Showing 93001 words to 96000 words out of 170049 words

Chapter 32 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7220

sauri dan Allah kar ku kaƙara minti shabiyar kaji.....,

Daga nan ya kashe wayar bakin sa na ta faman murmushi dan yaji daɗin dawowar bawan Allahn can, dan jiya ma dashi ya kwana aransa....,

Bossay ne yace "yaya Ayuba kai dawa haka naga kana ta faman murmushi kai kaɗai,

Wani murmushin yaƙara saki yace baza ka gane bane wallahi wani bawan Allah ne ya damfare ni kuɗaɗe masu yawa, da nayi bincike akan sa sai na gane ashe wata mata ce ta aiko sa to amma nayi bincike na kasa samun matar nadai san gidan ta, shine nasa aka bincika min cikin gida ake gaya min akwai wani agidan nasa akaje har gidan aka ɗauko min shi,

Naje kuma sai naga bashi bane, wani bawan Allah ne wallahi baka ga mutumin nan idan ka gansa sai ka tausaya masa ko magana baya iya yi sai hawaye kawai yake zubarwa, ina ta tambayar sa amma yakasa ce min komai shine nace aje agyara sa yadawo mutum dan gashi duk yagama rufe masa fuska ga kayan sa duk sun yage kana ganin da kasan daɗaɗɗu ne ya daɗe yana rayuwa a haka shiyasa nake son sanin ko shi waye,

Bossay yace "Allah sarki gaskiya abun atausaya masa ne, wata
ƙil wani abu ne yake sashi kukan, kuma ka tabbatar ba kurma bane,

Ɗaga masa kai Ayuba yayi yace "gaskiya ba kurma bane, kawai yanayi ne yasa yakasa maganar amma koma meye zamuji daga bakin sa yanzu idan sun shigo,

Bossay zaiyi magana kenan, sai wayar sa tayi tafara ringing da sauri ya ɗauka saboda ganin Dadyn Rasheeda,

Yana ɗauka sai ya tashi ya shige ɗakin dake kusa dashi,

Hamza ya bisa da kallo tare da cewa "dan munafurci wayar ma baza abarta ba sai anshige ɗaki,

Bossay najinsa yayi gaba saboda bayason kiran ya katse,

Shigar shi ba jimawa akayi nocking ɗin ƙofar falon,

Akusan tare Hamza da Ayuba suka miƙe zasu buɗe ƙofar, amma Ayuba ya riga Hamza zuwa sai kawai ya buɗe musu ƙofar, yana ganin su ya faɗaɗa fara'ar sa yana cewa "Oyo Oyo bissmillah ku shigo, matsa musu yayi suka shigo, yana ta faman bin su da ido yana jiran yaga wanda yake nema amma bai gani ba,

Juyowa yayi yana kallon su yace kai yana ganku anan shiɗin yana ina?

Dariya suka kwashe da ita gaba ɗayan su........,
[15/11, 10:52 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

'Dariya suka kwashe da ita gaba ɗayan su........,

-----'Sai ɗaya yace "sir wai baka gane saba kenan daman nace maka bazaka gane saba,

Da mamaki Ayuba yaje kallon su sai yace "kar ku raina min hankali mana bagaku kuku uku ba akwai wanda bansani ba acikin bane,

Ɗaya yace  sorry sir yanzu zasu shigo da Haruna,

Hararar su yayi yace "oh da ni zaku maida mahaukaci harda wani dariya irin gashi nan acikin ku ban gane saba ko?

Basu bashi amsa ba sakamakon shigowar wasu mutane biyu ne ta hanasu basa amsa,

Tunda suka shigo Ayuba ya kafe mutumin da idanu ko ƙiftawa bayayi, tunda idon sa suka sauka akan sa kawai yaga yasan mutumin to amma kuma a inda yasan shi ɗinne yakasa tunawa, hakanne yasa yakasa ɗauke idon sa akan sa har suka ƙarasa shigowa ciki,

Sanye yake cikin manyan kaya riga da wando milk color harda hular kayan, farine sosai amma halin rayuwar da yashiga yasashi ya ɗanyi duhu fuskar fayau da ita kana ganin sa kasan da rama ajikin sa, amma duk da halin da yake ciki hakan bai hana tsatstsan kyawunsa bayyana ba, ga hanci iya hanci masha Allah ga kuma idanu kamar ba babban mutum ba,

Ɗaya daga cikin sune ya taɓo Ayuba da ya tafi duniyar tunani,

saurin saita nutsuwar sa yayi tare da ɗan sakin murmushi yace "ah bissmillah sannun ku da zuwa, ku zauna, wallahi naji daɗin ganin sa haka lalle dole yau inbaku kyauta me tsoka, gaskiya kunyi ƙoƙari kundawo dashi yanda nake so, dan haka kowa ya jira zaiji alart me ƙarfi,

Ɗan Ladi yace "to godiya muke Allah yasa dai kar ya fasa mana waya saboda ƙarfin,

Dariya suka sanya gaba ɗayan su, sannan kowa ya samu guri ya zauna, Ayuba da kansa yaja hannun mutumin nasa ya zaunar dashi akan kujera,

Duk wannan abun da ake Bossay da Hamza suna ɗaki bayan shigar Bossay kafin su shigo shima Hamza ya bisa ɗakin sakamakon fitsarin da ya matse sa, da ya shiga kuma sai ya tsaya gurin Bossay dake waya da Dadyn Rasheeda,

Bayan shigar Bossay yana ɗaga wayar, ya gaida shi cikin ladabi da biyayya, bayan sun gama gaisawa, yace "Dady kana gida ne?

Sai Dady yace "a'a wallahi Aliyu Bama na garin naje wani gari amma zuwa yamma zandawo sai ka shigo lafiya dai ko?

"Ah Dady to ko kai nagani ɗazu, daman ina tunanin kai ne ko ba kai bane,

"Yana jiyo muryar yarsa yanda yace "Ni kuma a ina kaganni, ni da bana gari,

Bossay yace "Gombe ko bakai bane?

"Eh Eh nine, kaima kazo ne,

"Eh wallahi Dady nima ɗazu muka shigo, a ina ka sauka da nazo mungaisa naga motar ka ta shiga wani layi nabi wajen kuma bangan ka ba shiyasa nace bari in kiraka,

ƙitt...... Bossay yaji an kashe wayar,

zaro wayar yayi daga kunen sa yana dubawa sai ya ƙara kira atunanin sa ko kuɗin Dadyn ya ƙare amma da ya kira sai yajita akashe sai kawai ya haƙura, bai ƙara gwada kiran saba, dan bai kawo komai aransa ba,

Da Hamza ya fito sai ya haɗo da wanka ya fito gaba ɗaya, shima Bossay sai ya tashi ya shiga wankan,

Hamza na gama shiryawa ya jira Bossay saida yagama shiryawa suna shirin fitowa saiga Ayuba ya shigo ɗakin har yanzu fuskar sa ɗauke da murmushi yana kallon su yace "wai har kunyi wanka to kifito muci abincin ankawo tun ɗazu.....,

Hamza ne yace yanzu zamu fito daman baƙon naka har yazo kenan,

Eh wallahi yazo so nake sai yaci abin mun gama muma sai muyi magana dashi har yanzu dai baice min komai ba,

Ok to shikenan muje Ayuba da Hamza sukayi gaba sai Bossay ya biyo bayan su, suka fito tare,

suna fitowa daga ciki suka dawo cikin falon, loƙacin da suka shigo sauran mutanen ma duk sun tafi saura mutumin kaɗai yayi jigum yana kallon guri ɗaya,

muryar suce tasa mutumin ɗan ɗagowa yana kallon su,

Da ƙarfi Bossay yace "Kai..!! yana zaro ido,

Ayuba ne ya ɗago yana kallon Bossay da mamakin jin yanda yayi maganar da ƙarfi,

Hamza kam bai ɗago ba saboda shima yaga abun da yasa Bossay faɗar hakan shi saboda mamaki ma bai iya furtawa ba,

Ayuba ne yace "kai kam lafiyar ka ƙalau ko kasan shi ne naga sai kallon sa kakeyi,

Da sauri Bossay ya shiga girgiza kai amma still idon sa na kan bawan Allahn nan bai ɗauke sa ba,

Hamza ma saurin saita nutsuwar sa yayi yana mai mamakin ganin mutumin,

zama sukayi akan kujera, Ayuba bai ƙara cewa komai ba, kawai ya ɗauko ledojin da aka kawo musu ya baje musu tare da ɗaukan na kowa ya basa yakaiwa mutumin nan abun da yasan zai buƙata ba musu kuwa mutumin ya karɓa, ga mamakin sa sai ji yayi kawai yace "Nagode!

Saura kaɗan Bossay ya saki abincin dake hannun sa, dan yanda yaji mutumin yace nagogde sai yaƙara basa labari fiye da wanda yake ciki,

wani irin daɗi Ayuba yaji na maganar da yayi da har yana tunanin kurma ne ashe ba kurma bane,

Nan bawan Allahn nan ya shiga cin abincin nan dan daman yunwa yake ji sosai,

Ayuba ba ma komawa yayi ya ɗauki nasa ya hau ci, Hamza kuma ɗan yakuta yake kaɗan kaɗan yana kawai baki, shi kam Bossay ko taɓa sama baiyi ba, duk Abun da yake kuma Ayuba na lure dashi, ya rabu dashi ne kawai da ƙudurin idan aka gama komai zai tuhume sa kodai yasan shi, dan irin kallon da yake masa dole akwai wani abun da
abun da yaƙi faɗa masa,

Bossay dai ji yayi yakasa jurewa dan har wayarsa ya ɗauko ya shiga gallery ɗin sa ya duba wasu hotuna sanan ya ajiye ta,

Ɗan gyaran murya yayi sannan ya dubi Anyiba yace "baba Ayuba dan Allah tambaya nake ya sunan wannan mutumin dan Allah,

Ɗan jinjina kai Ayuba yayi sannan yace nidai nasan da wata aƙasa amma na tambaye ka kace min babu komai, kaman ta me nagaya muku ɗazu nima yau kwana nan biyu da sanin sa kuma bai gaya min ba, Ni banda yanzu ma bantaɓa bai taɓa cewa ko A ba sai yanzu da yace ya gode,

"kabari mugama cin abincin tukunna sai yagaya mana, tunda har ya fara buɗar ai zamuji komai,

"Okay" kawai Bossay yace tare da ƙara ɗauko wayar sa, ya cigaba da daddan nawa,

Shi kam mutumin da suke magana akai, duk ana jinsu amma yayi musu banza yaci gaba da cin abincin sa,

Tashi Bossay yayi yana dannawa number Ammi kira, yana shigewa ɗaki ya rufe daidai loƙacin kuma, Ammi ta ɗaga kiran da yake mata,

tana ɗagawa yace suka gaisa tayi mishi bangajiya, sannan yace "Ammi dan Allah wani tai mako zakiyi min,

daga can ɓangren tace injin ka Allah yasa xan iya,

"Yauwa Ammi ta nagode, dan Allah ɗakina zakina zakije ki ɗaga katifata, zakiga wata jaka a nanndaɗe da wani abu ki ɗauko ta sai ki buɗe cikin ta, idan kika buɗe zakiga wasu hotuna aciki ki ɗauke su a hoto da wayar ki, ɗaya bayan ɗaya zaki ɗauka sai kituro min ta WhatsApp, Ammi dan Allah yanzu yanzu,

"To, kawai tace masa daga nan sukayi sallama,


fitowa yayi daga ɗaki, ya koma gurin sa ya zauna,

tsawon loƙaci sannan suka gama cin abincin,

Bossay kuma yana cikin WhatsApp ɗin sa yana jiraan ta turo masa, tana turo masa hannun sa har yana karkarwa wajen buɗesa yana buɗewa ya kalli hoto ya ɗago ya kalli mutumin dake zaune.

Alahamdulillah Alahamdulillah Bossay kawai yake faɗa tare da saukowa daga kan kujerar yayi sujjada.....,,
[15/11, 10:52 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*


           *_Typing........✍️✍️_*


___'Alahamdulillah Alahamdulillah Bossay kawai yake faɗa tare da saukowa daga kan kujerar yayi sujjada.....,

Duk da mamaki suke kallon sa, basu gama cika da mamaki ba, saida Bossay ya ɗago yana ta dariya yaje ya rungume mutumin ƙam,

Shikan sa mutumin ƙamewa yayi saboda mamaki,

"To ikon Allah, Ayuba ya faɗa yana kallon Hamza, Hamza kam shima farin cikin ya farayi dan ya ɗauki wayar Bossay yaga hoton dake wayar sa hakan kuma shima ya tabbatar masa da nasa tunanin da hasashen sa akan mutumin,

"Aliyu wai me yake faruwa ne nifa kasakani a duhu a ina kasan bawan Allahn nan, dan Allah kayi min bayani ko ince kuyi min bayani naga kaima kana ta fara'a, yayi maganar duk a kiɗime yana kallon su ya kalli wannan ya juya ya kalli wancen,

Da ƙyar Bossay ya saki mutumin yana murmushi yana ta kallon sa kamar ya haɗiye,

"Kai nifa iskancin nan naka ya isheni kayiwa mutane magana ka tsaya kana yin wasu abubuwa kamar marar lafiya, cewar Ayuba da yagama gajiya da abun da Bossay yake...

juyowa Bossay yayi yana kallon Ayuba yana cikin murmshi kuma kawai sai kuma ya sauya loƙaci guda hawaye suka cika masa ido yayi saurin saka hannu ya goge su, yanayin wani murmushin,

Bossay fa ya kusan zarewa dan gaba ɗaya abun neman tarwatsa masa ƙwaƙwalwa take, mamaki, al'ajabi, da shiga ɗimuwa dan jin abun yake kamar ba gaske kamar ba gaske ba,

Gurin mutumin yaƙara koma ya zauna agefen sa, tare da ruƙo hannun sa, sai kuma ya maida duban sa ga Ayuba cikin wata iriyar murya shi ba ta murna ba shi ba ta baƙin ciki ba, yace "bansan shi ba kuma bantaɓa ganin saba yau na fara ganin sa....., Sai kuma yayi shiru bai ƙarasaba,

Wani iri Ayuba yaji na rashin jin daɗi dan so yake kawai yaji yace yasan shi sai kuma yaji akasin hakan.... Yana shirin magana kenan sai kuma Bossay yaci gaba dacewa,

"Amma nasan waɗanda suka sanshi kuma ina da tabbacin hakan, domin ina tare dasu akoda yaushe ma,

Karon farko da kenan da mutumin yayi magana tare da miƙewa tsaye yace "ƙaryane ni babu wanda yasanni kuma banda kowa nikaɗai ne awannan duniyar banda kowa banda komai kar ka ƙara cewa kasanni, yayi maganar cikin wani irin yanayi,

Shima Bossay ɗin miƙewa yayi kamar zeyi kuka yace "wallahi kaine Allah kuwa ga kamar nan nagani da idona, wallahi ina tare dasu,

Loƙaci ɗaya kamanni mutumin suka sauya yace "kai nace maka bani bane ni banda kowa idan ka sake cewa kasanni kuma zanbar muku gurin nan,

Bossay bai daddara ba ya kuma cewa dan Allah kayi haƙuri karka tafi bari innuna maka idan kagani nasan zaka yarda ya faɗa yana juyawa zai ɗauko wayar sa dan ya nuna masa hoton,

Bossay na juyawa shima mutumin yajuya zai bar falon, Hamza yayi saurin cewa "karka tafi dan Allah,

Shima Bossay da sauri ya juyo yana cewa dan Allah "ABBAN AMEESHA ka tsaya ka saurare ni wallahi kaine......

Cak mutumin ya tsaya yakasa ci gaba da tafiyar, a hankali ya shiga juyowa ya sauke idon sa akan Bossay, bakin shine ya shiga motsawa yana maimaita sunan Abban Ameesha, Abban Ameesha,

Bossay na kallon bakin sa yagane me yake faɗa dan haka yasamu ƙwarin gwaiwar ƙarasowa kusa dashi yana cewa "Eh haka nace Abban Ameesha ko ba kai bane, kalli wannan hoton kagani nasan zaka yarda da abun da nake nufi idan ka gani,

Yayi maganar yana miƙa nuna masa wayar, A hankali mutumin ya ɗora idon sa akan screen ɗin wayar, da sauri ya fusge wayar daga hannun Bossay,

ƙurawa hoton ido yayi tabbas hoton sune dashi da matar sa sai dadda daga bayan su loƙacin basu daɗe da dawowa sabon gidan da ya gina musu ba anan garin Gombe, (in baku manta ba asalin su Dadda garin damaturu ne, daga nan kuma bayan malam ya aure ta suka dawo garin Gombe anan suke da zama, bayan faruwar abun kuma dadda ta dawo Kano da zama, fahimtunna?)


Gaba ya gwadayi ko zai ga wani sai kwa ga wani hoton wannan kuma gaba ɗayan sune ajiki harda malam, gaba ya kuma yi sai gashi shida matar sa loƙacin ɗauke da cikin babyn su Ameesha, daman kuma tun tana ciki suke kiran ta da sunan, shiyasa da Bossay ya faɗi sunan ya dakata da niyar fitar da yake sai loƙacin ya yarda lalle yaron yasan shi, haka yai ta kallon su loƙacin da idanun sa suka cika taf da ƙwalla, bai ankara ba sai gani yayi suna ɗigowa kan wayar, sosai rayuwar su tada ta shiga dawo masa duk da daman a kullum cikin yinsa yake amma na yau yafi na koda yaushe,

Cike da jin daɗi Bossay yace kagani ko ka yarda,

Ɗagowa mutumin yayi yana kallon Bossay tare da jinjina masa kai, yayin da idanun sa sukaci gaba da cikowa da ƙwalla,

Hamza ne shima yaƙaraso kusa dasu tare da cewa "to Alahamdulillah nimadai tunanina yazama gaskiya yanzu zama yakamata muyi Abban Ameesha, kadaina kuka in sha Allah ƙarshen wahalar ka tazo, daga yanzu bazaka ƙara kukan wani abuba,

Hannu yasa ya goge hawayen nasa amma daga ya goge sai wani ya biyo baya, shi kansa baisan kukan me yake ba na farin ciki ne ko na baƙin ciki tunda ya tsinci kansa cikin wannan yanayin bai taɓa tunanin zai fito daga inda yake bare har yaga irin wannan rana,

Da ƙyar Hamza yajasa ya zaunar da shi akan kujera,

yana zama yaƙara miƙewa tsaye cike da fitar hayyaci yace "dan Allah da gaske kasan inda suke muje ka kaini suna nan gaba ɗayan su da ransu babu dai wanda ya mutu ko?

Hamza ne yaƙara kamasa ya zaunar dashi cike da kwantar masa da hankali yace "Eh zamu kaika duk suna nan amma ka kwantar da hankalin ka dan Allah kar ka ƙara saka kanka adamuwa in sha Allah gobe zamuje ka gansu,

Daɗi ne yakama sa nan yafara cewa da Umma (wadda loƙacin su Umma suke ce mata) da baba da ƙanwata (matar sa kenan ita yake cewa ƙanwar sa tada) sai yace "ga kuma ƴata kana nufin duk suna raye zan gansu gobe,

"Eh Hamza ya kuma ce masa amma duk da haka yakasa shiru sai ya kuma ɗorawa da cewa, "Allah sarki Ameesha yanzu ta girma ko Allah yasa bata fushi dani, natafi na barta ita da mahaifiyar ta loƙacin da suke buƙatar taimako na, Da Allah ku kaini wajen inne mi yafiyar su gaba ɗayan su nasan su baba ma suna fushi dani, suna tunanin na aika ta abun da ake zargina shiyasa na daina ganin su tsawon shekaru babu wanda ya nemeni, Wallahi bani bane shariine yanayi yana kuka saboda abun sosai yake taɓa masa zuciya dan wasu maganganun ma baisan yanayi ba,

jin gaba ɗaya yana shirin fita a hayyacin sa yasa sukayi saurin dakatar dashi tare da kwantar masa da hankali har ya ɗan lafa, tun a loƙacin Bossay yace zai kira gida Hamza ya hanasa, Ayuba kam sai gefe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login