Showing 114001 words to 117000 words out of 170049 words
jarrabawar inda aka fara dasu yau kwana uku ma, tun safe suke fita idan kuma suka dawo anayi musu lesson agida da yamma kuma su tafi isalamiya, dan tun a washegarin ranar da suka tattauna, aka shirya komai ta koma isalamiya boko kuma tasaka kayan su Amra suka fara jarrabawar WAEC,
shima kuma haka saboda kwana biyu ko zaman gidan ma bayayi, acikin kwanakin har Gombe suka je inda sukayi bincike agidan da aka ajiye Abban Ameesha basu samu wata shaida ba, yaran kuma Ayuba suma anneme su anrasa andai ga gawar mutum ɗaya, sauran kuma ba asan inda suke ba...,
Dole suka dawo suka ci gaba da binciken anan, mutumin kuma sa su Sam suka ɗauko a Abuja shima an kuma fito dashi ankarɓi number mutumin da yake kiran sa, an ƙara mayar dashi,
Sam kuma yabawa Meer sauran binciken da suka fara, harda wayar da dadda ta basu da wayar baban sumayya da suka karɓa, har wayar Ayuba da ya buƙace da su bashi, itama sun bashi duk da ta farfashe amma ya karɓa da haka...,
....A ɓangaren Ayuba kuma ya farfaɗo saidai kuma kwata kwata baya magana, da yayi yunƙurin yin maganar sai tari ya sarƙe sa, saidai suyi masa allura ya ƙara komawa bacci,
acikin kwanakin can garin nasu shima ansan komai maganar taje musu, inda har Dadyn Bossay da Hamza suka kuma shiryawa, har da Ibrahim ƙanin Papa, Papa ne yace yaje ya wakil ce sa, sunje kuma sun samu wacce Ammah ta gaya musu anje an karɓi duk wasu shaida, abun ya zo musu da sauƙi suna zuwa masarautar suka faɗi komai babu wanda ya tada husuma ko neman tada tanzoma, saboda wasun su daman duk sunsan gaskiya kawai dai babu wanda ya fito ya iya magana,
Dan haka suna faɗar abun da ya kawo su akace za asauka abasu kujerar su, Amma sai Dady yace su bari dai sai sun ƙara shiryawa, sannan zasu dawo sai aƙara yin komai a nutse, yanzun saboda abun da yafaru ne yasa suka zo sukayi musu bayani.....,
_____A ɓangaren Dadyn Rasheeda, aure babu fashi duk da halin da yake ciki ta wani fanni amma hakan baisa ya janye maganar auren ba, domin gida har yafara cika da mutane sosai ƴan biki dan kuwa gobe ma ɗaurin aure, Rasheeda ma zuwa yanzu ta haƙura zata aure sa, saboda wayon da dady yayi musu, nacewa ai baban Bossay shima ɗan sarki ne, dan haka idan ta aure sa mijin ta Bossay nan gaba shine sarki, shi kuma Meer da take cewa shi take so anriga anyi masa aure kuma koda ta shiga gidan baza taji daɗin zaman gidan ba saboda da ƴar uwar sa ce komai zaiyi sai ya fara yiwa waccen musamman ita da baya sonta,
loƙacin da taji labari kuwa tasha kuka sosai , saidaga baya ta haƙura ta yarda zata auri Bossay saboda ita bata son kishiya da ta auri wanda yake da mata gwanda ta fasa auren, amma kunya ta hanata kiran Bossay tabari kawai idan anyi auren zata basa haƙuri ta shawo kansa,
Yanzu hakama ana can cikin ƙawaye ana ta shirye shiryen tafiya dinner, duk zumuɗin bikin da cewa za'ayi sati ana shirye shiryen sai gashi ba'ayi ko ɗaya ba, Dady ya hana, itama kuma daman ta janye saboda bataso duk ayi Bossay yaƙi zuwa ƙawayen ta suyi mata dariya shiyasa tace musu duk ta fasa, dinner kaɗai za ayi sai ɗaurin aure,
_____A ɓangaren Bossay kam yana ɗaki a kwance babu lafiya saboda baya son auren hasalima babu wanda yagawa maganar auren wayoyin sa ma kuma duk ya kashe su, dan baya farin ciki da auren, Hamza ma yayi iya bakin ƙoƙarin sa wajen ganin anfasa auren amma abun yaci tura Dady ya kafe yace sai anyi, shiyasa shima Hamza ya ɗauke ƙafa ko gidan ma baya zuwa, saidai wataran su haɗu a asibitin wajen Ayuba,
Dan haka su kaɗai suke shirye shiryen su ko gidan ja shigo babu wasu mutane sosai, dan Ammi ma idan ta tashi sanar da maganar auren sai tace iya ɗaurin aure za'ayi shima kuma ba wani abu za ayiba ana ɗaurawa za akai amarya, to shiyasa ma gidan yakasan ce babu wasu mutane sosai, wasu duk sai zuwa gobe zasu ƙaraso....,
Amma dai can cikin masarauta ansan da maganar ƙarewa ma anan Papa yace ma za' a ɗaura auren a masallaci gurin,
Duk da sanin kuma sa akayi manyan ne kawai suka sani, labari bai isa kunnen Ameesha ba, shima kuma Bossay har yanzu baiji labarin auren Ameesha ba, da abun sai yafi masa illah,
yau da yamma Abban Ameesha yace Meer yazo ya kaishi yaƙara dubo jikin Ayuba,
Har sun shirya zasu sai su Ummy da Dadda Da Maama suma suka ce zasu je su dabasa, tun ranar farko basu ƙara komawa ba,
Koda sukaje yana bacci,haka suka gama zaman su, suna shirin fita kuma,
sai ga Dadyn Bossay da Dadyn Rasheeda sun shigo, komawa sukayi suka gaisa, suna cikin gaisawa kuma Ayuba ya farka,
yana farkawa idon sa ya sauka akan Dadyn Rasheeda, kamar zai faɗo haka ya yunƙura zai tashi sukayi saurin yin kansa Dady yamayar da shi ta kwantar,
Gaba ɗayan suka shiga yi masa sannu, amma baya jin na kowa idon sa da hankalin sa gaba ɗaya yana kan Dadyn Rasheeda, shi kuma inbanda kallon gargarɗi da yake binsa dashi,
Ayuba yana so ya buɗi bakin sa amma yakasa ga maganar abakin sa amma ta maƙale,
Kawai hawaye suka ga yana saukowa daga cikin idon sa, duk babu wanda baiyi mamakin ba, sun matuƙar tausaya masa dan atunanin su wani zafin ciwon ne ya tayar masa,
Abban Ameesha ne ya kalli Meer da yayi zaune acan gefe yana daddana wayar sa, tace "ko zaka kirawo likita yazo ya kuma duba sa, kamar da matsala, kayi sauri yayi maganar yana ƙara matsawa kusa da Ayuba yana yi masa sannu, da basa haƙuri, dan gani yake duk kamar shi yaja masa, yana matuƙar tausayin sa, musamman ma idan ya tuna ta dalilin sa ya haɗu da iyayen sa, nadan shi ba da tuni har yanzu yana can cikin wani irin hali, shiyasa yafi kowa jin wannan rashin lafiyar da yake ciki,
Da sauri Ayuba ya shiga girgiza kai tare da ɗago hannun sa da ƙyar ya shiga nuna inda Dadyn Rasheeda yake da tunkan hankalin su ya koma kansa Dadyn Rasheeda yayi saurin matsawa daga inda yake, duk da kallo suka shiga bin inda yake kallo amma basu fahimci komai, dake Meer yana nesa dasu kaf abun da ya faru akan idon sa, yaga loƙacin da Dadyn ya matsa daga inda Ayuba ya nuna sa kuma yaga idon Ayuba a inda ya sauka,
Dadda ce tace "Allah sarki gaskiya yana jin jiki kuma kamar da abun da yake son cewa naga yana ɗaga hannu,
Dadyn Bossay yace haka yake kullum muka shigo haka yake yi, daman ance ko ya tashi ba lalle kwakwalwar sa ta dawo daidai ba saboda buguwar da yayi,
Nan duk suka shiga tausaya masa suna ƙara yi masa sannu,
Ayuba yana so yayi kwana da hannun sa amma bazai iya ba, saboda dadyn Rasheeda gefe ya koma inda yasan bazai iya nuna saba,
Babu yanda ya iya haka ga haƙura sa nunasan da yake abun da yafi yimasa ciwo a zuciya kenan, kasa maganar da yayi,
sun daɗe sosai sannan su Maama suka ce zasu tafi, sai Abban Ameesha yace yau abarshi zai kwana dashi,
Da farko su Maama basu yarda ba, suka ce ai akwai masu kuka dashi ba a kwana a asibitin,
Dadyn Rasheeda yace Allah sarki ku rabu da shi mana yau ɗaya dai kunsan shi ya taimake sa shiyasa yake son shima ya taimaka masa, asibitin duk na gida ne ai, babu komai idan ya kwana, zai taimaka masa sosai,
"To shikenan gaskiya ce maganar ka, ka zauna ɗin tare dashi, tunda akayi maganar Ayuba yake faman girgiza kai nufin shi kar ya zauna ya tafi amma babu wanda ya gane hakan,
Nan suka fita suka barsu sai Dadyn Rasheeda ma yace ai daman suma tafiya zasuyi, sai gobe zasu dawo, tunda dare ya riga yayi,
Ɗaki ya rage daga Ayuba sai Abban Ameesha,
Dadyn Rasheeda da Dadyn Bossay suna fita suma kowa ya shiga motar sa, suka tafi, amma sunayin nisa dake ba hanya ɗaya zasuyi ba sai kawai Dadyn Bossay ya yanko kwana ya juyo, daman shirin shi kenan idan kowa ya tafi yadawo ya haɗa da Abban Ameesha da Ayuban yakawar dasu, dan ya fahimci Ayuba nason tona masa asiri, shiyasa kafin ya samu lafiya ya tona masa gwanda yayi gaggawar kawar da su gaba ɗayan su,
Tun yana kan hanya yagama shirya duk yanda zaiyi ya kashe su gaba ɗayan su ta hanya me sauƙi batare da kowa yagane,
______Gudu Meer game dasu kamar zai tashi sama da har saida Maama tayi masa magana akan lafiya yake irin wannan gudun sai yace mata bafiya ba tayi tayi kuma yagaya mata me yake faru amma yace zai gaya mata ba yanzu ba,
Duk yanda sukayi dashi yadaina gudun nan ko Yahaya musu dalilin gudun amma yaƙi jin koɗaya, Ummy har faɗa tayi masa, amma bai bi takan taba,
Aɗan ƙanƙanan loƙaci suka ƙaraso cikin masarautar suna zuwa bai gama daidaita parking ba, ya kashe motar ya fito yabarsu a motar,
Haka suka fito suma suna ta surutu da mita, Dadda tace tunda kuka ga haka wataƙil ko matsine ya kamasa yasa shi wannan saurin baki ga har ya fito ya tafi ba harda gudu gudu yake haɗawa,
Ɗan murmushi Maama tayi tace ai naga alama ko bayan gidane ya matse shi shiyasa yaƙi faɗa min, haka suka ci gaba da hirar su suna tafiya har suka ƙarasa suma,
Suna gama shiga shi kuma na fitowa, motar sa ya koma ya kuma janta aguje ya fita daga cikin gidan, ko da ya hau titin gudun ya cigaba dayi, kamar zai tashi sama.......
____Dadyn Bossay, yana ƙarasawa asibitin ya shige ɗakin da aka kwantar da shi, loƙacin da ya shiga Ayuba har ta koma bacci, Abban Ameesha kuma yana gefen sa akan kuje ra ya zuba uban tagumi yana tunane tunane, ko shigowar sama baiji ba,
Lura da hakan yasa dadyn Rasheeda yin saɗaf saɗaf ya ƙarasa shigowa ciki ya tura ƙofar a hankali yasaka mata muƙullin jiki yayi locking ɗin ƙofar, duk da haka Abban Ameesha baisan yanayi ba yana can ya tafi duniyar tunani,
A hankali ya shiga takawa yazagayo ta bayan sa, wani siririn zare ya ɗauko a aljihun sa sai kuma ƙyalle, ƙyallen ya ɗaga ya rufa masa a fuskar sa ya naɗe masa duka fuskar,
Hannu Abban Ameesha yakai yana ƙoƙarin cire abun yana cewa waye waye wai waye..........,
[15/11, 10:54 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
*_🅿️42_*
___Hannu Abban Ameesha yakai yana ƙoƙarin cire abun yana cewa waye waye wai waye..........,
Ɗaure masa fuskar yayi tamau da abun da ya rufe masa fuska, abun da ya dauko siririn zare shi ya miƙar dashi sannan ya saƙalo wuyan sa dashi, shirin ɗaurewa yayi niyar yi, zai shaƙeshi,
maganar Abban Ameesha ta sa Ayuba farkawa daga baccin da yake yana buɗe ido kuma idon sa ya sauka akan mugun abun dake faruwa, yunƙurawa yayi zai tashi da sauri sai Dady yayi saurin saka ƙafa ya tura sa ya koma,
Azaba da tashin hankali da gudun abun da zai faru tasa atake agun muryar Ayuba buɗewa, baisan loƙacin da hakan ta faru ba, da ƙarfi yace Doctors! Doctors!! taimako ba kowa anan waje, yanayi ne dan akawo taimako domin yayi iya bakin ƙoƙarin sa ganin ya miƙe yaje ya taimake sa amma haka sa,
Da ƙyar yaja jikin sa ya miƙa hannun zai dannan wannan socket ɗin da ake dannawa idan marar lafiya yana buƙatar wani abun, saidai yana dannawa yayi ƙara kaɗan, Dady yaje ya buge hannu sa da ƙafa,
mayar da hankalin sa yayi kan Abban Ameesha ya yaƙara tamke masa zaren dake hannun sa da niyar bazai sake saba har sai ya daina numfashi, ɗayan hannun sa kuma yasa adaidai saitin hancin sa da bakin sa ya toshe masa su,
Abban Ameesha jin azabar tayi yawa yasa shi tattaro dukkan ƙarfinsa da Allah ya hore masa yaji ana shirin rabasa da duniya, domin tseratar da rayuwar sa daga hannun wannan bawan Allahn dake son kashe shi da besan ko waye ba, da iya ƙarfin sa ya riƙe hannun Dady tare da miƙewa tsaye, idon sa a rufe shima yakai hannu ya shaƙo wuyan sa,
Dake baya gani dole dadyn Rasheeda ya fishi ƙarfi,
neman abun da zai mishi yake sai ya kalli gefe gefen sa inda ya hango wani ɗan katako dake jinkin window hannu ya miƙa ya zaro sa yaɗaga da ƙarfi zai sauke masa, yaji anriƙe hannu baikai ga buga masa ba,
cike da tsoro ya ɗago idon sa zuwa ga kan hannu sa da yaji anriƙe, zaro idon sa yayi kamar zai faɗi kasa cike da tsananin tsoro tare da mamakin ganin sa, saura kaɗan yasaki fitsari a wando,
Ana riƙewa aka murɗe hannu take yabada ƙara ƙas ɗayan ɓarin aka ƙara juya hannun aka lanƙwasa shi nan ma Saida yayi ƙara, sannan aka saki hannu ya fara raito dan an ɓala masa shi ta ciki,
Baisan loƙacin da ya saki ƙara ba yana kai ɗayan hannu yayi sauri riƙowa gashi kuma Abban Ameesha ya shaƙe masa wuya yaƙi saki,
jijiyo yin wuyan goshin sa duk sun fito sunyi raɗau, ga idon sa da ya juye ya canza, hannun sa yasa ya janye hannun Abban Ameesha sannan dunƙulle yakaiwa Dadyn Rasheeda wani irin kykkyawan naushi wanda bugu ɗaya saida ya zubar masa da haƙora biyu, ya tafi tagal tagal zai faɗi ya ƙara riƙosa da sauri ya kuma kai masa wani naushin ta ɗayan gefen,
Da sauri Abban Ameesha ya buɗe ɗaurin da yayi masa, yana kuncewa idon sa ya sauka akan su yaga yanda yake ta faman sauke masa naushi, a fuska yaƙi sakin sa,
Da sauri ya ƙarasa gurin tare da riƙe sa yana cewa ya isa haka kar ka kasheshi ka bashhi, haka ya faɗa yana ƙoƙarin janye sa daga jikin sa,
Da ƙarfi yace UNCLE! ka sake ni wallahi sai na kashe shi, saidai idan na kashe shi a ɗaure ni amma bazan taɓa barin sa, da rai ba,
Shima cikin ɗaga muryar yace "Meer ka sake shi nace kar ka kashe koma me yayi yakamata ka rabu dashi haka,
Meer bai ƙara ce masa komai ba yaci gaba da dukan sa har saida yaga baya yadaina motsi sannan ya sake sa, shima saida Abban Am.. ya riƙe sa ya janye sa sannan ya rabu da shi,
Abban Ameesha ne yace "wai me yake faruwa,
Ayuba dake kan gado yana maida numfashin jin daɗin zuwan Meer yace "wannan mutumin da kake gani mugune kadai na cewa a rabu dashi shine yasa aka ɗauke ka duk tsawon loƙacin nan dasa hannun sa yasan komai, shiyasa ya kuma biyo ka dan ya kashe ka kabari ai gwanda aka kashe shi kowana ya huta,
Cike da mamakin maganar da Ayuban yake faɗa Abban Ameesha yace "bangane me kake nufi ba mutumin da muka dawo a motar sa idan shine yasa aka ɗauke ni meyasa zai taimaka mana?
Nan Ayuba ya basu duk labarin abun da ya faru bayan tahowar su,
Sosai Abban Ameesha ya tsorata da lamarin, yana me mamakin yanda hakan ta faru dan baisan a inda wannan bawan Allahn yasan shi ba, bai sanshi ba bai taɓa ganin saba, amma shi yasan shi, Allah me iko kenan shine maƙiyin sa shi ya haɗa masa wannan sharrin, yayi shekara da shekaru a wani wajen,
Juyawa yayi ya kalli Meer yace "Nagode maka da kazo domin badan kai ba da tuni ya kashe ni shiyasa yasaka baki gurin cewa abarni anan saboda yasan abun da ya shirya, amma kai ya kaima kasan da hakan har ka dawo bakun tafi gida ba, taya kasan shi ya dawo......?
Meer bai basa amsa ba ya ƙara yin ka Dadyn Rasheeda yana zuwa ya hau caje jikin sa wayar sa dake aljihu ya ɗauko ta, ɗayan aljihun ya duba ko zai ƙara samun wani abun amma babu abun da yagani, dubawa yayi sai yaga da password hannun sa ya ɗago yasa yatsan sa ajiki ya buɗe wayar dashi, yasaka ta a 30 minutes after sleeping,
Sai loƙacin ta ɗago ya kalli Abba yace "UNCLE muje gida yanzu ba loƙacin baya ni bane,
Allah ya kiyaye gaba muje kawai ya faɗa yana kamo hannun sa, sannan ya maida kallon sa ga Ayuba yace ka ƙara kulawa zan turo yanzu a fita dashi,
Ɗaga masa kai yayi, yace "Nagode, ku kula dashi sosai dan inajin bashi kaɗai bane, duk yanda akayi yanzu hankalin su yana kansa a koda yaushe zasu iya kawo masa farmaki musamman ma yanzu idan suka san ka kama sa dole zasuyi wani abun dan gudun kar ka kamasa ya faɗi sauran, sai kun ƙara zafafa bincike, dan wannan ba ƙaramin criminal bane yana da mutane da yawa,
Meer ya ɗan dakata da niyar fitar da yake ya maida duban sa ga Ayuba sanan yace "Kar ka damu da wannan kaide ka kula da wannan zan nemo sauran, shima bashi yake ba sashi ake akwai ogan sa, a binciken da akayi mana angano yana yiwa wani aiki akan sa, kuma bazan bari kowa yasan nakama saba, ta hakan sai munfi saurin gano sauran,
"Eh