Showing 30001 words to 33000 words out of 170049 words

Chapter 11 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7238

wanda ya kula da saukowa warta tabi tajikin labule ta fice daga falon kafin ta fita kuma ta zare muƙullin falon tana fita ta rufe ƙofar tare da saka muƙullin ta ƙulle su ta waje,

Tana rufewa ta fashe da dariya harda tsugunnawa tana riƙe ciki tana tsalle, a fili tace "ashe yau da kallo bari inje inbaza idanu can wajen window ta zagaya ta yanda zatafi gani da kyau ta taka abu tana leƙen su babu abun da bata gani daga cikin falon, jira take kawai afara restring.......,

Rasheeda ce taje wajen Dady tace "Dady wai mai zai faru su rabu dashi mana idan ya dawo cikin hayyacin sa basai mubasa haƙuri ba mugaya masa abun dake faruwa, ai tsabar tashin hankali Dady baisan loƙacin da ya ture taba cikin ɗaga murya yace "ke baki da hankali baki san mai zai faruba, kubar falon nan, ku wuce ɗaki yafaɗa yana daka musu tsawa,

Kuka Rasheeda ta fashe dashi tana matsawa kusa da mom ta rungume ta cike da tsoron tsawar da Dadyn ta yayi mata,

Dady da ta kalli agogon yaga saura baifi 30 second ba time ya cika da kansa yasaka hannun suka fara jan Meer amma ko gezau baiyi ba,  a sukwane Dady ya ɗago kana ganin sa kasan ya shiga tashin hankalin da ya daɗe bai shiga irin saba,

Wata tsawar yadakawa su Rasheeda da suna gurin har yanzu sunƙi barin wajen, murya sa kamar zaiyi kuka yace wai baza kubar wajen ba ba magana nake muku ba to sai ku ta tsayiwa idan ya kashe ku kun huta yana kaiwa nan ya nufi ƙofar fita cikin sarsarfa zai bar falon,  saidai yana zuwa wajen ƙofar yajata zai fita yaji ta a datse......, A matuƙar razane ya juyo yana kallon su ganin Meer ya ƙwace riƙon da mutanen nan sukayi masa, ya miƙe tsaye yana kallon su da jajayen idanun sa masu kama da rurran garwashin wuta...✍️✍️✍️✍️
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

      Da sauri  ya ƙara juyawa ya murɗa hannun ƙofar sai yajita dai still a rufe, ai kafin yayi wani yunƙuri yaji anriƙo rigar sa ta baya tara da shaƙe mai waya akayo baya dashi aka jefasa ƙasa,

Cikin zazzaro idanu Dady yake bin Meer dake tsaye agaban sa yana wani irin fidda numfashi mai huci, ga idanun sa da sukayi wani irin ja kamar gauta, hannu yasa yaƙara ɗago sa yakai masa wani kyakkyawan mari a fuskar sa Dady bai gama tantance zafin ba ya kuma jin wani ta ɗayan ɓarin, ba tsaya ba saida yayi masa marika sunfi  goma ajere sannan yayi ball dashi ya turasa gefen kujera ta yanda yasan zai bugu yakwa bugun ba ƙarya amma zafin buguwar ba hanasa ƙara ɗagowa ba cikin hanzari  ya kalle sa yaga Meer ya ya juya baya yana koma kan sauran,

Ganin hakan yasa Da baya da baga Dady yafara ja yana maida duban sa ga su Rasheeda, da suke shirin hawa bene dan tsiratar da lafiyar su ga Meer tun kan ya waiwayesu,

Ƙara juyawa yayi ya kalli Meer da ya koma kan mutane biyun nan da suka kawo sa, ya caƙumi wuyan ɗaya wanda shine ya wanda yafara ganin sa acikin motar sa wanda yayi masa allura, dukan sa yake ta ko ina, saida ya tabbatar bazai iya motsawa ba sannan ya koma kan ɗayan shima ya lugude sa, ya ajiyesu gefe guda,

Dady da jikinsa gaba ɗaya yagama ɗaukan rawa sai kerma yake ganin yagama dasu, yasan kansa zai dawo hakan yasa shi tashi da sauri ya kwasa aguje yayi sama benen,

Meer na kallon sa sarai yaga guduwar sa, yabarshine yagama gudun nasa zai shigo hannun ne,

Kujera yasamu, ya zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana kallon su da hannun yayi musu alamun dasu matso inda yake da jan ɗuwawu suka ƙaraso gurin dan basu da ƙarfin tashi da kansu,

Sauke ƙafar sa yayi yana duban su da kyau Saida yagama ƙare musu kallo Muryar sa cike da ɗan dashewa bata fita sosai   yace "abu biyu zuwa uku nakeson ji daga gareku idan kuna so kucigaba da rayuwa, kunajina?

Kai suka ɗaga masa,

Sannan ya ɗora dacewa "ina son insan ta inda kuka shiga cikin gidan har kashigar min mota batare da sanina ba, waya baka damar shiga cikin gidan ma gaba ɗaya da iznin wa ka shiga, ya faɗa yana kallon wanda ya shigar masa mota dan bai manta fuskar saba,

zazzare ido yashiga yi yana shirin yayi ƙarya amma tunawa da irin bugun da suka sha yasan idan yayi ƙarya jikin sane zai zai kuma gaya masa, dan haka sai yace, "da iznin mai gadin gidan na shiga ciki shima kuma akwai wacce tagaya masa shiga ta ciki, nidai Alhaji yace kawai inje bakin gurin akwai wacce zata kirani tana kirana komai yazama ready shiga kawai zanyi kuma haka mukayi ina zuwa bandaɗe ba aka turo min message akace inshigo na shiga bayan nashiga sai wata mace ta kirani tagaya min inda motar taka take naje na tsaya agun sai tace na buɗe nashiga a buɗe take yanzu zaka fito ka fita, idan ka shiga muka fito daga gidan sai incaka maka allurar, amma nidai banga matar ba bansan taba kuma Alhaji ne ya haɗa mu da ita.....,

Shiru yayi yana sunkuyar da kansa ƙasa,

Jinjina kai Meer yayi "sai ya maida dubansa ga ɗayan yace "kai kuma fa,

Da sauri ya shiga girgiza kai yace wallahi babu abun da nasani akanka...,

"Sai akan wa kasani??? Meer yaƙara tambayar sa,

Shiru yayi bai basa amsa ba,  Saida Meer yaƙara maimai ta masa sannan yace "ba kowa,

Tashi tsaye Meer yayi ya nufi ƙofar fita Saida yake daf da fita har suna tunanin ya rabu dasu kenan saikwai sukaji yace "kubiyo ni sannan ya fita,

Kallon juna suka shigayi amma rashin sanin abun da zai musu ba yanda suka iya dole suka yunƙura da ƙyar suka bi bayan sa,

Suna fita suka gansa aawajen motar sa, buɗewa yayi ya shiga tsayawa sukayi akusa da motar, da hannun yayi musu alamun su buɗe baya su shiga babu yanda suka iya cike da tsoro da fargaba suka buɗe suka shiga cike da ɗarɗar suna tunanin ina kuma zai kaisu, suna shiga ya tayar da motar yajata suka fita daga gidan.......,

Loƙacin da Dady ya haura sama  yana zuwa yafaɗa dakin dasu Rasheeda suke suma duk a tsorace suka buɗe masa ƙofa yana shiga suka rufe ƙofar kowannen su cike da tsoro Rasheeda kam sai kuka take tana cewa Dady ka kira ƴan sanda wallahi idan ba a fita dashi ba sai ya kashe mu gaba ɗayan mu,

  Mom ma ta ɗora da cewa naga alamar yaron nan baida hankali fa, yakamata kayi wani abun yanzu dai munsamu mun tsira ba tayanda zaiyi ya shigo nan amma dai kasan yanda zakayi damu dan nasan ba barin gidan nan zaiyi ba, tana gama faɗar haka Rasheeda ta ɗora dacewa...

"Dady wai allurar mai kasa akayi mishi gashi nan yakoma kamar mahaukaci Dady ka cuceni maiyasa zaka saka ayi masa alluarar da zata cutar dashi yanzu ga abun da ka jawo mana nan duk da nasan halin sa amma da bakayi masa haka ba da ba abun da zaisa ya koma haka gaba ɗaya ya canza kamanni ya koma kamar wani dod......,

Tsawa Dady yadaka mata yace "ya isheki haka dame kikeso inji da kukan ki ko da maganganun ki ko kuma da halin da muke ciki, idan zaki iya fita ki ɗauko wayar tana can falo kije ki ɗauko idan kuma ba haka ba kada wanda ya ƙara min magana anan, ya faɗa cikin ɓacin rai da borin kunyar abun dake faruwa dashi agaban ƴarsa ga kumatunsa duk shatin hannun Meer ga gefen bakin sa har ya ɗan kunbura saboda bugewar da yayi da jikin kujerar,

Mom da taga abun ba mai ƙarewa bane bata bi takansu ba, ta ɗauki wayar ta da sauri ta lalubo wata number ta danna mata kira ana ɗagawa tace "mustapha kana ina ne, banji mai akace mata daga can ba, tace to kabar ko mai kake kazo gida ba lafiya, kataho da ƴan sanda, akwai matsala, da sauri Dady ta ƙwace wayar daga hannun ta yace ke mahaukaciyar inace zaki kira mana ƴan sanda cikin gidan nan, angaya miki shiɗin ƙaramin mutum ne idan aka tambayi dalilin zuwan sa nan ɗin kina da hujjar da zaki kare mune kina abun faɗa musu, wannan shashan cine, yana gama faɗa mata haka yakara wayar a kunnen sa yace kar kasake ka kira wasu ƴan sanda, kajini koh! yafaɗa tare da kase wayar,

Ya wurga mata ita ajiki, yana dafe kansa yana furzar da iska ta bakin sa, yana tunanin ta yanda zai sama musu mafita wannan yaron yabar gidan batare da ga taɓa lafiyar su ba, duk da yana tunanin mai yake faruwa a falo har yanzu bai biyo suba, Allah yasadai ya fita tunanin hakan yasakashi zuwa wajen window yaga ko ba motar sa da suka shigo da  bata nan, amma yana keƙawa sai yaga wayam babu motar, wani irin sanyi yaji aransa, cike da farin ciki ya juyo yana kallon su yace "Alahamdulillah ya tafi wallahi ya tafi amma Allah ya taimake mu daman nasan tunda muka rufe ƙofar nan bazai iya shigowa ba sai hankalin ku ta kwanta ya tafi, yana faɗa musu yana buɗe ƙofar ɗakin fita yayi dan ya tabbatar wa da kansa, tagani da idon sa, lallaɓawa yayi ya fara leƙawa yaga basa ciki har sauran mutane, amma duk da haka bai yarda ba saida ya fito har waje daga nesa ya tambayi mai gadi shin mai ya buɗewa musu ƙofa ne sun fita yace masa eh yanzu suka fita, sosai yaƙara jin daɗi aransa sannan ya koma cikin gidan......,

      ***************************           

Loƙacin da aka fito da su Ameesha tafiya kawai suke basu san inda suka dosa ba, dan tun suna hira har suka dawo yin shiru suka fara gajiya da hirar dan a ƙalla sunkai kusan awa ɗaya suna tafiya, Amra sarki surutu itace tacewa drivern wai ina zai kaisu shiru yayi mata baice mata komai ba dan Meer yana sa yace masa komai zasu tambaye sa kar yace komai kawai yaci gaba da tafiya har sai yace masa ya dawo gida sannan zai juyo ya dawo gida daman ba saƙon da zasu karɓo kawai yayi tarkone da fitar tasu shiyasa ya aikasu kuma gashi anzo an ɓata masa komai,

Bayan Meer ya fita daga gidan wayar sa ya ɗauka da yaganta inda ya barta basu ɗauki komai ba, daddingin number tasu yafara bi yana ganin inda location yake nuna masa, gudu kawai yake kamar zai tashi sama dan yana tunanin ma wataƙil wani abun ya samesu ga, ga inda alamar take nuna masa kafin yaje gurin wajen tazarar kilo mita hamsin ce kafin ya tadda inda suke,

Ƙure gudun sa yayi har ƙarshe Allah ma yasoshi babu mutane da yawa akan titi dan haka yasamu damar gudu yanda yake so yana ganin mota tundaga nesa zai fara danna horn abasa guri yana zuwa ya wuce,

Sudai suna baya suna addu'ar kalmar shahada dan sun riga sun saddaƙar da kashe su yake shirin yi kawai dan wannan gudun ya wuce na hankali.......,

Aɓangaren Meer kam yana sane ya taho dasu dan zaiyi amfanine dasu wajen binciken sa na gaba shiyasa ya taho dasu, dan ya riga a buga alamar tambaya akan Dady saboda yana zargin wani abu akansa saboda haka ne ma ya rabu dasu bai mishi komai zai dawo wajen sa daga baya,

Batare da ya kalle su ba kuma bai daina gudun da yake ba yace dasu zamu je wani guri daku duk abun da kuka ga ya dace kuyi zamuyi magana daku zuwa gobe idan kun ban haɗin kai zaku tsira idan kuma kuka bijire min kunsan sauran,

Da sauri har suna haɗa baki wajen cewa "in Allah ya yarda komai kace muyi maka zamuyi indai zaka barmu da ranmu koma wani kake so mukashe maka wallahi zamuyi,

Banza yayi dasu saidai ya girgiza kai kawai yaci gaba da tafiya aransa yana jin daɗi yasan daman bazai sha wahala dasu a shiyasa yake son haɗa kai dasu...........,


   *Su Ameesha*
______Suna cikin tafiya wata motar tazo tasha gaban su, gaba ɗayan su a tsorace suke kallon motar har driver ɗin saida ya tsorata saboda shikansa baisan da zuwan motar ba,

Suna cikin haka nacikin motar suka buɗe suka fito, wajen tasu suka matso cikin tsawa sukace duk su firfito daga cikin motar har driver ɗin suka fito,

Ameesha ta rirriƙe Azeema cike da tsoro ƙwalla har tafara cika mata ido, tace "kinga abun da nake gaya miki ko wallahi sune Saida nace masa kar mu tafi mu kaɗai amma yaƙi ji, Cikin ƙasa ƙasa da murya Azeema tace ke wai meye haka baza ki nutsu ba,  

Amra da Hamra suma suna riƙe da hannun su duk sun tsatstsaya suna kallon mutanen da suka ce su fito,
gadan gadan mutanen sukayo kansu kamar zasu dake su sai kawai sukayi kan Ameesha ɗaya daga cikin sune ya damƙo hannun sa a hannu ta sannan ya juya ya kalli sauran yace "wannan ce ko?

Ɗaya ya kaɗa masa kai na gefansu kuma yace ai su biyu ne ita da wannan ce, wanda ta riƙe mata hannun yace banda ita ɗaya akace,

Kuka Ameesha tafara yi tana jan hannun Azeema, da su Amra, shi kuma mutumin yafara janta kuka take tana cewa ku taimakamin kar kubari su tafi dani,

ganin haka yasa drivern yayi kansa da niyar ƙwatar ta amma sai sauran suka riƙeshi gam, suma su Hamra cikin kukan suka fara haɗa mutanen nan da Allah su saketa har tsugunnawa sukayi suna roƙon su amma basu kyale taba suka ci gaba da janta, mutumin yana daf da shigar da ita yaji saukar dutse abayan ƙeyarsa, da sauri yasake ta yana dafe gun da yaji zafi sosai har ma jini yafara fita,

Da gudu Azeema ta ƙara zuwa ta wawuro wani ƙaton dutsin da ta ɗaga sa da ƙyar tayi kan sauran zata jefa musu da sauri suka fara ja da baya gudun kar ta sami wani acikin su,

Ameesha ta samu damar barin wajen da gudu ta koma gurin su Amra amma sai wani yaƙara riƙeta zai fara janta,

Kamar mahaukaciya haka ta koma taƙara nufarsu tana zazzare ido tace "wallahi duk wanda yaƙara taɓa ɗaya sai na fasa masa kai,

ba shiri duk suka fara ja da baya ai da gudu Amra ta ƙara zuwa ta ɗauko wasu dutsina da yawa a hannun ta, tafara jifansu dashi, duk baya mota suka fara ɓuya, dan su Hamra ma duk ɗaukan duwatsun sukayi suka fara jifan su dashi,

Ganin sun korasu driver ɗin yayi saurin shiga motar yace suyi sauri su shigo su gudu,

Da sauri Azeema tafara tura Ameesha ciki sannan ta tura su Hamra sannan itama ta shiga,

Driver yana shirin tayar da motar kenan yasaka hannun sa gurin muƙullin motar sai yaji babu muƙƙuli ajiki da sauri ya juya yafara dudduba shi aƙasa ko ya faɗa amma bai gansa ba,

Amra tace wai me kake jira dan Allah mutafi gasu nan fa sun fara tahowa wajen mu Ameesha ma ta ɗora da cewa muje mutafi, gaba ɗayan su suka fara ɗaga masa hankali kowanne da abun da yake cewa, shi har ya rikice ma ya rasa ta inda zai fara neman muƙƙulin ga surutun su da yagama burkitashi, idan ya ɗaga kai yaga mutanen sun kusa zuwa wajen su, sai yaƙara shiga tashin hankali,

Cike da tashin hankali ya juyo ya kalle su murya na rawa yace "dan Allah kuyi haƙuri narasa muƙullin motar ko da wanda yagan sa acikin ku,

Gaba ɗayansu suka ƙara tsorata jin muƙulli wai ya ɓata, basu ankara ba suka ji bugun ƙofar su, ta ɓarin da Ameesha take aka buɗe motar, ana buɗewa suka jata suka fitar da ita daga ciki, suna cire ta kuma suka rufe ƙofar gaba ɗayan su suka zagaye motar suka hana sauran fitowa gudan kar suƙara yi musu abun da sukayi musu ɗazu,

Kuka su Hamra suka fara yi suna ƙoƙarin fitowa dan su ƙwace ta amma duk sun daddanne murfin motar sun hanasu fitowa,

Saida suka ga yakaita wajen motar ya buɗe bayan motar yasaka ta, sannan ya dawo wajen su yace ku buɗe musu mu rama abun da sukayi mana dukkannin su sai sun gane kuren su musamman wannan tsinanniyar yarinyar wanda aka fasawa ƙeyane yake wannan maganar,

Buɗesu sukayi zasu fito dasu kokawa suka fara yi dasu, su Azeema suka tubure suka ƙi yarda suyi musu komai kuma suka ƙi fitowa saboda duka suka ringa kai musu suna cizon su suna mintsinin su, sukuma suna famar fito dasu daga ciki amma ba dama,

Suna cikin kokawar sukaji zuwan mota wajen akusan tare suka ɗago suna bin inda motar take da kallo,

a tsakiyar motar su da ta su Ameesha, ya tsayar da motar ko kashe ta baiyi ba ya buɗe murfin motar, yana fitowa suma na bayan suka fito a sukwane sukayi kan mutanen, shirin guduwa suka fara yi, amma babu inda sukaje su Meer sukayi ram dasu gaba ɗayan su da taimakon mutum biyun nan, suna kamasu Meer ya basu umarnin subuɗe motar sa su saka su aciki Saida suka yi musu duka sannan akasa su abayan motar shi ya shiga motar ɗayan gefen kuma yace ɗaya ya shigo su tafi ɗayan kuma ya shiga ta su Ameesha da itama tun ɗazu aka fito da ita, mota dai biyu sukayi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login