Showing 132001 words to 135000 words out of 170049 words

Chapter 45 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7210

signing takaddu zasu zama namu,

sai muka saki kuɗi mukaje har can muka ce zamu biya belin sa, suka nuna basu yarda ba, sai muka haɗa baki da shugaban muka bashi kuɗeɗe mukace yace zai yi masa transfer to wani prison, kafin yayi mukaje aka haɗa duk yanda za'ayi awani prison ɗin ta yanda ba wanda zai gane ba akaishi ba, suna fitowa dashi aka kaishi wani prison, aranar muka shiga dashi aranar muka fito dashi, sai muka maidashi wani gida muka ƙulle sa.....,

Daga baya muka kai masa ya buɗe mana amma sai yaƙi buɗewa da muka ga haka sai muka ƙara dawowa wajen Khadija. (DADDAR ASALI😂)....


sai muka ci gaba da takura mata muna mata barazana, daga ƙarshe muka ce tagaya mana password ɗin da ɗanta yake amfani dashi, batayi tunanin akwatin na gurin muba shiyasa tagaya mana da taga de dagaske zamu iya kashe su ita da yarinyar,

da ta buɗe mana shine muka dawo wajen sa tare da wasu takaddun na manyan filayen sa, da gidajen sa,

Da ƙyar muka samu yayi mana wasu,

Tun daga wannan loƙacin muka ci gaba, da gudanar da rayuwar yanda muke so tunda muke abun nan bantaɓa tako ƙafata garin kano ba komai ina daga can nake sawa ayi shi, dan daga bayama ita matar ƙanin tane ya kashe ta, saboda ta nuna zata yi mana fin ƙarfi a kan dukiyar, dan harma ta salwantar mana da wasu, faɗa yaso ya kaure mana, daga ƙarshe ma kawai ya kawar da ita, ta inda muka bambanta dashi kenan ni a gaskiya rashin imani na baikai ga ɗaukan raiba banso inkashe mutum ko inzama nice nace a kashe, bana kisa, dalilin da yasa ma suka kasance araye har kawo yanzu, bana kashe duk wani wanda yake karkashina,

misali kamar shi yaron da ita ƴar uwar tawa da jikar ta, duk babu wanda nasa akashe dukuwa da nacin da yake min a kashe su basu da amfani, ni na hana damar hakan amma badan ba da tuni sun daɗe da mutuwa kamar yanda yasa aka kashe mata miji da ƴar bansan ma anyi ba saidaga baya yake gaya min yasa duk ankashe su,

Loƙacin da akace kuma ansamu inda a salin yaron ɗan gidan sarauta ne kuma akace ɗan sarkin Kano ne,

Ni kuma arayuwata ina son sarauta, kuma da na zauna nayi tunani naga idan na bar ƴar uwata zata kuma fina akomai da farko ta fini da kuɗi kuma ace ta cigaba da jin daɗin rayuwa a gidan sarauta, ni ina zaune duk soyayya ta da gidan, wannan tunanin ne yasa na shirya da kaina,

Dirata a cikin Kano kuwa nasa akaje aka nemomin duk wani information na ƴan gidan harda nombobin wasu Saida aka kawo min, kuma duk me gadin kune da wannan aikin...., dan akan kuɗi babu abun da bazaiyi ba,

kwana biyu da zuwa na kuwa naci Sa'a aka sanar dani fitowar ta, anganta ita kaɗai, saida taje can gidan nasu na da, inda ta ɓoye akwatin, anan nashirya nida wasu muka bita gidan, loƙacin da muka shiga tana ta faman haki tana ƙwaƙulo ƙasa zata ɗauko ta, ganin mu yasa ta tsaya da komai musamman da ta ganni,

Da na gaya mata ko wacece ni awajen ta sai tafara murna zata riƙeni na dakatar da ita tare da gaya mata duk wasu abubuwan da nayi, kuma na ƙara gaya mata next plan ɗina akan ta zan ɗauketa ni kuma inshiga gidan dake halina da nata ba ɗaya ba sai takama ban haƙuri harda su kuka, wai dan Allah kar inkuma cutar da wani kuma intaimaka indawo da yaron da yake hannu na ita ta yarda ma ko kashe ta tasa ayi amadadin sa, shi in sake shi in ta kuma in kashe ta,

"Amma duk da wannan magiyar da take mun ban saurare ta ba, nasa suka dake ta tare da shaƙa mata abu ta suma nasa suka kaita ɗaki, duk wani abun ado na jiki na na cire su na ajiye sannan na ciri kayan jikin ta nasaka da naga sunɗan yi min yawa sai nasa riga biyu, yanda zan ƙara cikowa, sak na dawo kamar ita, daga nan nasa suka fita da ita daga gidan,

"Ni kuma nace sukaini bayan masarautar sannan nayi amfani da layin wayar ta saboda daman dashi nake duk wani kira ma sirri, ni a loƙacin ma bansan number wa nakira na kawai ɗauka nayi na kira, sannan na basu sukayi maganar, da aka gama sukayi gaba ni kuma na kwanta aƙasan gurin tare da ƙaƙalo haɓo ta hanci sannan dai na canza yanayin fuska ta, tare da gotar da ɗan kwalin, a haka kuka ke kula sameni, daga nan na far rayuwa daku, a hankali a nan duk nagama karantar komai na gidan ta yanda babu me cewa ba ta asalin bace.....,

Finally nagama baku duk abun da na aikata ina fatan za'ayi min hukunci me ɗan dauƙi......., Har tayi shiru sai kuma tayi saurin cewa, "Laaa na manta ban gaya muku ba, naga yanda kuke wani son ta kuna ji, da ita to dai saidai kuyi haƙuri dan ansamu akasi tayi musu taurin kai da yunƙurin guduwa, su kuma suka kashe ta, dan haka yanzu DADDAR ku tana lahira, me son ganin ta sai ya bita.......✍️✍️


🥺🥺Ah wannan maganar ai da mu ake nidai inason ganin ta dan haka sai na bita, rayuwa ba Dadda ai akwai matsala, Hajiya ƴar uwar DADDA, nifa ko sunan ki ma baki gaya mana ba🤔


"To Readers me zaki iya cewa game da page ɗin....!!!!!🤗🤗🤗🤗
[22/11, 11:25 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                    48
                  
............"ƙarya ne wallahi Dadda bazata mutu ba, nasan baza mutu ba, wallahi sai kinfito min da Dadda ta, Ameesha ke magana cikin kuka,

Yawancin mutanen gurin saida sukaji labarin wani iri dan wasuma basu yarda ba, gani suke duk ƙarya take,

Cike da mamaki da al'ajabi, Abban Ameesha yake binta da kallo yama rasa me zaice mata, gaba ɗaya tunanin sa ya tsaya, ya rasa wannan wace iri rayuwa yake, abubuwa sai faruwa suke da rayuwar su, daga wannan sai wancen, har sai yaushe zaiji sa daidai kamar kowa,

Takowa yayi yazo har gaban ta, sannan cikin yanayin muryar tausayi, yace "wai dan Allah duk abun da kike faɗa da gaske ne kina nufin bakece Umma ta ba, da gaske amma me yasa kikayi mata haka ƴar uwar kice fa baki sanya ba baki taɓa ganin taba amma saboda son zuciya kika zaɓi ki cutar da baiwar Allah da bata jiba bata gani ba, ki so zuciyar ki da yawa, kinyi abun da baza mu taɓa yafe miki dan da ki taɓa ta gwanda ki kashe mu, kin san wacece ita a gurin mu, kinsan muhimmiyar rawar da ta taka a rayuwar mu, "Please ki gaya mana inda Dadda take ni jikina bai bani ta mutu ba, wallahi Dadda bata mutu ba,

"To tunda kace bata mutu ba ai sai kaje ka nemota a inda ka ajiye, shawara gwanda ma kadena wannan maganar dan ko bata mutu ba yanzu zan sa akashe ta, saidai mu rasa ranmu gaba ɗayan mu, dan bazan taɓa faɗar inda take ba, zuwa wani loƙaci kuma dole ta mutu, saboda halin da take ciki, bazata iya ci gaba da rayuwa ba wuya zata kashe ta,

Cikin ɓacin ran da bai taɓa tsintar kansa ba, ji yayi zuciyar sa na wani irin tafar fasa kamar zata fito, ransa inya kai dubu to duk ya ɓaci, (to ƴar gadon ce ta motsa kunsan duk wanda ya fito daga tsatstson gwaggo to akwai zuciya) a harzuƙe yakai hannu ya shaƙi wuyan ta, yace "wallahi duk da kina matsayin ƴar uwar ta hakan bazai sa inyi miki duk abun da na faɗa ba, ki gaya min ina kika kaita, ki gaya mana inda take!!

Ƙoƙarin ƙwace kanta ta soma yi amma yanayin shaƙar da yayi mata bata wasa bace, dan baƙaramar shaƙa yayi mata ba,

Gaba ɗaya ƙarfin sa yasaka ya, da shaƙar da yayi mata da haka ya miƙar da ita tsaye, yana ƙara matse mata wuya,

Idon ta har ya kaɗa yayi ja, ya furfito waje saboda azaba,

Gudun kar ya kashe ta yasa, Papa yayi saurin zuwa gurin yace "ka sake ta kar ka kashe ta,

Amma Papa na maganar kamar da bango yake dan ko gezau baiyi ba, bare yayi yunƙurin sakin ta,

Abuu ma saida yayi masa, sannan yace "Allah in bata faɗa ba bazan sake ta ba saidai ta mutu, Abuuu yace "to idan ka kashe ta taya za'a samu inda take ka sake ta haka ya isa ai, zata faɗa yanzu idan ya sake ta, duk da haka ƙin sakin tan yayi,

Meer ne ya miƙe daga gurin Ameesha ya miƙawa Maama ita, sannan ya ƙarasa gurin su, hannu sa ya ɗora akan na Abban Ameesha, sannan yace "UNCLE sake ta ka huta ni zan ɗora, kasan sai na fika iyawa da kyau, bari kaga yanda za'ayai mata,

Sai yanzu aka samu ya sake ta, yana sakin ta Meer ya ɗora shaƙeta tare da taka ƙafar ta da karfi sannan ya turata gaba ta faɗi ƙasa, binta ya kuma yi tare da fusge hijab ɗin jikin ta,

Meer kayi mata a hankali cewar Maama da matar ta fara bata tausayi.

gashin kanta me kitso ya kamo jelar gashi ya jawo ta, da ƙarfi hakan kwa yasa rabin kitson ya biyu hannun sa, alamun ya jijjgosa daga can ƙasan,

Karar azaba ta saki tare da cewa wayyo Allah na kaina, dan Allah kayi haƙuri zan faɗa zan faɗa,

Ai Meer bai saurare ta ya kuma jawo kitso na biyu da ƙarfi shima yakawo saitin da wancen ya tsaya, haka ya ringa jawo su saida ya jijjigo mata wajen guda biyar sannan ya dakata, (kun gane wace irin jijjigo wa, kamar kayi kitso sai ajawo kitso ɗaya daga ƙasa da iya ƙarfin mutun, daga nan kuma sai gashin ya taho tundaga toshin sa ya cire gurin yazama na babu gashi ko ɗaya, to haka yayi mata yajawo mata guda biyar)

Azaba kuwa jinta take kamar kamar me, kamar anzaro mata duka ƙwaƙwalwar kanta gaba ɗaya kan ya ɗauki wata iriyar azaba, gaba ɗaya ya firgita ta, har tana shirin fara hauka, ihu kawai take, duk wanda ya ganta sai tausaya mata yanayin da ta koma, ga jijini da ya fara fitowa daga mafakar gashin,

Ameesha damƙe idon ta tayi tana ƙara sakin kuka dan har yanzu gani take kamar daddar tata ake yiwa haka, duk ta ƙudundune kanta ajikin Maama, jikin ta sai karkarwa yake, Maama ce ta miƙe da ita, da ido tayiwa Ummy alamu tazo su fita, atare suka fita,

Dan wasu ma bazasu iya kallon abun da Meer yakeyiwa wannan matar ba, dan duk wanda yaga bazai iya ba ɗaya bayan ɗayna suka ringa ficewa daga ciki har Papa ma fita, abudai kamar wasa sai duk aka fara watsewa ɗaya bayan ɗaya, musamman matan mazan kwa basu wani tausaya mata, zaman su suka yi suka ci gaba da kallon Meer abun da yake, koda wani irin kuka da take fitar wa na ban tausayi, indai ba dakakkiuar zuciya ce da kaiba, baza iya zama ka saurari kukan da take ba,

Sosai yagama fitar da ita daga cikin hayyacin ta, taji jiki koda azabar kan yabar ta, ai ba shiri ta faɗi inda take ashe tana can gidan da aka ɗauko Meer a Gombe,

Sai loƙacin Meer ya rabu da ita, sauran kama inbanda shiga tashin hankali babu abun da suke, ɗayar matar kam harda suma dan tsabar tsoron da take ji tunkan a zo kanta,

kan Dady suka koma shima shida, Sam da Bosaya da suka, taya shi, Bossay daman da biyu yake dukan sa, saboda haushin sa yake ji akan auren da aka so ayi masa Allah ya tsare sa,

Basu rabu da shi ba saida suka karya masa ƙafa ɗaya, ne makon Meer ya kira Khalid sai, Abuu yabasa number wani soja, yace azo a tafi da su, aje ai ta basu horo me tsanani wanda baza su mutu ba, daga ƙarshe kuma za a miƙa su koto, bayan anyi shari'a da su, za'a garƙame su a kurkuku,

Adaren saida aka gama komai domin ha har wasu dake cikin gidan su Ammah har su Meer ya haɗa aka tafi dasu wajen sojoji, dan yace baza ayi shari'a da su ba sai kowa ya gane Allah ɗaya ne sai an ladaftar da su,,

Kafin kuma atafi dasu saida akasa suka faɗi duk wata dukiya dake hannun su da kuma filaye ashe harda wani Company da yake shirin buɗewa duk suka haɗa suka handime, gidaje kam sunfi biyar ga filaye wajen shida ahaka ma duk sun siyar da wasu, bankin sa kam kuɗaɗen da suka ci baza su irgu ba, duk an kwace komai daga hannun su hatta gidan da kowannen su yake zaune nasa ne, duk wani ma abu da suka mallaka duk nasane basu da ko tsinke, wanda ya rage mallakin su, illa jikin su, shi kaɗai ne yazama mallakin su, shima kuma yanzu yana hannun sojoji sai yanda sukayi dashi dan kullum sai ya karɓi gashin duka,

Da farko Abban Ameesha dagewa yayi akan sai sunje can wajen Dadda wai kar suje kafin safiya aka shata ko kuma wuya ta kashe ta, kamar yanda tace, da ƙyar aka lallasheshi ya haƙura zuwa gobe, yace kuma tunda asuba zasu tafi aka ce masa anyarda, sannan aka samu lafiya, amma da a tubure musu,

Ko abinci aranra babu wanda yaci na dare ana tashi daga nan kowa makwancin sa yayi,

Ameesha kuma daman tana gurin Maama suna ɗaki tun tanayin kukan har ta lallaɓa ta tayi bacci, tunkan su gama abun ma,

shigowar Papa yasa ta fara tunanin ta yanda zata fitar da ita, sai kuma tayi tunanin ko ta kira Azeema tazo ta fita da ita, amma tuna yanayin da take ciki sai taji bai kamata a tashe ta ba kuma dole tana buƙatar me kulawa da ita koda ta farka cikin dare, sai ta rabuda ita kawai da niyar idan Meer ya shigo sai ta kirasa ya ɗauke ta,


Meer kam bai shigo ba sai wajen ƙarfe 11:pm yana shigowa kuma ya wuce ɗakin sa, bai zauna ba saida yayi wanka yayi sallah sannan ya zauna abakin gado ya ɗauko kayan zaƙin sa da yasaba sha,

Hankalin sa kwance yake shan su da yau jinsa yake sakayau kamar an kwashe masa wani abun daga kansa, da dede yake jin sa duk a cunkushe gaba ɗaya baya samun sukuni, amma yau shikaɗai yasan yanayin da yake ciki na farin ciki, yau finally yayi handling ɗin duk wani bincike daga yanzu babu shi babu tunani koda yaushe, ada kullum tunanin yanda zaiyi wannan yanda zai kama wancen waye da hannu aciki waye babu, komai dai yanzu yazo ƙarshe babu wani criminal da yarage masa,

Yanzu abu biyu suka rage masa kuma shima zuwa gobe zai gama daga ɗauko dadda sai yaje ya lalubo wancen tsohon da baisan dalilin sa na ɓuya ba ranar da yagan sa, kawai ya rabu dashi ne saboda muryar macen da yaji amma yasan yana gurin dan ya riga yaga jakar sa ta fata dake saƙale ajikin mashin ɗin sa, haushin matar ce yasa yakasa yi musu komai ya fito tafi, sannan yasa wanda zasu kula masa da gurin kuma anbashi daddaɗan labari cewar angansa, daman ya ayau yayi niyar zuwa amma sai wannan abun yafaru shiyasa baije ba, amma gobe zaije da zarar sundawo daga Gombe zai wuce can, da ya matsu yayi yayi komai ya gama, dan yana kammala su zai bar ƙasar dan bazai iya cigaba da zama ba ta isheshi badan faruwar waɗannan abubuwan bama da suka hanasa tafiya da tuni yatafi,

yana zaune yana ta shan abunsa yana ta tunane tunane abubuwan da suka faru wasu su bashi mamaki wasu kuma subashi haushi wasu kuma su bashi nishaɗi kamar ɓangaren wajen da suka sakawa su Waziri karara da zuma, suka sauya musu halitta yana jin nishaɗi in ya tuna hakan,

yajiyo bugun ƙofar sa yayi, amma bai amsa ba kuma bai tashi ba Saida yagama cinye abun hannun sa, sannan ya miƙe a hankali ya shiga takawa kamar baya so, zuwa yayi ya buɗe tare da ɗan leƙa kai sai sukayi ido huɗu da Maama, ƙarasa buɗe ƙofar yayi gaba ɗaya yana kallon ta, cike da wasa dan yanzu jinsa yake sakayau bayajin haushi baya damuwa da komai,

"Murmushi ta sakar masa, zatayi magana shikuma yayi saurin cewa meye kuma zaki biyo ni, ko kinzo ki takura min ɗin da kika saba, to koma inda kika fito, yafaɗa yana wani harar ta kamar mace harda taɓe baki da girgiza kai,

Tsaye tayi tana kallon sa da mamaki kamar bashi ne ɗazu yagama dukan baiwar Allah ba, amma yanzu kalle sa kamar babu wani abu da ya faru dashi yau duk wahalar da yasha, ita ji tayi yama bata tausayi akan yanda yake ɗawainiya da jajircewa akan duk abun da ya taɓa su, shi kaɗai yayi musu maganin duk wata matsalar su da damuwar su, amma taga shi ko ajikin sa hakan baya taɓa damun sa ko nuna gajiyawar sa, daga yayi yanan sai yayi can shine kullum akan hanya......,

"Hy, yafaɗa yana saka hannu sa asaitin fuskar ta, ɗagowa tayi cike da tausayin sa tana kallon sa,

"Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login