Showing 39001 words to 42000 words out of 170049 words
yaji ance ga matarka a hannun mu mune muka sa ceta, amma dai kafara duba wayar ka akwai saƙo anturo maka ta WhatsApp idan kuma ka gani kayi gaggawar kare kanka daga nan zuwa safiyar gobe yanzu wasan yafara nabarka lafiya yana shirin kashe wayar Waziri yayi saurin dakatar dashi.......,
Da sauri Waziri yace "kaiɗin waye idan ka isa ka bayyana kanka ina kakai min mata Wallahi idan wani abun ya sameta sai na ka.......,bai ƙarasaba yaji ƙit ankashe wayar,
Sauke wayar yayi yana matseta da hannun sa,
Gaba ɗaya sauran kansa sukayo da kallo tare da tambayar waye ya kirashi,
Ƙasa amsa musu yayi daida suka ƙara tambayar sannan ya gaya musu abun da mai kiran yace,
Sannan ya ɗora cewa "waye shi waye daga ina yake wannan ba muryar yaron da muke zargi bane wata Muryar ce daban zagaye falon ya shiga yana girgiza kansa dan yafi zargin Meer aciki amma yanzu yagane bashi bane ransa yayi mugun ɓaci hakan yasashi fita daga gurin taron nasu ko buɗe wayar ma baiyi ba, duk da kallo suka bisa, suna jinjinawa ala'amarin suma basu daɗeba taro ya watse tunda wanda ya haɗa ya tafi, suma dole su tafi kowa yakama gaban sa,
Zuwa daidai loƙacin da Meer yasaki videon nan kowa yana part ɗin sa wasuma sun fara bacci waɗanda basuyi bacci ba ƙalilanne videon ya riske su har inda suke,
Waziri da yabar gidan ma gaba ɗaya ya tafi can wajen da zai haɗu da bokan sa, yagaya masa inda matar sa take,
Tun a daren waɗanda sukagani suka fara magana magana tun anayin ta kaɗan maɗan har tafara fitowa da yawa waɗan dama basu gani ba saida akasasu suka gani,
Tun adaren dangin matar sa suma da videon yaje musu ta yanar gizo, wasu suka kwaso ƙafa suka nufo gidan sarki, zuwan sune yaƙara tayar da wasu kan kace mai magana tayi ƙarfi sosai Waziri ya kashe matar sa da kansa gashi kuma anduba ko ina ba asame saba,
Papa ma ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba jin abun da yake shirya wa akansu wanda ya ɗauki yarda ya basa ashe da muguntar da yake shirya masa, wannan wacce iriin rayuwa ce da yazɓi yaudara ɗan unwasa wanda suka fito ciki ɗaya mai yasa Waziri zaiyi msa haka mai ya nema ya rasa gata kuma martaba duk yabasa amma dashi za a haɗa baki a cutar dashi,
gashi kuma yaƙarawa kansa laifi, daganin hakan daman yasan ta'asar da yayi amma shine yazo yakewa mutane kunfar baki, maiye ribar sa nayin hakan, shi kisan da yayi ma yafi komai ɗaga masa hankali, hankalin sa bai gama tashiba saida yaga zuwan ƴan uwan ta gidan,
Gida ya naimi ya hargitse ga dare yayi, sosai kowa yana mamakin abun da waziri yake aikatawa yana zaluntar ɗan uwansa ga kuma kisan dayayi ya kashe matar sa da hannun sa ya kuma fitar da ita daga gidan yazo yace ansace ta,
Ƙarfe ɗayan dare har ta wuce amma idan ka shigo gidan nan sai ka rantse ba dare bane saboda yawon mutane da kuma surutai da ake ta faman yi akan wannan videon,
Da ƙyar Papa da taimakon wasu daga cikin gidan dan Ibrahim ma ƙanin su dake wajen masarauta saida ya shigo sauƙin tama Allah yasa gwaggo tayi bacci kuma ba a tashe ta ba tana can tana bacci batasan wainar da ake toyawa ba mai zafi zafi,
Gaba ɗayan su babu wanda ba damuwa a fuskar sa, musamman Papa Maama kam batayi wani mamaki ba saboda daman tana zargin sa gashi yau Allah ya tonu asirin sa dole kuma ya fito da sauran, ita kam taji daɗin wannan rana da Allah ya nuna mata maƙiyin ta ido da ido, ashe zata ga wannan ranar da kanta basai ta mutu ba, itadai babu abun da zatace sai godiyar Allah da fatan Allah ya tona asirin sauran ma,
Da ƙyar aka samu kowa ya tafi makwancinsa aka bawa ƴan uwanta haƙuri subar maganar zuwa safiya idan an nemo shi wazirin sai aji inda yakaita, ƙin amincewa sukayi saida ƙyar suka haƙura saboda dangin ta basu da haƙuri ko kaɗan kuma duk da haka sun kafa sun tsare sunce babu inda zasuje zasu tsaya agidan har sai anfito musu da ƴar uwarsu anbimata haƙƙinta,
Da haka aka amince dasu sannan suka koma part ɗin ta duke suna masifa da kunfar baki kuma abun haushin ma maza da mata haka suka taho wai su antaɓa ƴar dangi,
Waziri nacan gurin boka ya riƙe shi yana shirya masa ƙabali da ba 'adi shine ma ya hanasa tafiya yace masa yabari sai gobe zaiyi masa aiki cikin dare duk inda take da safe za adawo da ita wanda ya ɗauketa da kansa zai dawo da ita har inda ya ɗauke ta, hakanne ya hanasa dawowa gida a ranar,
Washe gari kam da safe wajen ƙarfe takwas boka gabashi damar tafiya,
A masarauta kam tun asuba aka ɗora daga inda aka tsaya gida ya cika da muane dan yarama saidai suka fito waje gashi anrasa inda Waziri ya shiga,
Suna haka wata motar ta shigo cikin masarautar gaba ɗaya idanu suka koma kanta wasu har suna ƙarasawa gaban motar,
Wani namijine ya buɗe ya fito sai wata mace ma aɗayan ɓarin itama ta fito,
Namijinne ya zagayo wajen mutanen yayi musu sallama, yace dan Allah yana neman iso gun sarki yazo da wata muhimmiyar magana,
Tofa nan aka shiga ƴar kallon kallo jin yace sarki alhalin yanzu dai babu sarki a cikin masarautar, amma wasu sai sukayi hankalin cewar to, sai sukaje suka sanar da Papa saboda baya gurin,
Ba daɗewa papa ya fito cikin sauri yaƙaraso gurin,
Mutumin ne ya tsugunna har ƙasa ya gaida Papa cike da ladabi saboda ba wani babba ne kamar ma saurayi amma dai yana da manyan ta wataƙil ma yana da aure,
Bayan sungama gaisawar Papa yace yaro ina jin ka maiyake tafe dakai naji ance kazo da muhimmiyar magana,
Eh daman game da videon da aka watsane jiya a media kuma naga daga nan gidan sarkin akace abun yafaru to shine ɗazu da asuba munfita da matata zankaita gmasibiti mahaifiyar ta ba lafiya, sai mukaga mutumin da ya kashetan amota sai na ringa kallon sa naga ya shiga wani layi sai kawai nabisa muna zuwa muka ga ya fito da abu acikin buhu tunda ga nan nayi tunanin wataƙil gawar ce yakeson ya jefar shine muka tsaya daga ɗan nesa dashi, yana cirota ya ajiye ta agun ya shiga mota yabar wajen shine mukuma mukaje gurin muna taɓawa mukaji mutum shine muka ɗauko ta,
saboda a ƙasan videon anrubuta duk wanda yaganta ko yaga mutu min yazo yafaɗa shine mukazo, yanzu dai gata nan acikin motar mu ranka ya daɗe,
Ai kafin ma Papa yayi maganar ƴan gefen sa sun rigasa nan aka shiga sallallami ƴan uwanta suka ƙarasa bakin motar suka fito da ita, agaba kowa aka shiga kunce buhun ana buɗewa saiga Hindatu aciki,
Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un mutane suka shiga faɗi wasu suka fara kuka, ai tuni aka manta da wanda yakawota hankalin kowa ya koma kanta,
Suna cikin wannan koke koken saiga motar Waziri nan ta danno kai cikin masarautar ganin mutane dayawa yasa yafara sakin murmushi yana jin sanyi aransa zaton sa dawowar tane yasa aka haɗu haka tunda daman boka yagaya masa za a dawo da ita,
Da murnar sa fal rai yaƙarasa wajen tun kafin ya daidaita parking yayi saurin fitowa daga motar yana nufo inda mutanen suke ga mamakin sa sai yaga duk ana binsa da wani irin kallo wanda yakasa tantance kallar sa,
Gurin yaƙarasa cike dan shan jinin jikin sa ganin kallon da mutane suke yi masane yasa yafara jin wani iri.......,
_Ayi malej zuwa gobe plss bansan tsallaken rana gwanda ko yayane inringayi idan bansamu damar yi da yawan ba_
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
_____Gurin yaƙarasa cike dan shan jinin jikin sa ganin kallon da mutane suke yi masane yasa yafara jin wani iri.......,
Yana ƙarasawa gurin da mutanen sukayi rumfa yafara tambayar mai yake faruwa,
Gwaggo da zuwan ta kenan wasuma basu san tazo ba sai ji sukayi kawai tace "uwar kace ta faru ɗebabe marar mutunci makiri mai fuska biyu Allah wadai da haihuwar ka, wanda bai gaji mutunci ba da sanin yakamata kai muguntar taka karasa a inda zakayi ta sai akan ɗan uwan ka da matar ka dake kai kawo iya shege da ƙwarewa awajen iya makirci, watakon dan kana tsoron karta tona maka asiri shine zaka kashe ta, marar imani wanda ya kwashe kayan sa daga gaban ma'aiki,
Kai ko kunya ma bakaji ba yanzu ya zakayi da ƴayan ka gasu nan suna kallon ka a matsayin makashin mahaifiyar su,
Da hannun ka kayi kisan kai kinsan kai Alƙasim da hannun ka, na shiga uku ni na haifi makashi da cikina wannan wacce irin masifa ce wayasan ma adadin mutanen da kakashi ɗebabe wallahi wallahi wallahi badan tsinuwa ba kyau ba, na maka ma ita na godewa Allah da mahaifinku baya raye ka aikata wannan abun nasan da kaine sillar kashe shi dan sai ya haɗiyi zuciya ya mutu,
Daman ance makashinka yana tare dakai, ashe duk wata ta'asa da ake shukata acikin gidan nan ashe kai kake haɗata munafuki mai fuska biyu, anyama kuwa nice uwarka ni na haifeka, ba musanja akayi min ba asibiti,
Amma saboda kai riƙaƙƙe ne kafi kuɓewa riƙa shine zakazo kana wani tambayar mai yake faruwa saboda baka kunya,
Waziri da yake jin kamar ya fashe da kuka ko ya tsaga ƙasa ya shige saboda cin mutuncin da gwaggo take masa agaban mutane alhalin kuma shi ba wani kisan kai da yayi, duk da yaga matar tasa akwance kuma ya tabbatar bata numfashi amma bashi yakashe taba ai to maiyasa ake zargin sa har ake jifansa da waɗannan kalmomin shi tunda yake bai taɓa ɗaukan ran mutun ba,
Jiyayi ma ransa ya ɓaci da maganganun da gwaggo take masa,
Cikin ɗaga murya yace gwaggo kinsan kwa mai kike faɗa waye yace muku ni na lasheata ni bani nakashe ta, kuma babu wanda na cuta dan haka kidaina jifana da waɗannan kalmomin amatsayin ki na uwa agareni idan kuma bakin ki yakamani fa, ni bani na kasheta ba wanda ya sace tane ya kashe ta amma bani ba kudain zargina da hakan bazan taɓa iya kashe mutum ba...,
Papa ne ya ƙaraso wajen sa da sauri yana zuwa baiyi wata wata ba ya kwashe shi da mari cike da ɓacin rai ya shiga nuna sa da yatsa numfashin sa nayin sama da ƙasa ganin sa yasa kamar ya haɗiyi zuciya wani abu ne ya taso masa daga ƙasan zuciyar sa,
Ɗagowa Waziri yayi fuskar sa ɗauke da mamakin Papa,
Kafin Papa yayi wani yunƙurin yin magana, wasu ƙannen Hindatu guda biyu maza sukayo kansa zasu dake sa, Ibrahim (autan su Papa) yayi saurin dakatar da su tare da basu, haƙuri suka tsata afara jin ta bakin sa,
Yana faɗar haka yace "muje cikin fada yaya, gwaggo, dan Allah muje bai kamata a tsaya anan dagaban wanda yadace da wanda ma bai dace ba koma mai yayi shifa Waziri ne kuma ƙani ga sarki ga ƴaƴan sa harda jikokin sa ai baikama da girman sa duk girman laifin da ya aikata ai bai canci hukunci ta irin wannan hanyar ba, yin hakan agaban mutane ba daidai bane komai yana buƙatar girma,
"Ɗan Allah muje kuyi haƙuri muje kuma bai kamata ku ɗauki hukunci da kanku ba kubari afarayin magana asamu mafita,
Papa da gaba ɗaya jinsa yake neman ɗaukewa gaba ɗaya dan yakasa gasgata abun ji yake kamar har yanzu wannan bala'in a mafarki yake jinsa ba gaske bane,
Cikin wata iriyar murya yace "Ibrahim ka rabu dasu suyi masa duk abun da zasuyi masa ya cancanci fiye da haka, daman ance wanda yakashe akashe shi ni babu ruwana aciki mutumin da yake don ganin bayana da iyalaina mai kuma yarage tsakanina dashi, daga yau bani bashi yaje, kuma ku ɗauke shi daga nan bana son ganinka wallahi,
Gwaggo kam kuka tasaka agurin kunsan tsoho wani bai iya jure abu, Ammah ce taje wajen ta itama da jikinta duk yayi sanyi kowa na gurin kagani baya cikin kwanciyar, musamman waɗanda abun ya shafa,
Ammah takamata tafara bata haƙuri sannan tajata suka bar wajen ta maida ita part ɗinta, dan gudun kar taje ta haɗiyi zuciya dan ta ƙaici, idan yayi mata yawa za'a iya samun matsala,
Shima Papa Saura kaɗan ya faɗi awajen Maama tayi saurin kamasa tana raɗa masa yayi haƙuri yabi a hankali ya daure,
Zuciyace ta kuma ɗiban Papa yaƙara caƙumo wuyan sa cikin ɗaga murya yace "su waye sauran kafaɗa min kai dasuwa kuke son ganin bayan mu! mai yasa! mai yasa!! nace mai yasa zaka min haka mai na tsare maka? Kai da suwa waye...!!?
Shiru Waziri yayin da wani ɓacin ran yake taso masa daga ƙasan zuciyar sa, cikin ɓacin rai ya fara girgiza kai yana cije baki yace "kasake ni.
Papa yace "baza a sake kanba, kayi abun da zakayi,
Maama da taga abun nasu yana shirin wuce gona da iri yasa tafara jan Papa tana cewa dan Allah maiye hakan da girman ku muje ciki mu zauna, abar maganar nan yanzu muji da maganar mutuwar yakamata ake ayi mata wanka a sallace ta, gawa tunjiya a ajiye kamata yayi afara gamawa da ita kafin ayi komai daga baya, kasake shi dan Allah,
Ƙin sakin shi Papa yayi saboda tunda yake baitaɓa jin ɓacin rai irin nayau ba,
Abdullah ne(mahaifin sam kuma ɗa ga waziri shine babban ɗansa) yaƙarada gurin shima yana jan Papa amma duk sun kasa raba su sai kallo yadawo kansu aka manta da gawar dake kwance agun,
abundai ba daɗin gani, dan wasuma har sunfara barin wajen daga cikin ma'aikatan gidan,
Abu dake gefe shima ya gama cika ƙiris yake jira ya fashe dan idan yatashi baza aji daɗi ba sai ran kowa yaƙara ɓaci,
___Cike da takunsa na isa da ƙasaita yake takowa gurin, jin ƙarar takun sa yasa wasu suka juya suna kallon sa,
Hannun wansa gaba ɗaya acikin aljihun wandon sa, a hankali yake tafiya cike da kwanciyar hankali sanye akan fuskar sa, kamar baisan abun dake faruwa ba,
yana zuwa gurin ya nufi wajen su Papa kai tsaye, agaban su ya tsaya yana ƙare nusu kallo kamar bazai tanka musu ba, saidai yagama shan ƙamshin sa, sannan ya buɗi baki ahankali kamar mai ciwon baki, murya ƙasa ƙasa yace "Papa minti biyu yayi maganar yana kai hannun sa kan hannun Papa yana ɗan jansa, Papa baisan loƙacin da yasaki she ba,
Yana ƙara haɗe rai, Meer ya kalli Maama da ido yayi mata alamar da taja shi subar wajen, gyaɗa masa mai tayi sannan ta riƙo ɗayan hannun Papa,
Tunda Meer yazo wajen Waziri yake binsa da kallo sai yanzu wani abu ya faɗo masa arai,
Da sauri ya zura hannu aljihun gaban rigar sa zai ɗauko wayar sa,
Meer ya matso kusa dashi tare da dafa kafaɗar sa kamar abun arziƙi sai yayi ƙasa da murya tayanda babu wanda zaiji mai yake cewa,
Can ƙasa ƙasa yace "ka makara maiyasa baka duba ba tun aloƙacin da yadace yanzu loƙaci ya ƙure maka, yanzu muka fara muzuba mugani waye zaiyi winner,
Yana kaiwa nan ya haɗe rai tare da matsawa daga kusa dashi sai kawai yajuya ya kalli Papa da shima shi yake kallo ga mamakin Papa sai kawai yaga Meer ya ɗage gira ɗaya yana jinjina kai, sai Papa ya mayar da kallon sa kan Maama sai yaga itama tana murmushi da jinjina masa kan,
Mamaki abun yabasa to mai suke nufi da hakan,
Maama da taga kallon da Papa yake mata shima sai ta jinjina masa kai,
Wata macece daga cikin ƴan uwan Hindatu ta ƙaraso inda suke tana wani binsu da wani irin kallon banza, tace "wallahi wallahi baka kashe banza ba sai munɗau mummunan mutaki akan ka, a daren nan,zaka ga abun da zai faru,
Juyawa tayi ta kalli Sauran ƴan uwanta tace "ku ɗaukota muje gida ayi mata sallah, dan naga gaba ɗayansu neman wulaƙan tamu suke, kuma babu wanda zamu ɗagawa ƙafa daga shi har su, zamuyi shiri na musamman,
watama taƙaraso gurin tace yaya wai kina nufin ahaka zamu tafi murabu dashi idan kuma ya mutu ba ai wallahi dashi zamu tafi daga nan sai station dan wallahi sai munyi shari'a dashi baikashe banza ba,
Waziri da yayi wuƙiƙi da ido yana raba ido ya kalle su ya kalli su Papa da suna jin abun da ake cewa amma basu iya cewa komai ba, koda yake ba laifin su bane duk wannan abun laifin Meer da shi ya shirya masa komai kuma gashi sun gani bashi da damar kare kansa, baida bakin magana, dole ya amshi duk hukuncin da sukayi masa kafin gaskiya ta bayyana, kuma yayi alwashin sai yaci mutuncin Meer sai ya wahalar dashi sai yarama wannan wulaƙancin da yasa akayi masa agaban mutane, anci mutuncin sa,
Yana wannan tunanin bai gama
ba yaji saukar naushi ta bayan sa, da sauri ya juya yana kallon mai dukan nasa, maza biyun nanne suka rufar masa suka fara dukan sa,
Da sauri Meer yacewa kowa nagun yabar wajen da kan kace mai kowa yabar wajen gudun ɓacin rai saboda yanda yayi maganar kowa zaiyi tunanin idan bai tafi ba zai iya hucewa akansa,
su Papa ma tuni Maama tajasa suka bar wajen daman ƴaƴan sa sun daɗe da barin wajen,
Waziri tun yana jurewa yagadai basu da niyar barinsa sai yafara ƙoƙarin ƙwatar kansa, amma yakasa,
Saida sukayi masa dukan