Showing 129001 words to 132000 words out of 170049 words
ku suka kama kowa amma ita basu iya kamata ba? Me yasa basu kashe yarinyar ba tsahon loƙaci har suka bari ta girma bayan kuma tace neman ta suke ido rufe sannan duk inda taje suna sane da ita, taya har suka san da ita amma basu san da yarinyar ba,
Taya kike ciyar da gidan ke da ita, kama daga sutura kayan sakawa abinci abin sha, wutar nefa, kuma me yasa duk wanda ya raɓeki zai taimaka muku baki yarda,
Sannan kuma me yasa bayan dawowar ta kano har ta ita kama gida ta zauna basu taɓa zuwa wajen taba, ta akai shi da akai kashi Prison daga baya kuma ya kasance a wani gidan, da ban, me yasa idan sune suka ɗauke shi me ya hanasu kashe shi, tunda sunzo yayi musu signing ɗin takkaddun sun samu abun da suke, ɗan dakatawa yayi yana kallon su, kafin yaci gaba cewa.....
"Hmmm duk bama wannan ba meye dalilin ki na sa ƴarsa tafara aikatau agidan wanann mutumin alhalin kuma kince mahaifin ta yabaku dukiyar sa domin ku kula masa da ƴarsa, kusa ta makaran ta tayi karatu domin ta ceto sa, amma sai duk bakiyi hakan ba, kika ce kin ɓoye masa, sannan kince dukiyar sa tana ajiye kin ɓoye tsawon shekaru nan,to amma shi kuma yace loƙacin da yake can gidan ansha kawo masa ita ya buɗe yaƙi buɗewa saidaga baya aka kawo masa ita har anbuɗe, alhalin kuma yace duk kunsan password ɗin sa, dan haka ke da take hannun ki ke kika buɗe ta kenan?
Sannan bisa ga dukkan alamu sun nuna akwatin nan batayi kama da wacce aka binne acikin rami ba tsawon shekaru, an killace tane a guri me kyau,
A aranar da kika fita kikace kinje ki ɗauko dukiyar sa da kika ajiye ƙarya kike duk shirin kine, ƙarewa ma number da kikayi amfani da ita wajen kira number wayar kice, saboda aloƙacin bamu daɗe dawowa ba ba tayanda za'ayi ace wani daga waje yasamu number ta amma sai ki ɗauki number Maama, tunkan ki fita sannan da kika kira ki kashe wayar gaba ɗaya, dan kar ta shiga,
Tun daga wannan rana nafara saka miki ido, har na gano bakin ku ɗaya da wannan mutumin, ta hanyar mutumin da kika sa ya shiga mota ta, da na tambaye sa yaban number matar da takirasa, ina dubawa kuma sai naga number da aka kirace loƙacin da kika ce kinje ɗauko dukiya, kuma yace mace shiyasa na fara ganowa baki da gaskiya, sannan kika ɗauki hotona kika tura masa, sannan kika sa aka shigo har cikin nan aka shiga mota ta, saboda aranar da na shirya fitar, idon ki yana kan mu, saboda kin tambayi jikar ki ta gaya miki abun da muke shiryawa, aka hanata sai ki saka ido akan ganowa, loƙacin da nafita daga gidan nan keke kaɗace a falo kuma da na fita na ƙara dawowa ke kuma kikasan yanda zakiyi wani yashigo cikin mota ta,
Tambaya ta ƙarshe kince wayar sa wasu ta faɗi a asibiti, to me ya kawo sim ɗin sa cikin akwatin sa, kuma ajiya da muke cikin bincike, na saka layin ana ta zare kuɗaɗe daga ciki, alhalin kuma ATM ɗin sa yana hannun ki....,
Bari intsaya anan, ina buƙatar waɗannan amsoshin kafin in cigaba, idan kin faɗe su nafasa yin sauran, zan barki, namiki alƙawarin bazan ƙara magana ba,
Shiru yayi yana kallon ta, ita kuma tayi ƙasa da kanta,
Abban Ameesha kam inbanda wata uwar zufa da take tsatstsafo masa babu abun da yake jikin shi kam take yaɗau ɓari ya rasa inda zai sa kansa daga tsayen da yake yayi zaman dirshen a ƙasa,
Sauran mutanen kam babu me bakin magana kowa yayi shiru yana sauraron sa,
Shiru da tayine yasa ta fara fusata, cikin daka tsawa yace "answer the question I asked you, DON'T LET ME REPEAT IT AGAIN...!!!!!!
[21/11, 9:22 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
*_🅿️47_*
..........Duk wannan tsawar da yayi mata bata iya ɗagowa ta kalle sa ba, tadai yi ƙasa da kanta kawai, tana muzurai da idanu, dan bata san da kalaman da zatayi amfani da su ba wajen kare kanta akaro na biyu,
"Bazakiyi magana ba! Meer ya kuma nanata mata,
Ɗagowa tayi ta kalle sa, ido cikin ido tace "amsar me kake buƙata, bayan ka faɗi komai to ni banda wani dalili na, nayin hakan kafaɗi duk abun da nayi, kayi daidai, dan haka sai kayi min duk abun da zakayi min, ta faɗa tana sauke masa harara, cike da rashin danasani ko tsoro atattare da ita,
Saida kowa yayi mamakin jin furucin ta,
Basu san da farkawar Ameesha ba, sai ganin ta kawai sukayi a gaban ta,
Tsugunnawa tayi a gaban ta tare da riƙo hannun ta tana me ƙurawa fuskar ta kallo kamar zata cinye ta, ko kuma yauce ranar da ta fara ganin ta,
Cikin daskarewar murya, ta kira sunan ta cikin wani irin yanayi, tace "Dadda...!
Dadda kasa ɗagowa tayi ta kalle ta, saboda yanayin da ta kira sunan ta Saida taji sa har cikin ranta,
"Dadda me yasa? me yasa? me yasa Dadda zaki min haka, dan Allah kice da wasa kike, Dadda jinake kamar zata fashe zafi take, Dadda zafi take min Dadda ciwo taɓa kiji, Dadda kece komai na kece farin ciki na, dake na taso dake nake rayuwa banda wani sama dake a faɗin duniyar nan, please Dadda...Dadda ki gaya min ba gaskiya bane kifaɗi gaskiya ko zuciya ta, zatayi min sanyi, Dadda kisanya shalelan ki ciki farin ciki kamar yanda kika saba, kar ki canzan sabuwar rayuwa, rayuwa ta dake ta saba, bazan iya jurar zama a haka,
Sosai Ameesha take kuka tana riƙe mata hannu, kukan da take kamar ranta zai fita, cikin wani sabon kukan ta kuma cewa "Please Dadda ta karkiyi min haka kinji kaka ta kinga fa kece kika haifa min mahaifiya ke nake kallo kamar uwat..........., Ɗifa tayi ta tsaya da komai babu kukan kuma takasa ƙarasa maganar da take, sakamakon ture tan da Dadda tayi,
Da yatsa ta nunata tace "keda duk atunanin ki zaman da nake dake zaman tsakani da Allah nake, to kin yaudari kanki, kuma ni ba kakar ki bace kar ki sake kirana, da kakar ki, domin kakar ki ta daɗe da tafiya domin nadaɗe da aikata inda uwar ki ta tafi ita da mijin ta,
Saura kaɗan Ameesha ta faɗi jin kalaman ta, saida Meer yayi saurin riƙo ta,
Duk da shima daurewa kawai yayi baije ƙasan ba, domin furucin Dadda ba ƙaramin sakasu a ruɗu yayi ba, duk kan ilahirin mutanen wajen babu wanda be shiga sabon tunani ba, (kamar de yanda nima ta barni cikin tunani....,
Da sauri Abban Ameesha ya taso yana kallon ta kamar zai cinye ta, yace "me kika ce, harara ta watsa masa, sannan tace"abun da kaji na faɗa,
Shiru ya ƙara yi tare da ja baya dan lamarin nata yafara basa tsoro,
Meer kam a fusace yayo kanta zai sauke mata kwandon bala'i, Papa ya dakatar dashi cike da takun sa na manyan ta ya shiga takowa zuwa inda suke,
"Kallon Meer yayi yace "Babana samu guri ka zauna, ka kamata ku koma gefe, kaima nemi guri ka zauna ya faɗa wa Abban Ameesha, sannan ya kalli kowa yace ya isa ayi shiru kowa ya nutsu, yayi maganar da babbar murya,
Kowa guri ya samu ya zauna kamar yanda ya umarce su, sannan ya maida duban sa ga Dadda da tayi wani ƙeƙam kamar ƴar sanda, sai faman huhhura anci take,
Gyara tsayuwar sa yayi yana kallon ta da kyau sannan yace "Baiwar zaki iya zama,
Kwarjinin sa yasa bata iya musu dashi ba, tasamu guri ta zauna,
"Tom bama son ɓata loƙaci muna buƙatar bayani daga gare ki, me kike nufi da maganar da kika faɗa inso kiyi mana gamsashen bayani yanda kowa zai fahimta, ina fatan kin gane ko? dan gwanda kiyi bayani tun kan kijawo kanki,
yana gama faɗar haka ya koma gurin sa shima ya zauna,
Shiru gurin ya ɗauka na tsawon mintina ba tare da kowa ya ƙara magana ba, haka itama batace komai ba, har saida Abuuu ya kuma yi mata magana sannan,
......Ɗagowa tayi tana kallon wani wajen daban, sannan tace "kamar yanda kukaji na faɗa hakanne, niɗin ba wacce kuka sani bace, shiru ta kuma yi sannan tace,
"ME AND HER WE ARE TWINS.......!!!!!
kowa saida ya ɗan zabura da jin abun da tace,
Amma bata dakata ba da duban yanayin da wasu suka shiga ba,
of course Khadijah she is my twins sister, sannan wannan mutumin is my husband, and wannan kuma she is my daughter,
"Muna kama da ita sosai hakanne yasa.kuka kasa ganeni amma in kunlura da kyau zaku gane indai har kunyi mata farin ciki, na fita haske sannan kuma ta fini jiki, kuma yanayin fatar mu ba ɗaya bace, domin ita ajikin tata akwai wahala tattare da ita, Ni kam ƴar hutuce, ban taso cikin wahala ba, ko a yanayina zaku gane hakan Khadija batayi makaran ta ba, nikam da ilimina, idan kunyi tunani azaman da kukayi da ita babu wata wayer boko akan ta, amma bakuyi mamakin yanda nake amfani da waya ba, da kuma loƙacin da kuke ƙoƙari a laptop wajen gano ko waye, nayi muku yawo da hankali ni da kaina nake using system ɗin, a loƙacin da kukeyi ina cikin ɗakin mu wanda anan nake duk wani shirina, bayan na gusar da hankalin yarinyar da muke kwana da ita, tana bacci nake duk wani abu da zanyi, inmayar da komai in ɓoye sa, koma infita daga gidan tare da haɗin bakin tsohon me gadi kafin ku kamasa,
Tofa sabuwar magana hmmm,
"Daga loƙacin da kuka fara rayuwa dani tun loƙacin da kuka dawo gida, tunda naji labarin haka, na ƙara ɗaura ɗamara, aranar da kuka shigo gidan nan ni kuma aranar mukayi exchanging nasa aka ɗauke ta, ni kuma naci gaba da acting as itace, batare da sanin kowa ba,
"Hmmm, duk wannan abun da nake gaya muku ita kanta batasan ina nan ba sai ranar da nasa aka ɗauke ta, sannan na tasan dani kuma nayi mata bayanin ko wacece ni agare ta, itama tayi mamaki kamar yanda wasun ku suke mamaki yanzu,
Bari in baku labari ataƙaice, nasan sai kunfi gane yaren da kyau.....,
Asalin mu, ƴan garin damaturu ne, nasan tagaya muku,
Mu biyu mahaifiyar mu ta haifa bayan haihuwar mu kuma, ta rasa ranta, tun muna ƴan jarire, matar mahaifin mu ta raba kanmu, ta kaini can wani ƙauye, har na taso na girma bansan su waye iyaye na ba, na kasan ce fitinanniya marar jin magana da tsokana, kuma gidan da na taso bantaso naga ana tausyin mutane ba, inbanda rashin imani da mugunta babu abun da ƴan gidan suka iya hakan yasa nima na taso zama da maɗaukin kanwa shike kawai farin kai, hakan yasa babu abun da na bari nadaga halayyar ƴan gidan, na taso bansan ta sauyi ba bare kuma imani, dan ajunan mu yiwa ɗan uwanka mugunta kake ga hassada da nuna baƙin ciki idan wani yafika, so kake akoda yaushe ace kaine gaba da kowa a komai......
Muna ciki wannan rayuwar sai matar mahaifinmu tazo tace tazo karɓar ƴar da takawo sai ana nake jin labarin ni ba ƴar gidan bace, ganin ta fess ba kalar wahala ba hakan yasa ban wani damu ba, na haɗa kayana na bita,
Bayan munje nagane tama fimu a komai itama gwanace wajen iya makirci da mugunta, bamu wani daɗe da ita, ta nuna min hoton wata me kama dani, nayi mamakin ganin ta, sai take gaya min mu ƴan biyu ne loƙacin da mahaifiyar mu ta rasu mahaifina ya ɗauke ni ya kaini ƙauyen saboda baya sona yafi son ƴar uwata, kuma tunda ya kaini bai ƙara bibiya ta, da ta taɓa yi masa maganar da yayi niyar zuwa amma sai ƴar uwata tace kar yaje shi kuma duk abun da ta faɗa shi yake yi,
Aloƙacin naji haushi da na tambayi inda mahaifin mu yake tace ai ya daɗe da mutuwa, nace ƴar uwar tawa fa, tace "tanacen tana auren me kuɗi gashi ankawo mata wani yaro ɗan tsintuwa yayi kuma duk basu da mutunci dan ko su sukaje ba'a barin su su shiga gidan, wataran ma koro su ake, daga nandai taita ɗora ni akan mugayen hanyoyi, daman kuma faɗuwa ce tazo daidai da zama, hali ne ya tadda hali shiyasa duk abun da ta faɗa nake yarda, ta sanya min tsanar ƴar uwata tun kan inganta ma,
Kafin mufara bi takan su saida ta fara haɗani aure da ƙanin ta, itace komai namu duk wani abu da muke buƙata ita take mana a haka har muka samu ƙaruwa muka haifi ƴar mu mace, saida ga baya ma nake jin ashe yana da aure anan kano, hakan kwa bai dameni ba, dan ganin nake duk da haka taimakan akai, saboda yana da ɗan rufin asirin sa kaɗan amma bazaka kirasa da me kuɗi ba, shiyasa hakan bai wani dameni ba duk kuwa da tsatstsan kishin da nake dashi, sai naji nakasa nunawa mantawa nake yana da wani aure,
Bayan wasu watanni kuma muka samu maganar yaron da ke gidan ta ɗan tsintuwa ne ba asan inda iyayen sa suke ba, duk da haka ban taɓa tunanin son ingan taba ko inje gidan ta, kwata kwata ko zancen tama akayi sai abun ya ringa ban haushi,
Abu bai ƙara ƙular damu ba, saida muka kaga yaro ya tasa ga kyau amma ance baya kula ko wacce mace dan munso haɗasa aure da ƴar mukaga abun bazai ba, nan muka ƙara jin haɗin auren sa da ƴarta, da kuma kuɗin da yaron ya fara ajiyewa, ga kasuwanci ga aikin banki, loƙaci ɗaya ya kuɗance har suka canza mukuma abun ba ƙaramin tsaya mana yayi ba,
Nan ta kira mu nida mijina ta ƙara ɗoramu akan muguwar hanya, da ƙara zugamu, wajen mun aiwatar da abun da muke ganin shine daidai, muma zamuyi kuɗi zamu ƙwaci kuɗin ko ta wane hali"
Tundaga wannan loƙacin muka fara bibiyar rayuwar su, inda saida muka gama sanin komai da binciken mu sannan muka fara tura mutane sunayi musu barazanar su bada dukiyar su, sannan kuma duk wanda ya raɓi yaron da suka tsinta bazasu taɓa barin sa ya ci gaba da rayuwa ba, zasu kashe su, daga nan su kuma sukayi mana taurin kai sukaƙi bayar da duk abun da muke buƙata...
Da muka ga suna ta ɓata mana loƙaci shine muka shirya musu, ranar da matar yaron ta samu ciki suka kaita wani asibiti mu kuma loƙacin muka shirya aka ɗauke sa, muna sane kuma muka ƙara sakin sa ya taho asibitin saboda munaso mu ƙwace wayar sa, duk shirine, a ranar da yaje yabasu ATM ɗinsa da gaya masa duk inda abubuwan sa suke, aloƙacin ma akwai recorder agun, duk muna jinsa,
Loƙacin da suka shirya zuwa su kashe wuta, aloƙacin muka turo musu wannan matar ta taimaka musu ta nuna inda matar da aka shigo dasu tare.
Nan ta basu labarin loƙacin da Abunan yafaru, inzaku tuna, Abban Ameesha da yaje wani asibiti garin ɗauko wayar Nadeeya har wayar sa ta faɗi, da ya fito, yaci karo da wata mata, ta taimaka masa sukaje ta kaisu wani gida, har ta karɓe haihuwar Nadeeya daga baya kuma ta gudu ta barsu kuma agidan"....
Ɗora musu tayi da cewa " Bayan ta haihu kuma sai tayi mata, alurar wani ciwo wanda zaisa taji azaba daga ƙarshe kuma ta sume, kowa zaiyi tunanin ta mutu amma mu munsan bata mutuba, loƙacin da suka zo zasuyi mata sallah a loƙacin muka canzata da wata gawar ita kuma muka ɗauke ta, ta hanyar ɗauke musu hankali aka tsorata su agidan hakan yasa suka tashi suka shiga ciki dan neman abun dake ƙara suna shiga mukuma muka shiga muka canza,
Suna fitowa da ita sukayi mata sallah sukaje suka binne ta, daga muka saci kuɗaɗe da yawa hakan yasa akazo aka kamasa daga can banking, har Shari'a akayi basu da hujja dole akace za'a ƙullesa a prison,
Yayin da yake gidan prison, sai muka koma kan Khadija da mijin ta, inda sukayi mana taurin kai, suka ƙi bayar wa muka nemeta muka rasa, shi kuma me gidan nasa aka ɗauko min gidan aka cinna masa wuta,
shine muka duƙufa wajen neman ta har muka gano ta, loƙacin da zata koma kano muka sa aka bita har munso akamo ta aloƙacin amma sai ta gudu garin gudun kuma ta jefar da jakar ta,
acikin jakar na samu wayar ta inda nake amfani da ita a matsayin ta,
duk inda taje sai mun lalubota amma bama so mu kashe ta saboda idan muka kashe ta zamuyi asarar kuɗaɗen da takaddun da suke hannun ta, shiyasa muka ringa binta asannu har muka gano inda take inda ta sauka a wani gida, loƙacin da taje ta ɗauko akwatin muna bibiye da ita har, kafin ta koma gidan muka tura wani ya hau saman gidan, duk abun da take yana kallon ta, shi yake gaya mana inda ta ɓoye ta, awashe garin ranar bayan ta tafi makarantar da take saida abubuwa muka ne muka ƙwaƙwale akwatin muka ɗauko muka mayar mata dashi yanda muka gansa, ita kanta batasan a kwatin bata gurin ba.....
Saida muka ɗauko muka ga da akwai password ajiki,
sai muka fara tunanin ta ina zamu fito dashi daga gidan yarin sannan kuma dole sai yayi mana