Showing 48001 words to 51000 words out of 170049 words
kije kawai plss go yafaɗa yana nuna mata ƙofa,
Ƙin motsawa tayi daga wajen,
Ganin hakan yasa shi daka mata tsawa da ƙarfi tace " I say go, get out!!
tsorata tayi da yanayin sa bata san loƙacin da ta faɗa jikin sa ba tare da fashewa da kuka, tasa hannun ta gaba ɗaya tayi cropping ɗin tana ƙara sakin kuka, rumtse idonsa yayi yana maijin rungumar da tayi masa har cikin ransa, duk wani sassa na jikin sa saida ya amshi wani irin sabon lamari da shi kansa baisan wane irin yanayi bane,
Batare da ya buɗe idon sa ba yasaka hanu ya cireta daga jikin tare da janta yaje har bakin ƙofar ɗakin da kansa ya buɗe sannan ya turata waje cikin main office ɗin shi kuma ya rufe kansa acikin ɗakin dake cikin office ɗin,
Abakin ƙofar ta zube tana kuka tana basa haƙuri dan ji tayi bazata taɓa iya tafiya ba tabar sa ba,
Tun tana bashi cikin ɗaga murya har muryar ta tafara dishashewa, tana faɗa ƙasa ƙasa,
Sam shima yana bakin ƙofar kawai ya haɗa kai da gwiwa yana tunani, yana jinta amma yakasa haƙura ya buɗe mata duk da harcikin ransa yake jin kukan ta, amma bazai iya buɗe mata ba yanzu sai ta wahala so yake tafara jin yanda yake ji, da tanajin yanda yake ji da bazata ringa yi masa magana irin haka ba,
Tun tana jinta ƙasa ƙasan har yadaina jin ta hakan yasa ya tashi da sauri ya buɗe ƙofar, abakin gurin yaganta ta kwanta tana bacci, tsugunnwa yayi ya ɗauke ta ya shigar da ita ciki akan gadon ya kwantar da ita tare da rufa mata abun rufa, yana kallon fuskar ta da duk ta ɓaci da hawaye,
tashi yayi ya shiga wanka, yana fitowa yayi sallar nafila, sannan ya koma kan kujera ya kwanta da tunanin inda zai samamu su, zauna duk da yaje ya gargaɗi wasu koda anzo neman sa ko waye ace baya nan amma duk dahaka sai yabar cikin hospital ɗin bazai ci gaba da zama ba, wayoyin sa ma ya kashe su gaba ɗaya....,,
Adaren dai da ƙyar yasamu bacci ya ɗauke sa,
A ɓangaren momma ma haka dan har ta fishi shiga damuwa ma, gashi ita kaɗai abun yake cinta takasa gayawa kowa, sai juyi kawai take tana tunanin sa takasa bacci, Abban sa kam tunda ya tambaye ta mai yake damunta tace masa bata da lafiya ya tambaya tasha magani tace eh, daganan bai ƙara bi takan ta ba saboda shima ba acikin nutsuwa yake ba, dan shima da ƙyar yayi bacci,
Itakam takasa daga ta tashi zaune sai ta kwanta ko kaɗan takasa jin baccin (uwa kenan, Allah yaja da ran iyayen mu idan ba uwa ba waye zai iya yin hakan)
idon ta biyu har aka fara kiran sallah saida saidai tayi sallar asuba sannan bacci ya ɗauke ta akan sallayar da tayi sallar,
_*Washe gari*_
Azeema na tashi ta fara haɗa ina ta ina ta dan tace da wuri zata tafi, Maama har tasama mata motar da za'a kaita gida, amma saida tasan yanda tayi akace Hamza ne zai kaita, sai Ameesha ta rakata har gida, sannan adawo da ita,
Azeema na murna tafiya Ameesha ta taƙaicin tafiyar ta ta,
wajen ƙarfe shaɗaya na safe ragama shirya wa tsaf taje tayiwa su Maana sallama da Dadda, har part ɗin Ummy sukaje tayi musu sallama sannan sukaje part ɗin su Hamra, nanma suma basuji daɗin tafiyar da zatayi ba atare suka ƙara fitowa sukaje part ɗin Salahudeen da tare dashi zasu tafi sai Papa ya hanasa yace yabari ba yanzu ba, hakanne yasa yafasa zuwa,
part ɗin suka ƙara komawa saboda har yanzu Hamzan bai fito ba kuma ta kirasa baiɗaga ba, shiyasa suka koma falon suka zauna zaman jiran sa, su Ameesha na ta tsokanar ta Allah yasa kar yazo Allah yasa afasa tafiyar yau, ko na yimaga bakin kar ta tafi,
Meer me ya fito daga ɗakin sa zai fita saiga su Hamza nan sun shigo suma da sallama abakin kowannen su, su su uku ne, Hamza, shettima, bossay, da tun safe suke gidan saboda momma ta kirasu ta tambaye su ko yazo wajen su, sukace A'a shine daga nan kuma shettima yakifa Hamza dan yaji mai ke faruwa Hamza yaga masa iyakacin abun da yasani, shine yakira bossay suka taho gidan tare, tunda suka zo kuma suke kiran layi kansa amma akashe,
Shine momma tace suzo siyiwa Papa bayani dan bazata iya faɗa ba da kanta,
tsayawa sukayi tare da miƙawa Meer hannu suka gaisa ɗaya bayan ɗaya duk ya tsaya suka gaisa kuma fuskar sa ba yabo ba fallasa bazaka ce walwala yake ba kuma bai haɗe taba kamar kullum kawai dai asake take, ba ɓacin rai,
Tunda Bossay ya shigo idon sa yana kan Ameesha masoyiyar sa yayi kwar ta da yawa bai samu damar zuwa ganin taba a ƴan kwanan saboda tashin hankalin da shima yake ciki, tun ranar da sukayi waya da Rasheeda har yanzu komai yaƙi dawowa daidai, tace bata sonsa amma su dady da dad ɗin ta su dage aure ba fashi sunci gaba da shirye-shiryen su batare da sanin ita kanta Rasheedan ba,
Ganin ko kallon sa batayi ba irin kamar ma bata san da zuwan sa ba gurin,
A hankali yace babyna, yana kallon ta, bashi kaɗai ba gaba ɗayan su ɗagowa sukayi suna kallon sa, Meer ma zuba masa ido yayi yana jiran yaji wacece baby shidai tunda yake dasu bai taɓa jin an kira wata da baby ba,
Haɗe rai tayi tana turo baki gaba kamar zatayi kuma tace, "ba ruwana da kai kaje ka nemi inda babyn ka take shine tunda katafi kaƙi dawowa inganka sai yau zaka tuna dani saboda baka damu dani ba ko ƙara turo baki tayi a ƙarshen maganar har haɗa masa da harara,
Hakan ba ƙaramin burgeshi tayi ba dan haka yasama mata dariya yana cewa kaina bisa wuya nayi kuskure a yafe min nama dawo nan daga yau kullum muna tare,
Da sauri ta miƙe tsaye cike da farin ciki da kuma yarinta tace "dan Allah da gaske kake,
Kai ya ɗaga mata yace "ina miki wasa ne,
Cike da farin ciki tayi kansa da sauri tana shirin rungume shi saboda itama tayi kewayar sa, bata kai ga ƙarasawa ba, Azeema tayi saurin riƙota, tace a wajejen kunnen ta tace "ke bakida hankali ina kike shirin zuwa, ko jan aji babu,
Kunya ce takama Ameesha karom farko kenan da gafara jin kunyar bossay komawa tayi ta zauna,
Su kuma duk dariya suka saka mata saboda yanda tayi yasa suka fahimci abun da take nufi, ƙarasa zama sukayi akan kujerun falon,
Sannan su Amra suka shiga gaida su, duk suka amsa, Amra kam tashi tayi daga inda take ta koma gefen Shettima mutumin ta,
Shima shettima idon sa yana kan Azeema kuma sarai yana lure da ita dan ko gaida shi batayi ba kuma bata kalli inda yake ba hakan ba ƙaramin ciwo yayl masa ba abun ya tsaya masa arai,
itama kuma a ɓangaren ta abun da take rayawa kenan mai yasa baiyi mata magana ba, kuma tunda ya shigo taji ta kasa sukuni gaba ɗaya mood ɗin ta ya canza tunanin ta duk ya koma kansa, duk da ga Hamza agun da loƙaci zuwa loƙaci sukan haɗa ido sai ya sakar mata murmushi amma takasa mayar masa dashi koda sauɗaya ne,
Bayan sun gama gaisawa Shettima yake sanar da Meer abun da yakawo su, suna so ayi musu magana da Papa,
Shine ake sanar dasu ai Papa tun safe ya fita baya nan, saidai su jira yadawo,
Daganan Meer ya fice daga falon yabar su aciki,
Sai Hamza ma ya miƙe yace "to ko zakujirasa ni bari inje indawo ko ku bincika gurin aikin sa idan yana nan sai asanar da ita ko ya kuka ce?
Bossay yace eh hakan ma yayi amma maiyasa baza mu tafi tare ba ina zaka daman naga kamar sauri kake,
Ɗan shafa kansa yayi yace "eh wallahi zan ɗanyi rakiya ne Madam zan raka gida tun ɗazu ma zuwan kune ya tsayar dani, da mamaki Bossay yace wace kuma madam,
Da hannu ya nuna masa inda Azeema take,
Daram daram shettima yaji gaban sa na bada sauti, mai hakan yake nufi da ya kirata da Madam,
Take duk wani annuri na farin ciki ya ɗauke daga kan fuskar sa ji yayi kamar zuciyar sa na tsintssinkeya ga wani rin bugu da take masa fat fat fat
Da sauri yasa hannu ya dafe saitin dan ji yake kamar zata faɗo, loƙaci ɗaya gaba ɗaya yanemi nutsuwar sa ya rasa,
Bossay nayi masa ƴar dariya yace "to masu Madam adawo lafiya tunda ba a neman ƴan rakiya, nima bari na ɗauki tawa Madam muje mu shaƙara idan ka dawo sai mutafi cigiyar tare idan kuma shettima zaiyi gaba to danni ma sai nafita nayi kewar ta da yawa, ina buƙatar ta kusa dani ko baby yayi maganar yana kallon Ameesha tare da ɗage mata gira ɗaya,
Murmushi ta sakar masa tare da ɗaga masa kai alamar eh,
nan sukai tayin surutun sa amma shettima bai tanka musu ba ko eh baice ba,
Azeema tun tana dariya har cikin ranta har tafara yin ƙasa ƙasa saboda hakan nan ta ringajin wani iri game da rashin walwalar shettima duk tasan shi shi mai yawan surutu ne da tsokana amma loƙaci ɗaya ya canza baya ko magana wata zuciyar tace mata maiyasa zaki danu da samuwar sa, batasan loƙacin da maganar ta suɓuce mata ba a fili tace kuma fa hakane,
Ameesha tace hakane mai?
Azeema ta girgiza kai da sauri tace bakonai,
Hamza ne ya katsesu da cewa taso mutafi muna ƙara ɓata loƙaci anan, Bossay ya miƙe shima yace baby taso muje yaje har gaban ta ya riƙo hannun ta, yana kallon su Hamza yace idan wasu sun isa suyi haka man namu ba irin naku bane,
Kallon sa Hamza yayi yace ai na wannan salon na yara ne, mu namu yara basa gani Madam taso muje,
tana shirin tashi kenan taji ƙarar wayar ta kamar shigowar message dakatawa tayi da tashin ta shiga message ɗin tafara karantawa kamar haka________
_kar kisake kibishi nagaya miki kuma kisame ni a motata ina jiran ki nan da minti goma zaɓi ya rage naki kizo ko kar kizo_
Gabanta taji yayi wata irin faɗuwa bayan ta gama karantawa ɗagowa tayi ta kalli inda yake sai taga yan ya haɗe rai kamar anyi masa albishir da wuta, idon ta nakansa sai kawai taga yatashi ya fita batare da yayiwa kowa magana ba tunda take dashi bata taɓa ganin sa cikin ɓacin rai ba irin haka,
Hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,
Tana cikin wannan tunanin Hamza ya katse ta da cewa "Madam zafa su fita kinga har zasu rigamu tafiya kitaso muje,
Kamar mutum mutum haka ta tsaya tana kallon sa azahiri zakace shi take kallo amma a baɗini gaba ɗaya hankalin ta baya gurin........,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
'kamar mutum mutum haka ta tsaya tana kallon sa azahiri zakace shi take kallo amma a baɗini gaba ɗaya hankalin ta baya gurin.....,
Ameesha ce ta taɓota, tare da kamo hannu n ta ta miƙar da ita tsaye, tana ƙare mata kallo tace ke kam lafiyar ki ƙalau ana tayi miki magana bakijin mutane tunanin mai kike haka,
Cikin wani irin yanayi Azeema ta ɗan kalle ta, tare da cewa ba komai ta ƙwace hannun ta daga riƙon da tayi mata,
Ga mamakin su sai kawai suka ga ta nufi hanyar waje batare da tace da Hamza su tafi ba, ko ta tankawa Ameesha maganar da takeyi mata, ba tace da kowa komai ba,
Ƴar kallon kallo suka shigayi a tsakanin su kafin suka maida duban su ga hanyar fita suka bi ƙofar da kallo kowa na mamakin dalilin ta na fitar, ga yanayin ta da ya sauya, duk cikin su babu wanda yakawo wani abun,
Ameesha ce ta katse musu shirun da cewa bari inbi bayanta, ko mai yake damaunta haka, tana faɗar haka ta fice daga ciki gaba ɗayan su, suma suka bi bayan ta, akusan tare suka fito gaba ɗayan su,
Suna fitowa suka ganta awajen motocin da zasu tafi,
Ƙarasawa sukayi suna ƙara tambayar ta amma taƙi tayiwa kowa magana ta kalli waje ɗaya kawai, daga ƙarshe ta buɗe motar da zasu tafi ta shiga saboda tun da safe suka saka kayan nata aciki,
Buɗewa Ameesha tayi ta shiga itama fuskar ta ɗauke da damuwa tace besty wai meke faruwa mai akayi miki meye ya ɓata miki rai nasan dai ba haka kike ba, ɗazu ma kina ta murnar amma yanzu loƙaci ɗaya kin canza gaya min mai ya faru,
Shiru tayi mata na ƴan mintina sannan tace besty kije kawai ni zan tafi zamu yi magana awaya, koma meye zakiji, kar ki damu bawani abu bane,
Badan Ameesha tasoba ta rabu da ita akan zasu yi wayar,
Jikin Hamza duk yayi sanyi babu wani karsashi ajikin sa dan ko sallama yakasa yiwa Bossay kawai ya buɗe ya shiga, ya tayar da motar suka bar gurin,
Saidai su Ameesha suka ga tafiyar su sannnan suka shiga mota har Hamra da Amra suma ya fita dasu,
Shettima kawai kifa kansa yayi yana maijin ɗacin abun da tayi masa watakon yace kar ta shiga amma shine ta shiga, suka tafi bayan tasan yana mota yana jiranta,
Cike da jin haushinta da taƙaici da kishi ya tayar da motar shima yabi bayan su......,
*************************
Zaune suke agaban bokan su gaba ɗayan su, amma yanzu babu mutane biyu Waziri da matar sa,
Bokanne ya kwashe da dariya yace
"Kada wannan ɗan ƙaramin abun ya ɗaga muku hankali munfi ƙarfin su, daga yau komai zaizo ƙarshe, abun da yasa ma har yayi nasarar kama su dan kun jinkirta zuwanne da ace kunje tun ranar kun ƙaddamar da abun da nagaya muku da haka bata faru ba, amma yanzu ma ba wata matsala ɓace dan yakamasu babu abun da zai iya yi musu yanzu haka suna cikin kwanciyar hankali, babu abun da ya isa yayi musu kawaidai ya fita dasune daga cikin gidan,
Nayi muku alƙawari daga yau za amantar da kowa abun da ya faru babu abun da zasu tuna,
Ɗaya daga cikin su yace boka mai aiki kamar yankan wuƙa, kar kace na tare numfashin ka, taya zanuje mu zuba bayan kace gaba ɗayan mu zamu shiga cikin fadar gashi kuma babu guda biyu, kuma babbar matsalar ma shine ta yanda zamu shigar mata ɗaki gaba ɗayan mu nan babu wanda yake shiga ciki, kaga kwa idan wanin mu ya shiga ai zasu iya yin zargin wani abun,
Nidai a tunanin dama ka bamu wata hanyar da zamu bi banda wannan,
Nan sauran ma suka fara faɗar albarkacin bakin su, wajen nemo wata hanyar dan gaba ɗayan su hankalin su ya tashi da kama su Waziri da akayi, suna ganin kamar suma za'a gano su,
Suna gama faɗar haka boka ya ƙara saka wata irin mahaukaciyar dariya cikin dariyar tasa yace "kar ku damu da komai kawai kuyi abun da nace muku kar kubari ranar yau ta wuceku ita kaɗaice ranar ku, taƙarshe,
Abun da zaku fara yi da farko shine kuje ku fara shiga cikin fadar ku watsa shi kamar yanda nagaya muku ranar nan, daga baya kuma washe gari sai kuje kusaka na cikin ɗakin, ko wani zaku iya wakilta wa ba lalle sai ɗaya daga cikin ku ba,
Kudaina kokanto akan aiki duk abun da nasa gaba sai ya kasance, babu wanda ya isa yaja da aikina ko waye shi,
Idan kuma mutum yayi kokonto da aiki na to zanjanye hannu na daga kansa kuma duk inda zashi bazai taɓa samun yanda yake so ba,
Kutashi kuje na sallame ku, kuje kuyi abun da nagaya muku ku shirya atare, kushiga ciki kuma kar ku bari kowa ya ganku,
Saidai yagama gaya musu duk yanda zasuyi harda time yabasu, ya ƙara ƙarfafa musu gwiwa sannan sukayi sallama suka bar gidan dan wannan karon har gida sukaje bashi yazo ba,
loƙacin da suka baro wajen sa ana kiraye kirayen sallahr magariba, dan haka Bama kowa ne ya lura da shigowar su gidan ba,
Kowa nasa guri ya nufa da bayan sungama haɗa planing ɗin yanda zasu haɗu,
**************************
Azeema,
____tunda suka taho bata iya koda kallon inda yake ba bare ta bashi amsar tambayoyin da yake mata haka ya ƙaraci maganar sa har yayi shiru abun ya matuƙar ɗaure masa kai,
Abun da ya haɗa ta dashi kawai shine kwatance da tayi masa,
ahaka suka ƙaraso ƙofar gidan yayi parking, sannan ya maida dukkan hankalin sa gare ta, cikin nutsuwa da kwantar da hankali yafara yi mata
magana,
"Duk da bansan mai yasame ki ba amma ina mai baki haƙuri ko inna miki laifi bansani ba, ina neman afuwar ki, idan kuma wani abunne yake damunki daban kigaya min kafin murabu idan bahaka ba bazan taɓa samun nutsuwa ba, dan Allah ki gaya min,
jitayi ya bata tausayi idan tayi masa haka bata kyauta masa ba, bai kamata ta ɗora masa laifin da banasa ba,
Murmushin dole ta ƙaƙalo ta azawa fuskarta, ta kalle sa tace "kayi haƙuri bakayi min komai ba kawai nuna abun yana damuna wataran haka nake tsintar kaina cikin irin wannan yanayin, sai kayi haƙuri dani