Showing 57001 words to 60000 words out of 170049 words

Chapter 20 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7228

batare da sanin saba, todai bansan ya akai yagani ba, suka haɗa min wai tarko ne shine bayan na nuna masa videon yasaka min dariya tare da gaya min duk wasu ƙudurin su akan mu shi da matar sa aloƙacin na zuciya na shaƙe matar tasa ba luraba shi kuma sai yayi min allurar mantau na awa ɗaya baya,

Ɗayan videon da nayi musu tun farko shine wanda yawancin ku kungani videon da na turo, bayan sunyi min allurar ban san adadin da nakai ba agun su, sai farkawa kawai nayi naganni a cikin falon su, da mamakin abun da yakaini tun kan inyi wani tunanin saboda har loƙacin ban dawo cikin hayya cina ba,

Ina gurin bansu san na farfaɗo ba, sai shi Wazirin yafara yin waya yana cewa zaije wata unguwa ance masa unguwar da bokaye da yawa zaije ya lalubo wani bokan da zai kuma yi musu aiki,

Da naji haka sai kawai na koma na kwanta saida nagama jin sunan inda zashi, har ya tashi ya fita daga falon nikuma da naga ya fita sai kawai nabi bayan sa saboda loƙacin matar sa ta koma ciki kuma dai maganar gaskiya na manta mai ya kawo ni ɗin sakamakon allurar da sukayi min, saidai kawai naji yace boka nikuma na yanke shawarar binsa inga inda zashi,

Bayan na fito kuma har na nufi hanyar gate zan bishi danni nama manta ana zuwa a mota, har na kusa zuwa kuma shine Papa ya kirani dalilin da yasa banje ba kenan,

Da na dawo kuma na shiga ɗakina ina ɗaukar wayata sai naga wannan videon yafaɗa yana zaro wayar sa daga aljihu videon yayi playing ɗinsa yana nuna wa wasu wasu kuma suna jiyo muryoyin Waziri da matar sa, saida suka gama ji tundaga farko har ƙsrshe sannan ya kashe wayar ta mayar tare da ci gaba da cewa "bayan nagani na tuna komai duk abun da yafaru na tuna, nayi mamakin ta yanda akai yazo wayata amma sai nabar ta wannan,

Tunawa da yafita ɗin yasa nayi saurin kiran abokina nagaya masa unguwar da yake sai akaci sa'a ma ashe unguwar suce inda Wazririn zashi, sai nagaya masa abin dake faruwa nace inaso yasamomin shi yana nan unguwar yazo neman malami a unguwar ance masa da akwai malamai a unguwar yasaka masa ido akan sa idan yazo yasaka wani yataresa,

Rasa inda yake mukayi, sai Washe gari nasamu na ɗauki wayar Papa na ɗau number Wazirin a wayar sa, sannan na kirashi da wayata, yana ɗagawa nace masa naji yaje wata unguwa yana neman malami nasan inda wani malami yake aikin sa kamar yankan wuƙa bama a bashi kuɗi sai aiki yayi kyau baiyi wani tunanin ko waye niba kawai ya amince min nikuma sauna haɗasa da abokina nace yayi shigar bokaye muka samu wani ɗan daji,

Shikuma Wazirin yaje yasame shi suka gama magana sai Waziri ya buƙaci da shi bokan yazo cikin masarautar suna da guri mai kyau sai su haɗu gaba ɗayan su acan yanda zasu fi tattaunawa da kyau,

Da wannan damar muka samu suka haɗu agu ɗata gaba ɗayan su ta yanda basai na sha Wahalar bincike akan kowa ba, daga nan muka ringa shirya abun da zasuyi, ranar da suka taru nikuma ranar nasamu na ɗauke matar waziri sannan nasaki videon ya kashe matar sa ta yanda duk wanda yagani zai yarda, kuma yanda na tsara Alahamdulillah komai ya tafi yanda yakamata har zuwa ranar jiya da muka shirya bayyana muku hakan, yanzu gasu nan zamuji ko idan da wasu sai su fito dasu idan kuma sukaɗai kowa zai faɗi laifin da yayi da kansa sannan a yanke musu hukuncin da ya dace da su, dan barin wata matsalar ce,

Shiru yayi bayan ya gama maganar ya maida duban sa ga Papa yace "papa bissmillah gasu nan, ya miƙa sauran baya nin ga Papa,

Papa zaiyi magana gwaggo tayi caraf ta rigasa, da cewa ai yaron nan babu wani abu da za ace ka faɗi komai kayi ƙoƙari yanzu kawai ta bakin su muke jira muji dalilin da yasa su aikata haka,

Jinjina kai Papa yayi, yace "hakane mai sunan baba yayi ƙoƙari babu abun da zance yanzu sai muji ta bakin su inji ko nayi musu wani laifinne da yasa na cancanci wannan ɗanyen hukuncin na rabani da iyalina, musamman ku ya kalli Waziri da matar sa Ammah,


shiru sukayi babu wanda ya iya cewa ko uffan,

Meer ne yace matso kusa da mai gadin yace "kai ɗago dakai zamu fara, waye kai? sannan kuma wa kakeyiwa aiki? mai ya kawo ka cikin gidan nan?

kuma kar ka ɓata mana loƙaci muna sauraron ka,

Ɗan ɗagowa yayi kaɗan ya kalle sa, yasake sauke idon sa da baigama buɗewa ba har yanzu, shiru yayi na ƴan loƙuta kafin daga bisani yafara magana,

"Nidai ba kowa bane illa ɗaya daga cikin bayin gidan nan, ni ɗan mai gadin gidan nanne tun shekarun baya bayan mutuwar sa kuma sai nafara aiki tun kafin tsohon sarki ya hau mulki, bayan ya hau ne, wata rana ina zaune a bakin gate sai akace min UWAR BIYU (sunan da suke kiran ta dashi kenan abaya can) na kirana da sauri na tashi naje, har ɗaki aka jani na shiga,

Bayan shiga nagansu su su biyu na tsugguna na gaida su daga nan kuma sai UWAR BIYU take cemin wani aiki zata sakani akai indai har zanyi to bani da matsalar komai bazan ƙara neman abu in rasa ba daga ƙarshe kuma idan kaomai ya tafi daidai za a sallame ni daga masarautar tare da kuɗaɗe masu yawa inje inyi rayuwata a duk ƙasar da nake so, ina jin haka banma ji wane aiki bane kawai nace na yarda zanyi ko wane irin aiki ne, shine tace "aikin da zanyi musu shine duk wanda zai fita daga cikin gidan ko kuma yashiga babu ruwana koda antambaye ni kar nasake nace nasan wani abun, nace na yarda zanyi, daga nan suka sallame ni,

Tun ina ganin abubuwa da yawa har abun naga yayi yawa sai na fara bincike saidaga baya nagano ashe so suke mulkin yadawo hannun su shiyasa suka fitar da gimbiya da iyalanta, da na nuna zan tona asiri shine suka ƙara bani ƙwarin gwiwa sannan nadawo cikin su komai muka fara yi tare,

Itadai UWAR 2 da farko tana da nata ƙudirin akan Papa da bansan dalilin ba, abundai da nasani shine anaso masarautar ta lalace ta ta zama kawai mugunta ake acikin ta bama aso ɗaya daga cikin jinin Sarki Muhammad yayi sarauta, sarauta zata bar asalin gidan za a ɗauko wani daban a ɗora shi, yayi mulkin rashin gaskiya idan akayi hakan shikenan burin ta zai cika, idan mukayi nata haka zata sallami kowa,

Bayan wannan loƙacin da muka rasa ta yanda zamu bi a ɗora wani daba jinin gidan ba, sai kawai mukaje wajen boka muka gaya masa buƙatun mu, shine yabamu tabbacin saidai muje mu samu ɗayar matar da ta yarda ayi cikin ƙarya sai a rufewa kowa baki idan loƙacin haihuwa yayi sai aje asibiti a samo ɗan, idan yaso in ya girma sai yazama sarki,

Da haka muka baro wajen da muka dawo kuma sai tace zamu nemo wacce zataje gurin Fulani tayi mata zancen dan ba aso tagane mune, shine mukabi ta hanyar ƙawarta Hajiya Sarah itama muka biyata shine taje.....daga nan yabasu labarin da su Hajiya Sarah suka bayar kwanaki ta yanda suka samo Salahudeen har yazama sarkin daga nan kuma akasa ka musu mugunta da zalunci a zuciyoyin su ta hanyar asiri da akayi musu sannan kuma akace Fulani ta ringa kai kuɗi cikin ɗakin anan idan takai ta ajiye kuma sai musa jakadiyar ta taje ta kwaso kuɗin takawo mana,

Ana cikin haka kuma komai yana tafiya yanda yakamata, to bamu san ya akai waziri yagano ba, sai yayi mana barazana akan zai tona mata asiri sai loƙacin ta shiga tashin hankali taringa basa haƙuri tana so tasan hanyar da zata kauda shi, sai kawai yace zai rufa mata asiri amma shima yana da nasa ƙudurin akan sarki idan ta yarda kuma zata basa haɗin kai burin sa ya cika shima to zai rufa mata asiri,

Ta tambaye sa maiye nasa ƙudurin shine yace mata, yana so ɗansa yazama sarki, akori su fulani daga cikin gidan a ɗora ɗan sa(baban Sam) akan mulkin sarautar ta dawo hannun su, indai akai haka babu wata matsala da zata faru dan yayiwa ɗan sa alƙawarin zama sarki tunda suka gano Salahudeen ba ɗan masarauta bane, daman da nasu ƙuddurin akai sun rasa ga inda zasu fara ne sai kuma ga dama ta same su, shiyasa sukayi amfani da ita dan ganin cikar nasu burin,

Sai tace "masa hakan ai bazai taɓa yiyuwa ba amma dai akwai wata hanayar bazata ɗora ɗansa akan mulki ba saidai ɗansa shima kuma da sharaɗi zai auri ƴar ƙanwar ta, (ƴar hajjaju) inyaso Sarautar zata dawo hannun su gaba ɗayan su saboda gimbiya Sabreen baza ta sake dawowa ba ta tafi har abada dan haka shikuma jinin Muhammad (papa) bazai taɓa ci gaba da mulki ba,

Shima sai ya yarda da hakan, da tsarin shekarun murabu sa ɗin sarki Salahudeen nayi idan suka sauke sa zasu ɗora Sameer akai(Sam) tare da matar sa ƴar gidan Hajjaju,(ina fatan kun fahimci inda zancen ya dosa, dalilin da yasa ake so ahaɗa Sam da ƴar hajjaju aure, saboda shine Sarkin gaba kuma ta hakan aka ƙara samun haɗin kan sauran duk suka Amince daga baban Sam ɗin har ita hajjajun)

Sai gashi abu yana daf da cika burin kowa zai cika sai kuma muka tashi da karyewar asirin da duk mukayi acikin gidan nan loƙacin hankalin mu yatashi ganin faruwar hakan, saboda boka yabamu tabbacin duk ranar da jinin gimbiya yataka cikin gidan da ƙafar sa to ranar komai zai karye, saidai kuma nisan yanda zamuyi, to shine ranar da abun yafaru muka fara bincike acikin gidan dan gano wanda ya shigo cikin gidan anan mukayi tozali da wata yarinya mai kama da gimbiya sak, nan muka tabbatar da itace jinin ta, dan haka sai muka saka Abdallah ya ringa ganin duk wani takunta har muka ci sa'a suka fita shopping shine nida Abdallah muka bi bayan su har loƙacin da suka ƙarasa inda zasu, sai muka ƙara kiran wasu yaran mu masu yi mana aiki suka ɗauko ta, suka kawo ta cikin masarauta,

Mukuma muka shiga gurin muka gana da manajan gurin muka bashi kuɗi mai yawa ya goge duk wata ɗauka sannan muka hanasa faɗawa kowa idan anzo yin bincike,
Daga nan bamu ƙara ganin yarinyar ba, da muka tambaye ta sai tace taje taga yarinyar kuma tasa a fita da ita daga cikin gidan aje akashe ta, wataƙil ma ankashe tan, tunda ga nan muka ƙara kwantar da hankalin mu sannan muka fara tunanin samo wata mafitar bamu samu ba kuma ashirin Fulani ya tonu Hajiya Sarah ta tona mana asiri dan mu ta tonawa ba Fulani ba tunda ita bata san komai ba kawai muna amfani da itane ta yanda koda wani abun zargi yafaru ita za akama, ba wanda zai zargi Ammah,
nan ƴakarasa musu labarin har zuwa ranar yau da suke zaune agaban su.......,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

     
     'shiru fadar ta ɗauka kowa da mamaki yake kallon Ammah da ta durƙufar dakai,

Babu wanda yasamu damar yin magana saboda al'ajabi yagama kashe su,

Meer da ya nuna ɗayar baiwar yace "saura ke ke kuma nawa akace za abaki, wane aiki kike mata,

batare da ta ɗago ta kalli kowa ba ta jawo mayafin ta ta rufe fuskar ta sannan tace "nima kuɗ......., Meer ne ya dakatar da ita tare da daka mata tsawa yace ta buɗe fuskar ta sannan ta ɗago ta kalli kowa, kowa ya kalle ta,

Cike da jin kunya ta ɗago da kanta, tana ɗan ƙifƙifta ido tana kallon wani wajen daban, sannan taci gaba da cewa, ni matar ƙanin tace kuma wallahi duk abun da nake bada son raina bane tirsasani akeyi tunda mijina na ya mutu suka koreni daga tasu masarautar tare da yarana saboda suna tunanin wai ni na kasheshi hakabnuke zaune cikin wani hali ni da yara na saboda ni marainiyace auren ma da ƙyar suka bari akayi dande yanaso shiyasa suka bari akayi da ƙyar shima kuma tunda mukayi nake fuskantar abubuwa har Allah ya ɗauki ransa amma sai akace nice shiyasa suka koreni,

Ina cikin wannan halin watarana tazo har gidan da nake ta kawo min tayin aiki acikin gidan nan nayi mamaki jin tayin aikin da ta kawo min awata Masarautar da bata su ba kuma itama ba acikin ta take ba, da na tambaye ta dalili sai tace zata gaya min amma ba yanzu ba, yanzu tana so inshiga gidan in fara aiki zata nema min hanya kuma idan nashiga aiki zanyi mata, zata biyani kuɗi masu yawan gaske nikuma ganin babu abun da nake bana sana'a kuma bansamu wani mijin ba ga kuma halin da nake cikin na ƙuncin rayuwa sai kawai na amince mata duk da banji wane irin aiki zanyi mata ba na yarda da haka,

Ko sati ɗaya ba ayi ba na shirya komai ƴaƴa na kuma daman duk maza ne susu biyu sai tace zata sa a kula dasu, ahaka muka rabu dasu ta turo ni gidan tare da wani namiji tace angama komai aiki kawai zan fara duk inda aka bani inkarɓa zamuyi magana daga baya  nace mata to, daga nan nazo nafara aiki a sashen  Fulani nake da zuciya ɗaya nake zaune da ita tsakanina da Allah,

to saidaga baya kuma loƙacin da gimbiya tana da ciki wanda ita kanta gimbiyar batasan tana dashi ba saboda a loƙacin gaskiya banji ana cewa tana da ciki ba amma bansan ya akai ita tasan dashi ba, nayi mamaki sosai amma ban nuna mata hakan ba, sai SA'ADATU ta kira ni awaya ta neme ni tace ince zanje gida mahaifiya ta batada lafiya, haka kuwa mukayi na shirya naje na sameta a gida,

Da naje sai take ce min aikin da zan mata shine zata bani magani inzubawa gimbiya Sabreenan acikin abun shanta shine kawai aikin da take buƙata idan nayi haka zata baki kyauta mai tsoka sai abun da nazaɓa nake so shi zata ban, nace mata shikaɗai aikin da zanyi tace, sai kuma nayi wani tunani sai nace mata ai kuma ba a sashen gimbiyar nake aiki ba a sashen Fulani nake, sai tace min eh kar na damu da wannan zata san yanda zatayi za'a mayar da ita sashen,

nan dai na ƙara jefa mata tambaya ta nace badai na mutuwa bane ko dan bazanyi kisan kai ba, sai tace min eh "bana mutuwa bane na tambaya ta meye tace kawai inje inyi abun da tace min, na amsa mata da to saboda a loƙacin kwata kwata ban kawo wai na zubar da ciki bane saboda banyi karatun boko ba, ni tunani nama bai kawo ciki ba, 

Daga nan mukayi sallama da ita tasa aka dawo dani cikin masarautar,
 

bayan kuma na dawo ko sati ɗaya ba ayi ba na fara aiki a ɓangaren gimbiya Sabreenan kamar yanda mukayi da ita haka akai na zuba mata shi a shayi a washe garin ranar ranar kuma da na zuba mata ranar akace bata da lafiya aka tafi da ita asibiti bandai san mai yafaru da ita ba saboda zuwa dare suka dawo kuma lafiyar ta ƙalau shiyasa banyi tunanin ko maganin da nasaka mata bane,

Ana haka bayan wasu watannin sai SA'ADATU ta ƙara kirana taban naƙara saka mata, saboda wanccan ƙyautar kuɗaɗen da tayi min har yaro na ta ɗauki nayin karatun sa sai haka yamin daɗi dan haka tana ƙara nema hakan a karo  na biyu nayi saurin amincewa nan ma naje na zuba mata,

Saida mukayi haka wajen sau uku da ita sannan naɗan fara fahimtar wani abun da taban maganin sai naje na tambayi wani likita sai yake gaya min na zubar da ciki ne kuma indai aka saba shan sha koda yaushe zai zamana ko ansamu cikin ma zai iya zubewa da kansa saboda abun zai zamewa mutum jiki,

Tunda naji haka na dawo gida ina ta tunanin kuma ni abun dake mugun daure min kai har loƙacin ban taɓa ji ance gimbiya tana da ciki ba to amma kuma mai yasa take bani maganin zubar da ciki inbata, sai nace bari ingwada ta idan taɓani bazan ƙara saka mata ba,

Kamar yanda tasaba kuwa taƙara bani tace insaka mata a abinci wannan karon sai kawai a loƙacin na nuna mata rashin yarda ta sai tace idan ban amince ba ko kuma na tona mata asiri sai nayi da nasanin sanin ta sai tasaka gaba ɗaya dangin na cikin tashin hankali, hakan yasa na tsorata na amince mata badan ina so,ta bani maganin kamar yanda muka saba, ni kuma gaskiya tunda naji na meye nayi alƙawarin bazan ƙara bata ba,

Ko da na koma gida sai naƙi sakawa idan ta tambaye ni kuma sai ince mata nasaka ni kuma sai inje in zubar dashi, duk sanda taban haka nakeyi,

Abun da ya ƙara bani mamaki ana ɗaukan loƙaci bansaka ba, sai naji maganar gimbiya na da ciki hakan yasa na ƙara tabbatar da na zubewar ciki ne take ban ina saka mata bansan sani ba,

Da SA'ADATU taga haka cike da tashin hankali ta kirani nan taƙara bani wani tace wataƙil wancan ya daina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login