama basu labarin tare da dunƙufar da kanta ƙasa yayin da ƙwalla ta cika mata ido,
Gwaggo ce ta miƙe tana sallallami tana hawaye, tace amma wannan yarinya anyi tsinanniy marar albarka, ashe daman ba auren Allah da annabi bane ki shigo gidan nan, uban me muka tsare miki mai Muhammadu yayi miki kike yi masa irin wannan muguntar tun kan kishigo tun kan musan wacece ma ke, ke kika san damu, ni daman banso auren ba tun farko waya sanni ma ko da ƙulle ƙullen ki kika sa aka aura miki, nan gwaggo ta shiga surfo mata masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, harda sun kaiwa Ammah duka. Da ƙyar dai aka samu aka shawo kanta ta haƙura ta koma ta zauna,
Gurinne yaso ya kauraye da haya niya kowa na faɗar albarka cin bakin sa wasu kuma na kuka, irin su momma dan a yau bata ma samu bakin magana ba,
Meer ne yayi ƙoƙarin wajen dakatar da hayaniyar domin ci gaba da jin ta bakin sauran,
Shiri gurin ya ƙara ɗauka, sannan meer ya maida hankalinsa ga Ammah, cike da binta da kallon tsana yace "shugaba ke muke jira munji komai na sauran ba buƙatar su faɗa da bakin su, ta bakin ki kawai muke jira muji, shugabar su,
Yanda yayi mata maganar da rainin hankali tare da harara,
Ammah na jinsa amma sai tayi banza dashi kamar ma bada ita yake ba saima haɗe rai da ta kumayi dan daga kallon ta zakasan ba alamar nadama a tattare da ita,
Duk yanda yayi mata magana ƙin kulashi tayi ko ɗagowa ma batayi bare yasa ran zatace wani abu, hakan kwa ba ƙaramin ƙullar da Meer tayi ba, ta kaishi ƙarahe daman yana ɗaga mata ƙafa ne saboda darajar wasu daga wajen amma da tuni ya daɗe da canza mata kamanni,
Cike da fara hasala cikin ɗaga murya mai yanayi da ɓacin rai ya daka mata tsawa tare da kwashe da mari ta gefen fuskarta, yace "zaki yi magana ko sai nayi miki lahani,
Itama kamar wacce ta tsikara ta miƙe tsaye cikin ɗaga muryar tace bazan yi ba ɗin inka isa kasani inyi jaki kawai, marar tarbiya, idan da wanda ya isa agun nan yasakani abun da banyi niya ba, bazan faɗa ba nace bazan faɗa ba ko ubanka bai isa ba karan ƙaɗa miya bare kuma, kabari inyi da waɗancan dabbobin bin ta nuna inda Maama da Papa suke zaune sannan taci gaba da cewa sune sa'annin yi na ba kaiba, su idan sun cika ƴaƴan akuya suzo su sakan......
Ji tayi ankwashe da wani irin mahaukacin mari ta gefen kunnen ta wanda loƙaci ɗaya jin ta ya ɗauke hakan ya hanata ƙarasa maganar, idon tama saida ya ɗauke gani taga duhu sannan ya baje bayan ƴan sakanni ta dawo ganin haske, saidai bata gama tantancewa ba ta kuma jin wani ta ɗayan ɓarin cike da tsatstsan ɓacin ran da bai taɓa shiga ba Abu ya shiga nuna ta da yatsa yace "kisan a inda kike kuma kisan da waɗanda ba kowace kalma zaki faɗa ba abarki ki kiyaye tunda aka fara abunnan babu wanda ya tanka miki amma har kin samu bakin cigaba da cin mutuncin mutane,
kasa magana tayi dan har yanzu azabar bata gama barin taba, dan saida ta ɗimauce tunda take ba 'ataɓa marin taba bare kuma irin wannan zazzafan da Abu ya sauke mata su,
Meer da shima jira yake yakaimata mugun bugu Abu ya rigasa sai ya haƙura, juyawa yayi ya kalli inda momma take ya ƙara juyawa ya kalli wasu daga ciki, sai kawai ya kama Ammah ya zaunar da ita ta zauna da ɗuwawunta,
Maida kallon sa yayi ga ƴan cikin fadar sannan yace "dan Allah in badamuwa ina son wasu su bamu guri waɗanda bai dace da suji ba wannan sirri ne abun da ya shafe mune dan haka mu zamu ƙarasa jin sauran, ina tunanin taƙi faɗa ne saboda kunyar wasun ku, dan Allah kuyi mana afuwa ku fita zamuji ta bakin ta, baikamata ace kunji komai ba kuma daga bakin ta, shiru yayi yana satar kallon wasu daga cikin su waɗanda daman dan suɗin yayi maganar bazai iya cewa su fita bane kai tsaye shiyasa yabiyo ta nan yasan dole zasu fita dan baza suso su ciga ba da kallon abun da yake faruwa ba, dan yanaso idan suka fita ya ɗan sassamata ya koya mata hankali idan yayi mata yaren da zata gane to dolen ta ta faɗi duk abun da suke so, dan ya fahimci taurin kai gare ta,
Allah sarki momma daman ƙiris take jira dan haka kuwa ita gafara miƙewa daga gurin yayin da take jin wata juwa na shirin zubar da ita a ƙasa tayi saurin riƙe kanta saboda zuciyar ta ta fara bushewa dan ko kukama takasayi abun yakaita ƙarshe,
Mamy ce ta miƙe itama takama hannun ta suka fita daga ciki batare da sun kalli kowa ba, nagun, daman su kaɗai ƴaƴan ta acikin gidan sai jikoki su kuma babu wanda aka shigo dashi gurin,
Sunkai bakin ƙofa kenan zasu fita suka tsikayo muryar ta "tace ku dawo ku zauna cike da raunin murya da loƙacin ɗaya ta canza ita kanta batasan tayi ta ba,
Tsayawa sukayi cak batare da sun motsa ba, saida ta ƙara cewa nace ku dawo ku zauna babu inda zaku sai kunji komai,
Mamy ce ta juyo da ƙyar ta ɗan kalle ta sannan tace "muji komai fa kika ce to mai ya rage wanda bamuji ba, hakan ma ya ishe mu ko so kike kiƙarasa kashemu da ranmu Ammah wallahi nayi da nasanin kasancewar ki uwa agare ni duk wanda yasamu uwa irin ki yayi asara dan haka muma asararru ne munyi asarar uwa dan dake da babu yanzu duk ɗaya ne,
"Ya isa haka kizo mutafi kibar ta Allah zaiyi mana sakaya ranar gobe ƙiyama, ga duniyar nan ai ta isheta riga da wando, cewar momma da har yanzu bata yarda ta kalli inda Ammah take ba,
Juyawa sukayi zasu fita Papa ya ƙara dakatar dasu tare da basu umarnin su dawo su zauna sannan kar wanda yaƙara magana daga cikin su, babu yanda suka iya dole suka koma gurin su suka zauna badan suna son ci gaba da zaman gunba dan ji suke laifin ma kamar ya shafe su tunda za ace mahaifiyar suce,
Karon farko arayuwar Ammah da taji zuciyar ta ta karaya saboda ƴaƴan ta, loƙacin guda taji wani abu nayi mata yawo ajiki, ganin ƴaƴan ta cikin wannan halin da kuma maganganun da sukayi mata hakan ba ƙamin tsaya mata arai yayi ba,
Yanzu da kanta babu wanda yace tayi magana, tace "tabbas zancen da kuka faɗa gaskiya ne kunyi asarar uwa danni ba uwace ba irin ko wacce uwa ba, bancika duk wasu abu ba saidai kuma kusani tunda nakawo ku duniya to nagama yi muku komai har yanzu ina nan amatsayin uwar ku babu yanda zakuyi da ana canza uwa da nace ku canza ni daga yau amma babu hali, saidai kuyi haƙuri,
Maida dubanta tayi ga sauran tare da sakin murmushi wanda bansan dalilinta nayin hakan ba,
Sannan tace "yanda kuke tunanin wasu abubuwan to kunyi tunani daidai amma wasu ko hanya baku ɗauko ba,
Kunsan duk saboda me nakeyin hakan ba wani abu bane babba awajen ku amma ni a wajena babba ne,
Ƙiyayyar ta somone tundaga sama da tazo kaina kuma sai ta koma soyayya,
Wani murmushin taƙara saki kamar ma babu abun da yake faruwa da ita, sannan tace Kunsan duk waye silar faruwan abubuwan nan, ba kowa bane ko ince ba kowa bace face gwaggo, gwaggo itace tajawo muku komai tun loƙacin ƙuruciyar ta shine yake ta binta har kawo yanzu....,
Shiru taƙarayi tana kallon su ganin yanda kowa yake kallon ta, kamar zai cinye ta, gwaggo kam zunbur tayi zata miƙe akayi saurin dakatar da ita Ibrahim dake gefen ta ya hanata tashi,
"Hmm gwaggwo gwaggo gwaggon shagali mai ran ƙarfe wai ya akai har yanzu baki mutuba duk irin abun da ake miki amma kinƙi mutuwa,
Tunda na taso nida mahaifina muke bibbiyar ki, sakamakon abun da kikayi masa, zaki iya tuna wani saurayi da yace yana sonki kafin kiyi aure,
Mahaifina ba sarki bane ada hasalima shima ba jinin sarauta bane ta ƙarfi ya ƙwace ta duk dan saboda ke,
Mahaifina buzune ɗan nijar ne acikin nigar ɗin ma can