Showing 78001 words to 81000 words out of 170049 words

Chapter 27 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7239

nake son gani ka kawo min su, ko kagaya min ina zan gansu, ina Babuu na ko ya mutu,

Ƙara riƙeta yayi sosai tare da jawo ta ya rungume ta yana bubbuga bayan ta yace "zasu zo namiki alƙawari nan bada jimawa ba, Babuun ki zai dawo bai mutu ba yana nan,

kai ta shiga girgiza masa tana ture sa ta miƙe tsaye ta cire ɗan kwalin jikin ta, nan tafara sanbatu tana maganganu daga ƙarshema ta nemi guduwa daga cikin dajin, yayi saurin riƙeta da ƙyar ya iya kamata daman sun saba wasu luƙotan da haka yajata ya shigar da ita cikin bukkar yasamu igiyar da yake ɗaure ta idan hakan tafaru dan fisge fisge take tana sunbatu ita sai ta tafi,

Yanzu ma da ƙyar ya ɗaure ta, sannan kamar yanda yasaba yafara kwantar mata da hankali yana jawo mata hankali sannan yasamu ta fara sassauta abun nata......,

         **************************

                 *MASARAUTA*

      AFTER 1 WEEK
                 (bayan sati ɗaya)

       
          "A ɓangaren Azeema kuma acikin sati ɗayan nan sun ɗinke da Shettima ya shawo kanta har tafara mantawa da Hamza dan ko kiran ta yayi bata fiya ɗagawa ba sai taga dama,  su kam soyayya su kawai suke shiyasa ma ta manta da dawowa wajen Ameesha tana can tana soyayya......,

____A ɓangaren su Sam suma komai yana tafiyar musu daidai sun miƙa lamarin su ga Allah sun manta da duk wani abun da yafaru sun, sumayya kuma kwanan ta biyu momma da kanta tace suje gidan su sumayyan tare, tare kuwa suka tafi inda sukaje can gidan sukayi sa'a kuwa baban ta yana nan,  da sukaje akayi masa duk bayanin duk wani abun da yafaru tundaga farko har ƙarshe, inda mahaifin ta yake sanar dasu cewar ai tunda ya dawo yaji labarin barin ta gidan yaji haushi sosai dalilin hakan ma ya sake ta yanzu haka tana gidan su,

Bayan yagama basu labarin yayi musu godiya, daga nan su momma sukayi musu sallama suka tafi suka bar sumy a gidan, amma awajen Sam da ita kanta Sumayyar ba haka suka so ba saboda sun saba kullum suna kusa da juna amma yanzu zasuyi nesa, badan suna so ba haka suka rabu ko sallamar arziƙi babu saboda akwai idon momma da kuma mahaifin ta, dan haka ko ƙofar gida bata rako saba,

Amma ko kwana ba ayi ba ya dawo wajen ta daddare saboda missing ɗin ta da yafara yi tun ba aje ko'ina ba, tun daga nan kuma kullum sai yaje gidan su ahakan  ma haƙuri kawai suke.....,



______*Meer*

'Tun ranar da abun nan ya faru tsakanin Ameesha da Meer, Meer bai sake bari ko hanya ma basa haɗawa itama kuma haka ne awajen ta tun abun na damun tama  har ta manta saboda bama da wanda zasuyi maganar ga Azeema har yanzu taƙi dawowa bare suyi, shiyasa tayi saurin mantawa da abun, duk wani abun sama bata san yanai ba,

Abun kuma da ya fi bawa Meer mamaki shine har zuwa yau Abuu bai yi masa maganar ba, baice komai ba duk da yaga ransa ya ɓaci a ranar, amma baiji maganar ba kwata kwata, koda suka haɗu ma bai nuna masa da wani abun ba, shiyasa abun yake ɗaure masa kai....,

  "Yau sati ɗaya da maganar Papa akan cewar za' ɗora Abuu akan kujerar mulki,

To yau sati ya zagayo cikin masarautar cike take da mutane kowa ya hallaci wannan sabon naɗin da za'ayi sa yau ranar juma'a'tu babbar rana duk wani abu da ake shirya babu inda baikai labari kowa yasan labarin masarautar da kuma abun da yafaru tunda ga farko har ƙarshe har zuwa yau da za a naɗa sabon sarki kowa kaganni acikin masarautar yana farin ciki sabon naɗin nan da za'ayi,

Tunda safe ake ta karɓar baki gaba ɗaya kowa ga shiga busy, ga dokuna da ake ta shiryawa suma anayi musu ado, ana jere su, bayan sallar juma'a za ayi naɗin,

Duk wannan abun da ake Meer yana ɗakin sa da yaji ma surutun mutane musamman yaran gidan su Amra da wasu ma daga cikin gidan ga Azeema ma ta dawo saboda na ɗin da za'ayi sumy ma ba abarta abaya ba saboda daman da mahaifinta ma suka taho shima yazo ya taya ɗan uwansa murna, koda yagayawa maman sa cewar umaruru yana nan ga kuma asalin sa, ƙaryatashi tayi taƙi yarda dashi, da yace tazo suzo tare da har zatazo kuma sai zazzaɓi ya rufe ta, ta fasa zuwa,

Su Shettima ma ba barsu abaya ba shida hajiyar sa, ga su Bossay suma duk sunzo a taƙaice dai duk wani na kusa da su ƴan uwa da abokan arziƙi duk sunzo,

  _Wajajen ƙarfe sha biyu da wani abun na rana, Khalid ya shirya tsaf shima zai tafi gidan da niyar idan yaje sai su wuce masallaci da Meer saboda daman masallacin juma'ar akusa da gidan yake ta baya ajikin masarautar yake,idan sun dawo sai ya zauna acan ayi naɗin agabansu,

Yana fitowa daga ɗakin sa suka ya haɗu da Dady shima ya fito da shirin fita, har ƙasa ya tsugunna yace "uncle ina wuni,

"Lafiya ƙalau Khalid jiya ina ta neman ka ina kashiga,  cewar Dady,

Khalid yace "wallahi uncle na ɗanje wani aiki ne ban dawo da wuri ba, Allah yasadai lafiya kake nemana,

"Eh lafiya ƙalau daman akan maganar Musbahu ne yakamata yaron nan ya dawo gida ina ma kaje can inda yake ka gano min abun da aka turasa yake ko kuma dan yanzu ko awaya ma bana samun sa sai anci sa'a wataran ma tana ringing baya ɗagawa kuma bazai biyo bayan kiran ba, shiyasa nake so kaje kasa masa ido karka bari yasan kana garin,

"Tom Dady in sha Allah zanje gobe amma kuma idan na kirasa wataran ina samun sa, amma dai koma maiye zanje ingano ɗin,

"To shikenan bari inje ina sauri duk dai yanda ake ciki saika sanar dani,

"In sha Allah Dady sai ka dawo, a dawo lafiya,

"Allah yasa, Dady ya amsa masa tare da yin gaba,

Khalid na miƙewa ya bi bayan sa shima , yana zuwa falo zai fita Rasheeda ta fito da gudu tana cewa "yaya! Yaya! wai tafiya zakayi ka barni da alama kama manta dani,

Juyowa yayi yana dariya yace "wallahi kuwa na manta dake amma yanzu ai kin tuna min idan kingama muje dan sauri nake wallahi kar na makara sallah,

"Lalle ma yaya au baƙin ciki kake min zanga sarki shine zaka tafi kabarni to ni nagama babu abun da zanyi muje,

Kallon ta yayi yaga kalar rigar da tasa duk ta fito mata da surar jikin ta kayan sun kamata da yawa,

"Ina zani dake da wannan shigar watakon duk faɗan da nake miki baki daina sakawa ba, to sai kizaɓi ɗaya, ko kike ki canza su kisa kayan arziƙi ko kuma kije kisaka hijabi in bahaka ba kuma sai kiyi zaman ki inyi tafiya ta,

Ɓata rai tayi kamar zatayi kuka ta buɗi baki zatayi magana, yayi saurin dakatar da ita shima cikin haɗe ran yace "nagama magana idan kiyi abun da nace ki fito ki sameni a mota idan kuma kika ɓatan loƙaci inyi tafiya ta, yana gama gaya mata haka yayi gaba,

Tasan halin sa sarai shiyasa kawai ta juya da sauri gudun kar ya tafi ɗin,
Tana shiga ɗaki ta cire rigar jikin ta, sai kuma ta rasa waɗanda zata saka dan itadai bazata iya saka hijabi ba ta fita dashi tazama wata lokal acikin mutane,

Kayan ta zubo dasu gaba ɗaya can ta hango wata doguwar rigar material da tasan bata kamata ba sosai saboda yanayin ɗinki yana da ɗan faɗi ta ƙasa saboda adon da akayi masa, saman ma kuma bai wani matseta ba tana gama sakawa ko ɗan kwalin bata nema ba tasamu mayafin da zai shiga ta yafasa ta ɗauki jakar da ta ajiye saboda ta shiga da material ɗin kuma daman koman ta suna ciki bata sa loƙacin canza wata, takalmi ma kawai surarshi tayi batama sani ba ya shiga ko bai shiga ba,

Tana ɗauka tayi waje aguje saboda gudun kar ya tafi,

Tana fita yana tayar da motar dan daman minti goma yabata idan bata fito ba zai tafi saigashi time ɗin na cika tana fitowa,

Ƙaraswa tayi wajen motar ta buɗe gaba ta shiga tana sauke numfashi saboda saurin da tayi bata saba ba duk sai taji ta gaji,

Kallon ta yayi ya saki murmushi sannan yaja motar yana cewa "ko kefa amma da kawai sai inkama tafiya dake kina takawa da ƙyar saikace daga can na ɗauko ki,

Banza tayi masa ita adole fushi tayi dashi, har suka fita daga gidan suka hau kan titi bata kula saba, saida yabata haƙuri sannan ta sauko suka fara hira, suna ta hira yana tuƙin sa har suka ƙarasa, tundaga waje yaga mutane duk sun cika ƙofar gidan saboda sallar juma'a da ake shirin yi ana tayin huɗuba, abunne ya haɗu biyu ga mutanen da zasuyi sallah a masallaci ga kuma mutanen da suka zazzo,

a waje Khalid ya tsaya tare da zaro wayar sa ya lalubo number Meer tare da danna masa kira yana ɗagawa yace yana waje ne ko yana ciki yace masa yana ciki ya shigo,

Bayan ya kashe wayar yaja motar yabi ta gefen mutane ya danna kai cikin masarautar can wajen part ɗin ya nufa da motar yayi parki sannan suka fito Rasheeda tayi saurin dawowa kusa dashi tana ta faman bin gidan da kallo ko ina baza ido take,

Jan hannun ta yayi suka nufi falon Saida aka bashi izni sannan ya shiga cikin falon, su Ameesha duk suna falon suna ta hira, shigar su yasa suka dakata suka amsa musu sallamar tasu,

Idon Rasheeda akan Ameesha yafara sauka itama ita take kallo, cike da mamaki Rasheeda ta zaro ido bata san loƙacin da tace Ameesha!!

Karo na farko kenan da ta fara kiranta da sunan ta, da saidai tace "ke ko ƴar talaka dade duk sunan da yazo bakinta na rashin dacewa,

Itama Ameeshan miƙewa tayi iya kuma cike da murna tace Aunty Rasheeda kece agidan namu, ta taho da gudu kawai sai ta rungume,

Itakam Rasheeda ƙamewa tayi agun dan hankalin tama gaba ɗaya neman barin jikin ta yake, daɗin daɗawar ma jin kalamar yau kece agidan namu, mai hakan yake nufi kenan tazo gidan sarki amma taji tana cewa gidan su,

tana wannan tunanin, Ameesha ta katse mata da cewa "wallahi naji daɗin ganin ki daman wannan ɗan uwanku ne, ai ina ganin sa agidan nan amma bansan shi bane, ko dai shine yaya Khalid ɗin da nake jin ana magana a gida,ni daman ban taɓa ganin saba,

Kamar sokuwa haka Rasheeda ta ɗaga mata kai dan bata bakin yin wata magana,

Khalid ne yayi murmushin jin daɗin sun san juna, sai yace "Nine dai kin zauna agidan mu ne,

"Eh na zauna mana nama daɗe kawai dai bamu taɓa haɗuwa ba sai kazo ka koma amma bama haɗuwa,

"Ayya Allah sarki to shikenan bari inshiga gata nan to sai ku zauna bari inje yana ciki koh?

"Eh yana ciki Aunty Rasheeda mu ƙarasa besty wai baki ga Aunty Rasheeda bane, tana yiwa Azeema maganar tana jan Rasheeda suka ƙarasa kan kujera suka zauna,

"Ina wuni?

Azeema tacewa Rasheeda nan madai da ƙyar ta amsa sauran ma duk suka shiga gaida iya saboda sun ga ta girme su,

Jikin ta ƙaura yai la'asar Rasheeda tayi jigum takasa magana duk surutun ta da rashin mutumcin ta amma yau sai taji komai ya tsaya mata ji tayi ma kamar tace masa yazo su tafi,

Ameesha duk ta gama fahimtar ta tana sane duk take ta janta ajiki kuma tana nuna mata kamar babu wani abu na rashin daɗi da ya taɓa faruwa a tsakaninsu.....,

Ai Rasheeda bata gama shiga tashin hankali ba saida Khalid da Meer suka fito Meer na sanye da wani yadi mai shaigen laushi da sheƙi da ɗaukar ido, yayi kyau iya kyau saboda bai saba saka manya kaya ba, yanzun ma har ya saka wasu Khalid yasa shi gaba da Allah Annabi sannan yasaka,

Duk surutun da su Ameesha sukeyi ai suna ganin fitowar su kowa ya haɗiye maganar sa, suka saki baki suna kallon Meer duk wanda ya kalle sa bazai so ya ɗauke idon saba akansa,

Rasheeda bata san loƙacin da ta miƙe tsaye ba tare da cewa "what!! ta faɗa da ƙarfi hakan yajawo hankalin su Meer da suke daf da fita suka juyo akusan tare saboda yanda gurin yayi shiru tsit, sai yazamana tana yin wannan maganar duk Saida ta cika falon, sauran ma duk ɗaga ido sukayi suna kallon ta,

Meer ba ƙaramin mamakin ganin ta yayi ba dan bai manta fuskar taba, ranshi yaji yafara ɓaci, kawai wata zuciyar ce take zugasa yaje ya shaƙeta yaji uban da ya kawo ta, saboda tuna maganganun su, na cewar zasu sa taje inda yake zasuyi asiri, tuna hakan yasa kawai yaji abun da ya kawota kenan,

Yana niyar ɗaga ƙafar sa kenan zuwa wajen ta, sai kawai wani abun mamakin da ya kusan fin na farko ya dakatar dashi da niyar zuwan da yake,

Khalid yaje wajen ta yana binta da kallon tuhuma yace "Rasheeda lafiyar ki ƙalau kuwa mai yafaru kikayi irin wannan maganar haka,

Sai yanzu ta tuna katoɓarar da tayi loƙaci guda kuma sai ta rikice duk ta duburbuce ta rasa amsar da zata basa,

Ameesha ce tayi caraf tace "bafa wani abu bane kuyi tafiyar ku kawai wannan abun tsakanin mune wata magana nagaya mata da tasa ta yin hakan kuma sirrice bazai yiyi kaji ba, kayi haƙuri kutafi,

Maida dubanta tayi ga Rasheeda ta kamo hannun ta, tace "haba aunty Rasheeda sai kace ba babba ba daga wannan ƴar maganar sai ta firgita ki zauna dan Allah muƙarasa, tayi maganar tana dariya kamar gaske wani abun ta faɗa matan,

Wata uwar ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Rasheeda ta sauke tana jin daɗin wannan taimakon da Ameesha tayi mata dan wallahi da ta barta bata san abun da zatace ba, da saidai tayi abun da za akore ta daga gidan, dan a ganin ta tunda ta shigo ba fita saboda a ɗan ƙanƙanan loƙaci ta gano Meer ɗan gidanne saboda hoton da Dady ya taɓa nuna mata, dan haka tasan burin ta na daf da cika tunda ta shigo gidan, dan haka zata sauke komai ta ajiye gefe ta nunawa Ameesha ba komai ta jawota ajiki saboda tasan sauran abubuwan da bata sani ba, sannan tasan labarin Meer ta yanda zata shiga jikin sa, duk a ƴan mituna tagama waɗannan tunanin,


Saurin kawar da damuwar dake fuskar ta tayi, ta azo murmushin yaƙe ta aza a fuskar tace "yaya mai kuwa ya faru babu komai fa,

Shima sai yanzu yaji ɗan dama dama hankalin sa ya kwanta jin duk abun da Ameesha ta faɗa,

Dan haka sai yace "amma kin ban tsoro wallahi kawai ki kama yiwa mutane magana da ƙarfi harda su miƙewa tsaye,

"We are sorry yayan mu, cewar Ameesha,

Murmushi yayi kawai ya juya yana girgiza kai, dan tun kallon farko da ya shigo yaji yarinyar tayi masa ta matuƙar burge sa, sai da yaje kusa da sannan yace mata "kinfi ye surutu ko kece bakin ta kenan,

Ƴar ƙaramar dariya tayi sannan itama tace "eh ai yaya tace shiyasa nake kareta,

Batare da ya juyo ba yace "Allah ko? To bari inje indawo zakiyi bayani yarinya,

Bata bashi amsa ba suka ƙarasa fice daga falon saboda sunji ana shirin fara tayar da Sallah,


Kamar yanda Rasheeda ta shiryawa zuciyar ta takun da zatayi, tun yanzu tafara zuciyar cike take da tambayoyi amma ba yanda zatayi doke ta adana tambayoyin ta, ta fuskanci gaba, daga nan ta saki jiki da su kamar ba ita ba suka fara hira,

Suna zaune agun Maama da kai ya ɗau caji ana busy ta shigo cikin falon, tana yi musu magana tace duk su tashi suje suyi sallah azo aci abinci kafin a tafi ganin hawa,

Da murnar su duk suka tashi suka ƙara ɗunguma cikin ɗakin su.....,



Ƙarfe 1:30 daidai aka isar da sallar juma'a a masallacin kusa da masarautar, ana gama idar da sallah mutane na shirin miƙewa su tafi akayi saurin dakatar dasu, haka kowa ya tsaya dan jin abun da za ace musu,

nidai ina daga waje ban shiga cikin masallacin ba saiji nayi kawai ance Masha Allah, kowa ya shaida anɗaura auren yau ranar juma'a an ɗaura auren SAMEER SAMEER SAMEER tare da matarsa KHADIJAH SAMEER SAMEER akan sadaki dubu ɗari biyar lakadan ba ajalan ba...✍️✍️
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

  
                        *_🅿️29_*

   
     'nidai ina daga waje ban shiga cikin masallacin ba saiji nayi kawai ance Masha Allah, kowa ya shaida anɗaura auren yau ranar juma'a an ɗaura auren SAMEER SAMEER SAMEER tare da matarsa KHADIJAH SAMEER SAMEER akan sadaki dubu ɗari biyar lakadan ba ajalan ba...✍️✍️

___Duk girman masallacin nan da ɗumbun mutanen dake ciki, amma Saida wannan sanarwar ta isa kunnen kowa ana faɗa kuma gurin ya ɗauki wani irin shiru ɗif kake ji saboda abun yazo ba zato ba tsammani babu wanda yasan za ayi wani ɗaurin aure,

Fitowar Meer da Khalid kenan daga cikin masallacin dan ko da akece a tsaya za ayi sanarwa yace bazai jiraba ya miƙe shima Khalid yabiyo bayan sa dan so yake yaje gurin Ameesha,

Saidai suna daf da shiga kunauwan su sukayi musu mugun ji, duk da Khalid baisan wacce aka daura auren da itaba amma jin sunan abokin sa yasa shi saurin juyowa a zabure yana kallon Meer da shima ƙamewar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login