Showing 21001 words to 24000 words out of 170049 words

Chapter 8 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7205

mana ta yanda koda anga videon ba wanda zai yarda,

Miƙewa yayi yana kallon ta ido cikin ido yace kinga karfa ki nemi ki ƙara ɗaga min hankali ki barni da iya wanda nake ciki, bari in gaya miki abun da baki sani ba, a yanzu duk wani aikin mu da ƙulle ƙulle mu baza suyi aiki ba domin tun farkon aikin da aka ƙulla sa boka ya sanar damu cewa, indai har yayi aiki tabbas matar zata bar gidan zatayi nesa damu, sannan bazata ƙara dawowa hayyacin taba har abada, indai munyi yanda ake so, muka yarda akaiyi komai to amma inda matsalar take shine yace duk yanda zamuyi muyi kar musake mubar ƴaƴan ta araye adoron duniya idan kwa ba haka ba, ko ba daɗe ko bajima zata dawo cikin hayyacin ta da zarar jinin ta ya taka ƙafar sa acikin gidan nan to duk wani asiri sai ya warware kuma bazai ƙara ƙulluwa ba, kuma itama zata dawo cikin hayyacin ta sannan zata dawo cikin gidan, kuma gashi kinga komai ya faru yanda yace ɗin aranar da yarinyar nan ta shigo gidan nan tun aranar komai ya kunce,

Yanzu ba aikin boka bane zaiyi aiki saidai mu shirya mu sake ɗaure damtse gurin ganin cikar burin mu ya cika, yanzu hankalin kowa a tashe yake tun ranar da yarinyar nan ta shigo gidan komai ya fara canzawa, ƙungiya har sawa tayi a fita da yarinyar akashe ta amma sai gashi ta dawo, muddun muna son cikar burin mu saidai muyi dabarar da zamuyi mu kawar da su yaron da yarinyar domin sune kan gaba idan babu su burin mu zai iya cika idan kwa suna raye bazamu taɓa cika burin mu ba kuma asirin mu zai iya tonuwa, idan kwa nawa ya tonu wlh sai na tonawa kowa asiri dan bazanyi asara ba nikaɗai, dole kowa ya fito,

Ɗan murmushin taƙaici ta saki sannan tace kashe su ai ba abune mai wahala ba a yau ɗin nan ni da kaina zan saka akashe su kadai kwantar da hankalin ka indai wannan ce kawai matsalar da zata hana cikar burin mu, to matsala tazo ƙarshe yau zanyi naganin wannan matsalar, kafin nan kafin dare zan gama shirya duk yanda za ayi agaba bayansu gobe da safe za atashi da jana'izar su su duka biyun babu wanda zai ƙara kwana da rai acikin su, mu da masarautar duka tamu ce har akwai wanda ya isa yazo ya ɗaga mana hankali, kowa dake cikin gidan nan a ƙarƙashin ikon mu yake duk yanda muka ce haka za ayi, kowa namu ne, da kuɗin mu muka siye su dan haka dole zasuyi mana abun da muke so,

DOLE SU MUTU A YAU ƊIN NAN!!!!
ta faɗi haka cikin ɗaga murya har Saida ɗakin ya ɗau sauti mai ƙarfi tana buga fuskar gadon ta tana wani irin huci kamar ita zata tafi kisan tayi da hannun ta.........✍️✍️✍️
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

                 *_Typing........✍️✍️_*
                

______Da sauri yasa hannu yayi saurin toshe mata baki cike da mamakin maganganun ta yace "kiyi shiru kidaina wannan maganar uwa uwace ko me tai miki baikamata kiringayin irin waɗannan maganganun a kanta ba, tunda ta kawoki duniya to tagama yi miki komai rashin kulawar ta agare ki bazaki taɓa biyanta ba har yanzu amatsayin uwa take agurin ki dan haka kidaina wannan furucin akan mahaifiyar ki hakan ba daidai bane,

Girgiza masa kai tayi tace "ko me zaka faɗa nasan da hakan amma ita bata cika uwa ba da har za akirata, dashi tun ina cikin cikinta ta tsane ni har da nazo duniya aranar da nazo duniya loƙacin da nake buƙatat ta fiye da komai haka fiye da kowa kamata yayi tayi farin cikin zuwana amma sai baƙin ciki........,

                       *Labariiij........*
Ayanda mahaifina yaban labari sunyi auren soyayya da ita, tunda sukayi kuma bata taɓa haihuwa ba saida ga baya yagane ashe inta samu cikin zubarwa takeyi tayi haka ba sauɗaya ba babu adadi, Sai daga baya yagane hakan ta hanyar jin hirar su ita da ƙawar ta akan yanda zasu zubar da cikin loƙacin tana ɗauke da cikina,

suna tattaunawa akan yanda zasu zubar dashi amma tasha maganin yaƙe zubewa shine take gaya mata su ƙara zuwa wajen wani likitan azubar dashi,

Bayan mahaifina yaji hakan sai ya shiga yakamasu shine ya dakatar yace idan tasake ta zubar masa da ciki sai yayi shari'a da ita aloƙacin hardukan su yayi susu duka biyun, sannan ya fara yimata ƙulle ya hana kowa shiga gidan sa itama ya hanata fita ko ina, daga baya sai taƙara bujure masa ita ala dole sai ya sake ta yace shi bazai saketa ba tabari idan ta haifa masa abun cikin ta sai ta tafi duk inda zata yayi alƙawari zai saketa, amma duk da haka sai tace bata yarda atake aloƙacin zata tafi,

Duk yanda dai yaso ta zauna taƙi zama magana tun sunayi sukaɗai hartakai kunnen mahaifiyar sa, mahaifiyar sa najin haka daman itama ba mutuncine da itaba sai tace atake aloƙacin ya saketa ko ta tsine masa,

Yace to shifa saidai yakaita ƙara idan ta zubar masa da ciki bazai yarda, ba da jin hakan mahaifiyata tace indai zai saketa ta yarda zata rainin cikin har loƙacin haihuwar sa  tana haihuwa kuma zata kawo masa ƴarsa, yace "ya yarda, da haka suka rabu rabuwa ta rashin daɗi,

Saidaga baya bayan barinta gidan mahaifina yagane ashe akwai wani alhaji da yake hure mata kunne shine ma yake sata tana zubar da cikin suna da auren ta amma suna rayuwar aure da wani, kuma da tabar gidan ma gurin sa ta koma alhalin iyayen ta suna raye amma babu wanda yake mata magana saboda ta gama ƙulle musu baki awajen malamai, babu wanda yake mata maganar abun da take aikatawa,

Loƙacin da watan haihuwana yayi (bari ta ari bakin ta naci mata albasa dan nasan inbanfaɗa muku ba, ba iya faɗa zatayi ba, amma ni nasan komai kunaji Koh, loƙacin da watan haihuwar ta yayi haihuwa yau ko gobe amma duk da haka bata daina tarayya da wannan Alhajin ba, ataƙaice dai ranar haihuwar suna cikin aikata alfasha faya ta fashe mata alamun haihuwa na kusa, saboda bata da laulayi kwata kwara haka tayi rainon cikin yazo mata da sauƙi bai wani wahalar da ita ba,

Sai loƙacin da sauri Alhajin ya tashi daga kanta cikin tashin hankali saboda baya so ta haifar masa aɗakin, maimakon ya taimake ta sai ya rufeta da faɗa wai tasan ta kusa haihuwa amma bata gaya masa ba tazo wajen sa shiyasa fa daman tun farko yake sawa ta zubar da cikin saboda kartakawo masa cikas cikin lamuran sa,

Ba tausayi ko ɗigo a tattare dashi yasa ta tashi ta dole yace ta fice masa daga gida, ta fara roƙon sa tace yayi mata rai yakaita asibiti tana haihuwa shikenan fa yayi haƙuri kar yayi fushi da ita kuma kar ya koreta a irin wannan yanayin,

Amma fur Alhajin yaƙi yarda yace wlh sai ta fita ko kuma yayi maganin ta agun kuma idan yakasheta ba ruwan sa babu wanda ya isa yayi masa komai,

Duk da haka bata tashi ba saboda murɗawar da cikin ta yake mata na ciwo yasa ta kasa tashi, janta yafara yi daga kan gadon ganin hakan ya sata ta tashi a daddafe ta mayar da kayan jikin ta tashiga takawa ahankali taje gabansa ta durƙusa tace "dan Allah kayi haƙuri kar kace zakayi fushi agareni nima bansan zata zo yanzu ba, amma na yarda zan fita yanzu idan naje na haifeta zandawo wajen ka nayi maka alƙawari, bazan taɓa barin kaba, kasan bazan taɓa iya rayuwa babu kaiba, kayi haƙuri kamin rai,

Matsawa yayi daga kusa da ita yace "ta tashi ta tafi kuma karta ƙara dawowa inda yake daga yau sun rabu rabuwa ta har abada kuma kafin ya irga uku ta fice masa daga cikin gida idan kuma ba haka duk abun da yayi mata ita tajawa kanta,nan yafara irgawa yana kai na biyu ta tashi tana kuka kamar wanda yayi mata dukan tsiya ahaka ta fita daga cikin gidan tana kuka tana ƙara jin tsanar abun dake cikin ta, sai yanzu take da nasanin yarda da tayi zata haife masa ɗan sa da batayi hakaba ta zubar da cikin tun wuri da tuni haka bata faruba yanzu gashi sanadin sa Alhajin ta ya tsane ta ya koreta,

A haka ta fito daga cikin gidan ranta a ɓace tare da saƙa abubuwa da yawa aranta, aƙafa tafito ta fara tafiya dan ko kuɗin mota batada shi,

Tana cikin tafiya ƙafar ta taƙara riƙe mata takasa tafiya tare da jin wata azababbiyar azaba aƙasa marar ta, durƙushewa tayi agun tafara juye juye......,
   
A take agun naƙuda tazo mata, gashi babu kowa agun, kuka tafara yi tana ihu da nishi, sai daga baya wasu mata da suka zo wucewa, sukaga halin da take ciki da sauri suka ƙarasa gurin ta, suna tausaya mata sunso sukaita asibiti amma ina haihuwar ta riga da tazo, dan haka sai biyu suka kakkareta ɗaya kuma taje tafara taimaka mata, ba daɗewa saiga kukan jariri ya fara fitowa, ita kuma ta sauke wahalalliyar ajiyar zuciya,  ta baje agun sukuma suka ɗauki ƴar dan su goge mata jikin amma ahaka halin da take ciki Saida ta buɗi baki tace ku barta a haka kar wanda ya taɓa nagode kuma zaku iya tafiya,

Ba ƙaramin mamaki sukayi ba da jin batunta ita bata tausayin kanta ma zatace sutafi subarta acikin wannan halin sai suka ce "amma ki dubi halin da kike ciki baikama ta abarki a hakaba, kibari muje asibiti a dubaki aduba ƴar a tabbatar da lafiyar ku,

Hannu ta ɗaga musu tace "nace muku banaso ko kutafi kubarni ina ruwanku, tunanin suka fara yi anya ba mahaukaciya bace wacce macen ce mai hankali da zata haihu gata cikin jini ga jaririyar ma amma tace wai atafi abarta a tsakiyar hanya,

Duk yanda suka so su taimaketa amma tace musu bata so, sukuma sunƙi barin wajen saboda a tunanin su dai tana da taɓin hankali,

Ɗaya daga cikin su ce da taga abun nata kamar da rainin hankali sai tace dasu "dan Allah ku taho mutafi wannan matar tana cikin hankalin ta tunda ita ta zaɓi hakan ba sai muyi tafiyar mu ba nifa bansan rainin hankali, taƙarasa maganar tana jan tsaki tayi gaba, ɗayar ma ta bita ɗayar kuma tai ta kiransu su dawo amma suka ƙi dawowa, itama daga karshe sai ta ajiye mata ƴar agefen ta tabi bayan su badan son ranta ba,

Bayan tafiyar mutanen ba jimawa saiga wata mota tazo gabanta akayi parking sannan, matar dake ciki ta fito tana fitowa tayi kanta tace "an aiko ta  tazo ta taimaka mata, amma ita kaɗai,

Kamata tayi ta taimake ta shigar da ita motar zuwa loƙacin tafara jin jiki, jaririyar kuma tana kwance aƙasa cikin jini ahaka suka ja motar suka barta agun ita kaɗai,

Saida sukaje asibiti sannan ta nemi waya agun matar tasaka number mahaifin sumayya ɗin ta kirasa tana kiransa yana ɗagawa ba sallama ba gaisuwa tace "burinka ya cika na haifa maka ƴarka tana hanyar gidan kaji aƙasa anan na haihu kuma nabarmaka ita agun idan kanason ta da ranta sai ka gaggauta zuwa kaceceta, ni nagama nawa, tunda na kawo maka ita duniya, tana gama faɗar haka zai fara magana kenan tayi saurin kashe wayar tare da miƙawa matar wayar,  Daga nan doctor ya shigo ya fara dubata.......,

  kiran wayar ta ƙarayi aamma sai akaƙi aɗaga wayar haka yayi ta kira cikin ɓacin rai da tashin hankali amma taƙi ɗagawa, dan haka sai kawai ya rabu da ita, loƙacin bamaya unguwar haka ya kira ƙanwarsa yagaya mata abun dake faruwa yace ta gaggauta zuwa kar wani abun yasameta,

Duk wanda taji wannan batun sai yasha mamaki jin yanda tayiwa ƴar da tahaifa da cikin ta wannan wane irin abune anya kuwa matar nan tana da hankali kuwa ko alabari ba ataɓa jin inda uwar da ta aikatawa ƴarta haka ba, mahaifiyar sa ma kuwa ranta yayi mugun ɓaci sai taji tsanar matar ta ƙara ninkuwa akan ta da wanda sanadin hakanne tsanar mahaifiyar tata ya shafe ta itama,

Loƙacin da ƙanwar tasa taje wajen mutane sun ɗan taru agun suna kallon yarinyar amma duk sun kasa zuwa su taɓa ta, saidai kallo daga nesa,

Tana zuwa cike da tausaya mata tayi saurin ƙarasawa wajen ta saida ta zubar da hawaye ganin ta kwance agun gashi Allah mai iko ko uhm batayi ba ta yi  shiru tana motsi da ƙafarta ajikin jinin, bata wani damu da jinin jikin ta taba tasa hannu ta ɗauke ta ta rungumeta, tana kuka haka tabar gurin ta tafi gida da ita,

Amma tana shiga mahaifiyar su tace wlh jaririyar baza ta zauna mata agida ba saidai a ɗauketa amayar da ita can gidan baban ta shi ya kula da ita idan yaga zai iya amma bazata buɗi ido taringa ganin jaririyar nan ba acikin gidan ta,

Haka ƙanwar tasa ta fito da gidan takirashi tagaya masa abun dake faruwa yace gashinan zuwa,

Ba jimawa yaƙaraso gidan shima Saida ya zubarwa da yarinyar nan hawaye saboda yasaka ƙanwar tasa agaba yace su tafi gidansa ta kula da ita, sai mahaifiyar tasu tace fur babu inda ƙanwar tasa zata ta dawo gida shi yaɗauke ta yatafi da ita kuma koda wasa indai zaizo gidan kar yasake ya taho da jaririya,

Haka yana kuka yafice da ita daga gidan ya tafi gidan sa shi kaɗai ya shiga gidan da yarinyar anannaɗe acikin zanin da ƙanwar tasa ta nannaɗe ta, dashi,

Zama yayi akan kujera tare da ajiye yarinya agaban sa yana kallon ta sai kawai ya fashe da kuka, tunda yake bai taɓa tsintar kansa cikin irin wannan masifar ba shi ko akan wani baitaɓa jinta sai gashi yau ta faru akansa uwar da haifeshi takasa barin ƴar cikin sa ta zauna agidan ta wannan wace irin tsana ce haka, ko da yake baiga laifin taba tunda wacce ta haifi yarinyar ma ta ɗaga ƙafar ta tabar awajen acikin wani hali to wayema bazai guje taba duk ma abun da za ayi mata ai saidai yabiyo bayan nata,

Ya daɗe agun yana ta saƙe saƙe har saida ƴar tafara kuka sannan ya ɗauke ta sai kuma yarasa yanda zaiyi da ita, ƙanwar tasa yakira awaya yace mai zai bata da zatayi shiru sai kuka take, sai tace masa yasamu madara ta haɗa mata sannan ya goge mata jikin ta da ruwan zafi daga nan yayi mata sallama,

Duk abun da yafaɗa saida yayi mata amma bata daina kukan ba kuma batasha madarar ba, sai kuka kawai take, wayar sa ya ɗauko yaƙara kiran number da maman sumayyan ta kirashi yana kira kuwa taci sa'a aka ɗaga, amma ba muryar ta yaji ba cike da damuwa yace dan Allah ahaɗashi da ita, sai matar tace tana bacci amma idan ta tashi za abata,

haka yaƙara haƙuri yakashe wayar cike da mutuwar jiki,

Yana zaune agun saiga kiran matar da sauri ya ɗaga hannun sa har yana karkarwa ya ɗaga tunkan yayi magana yaji tace, minti biyu nabaka kafaɗi duk abun da zaka faɗa zan kashe wayar,

Da sauri yace na yarda, nan yashiga roƙon ta akan nawa zai bata tayi masa rainon ƴar koda nawata biyar ne yarinyar ta ɗan fara wayo sai yaci gaba rainonta dan Allah tayi masa wannan taimakon kartace a'a,

Ga mamakin sa sai ji yayi tace, bantsara haka kuma mungama magana tunfarko bazanyi naka rainon taba kaje kanemi wata tayi maka, sai anjima gargaɗi kar kasake kirana ko da wasa inba hakaba duk abun da nayi maka daga kai har ita kai kaja muku tana kaiwa nan ta kashe wayar ta,

Kamar wanda aka zarewa laka ajikin sa haka ya shiga bin wayar da kallon ƙurillah, baisan loƙacin da wasu hawayen tausayin kansu ba yakamasa yau ina zaisaka ransa yaji daɗi yazaiyi da rayuwar yarinyar nan taya zai bata kulawa, shi tsoron sama kar taje wuya ta kasheta, saboda rashin kulawa,


Zunbur yayi ta miƙe tsaye yana goge hawayen sa da hannu ya tashi yana jijjaga ta, bata daina kukan ba saida tayi mai isarta shima baccin wahala ne ya ɗauketa, kwantar da ita yayi ajikin sa, ahaka ya ɗauketa yaƙara fita da ita daga gidan, sai yatafi gidan ƙanin sa saboda matar sa ta taimaka masa shi ƙanin nasa baya gari, amma da yaje nan ma ba sa'a duk da yasanar da ita komai abun dake faruwa, amma matar tace wallahi bata haifi nataba bazata fara da rainon ƴar wata ba,

Yaji haushi sosai amma ba yanda ya iya dole yaƙara fitowa sai yaje gurin siyar da kayan yara yasiyo mata tare da madarar yara ashe shi normal yabata shiyasa inajin bata shaba,

Duk wani abu da yasan zai buƙata saida yasiya saboda ya yanke shawarar zaicigaba da kula da ƴarsa babu wanda zai ƙara neman taimakon sa, tunda duk nakusa dashima kowa ya gujesa to kuma ina zaije ya samu taimako.........,



   
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login