Showing 90001 words to 93000 words out of 170049 words
da zaɓi da ta shiga ɗin inyaso duk abun da zai mata sai yayi mata, daidai taje gurin Maama ta ƙaryata abun da ta faɗa,
Tunda ta ziro kafar da farko yake kallon ƙafar idon sa na kanta har ta ƙarasa shigowa ciki,
Tana shigowa idon ta ya faɗa kansa jitayi gaban ta ya tsannan ta faɗuwa amma duk da haka sai ta daure ta cije tare da basarwa taci gaba da takawa zuwa inda yake,
tana zuwa gaban sa ta tsugunna ta ajiye tana ajiyewa kuma ta ɗago batare da tace masa komai ba ta juya zata bar wajen.......,
_afuwan dan Allah kuyi haƙuri nasan wannan page ɗin sai a hankali babu wani armashi ni kaina nasani, to nima hakan nake sai a hankali wallahi da ƙyar nayi, dan har yanzu ban samu sauƙi ba, kawaidai nayi ne_,
*Amma in sha Allah inajin sauƙi zakuga canji dan wallahi so nai na zuwa wani satin mugama gama gaba ɗaya, saidai kuma kana takane Allah na tasa, amma in sha Allah dai baza mu daɗe ba komai yazo ƙarshe ku ƙara haƙuri'*
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
___tana zuwa gaban sa ta tsugunna ta ajiye tana ajiyewa kuma ta ɗago batare da tace masa komai ba ta juya zata bar wajen.......,
"Zonan... Meer yafaɗa yayin da idon sa yake kan try ɗin abincin,
Daman tasan za'arina dole sai ya dakatar da ita, dan haka sai ta tsaya tare da juyowa ta dawo inda yake amma bata ɗago ba kanta aƙasa tana jiran me zaice,
Shi kuma anasa wajen shirun da tayi masane tun farko ya kusan hassala shi gashi kuma yanzu ma tazo ta tsaya masa akai, kai zuciyarsa yayi nesa danji yake kamar ya tashi ya rufe ta da duka saboda ta raina masa hankali tashigo har ɗakin sa babu sallama kuma ta ajiye masa abinci ta juya stiil ya kirata nan ma ba magana, tama maida shi mahaukaci kenan,
Cike da fara hasala yace "ki ɗauke abincin ki kifita idan an koya miki sallama sai ki dawo,
Ga mamakin sa sai yaga bata tanka masa ba ta ƙara tsugunnawa ta ɗauka batare da tace wani abunba, saida ta fita sannan tayi sallamar kamar yanda yake buƙata shikuma bai amsa ba, haka taƙara maimaita wa sannan ya amsa ciki ciki, tashigo ta ajiye masa a inda ta ajiye ɗazu, ta ƙara juyawa zata tafi,
Still sai ya ƙara cewa "na sallame ki ne,
Kai kawai ta girgiza sannan ta koma sai ta tsugunna tafara buɗe abincin zata zuba masa saiji tayi yace nasakaki ko nace miki ina son ci,
Kai ta girgiza masa sannan ta koma gefe ta tsugunna,
Wayar sa ya ɗauka yafara daddanawa amma kuma ƙasan zuciyar sa tunani da mamakin canzawar yarinyar yake, kamar ba itace ba kwanaki tazo ta cikawa da surutu amma yanzu tayi wani sanyi gaba ɗaya ta canza duk abun da yace mata yi take ba wannan taurin kan nata da take nuna masa yanzu batayi, so yake ta kulasa yanda zaiji daɗin cin mutuncin ta amma taƙi kula sa, yana wannan tunanin ya ɗan ɗago ya saci kallon ta, sai yaga tana tsugunne ta zubawa waje ɗaya ido tana ta kallo amma bisa ga dukkan alamu hankalin tama ba agun yake ba idon tane kawai agun, hakan kuma sai yaƙara basa mamaki fiye da wanda yake a farko,
Ɗan gyaran murya ya gwada yi yana kallon ta, ko motsawa batayi ba alamun bataji sa ba, da ƙarfi yace " ke!
ɗan furgit tayi ta dawo daga tunanin da takeyi kuma duk da haka bata yarda ta kalle sa ba,
Haɗe rai yayi yace "watakon na lura dake daga jiya zuwa yau kamar raini ya shiga tsakanina dake ko har inayi miki magana ban isa ki buɗi baki kiyi min magana saboda raini kodan kina duba da auren da aka ɗaura shiyasa kike tunanin bari kiyi min abun da kika ga dama,
Yanzu ma da sauri ta girgiza masa kai hawaye na shirin fara saukowa daga idon ta,
Kawar da kansa yayi yace "kika sake kika min kuka anan sai nasaki me dalili kitashi kishaga ki wanke min toilet sannan kizo ki gyara ɗakin nan daga yau yazama aikin ki tunda kina tunanin ke matar aure ce, to ba daɗi zakiji ba wahala zaki sha uban da yace kibari a ɗaura auren..,
Da sauri ta ɗaugo batasan loƙacin da tace "nima fa baso nake ba kuma bansan anɗaura ba me yasa zakayi min wannan fahimtar nuna baso nake ba kuma ai nagaya maka tun jiya kasake ka huta nima in huta dan wallahi naci gaba da zama ahaka zan iya rasa raina saboda bazan taɓa iya rayuwa da kai ba, kafi ƙarfina kalar ka daban kalata daban halin mu ba iri ɗaya bane daga jiya zuwa yau ni kaɗai nasan halin da na tsinci kaina da zaka taimaka min da ka sauwwaƙe min tun ba aje ko ina ba na roƙeka kasake ni, kuma kama daina wannan tunanin kamar yanda kace wai na rainaka saboda ina tunanin auren dake tsakanin mu, to ko ɗaya bazan taɓa ɗaukan hakan ba, shigowa ta ma gurin ka bawai dan da son raina bane dole ce tasa nashigo na ajiye maka batare da na tanka maka duk maganganun da kake kawai ina yi maka biyayya ne saboda gudun magana banason abun da zaisa kaci mutunci na ko kamin muguntar da kasaba, amma idan ban kulaka ba sai mu zauna hakan to naga kai kuma duk yanda akayi ma ba'aburgeka sai kayiwa mutum masifa da bala'i, shiru tayi tana goge hawayen da yagama wanke mata fuska,
Tana giogewa kuma ta miƙe daga gurin cikin sauri ta shige banɗakin nasa, tana shiga ta rufo ƙofar,
Yana zaune agun yana jiyo shashsheƙar kukan ta a bathroom ɗin domin da ta shiga banɗakin guri tasamu kawai ta kama kuka saboda tsabar wani ƙatoton baƙin ciki da yake taso mata daga ƙasan zuciyar ta, da ita kanta mamakin hakan take, kawai dan anɗaura mata aure sai gaba ɗaya rayuwar ta ta nemi canzawa alhalin wanda ka ɗaura mata ɗin ɗan uwanta ne, idan kuma tunanin auren Bossay ai shi Meer ɗin yace zai sauke ta taje ta auri duk wanda take so, kuma ko a yanzu bai hanata kula kowa ba, to amma batasan me yasa take jin irin wannan yanayin ba gaba ɗaya batajin ta daidai, ta wani fannin kuma so take ta haɗu da tsohon nan hakan kawai taji tana buƙatar ganin sa,
A ɓangaren Meer kam maganganun da Yahaya masa ba ƙaramin tsaya masa arai sukayi ba, karon farko da maganar wata mace macen ma yarinya kamar wannan tagaya masa magana yatsaya yana tunanin maganar ta, gashi daman tun ba yauba ya tsani yaji tace masa mugu, hakan yaji tabasa tausayi, da ace akaran kansane da tuni ya saketa kodan yaga ta dena wannan tunanin akan sa gashi tace tana son wani, da ace yana da yanda zaiyi da sakin nata zaiyi, amma ta zauna yayi tunani kwata kwata bazai taɓa sakin taba indai ba su abune suka haɗu suka ce yasake taba shine zai sake ta a yanzu dai saidai kuma idan tayi haƙuri zai saketa ne daga zaran loƙacin da ya ɗibarwa kansa zai zauna da ita loƙaci na cika zai saketan ko da yardar su ko ba yardar su, amma kuma bayaso ya ganta cikin irin wannan yanayin da yaganta yau a kwana ɗaya har ta canza, kuma tabbas zata shiga wani hali kamar yanda ta faɗa idan suka cigaba da zama a haka,
Sosai ya shiga tunani samowa kansa mafita akan wannan sabon al'amarin da yake neman hanasa sukuni, baitaɓa tunani yarasa mafita irin na yau ɗin, yanke shawarar kiran Khalid yayi dan yazo su tattauna akan yaji ta bakinsa, dan yana buƙatar neman shawara dole ya kirasa,
Ya miƙa hannu zai ɗauki wayar kenan ita kuma ta fito daga bathroom ɗin bayan tagama kukan nata ta wanke banɗakin shine ta fito,
Fitowar tace tasa yafasa ɗaukan wayar yana kallon ta, ta fara tattare ɗakin, sai kawai yace "zo kifice min daga ɗaki, anjima ki dawo ki gyara idan na fita,
Ko uffan bata ce ba kuma bata ƙara ɗaukan komai ba ta dakata da tattarar da take duk da daman ba wata tattarar arziƙi bane dan ba wani datti a ɗakin kawai dai ledojin abarsa da yasaba shane sai wata jaka da ya ajiye ta kan kujera,
zata fita yakuma cewa "wazai ɗauke miki wannan tarkacen ko ance miki mayunwaci ne ni,
"hmmmm tace aranta kawai ta dawo ta ɗauka ta fice abun ta bata kuma tanka masan ba,
Binta yayi da ido har tagama ficewa daga ɗakin sannan ya ɗan jinjina kai tare da dafe kansa, shi kansa yasan bazai taɓa canzawa ba kafin fa ta fito yabarwa ransa bazai kuma tanka mata ba har ta fice amma sai gashi daga fitowar ta ya koreta,
wayar ya ɗauka ya kira Khalid yana ɗagawa yace "ko me kake kabari kazo yanzu ina son muyi wata magana Please,yana jiyo sa zai fara tsokanar sa kawai ta kashe wayar daman yasan halin sa inbaiyi ba ai ba shi bane,
yana ajiye wayar yaƙara luluƙawa wani dogon tunanin game da sabon lamarin da yake shirin tunkaro sa......,
************************
____Su Hamza sun ƙaraso gidan su Bossay inda suka samu tarba me kyau daga ɓangaren su Ammi, a babban falo suka sauka inda aka baje musu kayayyaki masu yawa itadai Ammi taji daɗin zuwansu musamman ma Ayuba da akace shi ɗan uwansu ne,
Bayan sun gama ciye ciyen su a kwashe kwanukan akan kira duka sauran yaran gaba ɗayan su suka hallara acikin falon inda Dadyn su Bossay ya ƙara gabatar da su Ayuba da Hamza agaban sauran yaran sannan aka ɗan basu taƙaitaccen bayani game da abun da yafaru, sannan Ayuba ya ɗora musu da nasa bayanin da kuma buƙatar da yazo musu da ita akan zasu koma can gaba ɗayan su domin su gabatar da kansu acan kowa yasan su yasan dasu,
Gaba ɗayan su sunyi matuƙar farin ciki dajin asalin su,
Dadyn su Bossay yace ta amince zasuje ɗin amma za abari a ɗan ɗaga masa ƙafa saboda shirye shiryen bikin Bossay da ya riga ya gabato saura kwana shida baikama ta ace sun tafi ba gwara idan akayi ko sati ɗaya ne sai su tarkata har ita amaryar tashi su tafi amma yanzu idan sukaje hankalin su ma duk ba'a guri ɗaya ba kuma bazasu daɗe ba zasu ƙara dawowa saboda auren,
Sai Ayuba yake cemasa yayi haƙuri dai ko susu biyune su fara zuwa ko inyaso sai adawo ayi bikin ko kuma su ɗaga bikin idan komai ya daidai ta sai ayi bikin ma acan,
Nan shima Dady yace gaskiya aure ta matso bazaiyiyu ace an ɗaga saba, yanzu dai abun da za'ayi shine kawai su kwana anan inyaso gobe da sassafe sai su shirya dashi Ayuban da Hamza su fara yin gaba inyaso shi ya biyo su daga baya,
Duk dai yanda Ayuba yaso yaja ra'ayin Dady ya amince amma yaƙi yarda dole suka tsaya akan goben zasu tafi su kaɗau ɗin,
Nandai zama ya tashi inda Bossay yaja Hamza ya sauka aɗakin sa shikuma Ayuba tunda ba sa'ansu bane dady ya ajiye sa aɗakin sa na ɓangaren baƙi, da suka shiga kuma nan suka ƙara zama Ayuba yana ta basa labarin abubuwan da yasani nagame da masarautar da labarin mahaifin su......,
Su Hamza kuma suna ɗaki suma Hamza yana tambayar Bossay wai dama aure za ayi masa, nan Bossay shima yake basa labarin baya son auren yabasa labarin yarinyar gaba ɗaya tun farkon haɗuwar su har zuwa yanzu yabasa har labarin yanda yarinyar ta kirasa tagaya masa bata sonsa amma shi baisan meyasa Dadyn sa yana ce sai anyi auren ba, duk da yaji komai, yagama basa labarin cike da ɗinbun damuwa afuskar sa,
Hamza yayi mamaki sosai sai yacewa Bossay ya kwantar da hankalin sa zaisa afasa auren indai bayaso amma da sharaɗi sai yafara samun wacce za'aɗauara masa auren da ita saboda inya fahimci Dadyn sa bayaso yaji kunya ne idan aka fasa auren amma idan ya kawo wata za'a iya fasawa da wacce sai ayi da wacce yake so ɗin,
Bossay yace masa "ai dady bazai taɓa yarda ba saboda yagaya masa tunfarko akwai wacce yake so yace masa saidai yabari idan akayi wannan sai yaƙara wani daga baya amma wannan ba fashi sai anyisa tunda shi yace yanaso tunfarko dan haka bai isa yace yafasa auren taba,
"Tofa Hamza yace yana kallon Bossay sundaɗe suna tattaunawa akan yanda zasu shawo kan al'amurin Dady ya yarda afasa auren, daga ƙarshe dai Hamza yace yabar masa komai ahannun fasa aure kamar anyi angama ne indai yana nan sai anfasa auren nan,
Sosai Bossay yashiga jin daɗi da murna harda rungume shi yana cewa nagode ƙaramin babana,
hararar sa Hamza yayi ya ture sa, yana cewa wallahi saima in fasa,
Dariya Bossay yayi, yana cewa yi haƙuri baba Hamza,
Nan sukai ta hirar su tare amma duk hirar nan maganar auren Ameesha bata zowa Bossay ba har yanzu, sallace kawai take tashin su daga hira, haka suka wuni har dare, bayan sunyi dinner a falo kowa da kowa aka ƙara dasa wata hira har wajen ƙarfe goma, sannan kowa ya tashi ya tafi makwancin sa,
*Washe gari*
Tun wajen ƙarfe goma suka gama shirya inda Hamza ya nemi izinin Dady akan zasu tafi da Bossay, da farko yaƙi amincewa amma sai Hamza yace gobe zai dawo ko jibi, saboda shi zai wakilci shi idan sukaje, da wanann dabarar suka shawo kansa ya amince,
Bakin Bossay har kunne Dady ya amince a tafi dashi, dan haka tare suka rangaya gaba ɗayan su wajen ƙarfe goma da rabi motar su ta ɗaga zuwa Gombe,
Basu suka sauka ba sai wajen ƙarfe shida na yamma suka sauka,
Suna shiga garin Gombe sakamakon magariba da ta kawo kai sai kawai Ayuba ya kaisu wani gidan bai kaisu cikin masarautar ba saboda wani dalili yace su bari sai zuwa gobe da safe sai su shiga,
yana kai su gidan suka fito suka tafi masallaci saboda kiran sallar da akayi Saida sukaje sukayi sallah sannan suka koma gidan, gidan shiru babu kowa sukaɗai ne aciki gida ne madaidai ci ciki da falo, sai falo a tsakiya,
Duk a falo suka baje kowa yana sauke gajiya, zaune agun har aka kira salar isha'i suka ƙara fita zuwa masallaci,
Bayan an idar suka fito suna cikin tafiya, sai sukaji horn a bayan su da sauri duk suka matsa saboda daman sun ɗan shiga hanya,
Ta gaban su motar ta gifta ta wuce daidai loƙacin kuma idon Bossay ya sauka akan Dadyn Rasheeda sai wata mata agefen sa da niƙab ta rufe fuskarta,
Cike da mamakin ganin sa, yace "Dady kuma me yake a garin nan,
Gaba ɗayan su suka shiga kallon su, suma suna mamaki dan duk azaton su ko Dadyn sa yake nufi,
Hamza ne ya fara tambayar sa da cewa wai wace magana kake mutumin da muka barsa agida taya ya akai kuma yazo nan,
Idon Bossay na kan motar yace ba Dady na ba, Dadyn yarinyar da ake son a naniƙamin,
Akusan tare suka saki ɗan ƙaramin tsaki, sannan Hamza yace "kuma shine duk ka tsorata ka ɗaga mana hankali,
Bossay yace "Ai nayi mamakin ganin sa ne wallahi,
"To meye abun mamaki daman duk inda zasa sai yagaya maka ne ko kuwa me kake nufi da mamakin ganin sa,
shiru Bossay yayi yana tunanin me yasa yake mamakin ganin sa,
Hakan nan yaji bai yarda dashi ba saboda matar da yagani da niƙab shidai iya sanin sa yasan mahaifiyar Rasheeda bata sakawa asanin da yayi mata ko hijabi ma basawa take ba bare kuma ta ƙara da niƙab hasali ma kuma matar ciki bata kaita jiki ba.......
Ayuba ne ta ƙara taɓo sa, amma sai kawai yace muje kawai,
Nan suka ci gaba da tafiya har suka ƙarasa suna shiga Bossay yayi saurin ɗaukar wayar sa a inda ya ajiye ta,
Da har zai kira Rasheeda sai kuma ya tuna yayi alƙawarin bazai ƙara kiranta ba har abada,
Juya akalar kiran yayi ga number Dady amma kuma sai tai tayin ringing bai ɗauka na haka yai ta kira har wajen sau uku ba'a ɗauka ba sai kawai ya haƙira amma gaba ɗaya tunanin sa yana kansa,
Ayuba ne yace "bari insa akawo muku abinci me kuke son ci?
Hamza yace koma meye zaici, shi kuma Bossay yace ya ƙoshi babu abun da zaici,
"A'a fa dole kwa kaci wani abun dan kanajin yunwa ga gajiya, baridai inda ayo mana order sai kazaɓi zaɓi wani abun, yana gama maganar ya zaro wayar tare da lalubo wata number ya danna mata kira.....
Bugu biyu tayi aka ɗaga ana ɗagawa yace "yauwa Ɗan ladi abinci nake so kayo mana take away kamar guda huɗu sannan ka haɗo da snakes asaka komai da komai kayi sauri dan Allah ka kawo mana,
Shiru yayi yana sauraron abun da wancen ɗin yake cewa, bayan ƴan sakanni sai yace to shikenan gaskiya baza samu ganin saba saboda nayi baƙi zan shigo gobe ingan sa,
Shirun yaƙara na ƴan sakanni sai kuma yaƙara cewa "ah hakane to yanda za ayi ku taho min dashi nan ɗin kawai sai mukwana tare, daga nanma ma tattauna dashi, kundai tabbatar anyi masa askin kuma ya canza kaya dan bana son inƙara ganin sa kamar yanda na gansa jiya kaji ni,
Shiru yayi yana sauraron sa, sai can yace masha Allah haka nake sonji aikin ku na kyau, sai kun ƙaraso ɗin dan har na matsu ingansa yanda kake faɗaɗin nan kana zuzzuta sa, har na matsu kuyi